Free chapter · Read without an account
BABI NA HUDU
Nana shirun data jine saya, ta gane har yanzu Bata Ida sallan ta ba, na am umma ganan, zoki ji ki sayo mana battery na lanta Kinga ba'a kawo wuta ba to tace, ki daga kasan kwanon can ki dauki kudin, daga wa tayi ta dauki kudin, sai na dawo,
A dawo lafiya Amma kar ki Dade, to insha tace, tana daga labulen dakin, takalmin ta tasa wadda yake bakin kofar, shagon ta je ta sayo battery din tana dawo, maguwan shiru mutane duk sun shiga masallaci sallah, tana cikin tafiya taji an rufe mata baki da da hanci, kiciniyar kwace kanta ta fara yi Amma suuuuu, ta Fadi Bata sake sanin inda take ba. Umma ce har ta gaji da jira, ta tashi ta ninke sallaya ta ajeye ta fito daga dakin takalmin ta ta sa, tayi hanyar wajen shagon taje ta tambayi Mai shagon yace mata ai tun ana shiga sanlan insha, tazo ta sayi battery. INNALILLAHI WAINNA'ILAIHI RAJUN'UN, Tun sallan insha Yan zu fa Tara ta wuce 9:pm, Yaya nura ne ya zo wajen nata da sauri, yaron makofcin mune, yace umma lafiya?
Ina ko lafiya nura, nana ce na aika battery tun 7pm gashi yanzu har Tara ta wuce, subhanallah, umma bari in gayawa abokaina sai mu neme ta, tohh na gode sosai nura, Allah ya maka albarka, ameen thumma ameen, yace yanufi inda abokan nasa suke ya sanar da su a take suka tashi, Dan kowa Yana son halin nana, Bata da raini sam,
Ne man ta suka shiga yi har goma tayi
Suna cikin Neman ta aka kira nura a waya, yace Kun ganta, ok gamunan zu, umma tace nura anganta ehha yace Yana kokarin tare machine, GENERAL HOSPITAL, Yace wa Mai machine
Asibiti Kuma ? Umma ta ta tambayar shi, ehh umma muje da sauri ta shiga dan shikan har ya shiga ya zauna, lafiya zamu je asibiti me ya samu Asma'u tace a rikice, Babu komai, kaman ya Babu komai nura nifa ba yarinya bace kace asibiti Kuma lafiya.
GENERAL HOSPITAL
kwance take akan gadon asibitin Umma suka shigo, Kara sowa umma tayi na KUKA Asma'u me ya same ki, shigo war likita ne yasa tadan sayar da kukan ta, ta nufi shi likita me ya same ta?
Ki yi hakuri ki kwantar da hankalin, wacece ke a wajen ta mahaifiyar tace ni, ok ki biyo ni office Dina, toh tace ta bishi a baya, office din suka shiga zama yayi yayi mata nuni da kujera please have a site zama tayi tace Ina jinka likita, dogon nunfashi yayi yace kaman yadda na gaya Miki yarinyar ki na lafiya, ajiyar zuciya tayi Alhamdulillah tace, yace am ma, Amma me?
Tayi surin tambayar shi, Amma a gaskiya a kwai matsala, domin anyi wa yarinyar ki REPE, likita menene Kuma REPE, yace Ina nufin anyi mata fyade, zaro ido tayi da sauri tace INNALILLAHI WAINNA'ILAIHI RAJUN'UN, fyade ta Kara nanata wa, jiri taji Yana Shirin diban ta a zaune, hakuri likitan yake Bata Amma Ina Bata ma San Yana yi sai nana ta kalman fyade take yi.
bude kofa da akayi wata nurse ce ta shigo, Doctor wan yarinyar da aka yi wa fyaden nan ne ta tashi, okay ganinan zuwa ya fada ya mike wa, umma tace nana ce, ehh yace mata yanufi hanyar fita da sairi ta bi bayan shi.
shigo wa suka yi umma na biye da shi a baya,
KUKA ta fashe da shi ganin umma ta shigo, umma me ya kawo ni nan?
kara sowa umma tayi tace sannu nana kin tashi, kara tambayar umma tayi na kuka, umma ba aika na kika yi ba me kuma ya kawo ni nan, dan har yanzu bata tuna komai bayan aikan Umma data je natana dawowa, rungumota umma tayi nata, kuka ita ma dan tausayin yar ta take yi sosai, kiyi shiru nana,
babu abin da ya sameki, kuka umma take yi sosai, dan tausaya wa marainiyar yar ta,
taya wani mara imani zauyi wa nana haka
amma tasan kowa da nashi kaddaran ne ita kuma NANA ASMA'U haka Allah ya rubuta mata nata.
ALHAMDULILLAH, karshen babi na hudu4 kinan ku biyo ni a babi na biyar 5 dan jin yadda za'a kaya, SHIN WANENE YAYIWA NANA ASMA'U FYADE, SANNAN KUMA WACECE NANA ASMA'U, WANENE FARUQ, SHIN NANA ASMA'U ZATA IYA TUNO WADDA YAYI MAT FYADE, DUK KU BIYO NI A BABI NA BIYAR.
ku biyo mo a cikin babi na biyar dan jin yadda zata kaya.