Free chapter · Read without an account
Chapter Six
by Sadiya Umar Turaki · IMAANI
Mazewa Imaani tayi jin an kafeta da idanuwa taƙi kallon inda yake.
Shi kuwa yace ma abokananshi, "Baba nifa nasamu wurin zama ku nemi wani wurin." Ya ƙara gaba jin zasu fara mishi shegantaka.
Jan kujeran gabanta yayi ya zauna, yayi shuru kawai yana kallonta.
Ita kam bata kulashi bama tana ta kallon wani wurin daban kaman batasan dashi ba awurin. Zulaihat ta gani tana dososu da glass container ahannu. "Ma, angama haɗawa sorry for the delay."
Imaani ta amsa ta buɗe. Komai yayi to satisfaction, feta cheese ɗin ba'a cikaba, kuma ƙamshin dressing ɗinma yayi. Rufewa tayi tasa a basket ɗin tace mata, "Well done Zulaihat, ki haɗa da zobo idan akwai sai ki miƙama Cynthia su kaima Abbu."
Zulaihat ta ɗauka basket ɗin tace, "Okay, akwai ma zansa yanzu." Ta juya ta koma KItchen ɗin.
Imaani ta ɗaga kai ta kalli Zunnurain, ya ɗaga mata gira kafin yace, "Assalam alaiki Imaani."
Ta amsa mishi da, "Wa alaikas salam." Sai tayi shuru.
Sanye yake da navy blue yadi da akaima aiki kaɗan agaba, babu hula akanshi sai silver agogon Tissot PRX Powermatic 80 da zoben azurfa.
A hankali Zunnurain yace, "Bazakiyi laifi ba tunda ni nagani nace inaso." Kauda kanta tayi tana murmushi tasan yana magana ne akan rashin kiranshi da batayi ba. Sai yace, "Amma fa kisani yau saina kaiki har gida, kinga numberki can come later tunda zansan inda zan nemeki hankalina zai kwanta."
Bata ce komai ba ta ɗaga hannu ta kira mishi waitress. Saita ce mishi, "Me zaka ci?"
Bai damu da ya duba Menu ba wanda da wayarka zakayi scanning QR code dake jikin wani metal acrylic plaque akan kowane table sai ka zaɓi me zakaci. Ce mata yayi, "Kimun recommending, this is my first time being here actually."
Imaani tace, "Okay, I hope you'll like it though."
Yayi murmushi yace, "I know I will."
Da waitress ɗin tazo Imaani tace mata ta kawo sabon abincin da tayi Fried Spaghetti with Seasoned Beef and Greek salad idan akwai saura. Da girmamawa waitress ɗin ta amsata.
Bayan ta tafi Zunnurain yace ma Imaani, "So, meya kawoki nan?"
Imaani tace, "Aiki nakeyi anan."
Sai ya juya yana kallan restaurant ɗin kaman me neman abu yace, "As what?"
Tace, "As a manager."
Cikin raha yace, "Ashe special treatment zan samu yau Madam Manager." Taɗan yi murmushi kawai. Sai yace, "I thought you're a student a Northern Gate."
Tace, "Yeah ina Master's ne yanzu."
"Okay, wani department kike?"
Kafin ta amsa waitress ɗin ta dawo, bayan ta ajiye plate ɗin hannunta Imaani tace mishi, "Sorry na manta ban tambayeka wani drink za'a kawo maka ba."
Zunnurain yace, "Akwai kunun aya?"
Imaani tace, "Akwai amma meal din zaifi tafiya da zobo ko pineapple and ginger drink."
Sai yace, "Zobon yayi, let me try na nan naji." Yasa fork ya fara cin abincin.
Bayan waitress ɗin ta tafi ya kalli Imaani yace, "This is actually very good." Sai yakai lomarshi ta uku.
Murmushi Imaani tayi tace, "Thank you, sabon recipe ne idan babu damuwa abar mana review a website ɗinmu please."
Yace, "Dolena ai, it deserves it."
Girgiza kai tayi ta barshi yaci abinci, ta lura akwaishi da surutu. Abokanshi kuwa sun kammala har sunfara haramar tafiya, kiranshi ɗaya daga cikinsu yayi yace tafiya fa zasuyi sunga alama ba yanzu zai gama ba.
Zunnurain yace, "Just go, zan sameku a Golf Club da yamma." Ya yanke kiran ya maida wayar kan table.
Bayan ya kammala akayi clearing table ɗin Imaani tace, "Akawo desert ne?"
Yace, "Cikina yacika indai ba so kike nakasa tashi ba. Zandai tafi dashi." Tayi dariya kawai.
Idonshi ya zuba mata ita kuma tama kasa haɗa ido dashi saboda rashin sabo, tace, "Nifa kadena min wannan kallon."
Naɗe hannunshi yayi ya jingina bayanshi da kujera, da kakkausan muryarshi yace, "Wa kikeso in kalla toh? Faɗamin."
"Kawai dai kadena kallona."
Shuru yayi mata, murya a ƙasa yakira sunanta. "Imaani."
Dum dum taji ƙirjinta ya buga. Tasan sunanta yanada daɗin faɗa amma akwai wani yanayi da yake amfani wurin kiran sunanta wanda yake sa ilahirin jikinta ya amsa.
Ta ɗaga ɗara ɗaran idanunta ta kalleshi dasu, zubama juna ido sukayi. Mamakin kanta takeyi da bata iya ta janye nata idanunba yanzu.
Ma'aikatan da suka lura da jimawarta zaune a wurin sunata gulmarta a ransu, bata taɓa zama da client a bainar nasi kamar yau ba. Shikenan kuma sun samu abun faɗa.
Janye idanunta tayi daga nashi tace, "Hospitality and Tourism Management, my Master's Programme."
Zunnurain yace, "Such a peculiar course to study, especially anan Arewa."
Tace, "Har yanzu ba'a waye akan aspect ɗinba especially Hotel Management."
"Hakane kam, kinfara practicing ne?"
Tace, "Inayi sometimes a Abuja idan Ammi ta buƙata."
Zunnurain yace, "Okay, acan kuke zama kenan?"
Imaani tace, "A'a ina overseeing Hotel ɗinta dake can ne tare da Hamma na."
Sai ya ɗaga kanshi ya duba sunan restaurant ɗin dake maƙale ajikin bango. Ya tuna akwai wani Luxury Hotel a Abuja mai irin sunan. "The Olive Room?"
"Eh, wannan extention ɗinshi ne. Just the Restaurant babu Hotel anan."
Daga haɗuwarsu a makarantarsu yasan daga babban gida tafito amma nothing could've prepared him for this. He was very impressed jin mace ce take cikin harkar business haka kuma very deeply, abun burgewar ma uwa da ƴa ne, don shi bai taɓa kawo wa wai Imaani ce keda Restaurant har Hotel ɗinba.
Tunawa yayi da inda ya fara ganinta a Dadan-Garba Chambers, sai yace, "Ranan da muka fara haɗuwa a DG Chambers inasha anan kike aiki."
Imaani tace, "A'a nakai ma Abbu lunch ne lokacin."
Da mamaki yace, "Badai Barrister Ibrahim Mu'azzam SAN ba?"
With pride a muryarta tace, "Shi ɗin dai."
Zunnurain yace, "Mahaifina ya sanshi sosai, sunyi aiki tare ada har yayana yayi serving a office ɗinshi few years back. Yanada wani ɗa kaman Rilwan ne ko?"
Imaani tace, "Rafeeq, Hamma na ne."
"Yeah that's the name. Sunan ƴan gidanku ba'a jinshi a gari sosai."
Dariya tayi tace, "Naka ma haka."
Gefen bakinshi ya ɗaga yace, "Ashe kintuna suna na, faɗamun yama yake?" Ɗan harararshi tayi yace, "Ai nayi tsammanin kin manta ne."
Batace komai ba, ya lura bata cika magana ba. Bata da surutu sam shi kuma yana dashi tunda girman kaka ne shi.
Kiran sallahn Asr aka fara Imaani taɗan buɗe idanunta, batayi realising sun daɗe haka ba.
Zunnurain yace, "You've made my afternoon today. Gaskiya naji daɗin time ɗinda kika bani yau, so yaushe zaki tashi nayi dropping ɗinki a gida?"
Nanfa ake yinta, don Imaani dai bata taɓa shiga motar wani ba. To me zata ce a gida idan securityn bakin gate sukaga an sauketa da baƙuwar mota? Ai kafinma aje can Mr. Samuel da Cynthia bazasu bari bama tunda haka bai taɓa faruwa ba kafinma yaje kunnen Abbu.
Kafin ta amsashi yace, "Don't you trust me enough? Nafa baki enough info akaina da zaki iya sa a bincikani."
Rolling eyes ɗinta tayi mishi reflexively tace, "To aini ba wanda ya taɓa kaini gida inba driver naba."
Da sauri yace, "To saiki bani contact ɗinki kawai if not kullum zanzo nan na addabeki. Besides I have my ways of getting it fa Imaani amma inason nayi respecting boundaries ɗinki ki bani da kanki."
Miƙa mata wayarshi Samsung Galaxy Z Flip7 yayi. Ta samishi numbern ta maida mishi sai yayi dialing ya yanke bayan yayi saving.
Imaani da taga call ɗin yashiga wayarta bata damu da ta dubaba. Hannunshi yasa zai ɗauka wayarta yace, "Mugani." Miƙa mishi wayar tayi tana dariya yace, "Do you blame me? Nafasan halinku mata."
Daya duba yaga already tayi saving contact ɗinshi using complete sunanshi, ɗan murmushi kawai yayi a ranshi yace nan gaba kaɗan matsayina zaifi haka a wurinki da yardar Allah.
Baice komai ba ya maida mata wayar. Tashi yayi ya tsareta da idanunshi kafin yace, "Sai na sake ganinki, which is very soon In Sha Allah."
Bata ce komai ba sai ya nufi cashier don ya biya kuɗin abincin dayaci. Texting ɗin Cashiern Imaani tayi kafin ta tashi ta shige hanyar zuwa ciki da sauri.
Yana zuwa wurin yace ma Cashiern ta faɗa mishi cost ɗinshi, sai ta ce mishi, "Don't worry sir, Madam tace it's on the house. Please kaɗan jira akwai package da za'a kawo maka."
Juyawa yayi zuwa inda ya zauna yaga batanan, girgiza kanshi kawai yayi yana smiling. Wata waitress ta zo ta miƙa mishi wani transparent plastic package, ciki akwai varieties ɗin cakes anyi decorating ɗinsu sai finger snacks, abun yayi kyau sosai.
Zuciyarshi na bugawa da wani sabon yanayi ya nufa ƙofar fita da sassanyar murmushi, fuskarshi cike da annuri.
***
Guys, I am so in love with this guy.
😭😭