Free chapter · Read without an account
BOOK ONE CHAPTER 12
Ya yi murmushi. Yace "ƙwayannin idanuwan ki suka faɗamin lokacin da kike maganar ice cream"
Aliya ta yi shiru.
Sai ta yi murmushi wanda ta kasa boyewa.
“Ustaz…”
“Hmm?”
“Ni kam banyi expecting ka iya irin wannan ba."
"Me kenan?"
"Ka kalli cikin idanuwana ka hango abinda na keso a ƙasan zuciya na."
“Wasu abubuwa mutum yana lura da su ne ba tare da ya sani ba.”
Kalmar ta sauka a zuciyarta da wani irin yanayi mai daɗi fiye da yadda ya yi tsammani.
Hannunta ya kamo cikin nasa batareda yayi magana ba.
Aliya ta bisa tana murmushi mai ƙayatarwa.
A bakin gado ya zaunar da ita. Shima ya zauna a gefen ta.
Ya miƙa hannu zuwa kan bedside drawer ya ɗauko system dinsa yai playing film din da yai downloading.
Cike da nishadi Aliya take kallon duk wani motsi nasa, tana murmushin daya kasa barin fuskar ta.
A tsakiyar gadon ya ajiye system din. Suma suka hau gadon da kyau.
Rayyan ya buɗe ice cream ɗin, ya miƙa mata cokali.
Ba musu ta karɓa tana furta kalmar"Nagode".
Be amsa ba sai kansa daya jinjina mata yana murmushi.
System ɗin ya haskaka ɗakin da haske mai laushi, yayin da fim ɗin Piku ya fara gudana.
Aliya ta gyara zamanta a kan gadon, tana riƙe da roban ice cream ɗin ta.
A nutse suka soma kallon film ɗin. Rashin sabo yasan yashi jin wani iri. Sai yamiƙe ya ɗauko littafin sa yana nazarin sa a hankali.
Aliya ta ɗan leƙa littafin.
“Ustaz…”
“Hmm?”
“Za ka karanta littafin ne ko za ka kalli fim ɗin?”
Ya ɗago kansa.
“Dukansu.”
Ta yi murmushi.
“Ta yaya zakayi abubuwa biyu a lokaci guda.?”
“Karatu ina yi. Fim kuma ina ji.”
“Wato idan na tambaye ka abin da ya faru yanzu?”
“Zan amsa.”
Ta ɗan runtse idanunta.
“Toh.”
Ta koma kallon system.
A farkon fim ɗin, Piku da mahaifinta suka fara bayyana yadda rayuwarsu take—rayuwa mai cike da ƙananan gardama, korafe-korafe da kuma wata irin kusanci da ba a cika ganinsa ba sai ka kula sosai.
Aliya ta fara dariya.
“Kai kai! Wannan mutumin yanada abin takaici yasin...!”
Rayyan ya ɗago kansa daga littafinsa.
“Me ya faru?”
“Ka kalla mana.”
Ya kalli screen ɗin.
Piku tana ƙoƙarin jure halayen mahaifinta, shi kuma yana ta korafi kan abubuwa marasa yawa.
Aliya ta girgiza kai.
“Wallahi irin wadannan iyayen gajiyar da mutane suke yi."
Rayyan ya yi murmushi. Yana tambayar ta.
“Amma har yanzu tana kula da shi?.”
“Eh.”
“Saboda?”
Aliya ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai ta ce,
“Saboda ko mutum yana wahalar da kai, idan ka san cewa jinin ka ne… ba ka iya watsar da shi.”
Rayyan ya kalleta. Badon abinda ta fada yanada wani ma'ana na daban ba, se dan yanda tai maganar da dukkan gaskiyar ta.
Ya mayar da idanunsa kan system. Yana ajiye littattafin sa agefe. Ya soma kallon.
Fim ɗin ya ci gaba.
Lokacin da Piku ta shiga gardama da mahaifinta, Aliya ta sake yin dariya.
“Ni wallahi da na kasance ita, da na gudu.”
Rayyan ya kalleta.
“Da gaske?”
“Eh.”
“Za ki iya barin iyayenki saboda suna damunki?”
Aliya ta yi shiru. Ta ɗan rage murmushin fuskarta.
Tace“Ba haka nake nufi ba.”
“Na sani.”
Ta sake kallon screen ɗin.
“Wasu abubuwa dai suna da sauƙin faɗa idan kana kallonsu a fim.”
Rayyan bai ce komai ba.
A wannan karon shi ma ya mayar da hankalinsa sosai ga fim ɗin.
Labarin ya ci gaba da nuna rayuwar Piku, aikinta, da kuma irin yadda take ƙoƙarin daidaita rayuwarta da kula da mahaifinta.
Daga baya sai Bhaskor ya fara shigowa da maganar matsalar cikinsa da kuma yadda komai yake zama babban batu a wajensa.
Sosai suka maida hankalin su kan film din. Da anyi abu kadan zasu tsaya suna sharhi akai, ko su fashe da dariya.
Seda aka ja lokaci sosai, wani abu mai ban dariya ya faru a fim ɗin.
Aliya ta yi dariya har ta kusan zubar da ice cream ɗin hannun ta.
Rayyan ya kalleta.
“Ki yi a hankali.”
"Tom." Ta amsa.
Sai ta ci gaba da kallon fim ɗin.
Amma ba ta lura da ɗan ice cream ɗin da ya shafi gefen bakinta ba sanda take dariya ba.
Rayyan ya lura. Ya ɗan kalleta. Ya sake kallon system. Sai ya sake kallonta.
“Aliya.”
“Hmm?”
“Ki share bakinki.”
Ta goge gefen bakinta.
“Ya gogu?”
“Har yanzu akwai."
Ta sake gogewa, amma ta wuce wurin.
“Yanzu fa?”
Ta tambaya tana kallon sa cikin idanu.
Rayyan ya yi shiru na ɗan lokaci. Bai amsa ta ba.
Sai ya ɗauki tissue ɗin da ke kusa da shi.
Ya matsa kusa da ita kaɗan.
A hankali ya share ɗan ice cream ɗin da ke gefen bakinta.
Aliya ta yi shiru.
Kamar ta manta da abin da suke kallo na ɗan lokaci.
Rayyan kuma ya janye hannunsa cikin natsuwa. Yana mata magana
“Yanzu ya gogu.”
Ta sauke idanunta.
“Na gode.”
“Ba komai.”
Sai dukansu suka koma kallon fim ɗin.
Amma wannan karon Aliya ta ɗan yi shiru.
Rayyan ma bai ce komai ba.
A hankali labarin Piku ya ci gaba da tafiya—daga barkwanci zuwa wasu lokutan da suke nuna yadda dangantakar uba da diya take da rikitarwa, amma a ƙarƙashinsa akwai kulawa da ƙaunar da ba sa yawan faɗa da baki.
Aliya ta yi shiru tana kallon screen.
Sai ta ce a hankali,
“Ustaz…”
“Hmm?”
“Ka lura cewa wasu mutane suna iya wahalar da kai, amma har yanzu kana son su?”
Ya kalleta.
“Kin tambaye Ni ne ko fim ɗin kika tambaya?”
Ta yi murmushi.
“Dukan Ku.”
Rayyan ya yi murmushi kaɗan. Ba tare da ya bata amsa ba. Itama ba ta sake cewa komai ba, ta cigaba da kallon ta.
Bayan wani lokaci, shiru ya mamaye ɗakin.
Aliya ta jingina kanta a kan pillow. Idanunta suka fara yin nauyi. Ta yi ƙoƙarin buɗe su sosai. Ta ci gaba da kallon fim ɗin.
Amma bayan ƴan mintuna, sai ta soma gyan gyaɗi.
Jin ta shiru ya sanya Ustaz kallon ta yana tambayar ta da“Kin fara bacci ne?"
“Ban fara ba.” Muryarta ta fito can ƙasa irin na masu bacci.
“Hmm.”
“Da gaske nake.”
“Na yarda.”
Jin yanda yai maganar yasan yata yin murmushi mai sanyi. Bacci baya wahalar ɗaukan ta tun asali, hakan yasa Ustaz na ɗauke ƙwayannin idanunsa daga kanta, nata idanuwan suka rufe.
Kamar yaji ajikinsa. Ya ƙara juyowa gareta sai yaga tai bacci, domin tabbatar wa sai ya kira sunanta.
“Aliya?”
Babu amsa.
Ya ɗan matsa kusa yana kara kiran sunanta amma babu amsa.
Ta riga ta yi bacci.
Ya kalli fuskar ta na ɗan lokaci. Sai ya sauke numfashi.
“Tun ɗazu kike cewa ba ki jin bacci…”
Ya faɗa a hankali.
Ya kashe system din sannan ya tashi..Ya zo inda take cikin natsuwa.
Sai kawai ya gyara mata kwanciya, ya ɗora kanta a kan pillow, sannan ya ja bargon ya rufe ta har zuwa kafadarta.
Fuskarta ayanzu ta yi wani irin kamewa. Ba Aliyar da take masa magana ba. Ba wadda take masa dariya ba. Ba wadda take ta gardama da shi kan fim ba.
Sai Aliya kawai.
Wata yarinya da ta shigo rayuwarsa a hankali ta soma sauya shi ta fannin da baiyi zato ba.
Wani murmushi ne ya suɓuce mai, ya tsaya a gefen leɓensa, ba tare da ya shirya ba.
Hannu ya kai da niyyar cire mata hijjabin jikinta sai kuma ya fasa.
Ya miƙe ya kauda system din. Ya shiga bathroom yai brush. Ya ƙara kimtsa wa, ya kashe musu light ya hayo kan gadon yana kallon fuskar Aliya dake bacci a nitse.
Karo na farko da zuciyar sa ta buɗe dan kanta, Ta soma kallon Aliya da sabon fata, tana ajiye ta awani wuri da bai san akwai shi acikin zuciyar sa ba.
Ya ja numfashi mai nauyi. Ya janye ƙwayannin idanunsa daga kanta, akaro na ba adadi abinda yake dannewa a ƴan kwanakin nan na taso mai.
Seda ya soma mata addu'an kwanciya bacci ya tofa mata, sannan yai ma kansa addu'an, ya lumshe idanunshi.
Bacci mai cikeda natsuwa na musamman ya ɗauke sa.
*ZAINAB*
Siph dinta tabuɗe taɗauko duk wasu sarƙoƙinta da bangles ɗinta na zinare da Ahmed kan siya mata amatsayin kyauta.
Idanuwanta ne suka kawo ƙwalla, akan dole ba don tanasoba se don matsalar gidanta, tun jiya kayan abincinsu yaƙare yauma dabaru irin na mata tayi tahaɗa musu abincin da sukaci.
Ga school fees ɗin yara da kuɗin exam ɗin Khadijah na WAEC dubu talatin da biyar, ita ba kuɗi take dashiba cash a hannu saboda Ahmed baya bata kyautan kuɗi, ita kuma Allah beyita a mace mai roƙoba.
Indai tanada bukatar abu sedai tagaya mai, amafiya lokuta shi yake siyo mata da kanshi ya kawo mata ko kuma yabata kuɗin tasiya.
Ga ace tana yin dabarun mata ta ƙara kuɗin abu to wataƙila da ayanzu tayi saving wasu kuɗade masu ɗan nauyi.
To amma ba tayi komai nata gaskiya da gaskiya ne.
A ranar taje kasuwan sabon gari ta saida sarƙoƙin nata tadawo da kuɗaɗen ta tsaph a hannu Naira dubu dari da hamsin.
Sedai bata tsirada ko asi ba. Dan ma saida ta duba tsohuwar ajiyan ta ta dauko dubu biyar ta cika taje ta biya musu kudin makarantar.
Ragamar ɗaukan nauyin gida ba sauƙi bane dashi. Musamman yaran da ba ɗaya ba, ba biyu ba. Har yara hudu.
Ta kauda matsalar kudin makaranta. Ga na abinci ya taso saboda komai yaƙare duk wani dabara da take musu ayanzu an cimma matsaya.
_____
Misalin ƙarfe 3:30pm.
Kwance suke a falon. Kallo ɗaya zakai mai fuskokinsu kasan cikin su babu lafiya.
Anis dake kife da kanshi a jikin kujerar se zuban hawaye yake.
Ramlat na kwance tana nishi. Ita bata taɓa sanin haka yunwa ta keba se yau, da ƴan hanjin ta suke nannaɗewa suna murɗe cikin ta dake lafe yana ƙugi.
Rabon su da abinci tun daren jiya. Da safe hakanan suka shirya suka tafi makaranta.
Ba tasan ɓarayin suba, amma ita dai tunda 12:00pm tayi ta daina gane abinda akeyi a ajin. Malaman suma duk yanda suka so suga ta maida hankali barinta sukayi.
Ƙwayen ta sukai ta magana tai musu banza. Hakanan aka tashi, suka jero hanya kamar masu ciwon haƙwara.
A yanzu ma, kuwwa kwance yake ba yako iya motsawa.
Zainab ta miƙe"Khadija ki zauna dasu bari in je in dawo."
"Ina zakije?" Khalid ya tambaya yana kallon ta da kyau.
Zainab ta ɗanyi shiru, ita kanta batasan inda zata jeba. Kawai dai zata fita ta samo musu wani abu ko yayane su sanya ma cikin su, zamansu a haka bazai yiwu ba. Nauyi ne akanta ta nimo musu duk wani abu da suke buƙata a rayuwa.
"Ba zanyi nisaba yanzu zan dawo"
Baki yabuɗe zai magana, ta girgiza mai kai alamar yai shiru.
Shirun kuwa yayi. Da yike akwai hijjab ɗin da tai sallah bata cire ba se kawai ta fita.
Tai tsaye a kofar gidan tana kallon anguwar tasu da tai tsit babu hayaniya, kuwwa yana cikin gida.
Imbanda Zaliha babu wanda sukai sabo da ita a anguwar, kuma iyanzu dai tasan maƙotocin nan duk ƴan baran dan tane.
Tafiya kawai ta soma yi. Zuciyar ta na dokawa. Rana da yunwar da takeji na walagi-gi da ita a tsakiyar ti-ti. Jefa ƙafafuwanta ta keyi aduk inda ta samu. Tai tafiya mai nisan da bata tsammata ba.
Idanuwanta basu tashi budewa ba seda tazo ƙarken layin su, Inda restaurant din Good and Best yake.
A lokutan baya sukan zo da Ahmed da yara suci abinci susha ice cream, Amma ayanzu tasan ko shiga security bazasu barta tayi ba.
Tai tsaye kurun tana kallon wurin da befi tai taku uku ta isa gate ɗin ba.
Wata motace red color tazo ta gifta ta, ta shige wurin. Ba'a jima ba se gashi wani babban mutum ya fito daga ciki.
Amemakon ya shiga ciki kamar yadda Zainab tai tsammani se taga mutumin ya nufo inda take.
A gaban ta yai tsaye yana kallon ta ta cikin glass din dake sanye a idanunsa.