Free chapter · Read without an account
NEW BEGINNINGS 3
by Saddiqah M · NURI
2 YEARS LATER......
Da kyar cike da tarin dauriyar da duniya ta koya mata hake take tafiya adan durqushe hannunta dafe da cikinta da duk taku dayan da za tayi tana jin ciwon da yake mata yana qaruwa. Kamar ko yaushe tsakar gidan cike yake da matan gidan da ko wacce ke hada-hadar dora girkin dare don magariba ta doso har duhu ya fara yi Azan kawai ake jira yayi kira.
Babu wanda ta kalla kamar yadda itama babu wanda ya kalleta haka ta kama hanyar bandakin nasu dake nan tun kamin ka Isa kana iya jiyo yadda zarninsa ya cika wajen amman wannan idan da sabo duk an saba.
Da yake kanta yana qasa bata dago ba take tafiya hakan yasa bata lura da Nusaiba daya daga cikin matan gidan hanyan nasu ta taho ba ita ma kuma Nusaiba da yake hankalinta yana kan wayarta bata ganta ba. Bugewa suka yi lokaci daya ta durqushe qasa tana jin kamar an qara mata azabar ciwon da cikin nata yake mata.
"Mtswwww aikin banza, baki da ido ne kina ganin mutane ba zaki kauce musu a hanya ba..."
Da sauri Maman Nusaiba ta taso daga bakin murhun dake qofar dakinsu tunda ba kitchen gidan sai dai kowa yake girki qofar dakinsa idan ya gama ya tattara ya mayar dan dakin da shima dai ba wani girma yake dashi ba. Wurinsu ta nufa da sauri tana cewa "ke Nusaiba don Allah ya isa bana son fada kinsan halin wannan jarababbiyar jikar nata sarai.."
Takaici ya qule Nusaiba da dama a fusace ta shigo ta kalleta da har sannan tana kwance aqasan bata dago ba tasa qafa ta shureta tana cewa "wace ita jikar nata da za'a ke jin tsoron....." Ji kake Tasssss and dauke fuskar Nusaiba da wani lafiyayyen mari, gaba daya hankalin mutanen gidan ya dawo kansu duk da dama can yana kansu amman kowa yana tsoron taba wannan matar ne saboda gudun masifar jikarta da sam baya qarewa.
Dafe inda aka mareta Nusaiba tayi ta dago idanunta tana saukewa kan NURI dake huci tana mata wani banzan kallon tak kika sake cewa sai nayi miki wanda yafi wannan..
Bata kalli Maman Nusaiba ba ta durqusa qasa tana cewa "sannu Inna tashi me ya fito dake kema? Bayan nace miki ki jira na dawo gida zan kai ki asibitin..."
Abinda zai baku mamaki was duk cika bakin da Nusaiba take ta kasa koda kwakkwaran motsi haka ma Mamanta wanda tayi shiru kamar ruwa ya shanyeta. Taimakawa Inna Nuri tayi ta miqe tsaye tana sake cewa "mu koma daki Inna..."
Da hannunta ta nuna mata bandaki ba tare da tayi magana ba don kamar turetan da Nusaiba tayi ya mugun fama mata dan ciwon da take fama dashi.
Bandakin Nuri ta nufa da ita tana yatsine fuska har yanzu ta kasa sabawa da warin da bandakin gidan yake. Tasan da itace ba zata iya shigarsa ahaka ba amman Inna babu ruwanta haka ta shiga Nuri ta koma daki ta dauko mata buta cike da ruwa ta kawo ta bata ta tsaya daga dan nesa da bandakin fuskar nan ahade kamar wadda akayiwa bushara da mutuwa sam babu annuri a tare da ita. Tayi folding arms dinta kamar wadda ke shirin yin dambe sai dai sam babu wanda ta kalla acikin matan gidan da kowa ya shiga saitinsa duk tarin gulmar dake cin ransu suna tsoron yin magana ta yanka musu rashin mutuncinta da har yanzu sun kasa sabawa dashi.
Sosai Inna ta dade a bandakin har Nuri ta fara tunanin lafiya sai gata ta bude tana haki da wani kalar kallo tabi Inna dashi da yasa Inna saurin sauke kanta qasa ta bude baki da kyar da wahala tace "kiyi haquri Nuratu.." bata kulata ba sai kamata da tayi suka nufi dakinsu dake can qarshen jerin dakuna goma dake gidan. Suna shiga ta samu waje kan wata yaloluwar tabarmar da gwara babu da ita ta zaunar da Inna tana miqewa tsaye jin anyi kiran salla. Tsayawa tayi har Azan ya idar da kiran sallar sannan ta sake daukar butar data ajiye ta fita taje ta dauro alwala. Ko awajen dauro alwalar tana zuwa suka dare suka bata waje sai data idar ta bar musu wajen sannan kowa ya samu zarrar binta da kallo yana Allah wadan wannan jarabar da aka kawo musu don basu da halin bata mata, duk kuwa ranar da suka sake suka bata mata to kwanansu gidan yazo qarshe korarsu za'a yi and gashi basu da halin kama wani gidan hayan wannan din dai shine daidai qarfinsu da zasu iya affording kudin da buga buga su biya.
Dan kwalin kanta ta cire ta shimfida ta tayar da sallar akai sai bayan data kammala addu'o'inta tsaf sannan ta juyo kan Inna dake kwance rigingine hannunta a usual spot akan cikinta da ko yaushe nan yake. Kamar ta kulata sai kuma ta basar da ita ta miqe tana dauko Qur'aninta ta fara bita hankalinta kwance kai bakace patient ne da baya da lafiya tare da ita ba ko digon damuwa kan fuskarta babu idan ma akwai to tabbas ta mugun koyan shanye abarta.
Tana nan zaune aka kira Isha sai ta ajiye Qur'anin ta jira Azan ya idar da kiran sallar sannan tayi addu'a ta shafa kayarta ta miqe ta tayar da sallar Isha data daura alwalar magariba da niyyarta. Sam wai ba taji tana sallar tayi sauri ta idar ba saboda yadda Inna ta fara sauke numfarfashi mai zafi da tana ji. Ba iya Isha ba hatta shafa'i da wutiri data saba yi sai da tayi sannan ta hada da addu'a ta miqe tana binta da kallo babu digon tausayi ko wani hali sam kan fuskarta.
It was as though life had taught Nuri to suppress every emotion within her. No matter what kind of turmoil she faced, not even a trace of it showed on her face.
Waren Inna ta qarasa ta durqusa tana Kai hannunta kan na Inna da yake nan a yamushe, wahala da tsufa duk sun qarar da ita tayi wani baqi na musamman kamar ka lakata ka shafa sam ba zaka kalleta kace itace Innan shekara biyu da suka wuce ba.
Ba ita kadai ba ita kanta NURIYYA wahala ya canzata, dama ba fara ce ba ta qara wani baqin akan nata na da, rashin abinci mai kyau da halin da suke ciki ya qarar da ita ga tarin jarabar masifar data arowa kanta ta qarfi da yaji da sam baka isa ka takata ta kyaleka ba ko waye kai kuwa.
Life teaches and changes people in different ways. Some people become cold and withdrawn, turning into quiet versions of themselves even when they were once lively and outgoing. Wasu Kuma dake very cold and easygoing rayuwa sai ya mayar dasu masu fada da rashin daukar raini. Kamar dai Nuri da ada take da mugun haquri da komai zaka yi mata zata shanye ta rabu da kai amman yanzu sam ba haka take ba.
Tsugunnawa tayi tana kallon Innan da wannan fuskar nata dake nan sak na Nuri, but a change Nuri that's struggling to live in this terrible world where selfishness is what's bound people.
"Sannu Inna kiyi haquri yau ma ban samu kudin da nace zan kai ki asibitin ba.."
Kai ta gyada mata da kyar tana bude baki cike da tarin wahala tace "karki damu kanki Nuratu ki samu abu kici karki zauna da yunwa." Bakinta kawai take kallo yadda komai na Inna ya sauya ciki har da halinta shine abin mamakin anan, what changed Inna har haka?
"Ke zaki ci abinci dai Inna bara na fita na samo mki awara sai kici kisha tsumin maganinki tunda na asibitin ya qare...." bata iya bata amsa ba saboda halin da take ciki ita kuma jin bata amsa ba yasa tayi tunanin ta yadda za taci awarar ne hakan yasa ta miqe ta dauki hijab dinta ta fita.
Bata kalli kowa cikin wanda suke zaune a tsakar gidan ba duk kuwa data lura da yadda suka shiga taitayinsu daga fitowarta haka tayi ficewarta. Ita sam ba tace suke jin tsoronta ba hakan ya samo asali ne daga mai gidan hayan da yake bala'in son Nuri da duk wanda ya bata mata rai yake korarsa. Hasalima da ace sun fahimci Nuri da kyau zasu ga idan dai har ba gonarta ka shiga ba kanzil ba za tace da kai ba.
Babu nisa wajen da ake siyar da awarar hakan yasa bata dade ba sannan babu layi tana zuwa ta amso na two hundred don shi kadai ne kudin daya rage mata ta dawo ta samu Inna a yanda ta barta.
Ajiye 'yar farar ledar tayi kan tabarmar ta dago Inna tana jinginar da ita da bango. Miqa mata tayi tana cewa "Bismillah Inna kici sai ki sha maganin wannan ciwon naki har da yunwa ma.."
Kai ta girgiza mata tana cewa "kici kawai Nuratu..."
Bata kulata ba sai hannu tasa ta dauko guda daya ta kai bakin Inna "bude bakin Inna.."
Maimakon Inna ta bude bakin sai kawai ta fashe da kuka tana cewa "kiyi haquri Nuratu don Allāh, nasan na cuceki da yawa keda mahaifiyarki..."
Wani kalar hade rai Nuri tayi tana cewa "da zaki yi shiru da wannan maganar kamar zai fi miki alkhairi Inna... " alokacin idan ka kalli cikin idon Nuri babu abinda zaka gani sai tsantsan kiyayyar da take wa Inna.
A person can love and hate someone at the same time. Nuri loves Inna, but the hatred she feels towards her goes far beyond explanation. And Inna knows it.
Ajiye mata abincin agabanta tayi ta miqe ta koma can qarshen dakin ta tsiri gyara 'yan kayanta da basu da yawan kirki tana mayarwa cikin bakkon da suke. Inna tana daga can gefe tana kallonta cike da tarin abubuwa aranta kamar irin tana feeling guilty conscience haka.
Bayan Nuri ta gama ta miqe ta fita tunawa da tayi bata yi waya da Afif yau ba. Of all that had happened in the past two years, she and Afif were still in touch, though not every day. She was always counting down the days da zai kammala karatunsa ya dawo. At least, she wouldn't have to live alone with Inna anymore.
Bata da waya ynzu hakan yasa data fita sai ta tsaya tana bin wanda ke zaune a tsakar gidan da duhu yasa basu gane ta fito ba. Hasken waya data gani ya haske fuskar wata Nabila daya daga cikin yan hayan gidan nasu yasa tayi wajenta Kai tsaye.
Suna cikin hirarsu ita da mamanta da qaninta kawai suka ga Nuri akansu da sauri kowa yayi tsit kamar an daukesu awajen. Nabila kawai ta kalla tana miqa mata hannu ba tare da tayi magana ba alamar ta bata wayar dake hannunta.
Babu musu Nabila ta miqa mata wayar ta amsa tayi dialing number din Afif data haddacesu akanta tayi saving sannan ta koma ta kunna data ta kirashi Whatsapp call. He's online and kamar yana jiran kiranta yana shiga ya dauka.
Her vulnerability only showed when she was talking to Afif, who spoke to her like an older brother would.
"Adda kin dade baki kira ba yau?"
"Inna ce bata da lafiya..." Bai amsa ba kamar yadda Nuri ta tsani Inna haka Afif ya tsaneta sai dai unlike Nuri da take iya jin sonta atimes shi sam ba yaji tsana ta gaske yake mata.
"Kinci abinci Adda?"
Kai ta girgiza masa tana cewa "a'a Biyayye bana jin yunwa.."
"Kije kici abincin sai muyi wayar.."
"Kar ka katse wayar Biyayye.."
Shiru yayi yana jin yadda muryarta yayi kamar za tayi kuka.. Ta fada masa komai that happened da baya nan ciki harda auren Mami da ya mugun tayar masa hankalin da yayi affecting karatunsa a semester din. Yanzu wata uku kawai ya rage mishi ya gama ya dawo, dashi da Nuri sai ka rasa waye yafi qaguwa ya dawo din.
"We'll talk again Adda but please go and eat something first, okay?"
"Kasan ba wayana bane ko biyayye.."
Shiru yayi yana sauke ajiyar zuciya kamin yace "zan saka miki kudi a wannan account din don Allah Adda ki dena zama da yunwa.."
Da sauri ta mugun danne hawayen da taji kamar yana shirin zubo mata ta amsa masa "nagode Afif.." don ba qaramin buqatar kudin take ba saboda Inna da bata da lafiya yanzu. Duk kudin da yake turo mata akan Inna yake qarewa duk yawansa hakan yasa ta nemi aikatau a wani gida tana hadawa amman ba wani pay mai yawa suke mata ba 8 thousand kawai suke bata wanda ko sati bai fiya yi musu ba saboda tsadar rayuwar da ake ciki. Ba dan Allah yasa akwai Afif din ba kuma ta fada masa halin da suke ciko yana turo mata da dan kudaden da shima da buga buga yake samowa kuma daya samu kudi ita yake turowa ya dena ta kansa.
"Don't thank me Adda. It is my responsibility to look after you now that Abba and Mami are no longer here..."
To be continued...
like
comment &
share