Free chapter · Read without an account

BABI NA BAKWAI

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

A GIDAN SOJI, sojoji basa zaɓe kuma ba za'a zaɓe su ba. Matansu dai suna da ƴancin suyi zaɓe ko kar suyi. To a zaɓen da yazo, tun kafin shugaban ƙasa ya hau mulkin shi na mulkar ƴan Nijeriya ya faɗa kudirin shi na cire tallafin man fetur. Mafi yawan matan da suke Bariki, saboda ƙabilu ne inyamurai, an aje cewa duk wanda ze yi zaɓe, to kada ya zaɓa shugaban da yace ze cire tallafin mai kuma kowa yasan wanda inyamurai suke son azawa akan mulkin Nijeriya; Peter Obi. 
Da aka fita zaɓe, mafi akasarin matan soji da suka yi zaɓe kuri'ar su ta Peter Obi ce duk da irin rabon abinci da akayi a wancan ɓangaren shugaba. Ni bana zaɓe duk da ina so nayi. Jurewa zuwa zaɓen ne ba zan iya ba. 
Bayan an gama zaɓen shugaban ƙasa, hukumar dake alhakin faɗin wanda yaci zaɓe, INEC, suka faɗi cewa Bola Ahmed Tinubu ne yaci zaɓen shekarar dubu biyu da ashirin da uku. Duk da garin Lagos da Tinubu yayi zama gwamna basu zaɓe shi ba amma de haka akace shine yaci zaɓen. 

Mu mutanen mu musulmai Hausawa suna jin tsoron zaɓen Peter saboda tsoron tashin hankali, raba kawunan ƴan Nijeriya da kuma tsabagen tsoron da suke ji idan akace inyamuri Christian ne ke mulkar Nijeriya. Gani suke waɗannan abubuwan ba za'a iya samu daga wanda yace addinin shi musulunci ne. 

Bayan an rantsar da shugaban ƙasa, abu na farko da yayi shine cire tallafin man fetur kamar yadda ya faɗa. A lokacin ne komai ya hauhawa. Duk wani abu da zaka taɓa a kasuwa zaka ji da tsada, ko ka saye ko kuma kayi haƙuri ka koma gida hannu wayam. 

A lokacin ne matsalar da muke fuskanta ta ƙara yawa na daga abinci da duk wasu buƙatocin rayuwarmu. Idan mutum ya shiga aikin soji ko duk wani aiki na Khaki da ma wanda ba na Khaki ba, ka shiga da takardun gama Sakandire kawai, albashin ka ba wani abu bane ba. Idan ma an tura ka wani gari inda zaka yi aiki, wata sabuwar matsala kenan duk da ana bada allowance na cin abinci. To allowance da ake badawa naira dubu da ɗari biyar ne, wancan lokacin da akwai tallafin man fetur zasu isa kaci abinci amma banda yanzu. Me ka ajiyewa kanka kuma me ka turowa iyalanka su kula da kansu?

Zaune nake nayi tagumi ina tunanin irin halin da muka shiga cikin ƙanƙanin lokaci. Dama itama waccan gwamnati ba wani abun kirki ne tazo tayi ba bale kuma yanzu da aka cire tallafin mai. 
 “Farida” na kira ƙaramar ƴa ta. “Farida” na ƙara kiranta ganin bata taho ba. “Farida zan ci ubanki nan wurin fa”
  “Umma gani tafe fa. Yanzu ina fitowa” Farida tace se kuma gata na gani
   “Me kike jira da ba zaki taho ki wanke uniform naki ba?”
      “Na duba babu tokar wanki shiyasa”
Ɗago kai nayi na kalle ta “Babu toka kuma?”
  “Eh, gaskiya ban gan ta ba”
   “Mtswwcchhh” nayi tsaki kaɗan gaba-ɗaya raina yana ɓaci. Tashi nayi na shiga ciki na duba ɗan chanjin da nake dashi na dawo mata dashi na bata taje ta siyo tokar da zata yi wanki dashi. 

Shekaran jiya Baffa ya dawo gida bashi da abinci a hostel dole na ɗauki abincin mu na bashi. Har da wasu sauran ƴan chanji na duka na ɗauka na bashi tunda ba ze ci shinkafa ita kaɗai ba. Zama nayi ina tunanin abinda zan ci tare da Farida tunda mu kaɗai ne a gidan. Ina cikin tunanina mahaifin su ya kira ni. Daidaita murya ta nayi tukunna na ɗauke kiran shi. Watan shi biyu yanzu baya nan. 
  “Kuna lafiya, Madam?” 
    “Lafiya, we're fine” na amsa mishi 
  “Kiyi haƙuri nasan wata ya taho ƙarshe amma ina kokari na samu wani abu me yawa na turo muku. Har yanzu shinkafar bata ƙare ba?”
Abinda nake ji na ƙara haɗiiye wa nace “Da saura. Zata iya kai mana kwana biyar” na faɗa mishi ƙarya. Duk jiya bamu samu wani abinci na kirki nida Farida a gidan nan ba. Garri ne muka ci tunda safe har da dare.
   “To dan Allah kuyi haƙuri ku lallaɓa da ita kafin na tattaro kuɗin se na turo muku kiyi siyayya” ya faɗa min. Shiru nayi ban ce komai ba ina ta tunanin rayuwar mu “Maryam” ya kira sunana ahankali. 
   “Na'am Ibrahim”
   “Dan Allah ki ƙara haƙuri. Nasan kina haƙuri amma dan Allah ki ƙara haƙuri. Watarana se labari. Kina ganin yaranmu duka suna kan girma in sha Allah komai ze taho ƙarshe. Kuma ina jin kamar za'a ƙara mana albashi kinga wahalar ze dinga zuwan mana da sauƙi”
   “Babu komai Ibrahim” nace tare da share hawayen dake zubo min ”Babu komai kar ka damu. I understand everything”
  “Yawwa nagode sosai. Allah yayi miki albarka”
“Amin, nagode”
“Jiya Baffa ya kira ni akan wasu kuɗaɗe a makaranta amma bana tunanin aikin makaranta ze yi dasu”
“A'a, kar kace haka. Indai Baffa yace aikin makaranta ze yi da kuɗi to gaskiya yake faɗa kar ka hana mishi”
“Shikenan na dinga ɗaukar kuɗi anyhow ina bashi? Ko watan chan fa ya amshe kuɗi yace makaranta. Ke kike ɗaurewa yaran ki suna yin duk abinda suke so ko?”
Shiru nayi nan take naji haushi da fushi ya cika ni amma haka nayi haƙuri na danne abinda yace, nace “Allah ya baka haƙuri ba haka bane ba. Se anjima”
“Se anjima kuma? Fushi kika yi dani ne Maryam?”
“To naga baka so a faɗa maka gaskiya Ibrahim. Baffa ze zo yace ka bashi kuɗi ba aikin makaranta ze yi ba duk da yasan irin halin da muke ciki? Yaron nan fa ba ze taho yace a bashi ba idan babu lalurar badawa kuma naga kana son ka ɗaura min laifi akan duk wani abubuwan yaran ka”
Ina ji lokacin da ya sauke ajiyar zuciya “Akan wannan abun zaki yi fushi to Maryam? Idan ba ke ba, wa nake da kuma wa zan je nayi wannan maganar da idan ba ke ba? Dan Allah ki dinga min uzuri”
   “Allah ya bamu haƙuri da fahimtar juna. Yanzu ka tafi ka huta ko kuma kayi aikin da kake tunanin zaka yi”
   “Kenan baki yi haƙurin da kike cewa Allah ya bamu ba, Maryam. Magana ba zata wuce a wurin ki ba?”
Shiru nayi ina sauraren abinda ze ƙara cewa. Da kuma naji be ce komai ba yasa na kashe wayar saboda bana son faɗa kuma bani da ƙarfin ya faɗa na faɗa. 

Inaso na kira ƴar uwata amma idan na kira ta abu na farko da zanyi shine na fashe da kuka kuma bana son tonawa gidana asiri. Tagumin na cigaba da yi har se da Farida ta gama wanki ta daka mana ƙulin cin Garri.

                                     _____________

HOSTEL ɗin mu ya kan zama lively idan ƴan ajin ƙarshe suna gab da gamawa saboda irin wasannin da suke yi wanda makaranta ta amince musu dashi. Mata da maza kake gani sun dawo daga cikin makaranta shirye a cikin kayayyakin su na al'adun su. Tun daga Inyamurai, Yarbawa, Hausa, Ebira, Igala, Idoma, Shuwa Arab, Kanuri, Babur da Gbayi da duk wata ƙabila da take karatu a cikin yaran da suke bukukuwa da ma wanda duk basu nan, da wanda ma ba wannan kabilar yake ba. Kowa yana da damar yayi representing ko wace ƙabila yake so. Duk zaman da zasu yi jami'a, zasu na tunawa da waɗannan abubuwan da suka maida tafiyar tafiya me cike da ƙauna da kuma nuna cewa ana tare da juna. They'll one-day look back and see the bigger reason they all participated in this and they'll smile and be glad they did. 
Ina da wata yarinya kyakkyawa me nuna tana ƙaunata a makaranta kuma tana daga cikin masu yin waɗannan bukukuwan saboda itama a ajin ƙarshe take a jami'a, aji na biyar a Faculty of Law. Temi tana ɗaya daga cikin kyakkyawan matan da suke Faculty of law. Fatar ta baƙi ce irin me kyau ɗinnan wanda be yi duhu sosai ba amma ba za'a ce fara ce ba. Tana da kyakkyawan murmushi kuma ana iya gano idan bata farin ciki akan fuskar ta saboda bata kasance me iya ɓoye ɓacin rai ba. 
Mafi kusan abinda take so a wuri na shine muyi dating juna kuma idan akace dating juna a wurin waɗannan mutanen da nake da banbancin addini da al'ada dasu, to ya haɗa da zama tare. Ko ita ta dinga zuwa ɗaki na a hostel ko kuma na dinga kai mata ziyara a apartment nata. Ban tashi naga wata al'ada ba wannan ba saboda ni ba a ƙasar Hausawa na tashi ba amma dai mahaifiyyar mu ta kan faɗa mana al'adun mu da kuma addininmu. Takan faɗa mana wannan shine al'adar da muka tashi muka ga anayi amma wannan al'adar ba namu bane ba, saboda haka, ba zamu ɗauki al'adar wasu ba don mun tashi a cikin su ba.
 
Tun da na hango ta chan nake kallon ta da kanta da jikin ta. Bata da jiki kuma bata da wani tsawo tana daidai ga jikin mace. Fuskar ta na ɗauke da murmushi waya na kan kuncin ta. Riga wacce ke short sleeve ce sanye a jikinta se kuma skirt wanda ya tsaya a guiwar ta. Kanta na ɗauke da wani wig wanda gashin shi ya zubo akan kafaɗun ta. Tana birgeni iya birgewa. Abinda ke hana min zama tare da ita shine ban shirya yin alaƙa ba kuma ban shirya commitment ba. Kuma har yanzu na kasa sanin babban dalilin da yasa ban bata dama ba. Ko don saboda al'ada ne da addini? 
  “Baffa. How are you?” ta faɗa bayan ta iso tana kallo na
  “I'm good Temi” na faɗa ina kallon ta. Daga ganin yadda take rayuwa a cikin makaranta, za'a san ta fito daga gidan masu kuɗi ne. Wani lokaci muna zaunawa muna yin hira da ita tana faɗa min labarin ta kuma anan ne tasan ni ɗan Barracks ne. “And you?” na tambaye ta. Duk pidgin da nake yi a gida da kuma tare da abokanaina bana yi idan Temi ta min magana. Ina so na mata magana kamar yadda take min tunda ba pidgin take yi ba idan muna magana tare da ita. 
   “I'm good. Just craving for you” tace tare da kai hannun ta akan sumar kaina tana min to and fro. “Come to my room. I'll want to cook for you before I leave this school”
   “I'm not really hungry, Temi”
“This boy! I don't understand the thing that's in your head. Why are you always turning me down? Come on let's go” ta faɗa tare da riƙe hannuna. 
Hannuna na fara ƙoƙarin cirewa a nata “It's not like I'm always turning you down. I'm just not hungry”
   “Okay see ehn, anytime you are hungry and you know I'm available, just text me and tell me you're hungry. I want to cook for you before I leave this school. And I'll do it”
Dariya nayi “Are you so desperate, Temi?”
   “No, I'm not. It's just that I like you Baffa. And you keep on turning me down. I wouldn't mind dating you for a week, just a week”
Shiru nayi ina nazari. Wayasani ko ina so na shiga a cikin fantasyn Temi. Wancan lokacin alaƙa me ƙarfi take so, yanzu kuma tace na sati ɗaya. Na yarda nayi wannan relationship na sati ɗaya and see how to be loved by a woman that loves you so much or I should brush this off? 
Kallon ta nayi ta gyaɗa min kai. “Just one week and we'll be done”
   “Why?”
  “I just want to feel loved by you. Is it your religion that's holding you back?”
Ahankali na girgiza mata kai “We are even allowed to marry your kind”
  “So you see, Baffa. Just give this a chance you won't regret being with me. I promise. Who knows if I'm the one?” tana faɗin haka se tayi dariya
   “Won't you be ashamed to be seen with your junior?”
   “I'm not a public property. I have a mind of my own”
Nodding Kai nayi. 
   “You agree?”
Ƙara nodding kai nayi ina tunanin abubuwan da zasu iya faruwa. Nan take idanun ta suka yi sparkling. “Baffa has said yes!” tace cikin murna “That's my Muslim boy” ta ƙara faɗa cikin murna se kuma tayi hugging ɗina tana jin daɗi “You won't regret this, Baffa”
Hugging nata back nayi “You won't regret this too, Temi”
   “Thank you for giving us a chance. You know, I have got to go. See you in the evening. I'll call you”
Nodding kaina nayi ina kallon ta. Har ta fara tafiya ta dawo “Won't you escort me to the garden and come back? You don't even know how to do this love thing”
Murmushi nayi na tashi na raka ta.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.