Free chapter · Read without an account
MADUGU
INUWAR ƘADDARA 🖤
Book 1
Page 7 ✍️
Meelah Bazata
Da gudu Leenah ta shiga gidansu, tana waige-waige. Numfashinta sama-sama yake, jikinta kuwa har yanzu rawa yake yi. Tana shiga cikin gidan, sai ta ƙara wani irin gudu, tana cewa:
“Wayyo Mama, na shiga uku! Yau shikenan, tawa ta ƙare!”
Ƙoƙari take ta nemi gurin buya, domin gani take har yanzu kamar zai biyo ta. Ƙyallin wuƙar da ya ciro kawai take gani, hankalinta yana sake tashi.
“Leenah?”
“Ke, Leenah! Lafiya? Me ya same ki haka?”
Leenah tana ganin mamanta, ta nufe ta da gudu ta ƙankame ta kamar za ta koma ciki. Yadda take rawa, ga wani zafi a jikinta, alamar zazzaɓi ne, ya sa a zuciyarta ta ce, kila ta haɗu da Sayyid ne, domin Leenah Sayyid kawai take tsoro.
Ƙoƙarin buɗe baki take ta yi magana, amma kalmomin suka ƙi fitowa. Sai kawai ta girgiza kai, tana nuna wa Mama hanyar gidan.
“Da ke nake magana, Leenah! Lafiya kuwa? Ban hana ki shigowa gida haka ba da gudu kamar wata yarinya ƙarama?”
“Mama... Mama...”
“Ya kashe ni, Mama! Wallahi, yau ya kashe ni!”
Mahaifiyarta ta ɗago ta daga jikinta, tana kallonta tana jijjigata.
“Ya kashe ki kuma? Ki natsu, wace irin magana ce haka? Wane ne ya kashe ki?”
“Madugu ne, Mama! Wallahi, Madugu ne!”
Sakin ta matar ta yi, sannan ta yi tsaki. Ta san za a rina. Leenah akwai sanyin hali, amma sai ka zauna da ita za ka fahimci tana da tsiwa, ga tsoron masifa. Ita ba ta san sanda yarinyar za ta daina jin tsoron Madugu ba.
“Ganin na shi ne ya sa kika yi fitsari a wandonki, Leenah? Wai me ya taɓa miki ne da kike masa wannan tsoro? Wa ya ce miki Sayyid yana yin abu haka nan? In ba ki daina wannan tsoron ba, ke za ki sha wahala.”
“Wai ke, a ina ma kika ga Sayyid ɗin?”
“Mama, da muka dawo daga makaranta ne, shi ne muka ga wannan dodon garen nasa, yana bin Kawu Manu da gudu. Ba ki gani ba, shi ne da Rooman ta hana shi cinye Kawu Manu, muka tawo. Yana tsaye a ƙofar gidansu. Ni kuma ina ganinsa, shi ne... shi ne... na ji tsoro. Shi ne yana kallona da waɗancan idanunsa nasa. Sai ya ciro wuƙa, ya ce ko na gaya masa abin da yake ba ni tsoro a jikinsa, ko kuma ya yanke mini maƙogwaro.”
“Ai ya yi daidai, kin ga sai ki gaya masa abin da kike tsoro.”
“Shi ne na ji tsoro, na ce masa idanunsa ne suke ba ni tsoro. Na ce masa irin na aljanu!”
Girgiza kai kawai Mama ta yi, ta yi tsaki, ta ce:
“Kin taɓa ganin aljani ne har kika san idanun aljanu gare shi?”
“Wallahi, ban san na faɗa masa haka ba, Mama! Maganar ce kawai ta fito daga bakina. Da ya sake juya wuƙar, sai na yi ihu, na faɗi ƙasa. Ban san na faɗa ba, ban san abin da ya faru ba sai da na farka na ga Ammah.”
Ta sake fashewa da kuka.
“Wallahi, Mama, ba zan sake zuwa ko ƙofar gidan nan ba. Ko Rooman ta zo, ba zan bi ta ba. Ni dai na daina zuwa makaranta da ita idan har zan riƙa haɗuwa da yayan nata. Wallahi, yau na ga mutuwa da idona!”
“Ai kuwa yanzu ma can zan aike ki. Maza ki je ki yi wanka, ki zo ki ci abinci tukuna, sai ki je ki kai wa maman Rooman wannan maganin. Tun dazu nake son in aika mata, sai dai babu yaron da zai je, shi ya sa...”
Ai Mama ba ta rufe baki ba, Leenah ta sake barkewa da sabon kuka, tana faɗin:
“Mama, don Allah, kada ki ce in je. Wallahi, tsoro nake ji, ba zan iya shiga gidan ba. Ya ce sai ya yanka ni!”
Kishiyar Mama ce ta yi zaraf, wadda take gefe tana wanke-wanke, yaranta suna ɗaki a zaune suna danna waya.
“Ai dama ya yanke ki ɗin ko a rage mugun iri, yarinya sai bakin hali da mugun abu irin na uwarki, wanda kika riga kika tsotsa a nono. Allah dai Ya yi wadaran naka ya lalace!”
Ko ɗago kai Mama ba ta yi ba, sai ma cewa Leenah ta yi ta je ta yi wanka maza ta wuce. Ita kuma ta je tana kwaso kayan shanyar ta. Haka ta gama kwaso kayanta, sannan ta wuce ɗakinta, ko da matar ta ci gaba da habaice-habaicenta, ko kaɗan ba ta nuna ta san da ita take ba, domin inda sabo ta saba.
---
Anan gidan su Madugu kuwa, tun bayan abin da ya faru a gidan, kowa ya shiga harkokinsa, sai dai babu wanda ya samu nutsuwa a zuciyarsa. Duk da suna jin haushin Madugu, amma kuma ba za su iya nuna hakan ba, yayin da wasu suka ɗauki alwashin ba za su sake sa gigin shiga harkarsa ba. Wannan ma Hajiya Iya ce ta ja musu wannan fitinar.
Kawu Manu kuwa yana ɗaki, matarsa tana jinyarsa, ga inda Rocky ya kai masa cizo. Sai da ya sha allurai, amma duk da haka ƙafarsa tana nan ta kumbura, ga tsamin jiki yana fama da shi. Don ma Allah Ya taimake shi, waccan shegiyar ta cece shi, da yanzu ba wannan batu ake yi ba.
Inda sabo ya kamata ace sun saba, domin wannan kaɗan ne daga aikinsa. Zai yi ma fiye da wannan.
Yaron Kawu Manu kuwa, haka ya dinga zage-zage da ƙarya, da kurin banza. Shi ma a cikin ɗaki, gaban iyayensa, amma ko motsin kirki ba zai iya ba in yana gaban Madugu.
A ɓangaren Ammah kuwa, tana zaune a ɗakinta bayan ta idar da sallar azahar. Ta jingina jikinta da bango, idanunta a rufe, tana ta addu'a a bayyane, tana yi wa ɗanta addu'a.
“Ya Allah, Kai ne ka san abin da yake cikin zuciyar yaron nan. Ya Allah, Kai ka fi kowa sanin wanene Sayyid. Ya Allah, Ka sauƙaƙa masa. Ka shiryar da shi, Ka kare shi daga dukkan sharri, Ka kuma dawo mini da Sayyid ɗina yadda na san shi a baya.”
“Kaine Mai shiryawa, Ya Allah, Ka shirya Sayyid.”
Ammah zuciyarta ba ta da daɗi sam. Ba ta san ya za ta yi da Sayyid ba. Duk yadda mutane suke aibata shi, yana dawowa kunnen Ammah, amma kuma ba ta wani magana, domin ta san abin da ake faɗa a kan Sayyid ɗin gaskiya ne. Sai dai kuma ɓangare ɗaya suka sani na Sayyid ɗin, ba su san ɗayan ɓangaren nasa ba.
Da wannan saka da warwara, Ammah ta ɗauki lokaci a zaune a gurin, sai da Rooman, wadda ta fito daga kitchen riƙe da plate na abinci, ta zauna gefen Ammah ɗin, suna ci a hankali suna hira.
---
Koda Sayyid ya bar gurin, dama akwai inda zai nufa.
Ban san me ya sa ba, duk da motocin da yake da su, amma ya fi gane tafiyar ƙafa da wuya ya hau mota, sai dai ya tafi a mashin.
A bakin ƙofa ya tarar da Jagwa, Duna da Baushe. Dama jiran sa suke, sun san inda za su tafi.
“Takawarka lafiya, Madugu.”
"Ahuce haka."
madagu yafada yana daga musu hannu.
“Mutanenmu suna nan suna jiran umarninka, sun zagaye gurin gaba ɗaya, umarni kawai suke jira.”
Sayyid ya zuba masa ido na ɗan lokaci kafin ya ce:
“Ka tura Reza ya je ya kwaso kayan. Wannan yarinyar kuma ku kai ta asibiti, sannan a ce yaran duk su ware a gurin. Kai kuma, ɗauko mota mu je gidan wancan tsohon.”
Aikuwa da sauri Jagwa ya nufi inda ya san motar da za su fita da Sayyid ɗin. Ya san gidan Alhaji Haladu za su je yau. Aiki ya biyo ya kansa kenan.
Koda Sayyid ya shiga motar, Jagwa ya tada ta, Duna da Baushe kuma suna zaune a baya. iya su kadai suke ta maganar su,madugu baice komai ba.
Sayyid yana zaune, ya jingina da kujerar mota, idanunsa a kan hanya. Fuskarsa babu alamar wasa, ga wani irin yanayi da ya sa hatta Jagwa, wanda ya daɗe tare da shi, yake taka-tsantsan da duk wata magana da zai yi.
“Jagwa!”
“Na’am, Madugu.”
“An tabbatar min da cewa Alhaji Haladu yana nan a gida ko?”
“Eh, Madugu. Yana gida.”
Sayyid ya gyara zamansa, ya ɗan karkatar da kansa.ya sake jingina da kujerar, ya zaro wayarsa ya duba ta, sannan ya mayar da ita aljihunsa.
Bayan wasu mintuna, Jagwa ya ce, “Madugu, mun iso.”
Sayyid bai amsa ba. Ya buɗe ƙofar motar, ya sauko a hankali, sannan ya tsaya yana kallon hamshakin gidan da ke gabansa.
Ya gyara hannun rigarsa, ya ɗaga kai ya kalli Jagwa.
“Ku jira ni a nan.”
“An gama, Madugu.”
Ya nufi ƙofar gidan da takunsa mai cike da izza. Bai zo wasa ba.
saida ya gayawa alhaji haladu sharadinsa kafin ya amsa aikinsa,amma yanzu ya lura yana ketare iyakar sa,don haka bari ya kankara masa warning.