Free chapter · Read without an account

Chapter 34

by Narrnarhh Bukar · NACINA YA JAWO MINI..

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*








NACINA YA JAWO MINI...



034

Ɗan murmushi tayi sannan ta  ce

"Wata shawara ce nazo da ita kuma ina fatan zata karɓu  a gareka,ganin Umma Kande a irin wannan hali,gashi su Iklima sun kusa aure,ita ma Nusaiba muna mata fata samun miji a nan kusa tayi auran ita ma,shi ne nace mai zai hana ka auri Maman Jummalo domin idan yaran sukayi aure gidan watsewa zaiyi,ya zama babu kowa don kasan Maman Jummalo da wuya ta cigaba da zama a gidan,kaga idan ka aureta zata cigaba da kula da Umma Kande sannan yaranka zasu samu madogara tunda ni ba'a gidan nake ba yanzu,kuma yaran sun ɗauki Maman Jummalo a matsayin mamansu,a tunanina hakan zaifi dacewa"


Shiru yayi yana kallonta ko ƙifta idanunsa baya yi,sai can ya sauke goron ajiyar zuciya sannan ya ce

"Kenan bakya kishina Hussaina"

"Haba ina kishinka sosai ma kuwa,saidai duk abinda mutum zaiyi a rayuwa dole idan zaiyi *sara ya dinga duban gatari* ,taimako ne zamuyi Sulaiman na farko mun ƙara inganta rayuwar Maman Jummalo saboda aure shi ne cikar martabar ɗiya mace sannan bazata koma kauye ba,kaga tana buƙatar aure tunda ba tsufa tayi ba sannan zata kular matlka da matarka sosai saboda aminiyarta ce,kaima karan kanka zakaji daɗin ganin ana kula maka da matarka haɗi da yaranka idan hidimar hakan ta taso tunda ni ba gidan nake ba,da ace a gidan nake da wallahi bazan kawo shawarar ka aure Maman Jummalo ba saboda ina matuƙar kishinka amma yanzu babu maganar kishi tunda ba gida daya muke ba"


Shiru tayi yana kallonta sai can ya ce


"Hussaina kinzo min da magana mai girma wacca ƙwaƙwalwata ta kasa ɗauka,zanyi shawara tukunna idan da hali  ƙila na amince,idan kuma zuciyata taƙi yarda wallahi komai zakiyi bazan amince ba,to wai da kike cewa na auri Maman Jummalo, idan kuma taƙi amincewa fa"

"In Shaa Allah zakama amince itama haka zata amince angon Hafsy"

Tana maganar tana dariya

"Au! zolayata ma kike Hussaina,ya miki kyau"

"Ni na isa na zolayi gwarzon namiji kamarka,wace ni Hussaina"

Dariya shima yayi ba tare da ya bata amsa ba suka cigaba da kallonsu.Bayan kwana biyu yayi shawara sai ya amince itama Maman Jummalo ta amince,nan da nan maganar aure yayi ƙarfi har ƙauyensu Maman Jummalo Abban Sa'eeda yaje,ba tare da ɓata lokaci ba aka daura musu aure a can tunda har sadaki ya biya,su Nusaiba da Iklima sunyi murna sosai da wannan auran.

A ɗakin Umma Kande ta tare bayan an cire komai na ɗakin tare  da ƙara gyarashi haɗi da sabon fenti,kayanta ta dawo dasu ɗakin Umma Kande, saida suka sha amarci har na tsawan kwana uku sannan suka raba kwana bayan yakai Maman Jummalo gidan Umman Sa'eeda wanda yanzu har da mota garesa wanda sirikinsa Sadam ya siya masa,Sa'eeda ma tayi murna sosai duk da kishiya aka ma Ummanta amma dai koba komai Maman Jummalo zata kula da tarbiyyar su Nusaiba kamar wacca ta haifesu sannan zata kula da Umma Kande idan yaran sunyi aure kasancewsar auransu baifi wata uku ba.

Bayan sati uku da bikinsu Maman Jummalo da Abban Sa'eeda jikin Umma Kande ya tashi gadan-gadan,hauka tubaran ga surutai barkatai babu daɗin ji balle sauraro,gashi gabanta yanzu yama tashi aiki saboda tsutsotsi ke fita mararan ga wari,yaranta sunyi kuka sosai da wannan halin da Mamansu ke ciki.Yau kowa yazo ɗakinta harda Umman Sa'eeda da Sa'eeda saboda ciwon nata yafi na kullum tashi,sai faman ihu take tana cewa

"Sankeruuuu!!! Sankerunaaa kazo!!! Kazooo"

Haka take ta faɗa tana girgiza kanta,idanunta duk sun fiffito waje,sai faman kokawa take da lumfashinta still bakinta bai bar kiran Sankeru ba,kowa na ambata maka kalmar shahada amma ina  Allah ya rufe mata bakin ambaton sunansa saidai Sankeru😂.Haka har rai yayi halinsa kalmarta da karshe ita ce Sankeru.(Allah ka tsaremu da yin mummunan ƙarshe😞😞😞)

Kuka yaran nata suka fashe dashi babu ji babu gani suna kiran sunan mamansu,amma ina rai ya dade da yin halinsa,haka aka kira wata malama tayi mata wanka sannan aka saka mata likkafani haɗi dayi mata sallah sannan aka kaita gidanta na gaskiya.Haka su Maman Jummalo,yaranta,Umman Sa'eeda da ƴan uwanta na Maiduguri suka cigaba da karbar ta'aziyyarta har na tsawan kwana bakwai sannan gidan ya watse kowa ya kama gabansa,aka bar Maman Jummalo da yaran Umma Kande suka cigaba da  zaman makoki.Bikinsu Iklima da Jummalo baifi saura wata biyu ba.

A rana ta goma da rasuwar Umma Kande Abban Sa'eeda ya shigo gidan a fusace yana ƙwallama su Iklima da Jummalo kira,su kuma lokacin suna ɗakin Maman Jummalo suna hira har Nusaiba da Mamam Jummalo,sai suka tsinkayi kiran Abban Sa'eeda,da sauri su Iklima da Jummalo suka fito tare da amsa masa kiran,su Maman Jummalo da Nusaiba daga baya suma suka fito saboda jin yadda Abban Sa'eeda yayima su Iklima kiran kamar yana cikin ɓacin rai,tabarma ya umurci Jummalo ta ɗauko haɗi da kujera domin maganar mai muhimmamci ce,a tsaya bazasu iya tattaunata ba,da sauri da ɗauko tabarma da kujerar daya umurceta tare da shimfiɗa tabarma shi kuma ta mika mishi kujerar kasancewar ya mata nuni da ta miƙa mishi kujerar, zama yayi a bisa kujerar sannan ya umurci su Iklima da Jummalo su zauna bisa tabarma,babu musu suka samu wuri suka rakuɓe kamar marasa gaskiya,su Mamam Jummalo da Nusaiba wani ɓangare na tabarmar suka zauna tare da maida hankulansu kacokam! ga Abban Sa'eedan.Gyaran murya yayi sannan ya fara magana cikin ɓacin rai

"Iklima da Jummalo kai harma da Hasfy kun kyauta kenan da baku sanarmin da mazajensu Iklima basu *Sakesu ba* kunyimin adalci na rashin faɗamin saidai naji majalisar layi ta ɗauka akan inaso na aurar da yarana akan wani auran,hakan ya dace da kuka ƙi sanarmin"

Dummmmm!!! Haka ƙirjinsu Iklima da Jummalo ya bada jin an anbato musu bala'in da Allah ya kuɓutar dasu a baya,tuni Iklima uwar hawaye har ta fara zubda ƙwalla,itama Jummalon zubda ƙwallar take,ƙara tambayarsu yayi amma shiru babu amsa domin basu san taƙamaiman mai zasu ce dashi ba,Maman Jummalo ce ta ce


"Baban Nusaiba kuskure dai an riga da an tafka,ayi haƙuri na rashin sanar makan da bamuyi ba,wallahi ba yaran kaɗai ba koni tsoron mazajen yaran nake, domin ni da mariyanya Umma Kamde da ƙyar muka sha a hannunsu balle yaran da sukayi rayuwa dasu a gida ɗaya"

Taɓe baki yayi sannan ya ce

"Wannan kuta shafa bani ba,ni nace kuje wurin boka nemama yaranku mazaje? Ko kuma sanda kukayi shawararku keda ita kun saka dani ne,ce nike ku kuka yi *Kiɗinku kuma kuka yi rawarku* to sai yanzu zaki ce tsoro kike ji,kina nufin su Iklima da Jummalo a ɗaura musu aura akan wani auran kenan"

Da sauri ta girgiza masa kai tana cewa

"A'a Baban Nusaiba ba haka nake nufin a ɗaura musu aure bisa wani auran saidai na faɗa maka ne mazajen  suna da matsaloli da dama,sannan Baban Nusaiba don Allah ka daina tado da maganar baya,kuskure ne mun aikata a baya sannan munyi nadama tafi ƙarfin cikin kwando,bayan mun kwashi kashinmu a hannu,don Allah kabar tado da zancen baya na roƙeta"

"Naji, yanzu dai dole ku kiramin samarinku kuce inason ganinsu saboda zama zanyi dasu tare da fahimtar dasu akan auran da basu san dashi  naku ba,idan sun ji sun amince akan zasu aureku to  dole a ɗaga ranar auran sai bayan kunyi idda sannan za'a ɗaura,wannan shi ne abinda shari'ar musulunci ta gindaya akai,sannan kowaccanku ta bani address ɗin gidan mijinta da numban wayarsa"

Cikin rawar murya da tashin hankali Jummalo tace

"Baba address ɗin gidan kawai na iya riƙewa amma banda numbansa"

"To ai saiki rubutamin address ɗin  a paper,ke kuma fa Iklima"

Itama kamar Jummalo bakinta na rawa ta ce

"Amm Amm nima banda numbansa saidai address ɗin gidan"


Dariya Abban Sa'eeda yayi sannan ya ce

"Au Allah kamar haɗin baki kowa maida numban mijinsa,to idan nace komawa gidan mazajen naku......"


Ai da wani irin sauri su Iklima da Jummalo kamar haɗin baki suka ce

"A'a Baba,kayi haƙuri"

Kuka riris suke yi suna roƙonsa akan kar a maida auran,hausawa suka ce *Mai ɗaki shi yasan inda yake  masa yoyo* wannan haka yake domin su kaɗai suka san walaha,bala'i haɗi da azabar da suka sha a baya.Tausayi suka ba Abban Sa'eeda sai ya ce

"Wasa nake muku ai, ku share hawayanku,yanzu ina waje ku rubutomin  address ɗin gidajen nasu ku kawomin saboda yau nake so na kira Hassan akan batunsu don bazan iya tun kararsu ni kaɗai ba saida babba sannan tsayayye, karku manta da kiran samarin naku akan ina nemansu anjima da daddare"

"To Baba"

Fita yayi daga gidan,Iklima ta shiga ɗaki tare da ɗauko musu jakar islamiyarsu,address ɗin gidan mazajen nasu na baya  suka kwafe a takarda domin kamar *zane ne a bisa kan dutse* wanda baya iya goguwa a zukatansu.Jummalo ce ta kaima Abban Sa'eeda papar a waje, a lokacin da ta kawo masa paper yana waya ne da Uncle Hassan tare da yi masa bayani akan matsalar data bullo na auran yaransa bayan akwai wani auran akansu,sosai Uncle Hassan ya ce zaiyi jagora zuwa gidan  mazajen nasu,amma sai ya fara jin ta bakin yaran tukunna don ya tabbatar ba ƙarya suke ba sannan  sai ya ɗau mummunan mataki akan mazajen nasu saboda *Cin zarafinsu* mazajen sukayi,a haka ya kammala wayan tare da amsar paper ta koma cikin gidan.

Washe gari da safe saiga Uncle Hassan yazo gidan tare da kiran Abban Sa'eeda kasancewar yau Saturday shi yasa ya samu damar zuwa,shigar dashi gidan yayi bayan ya umurci su Iklima da su fito da tabarma waje.Da sallama ya shigo gidan tare da zama shi da Abban Sa'eeda a tabarma, su Iklima da sauran ƴan gidan suka fiddo da wata tabarmar suka zauna,Abban Sa'eeda ne yayi gyaran murya tare da cewa

"To Alhamdulillah,yanzu ga Hassan yazo don kuyi masa bayanin komai akan zamanku a gidan mazajenku kar ku ɓoye komai sannan karku ƙara komai,iya gaskiya muke buƙatar, ko ba haka Hassan"

Ɗaga masa kai yayi alamun *EH* sai ya cigaba da cewa

"To yanzu muna sauraranku"

Shiru wurin yayi, Jummalo  ce ta fara kwararo labarin rayuwar da tayi a gidan mijinta tun a daren farkonta har zuwa ranar da Ubangiji ya bata ikon guduwa daga gidan,bata ɓoye komai ba sannan bata ƙara komai ba.Itama Iklima sanar musu komai tayi a game da zaman auranta a gidan mijinta tun daga daran farkonta,da amfanin da yake da ita ta bayanta tare da abokanansa har video ɗin abubuwan da suke mata ta sanar ma Uncle Hassan, Tabbas! Ko ba'a faɗa ba Uncle Hassan da Abban Sa'eeda sun girgiza da jin labarin Iklima musamman Uncle Hassan labarin yayi matuƙar tayar masa da hankali,jin labarin yayi kamar wasan kwaikwayo,gyarar murya Uncle Hassan yayi sannan ya ce

"Naji bayananku,sannan in shaa Allah zamu kwato muku hakƙinku musamman ma ke"

Nuna Iklima yayi kasancewar bai san sunanta ba,ya cigaba da cewa

"Ina da aboki babba a *STATE SECURITY SERVICE* wato jami'in sirri ne kuma babba,zan tura masa bayananku domin nayi recording ɗin abubuwan da kuka ce saboda ita ce hujjarmu babba a yanzu,in shaa Allah zamu ƙwato muku hakƙin tare da hukuntasu saboda wannan cin zarafin ɗan Adam ne suka yi"

Godiya sosai suka shiga yi masa,shi kuma yana ce musu ai ba damuwa sun zama ɗaya.A ranar Uncle Hassan ya kira abokinsa babban jami'in sirri yayi masa bayanin komai tare da tura masa addresses ɗin gidajensu da kuma recording ɗin da yayi lokacin su Iklima suke bayanin rayuwarsu a gidajen mazajensu,sosai abokin nasa yayi alƙawarin yin bincike mai zurfi tare da taimaka a hukunta masu laifin.

Bayan sati ɗaya da wannan zancen da Uncle Hassan yayi da abokinsa,lokacin Uncle Hassan yana gida saiga kiran abokinsa ya shigo wayarsa,da sauri yayi picking daman yanaso ya kira yaji what's going on akan case ɗin.Sallama yayi,a can abokinsa ya amsa,abokin ne ya cigaba da cewa

"Kana gida ne? "

"Eh" cewar Uncle Hassan

"Yawwa gani nan zuwa don bayanin bana waya bane"

"Ok Allah ya kawoka lafiya fatan dai kun samu nasara"

"Sosai ma kuwa ai nasarar ma *min indillahi ne* ba daga wurinmu take ba"

"Maa shaa Allah can't wait to hear from you"

"Ok sai nazo"

Katse kiran yayi tare da kiran Dr. Nabila akan ta shirma musu girki yanada baƙo yanzun nan,"To"  ta ce masa sannan ta wuce kitchen tare da kiran ƴar aikinsu Jamila, kasancewar yau lahadi dukkaninsu suna gida.Ba'a ɗau awa ɗaya ba saiga kiran abokin Uncle Hassan kenan ya iso,ce masa yayi ya shigo cikin gidan,gyara parking ɗin motarsa yayi a gefen gida  sannan ya shigo cikin gidan har falon gidan da yake gidan ba baƙonsa bane yakan zo wani lokacin harda matarsa da yaransa,su Uncle Hassan suma sukan zo gidansa,abokanai ne sosai tun suna jami'ar suke abota har zuwa yanzu suna tare saidai aikin kowa ne ya banbanta.Da sallama ya shigo falon,amsa masa Uncle Hassan yayi tare da miƙewa suka rungume junansu,abinci da kayan sha Dr. Nabila ta kawo tare da yi masa sannu da zuwa,twins da Kauthar zuwa sukayi  gaisheta sannan suka koma sama.Bayan ya sha ruwa sai yayi gyaran murya tare da cewa

"Sarkin ƙaguwa nasan you're eager to hear from me"

Dariya Uncle Hassan yayi sannan ya ce

"Kaima kasani ai,akwai ni da son jin labari,kace Ubangiji yayi ikonsa akai,gist me brooo"

Dariya sosai abokinsa yayi sannan ya fara magana

"Alhamdulillah Alhamdulillah,kawai zan iya cewa domin kuwa Allah yayi ikonsa akansu,Ubangiji baya yafe hakƙin wani a bisa na wani,so bayan ka bani informations a game dasu tare da address nasu sai na miƙa case din ga hukumarmu,sosai aka amincemin akan nayi jagora a case ɗin,nayi bincike sosai a game dasu har na tsawan kwana hudu sai a kwana na biyar muka shirya tsaf! Zuwa ɗaya daga cikin gidajen da kabani address ɗinsu,bayan mun isa gate ɗin gidan ko mintuna biyar ba muyi da fitowa daga motocinmu ba sai gashi an wangame gate ɗin gidan,wasu matasa ne biyu riƙe da wasu mutum kamarsu sai faman aman jini yake ta hanci ta baki gashi ya rame sosai kamar mai ciwon *HIV AIDS* sai wata tsohuwa tana biye dasu a baya tana kuka suka shiga wata mota wacca take suka da namu motocin,mudai  kallonsu kawai muke,bayan sun fito sai mai gadin gidan zai rufe gate ɗin gidan nayi sauri masa magana babu musu ya tsaya da rufe gate ɗin,tambayarsa nayi akan ina neman mai gidan,cemin yayi ai wanda matasan nan suka riƙo shi ne mai gidan sannan wacca naga tana kuka ita ce mahaifiyarsa,ƙara tambarya nayi meke damunsa haka,hmmm kasan abinda mai gadin ya faɗamin cututtukan da yake damunsa saida na girgiza sosai"

Cikin zaƙuwa Uncle Hassan ya ce

"Don Allah faɗamin wasu cututtuka suke damunsa"

Gyara zama yayi tare da kurɓar ruwan sannan ya cigaba da cewa

"A yadda ya sanarmin mutumin yana shan giya sannan mai neman mata ne sosai,cututtukan da yake damunsa akwai ciwon hanta wanda a sanadiyar shan giya ya samesa,sai ciwon sanyi,sannan kuma wacca tafi tadamin hankali ita ce *yana ɗauke da cutar dake karya garkuwan jikin ɗan Adam wato HIV AIDS* wa'innan su ne cututtukan sannan asibiti suke son kaisa saboda ciwon yaci ƙarfinsa yanzu"

Sosai wannan labarin ya tada hankalin Uncle Hassan,ace mutum ɗaya yana ɗauke da wa'innan manya-manya cututtuka haka,katse mishi tunani abokinsa yayi da cewa 

"Ai na wannan mai sauƙi ne akan ɗayan mutumin mai luwaɗi"

Da sauri Uncle Hassan ya kallesa tare da cewa

"Kace wannan mai sauƙi ne,mutumin dake tare da wa'innan manya-manyan cututtuka ace nashi mai sauƙi ne,how? "

Murmushi abokinsa yayi sannan ya ce

"Ai shi at least yana lumfashi sannan zai iya roƙon yafiyar wanda ya cuta amma wannan fa,da muka je layin tare da ƙwanƙwasa ƙofar gidan,bayan mai gadin ya fito na tambayesa game da mutumin,shiru yayi mai gadin yana kallon nima din kallonsa nake ina jiran bayani,saida ya shafe mintuna huɗu still idanunsa a kaina nima ban cire nawa idon akansa ba,sai can ya cemin,yau kwanan mai gidansa shida da rasuwa bayan yayi fama da *yoyon kashi da cutar Cancer a al'aurarsa" saboda abubuwan da yakeyi,gashi ko nan da can bai iya fita duka abokanansa sun gujesa,daman tuntuni ya rabu da ƴan uwansa balle su taimakesa,kashi,fitsari duk a wajen yake,ga penis ɗinsa ya tashi aiki kwata-kwata saboda ruwa mai yauki ke fita ga shegen wari,idan mutum ya dunfaro ɗakin da yake wallahi dole ya toshe hancinsa saboda warin da ɗakin ke fitarwa,hmmm in taƙaice maka bayani shidai wannan,wucewa kawai mukayi ba tare da ce ma mai gadin gs abinda ya kawomu ba,kasan ban dandara ba na sake komawa gidan mutumin nan na farko don sake tambayar what's going on,wallahi shiga tashin hankali nayi jin a ranar da muka zo gidan a ranar Allah yayi masa cikawa,in short dai ƴan uwan naka *TAKABA* dai ya kamasu yanzu, Allah yayi musu sakayya a ta yadda babu wanda yayi zaton haka"

Sun daɗe suna hira har yaci abincin da Dr. Nabila ta girka masa sannan  Uncle Hassan ya rakashi har wurin motarsa sukayi sallama. A ranar Uncle Hassan ya kira Abban Sa'eeda tare da sanarma takaba ya kama yaransa domin kuwa Allah yayi ikonsa akan mazajen namu tare da sakanya musu tun a nan duniya,Sosai Abban Sa'eeda yaji dadin wanga batu tare da yi masa godiya maras adadi,daman samarinsu Iklima da Jummalo sunzo wurinsa tun a ranar da ya umurci su Iklima, yayi musu bayani akan igiyar auran dake akan su Iklima da Jummalo kuma sunce sun ji sun gani suna sonsu a haka,shikenan *Faduwa zato daidai da zama* katse kiran yayi tare da shiga gidan ya sanarma su Iklima da Jummalo, murna iya murna sunyi jin wannan batu,lallai Allah mai iko ne,gashi suna nan Allah yayi musu sakayya tun a nan duniya ba tare da saninsu ba.

Sake ɗaga ranar auransu Iklima da Jummalo a kayi tare da haɗawa dana Nusaiba daman akwai wani mutum mai mata biyu Allah ya haɗata dashi,kuma sun fahimci junansu sosai,sai kawai aka haɗa bikin nasu zuwa nan da watanni shida masu zuwa saboda su ƙara kimtsama bikin sosai saboda ƙaruwar bikin Nusaiba a yanzu. Umman Sa'eeda ma da Abban Sa'eeda ya sanar mata ba karamin farin ciki tayi jin Allah yayi masu Iklima da Jummalo sakayya tun kan abar duniya ga kuma wani sabon farin ciki Nusaiba Allah ya kawo mata miji duk da yanada mata amma Alhamdulillah.Wannan Kenan



     @@@@@@@@@@@@



A ɓangaren *LOVE BIRDS* 🕊️🕊️ wato Sauban Maryam,babu abinda za'a ce sai dai godiyar Allah domin yanzu sun samu natsuwa haɗi da fahimtar junansu sosai ga cikin Maryam yayi girma sosai haihuwa yau ko gobe don tana cikin watan haihuwarta,yanzu Maryam an iya girki da wasu abubuwan da suka shafi mace ta sani a zaman auranta duk Maryam ta sansu ta hanyar abokiyar zamanta mai ƙaunarta tsakani da Allah.


Cikin hikima da ƙudirar Ubangiji Khairat ta samu juna biyo itama,hmmmm zo kuga farin cikin mara misaltuwa a wannan family,sosai cikin Khairat ya saka Maryam farin ciki,daman bata jin daɗi ganin ita Allah ya ƙaddara ta samu ciki amma Khairat lokacinta baizo ba,sosai take adduar Allah ya kawo ma Khairat ciki,haƙiƙa Allah ya amshi adduarta don yanzu haka Khairat cikin yana a wata na uku amma bai kai na Maryam wahalarwa ba.


A ranar Monday Maryam ta haifo kyakkyarwa yarinyarta mai kama da ita bayan tasha wahalar naƙuda,sosai Sauban da sauran family suka shiga c farin cikin wannan haihuwar da Maryam tayi,yanzu Momin Sauban da su dangin Maryam sun koma sun ɗunke kamar da bayan sun kammala yaƙin duniya na uku🌍🌍🌍a baya tare da neman yafiyar juna.Ƙawar Maryam Rahma tazo gidan Maryam tare da sanar mata itama taje har gidan Sa'eeda ta nemi yafiyar abubuwan da ta mata a baya kuma ta yake mata,yanzu ma haka bayan zuwa barka harda invitation card na auranta ta kawoma Maryam,bikin nata baifi saura sati uku yanzu ba,sosai Maryam taji dadin auran da Rahma zatayi sannan da neman yafiyar da tayi a wurin Sa'eeda. Haka ta wuni a gidan sai yamma ta wuce gida.A ranar data zagayo Monday aka raɗama jaririya sunan Momin Sauban wanda Mom dinsa tayi murna sosai dayi mata takwara ,haka akayi taron sunan lafiya ba tare da wata hatsaniya a ɓagagorin biyu ba har kowa ya koma gidansa,Sa'eeda kuɗi mai yawa ta turo ma Maryam asiya ma baby pampers. (My Esteem Fans ba pampers irin na Nusaiba ba a'to😂😂😂)


A ɓangaren aikin Sauban a sabon kamfanin da Sadam ya bashi aiki babu laifi yana samun albashi mai tsoka kuma yanzu ya riƙe gaskiya da amana,yana aiki tsakaninsa da Allah.Wannan Kenan.



             @ @@@@@@@@@ 


A ɓangarensu Gwaggo ladi kuwa dawowansu birni bazaiyu ba saboda rashin lafiyar da ƴar yaya take fama dashi na ƙaiƙayi saidai Uncle Hassan ya gyara gidan nasu sosai ya koma ginin zamani har funitures aka canja masu kyau irin na birni,a duk wata ana sauke musu kayan abinci da kuma dubu hamsin na cefane,kullum cikin godiya suke tare dayi ma Maimuna kakar Sa'eeda addua akan Allah ya gafarta mata tare da dawwamar da haskensa a ƙabarinta dana musulmai baki ɗaya.


Tsufa ya ƙara kama Baba sosai don yanzu ko fita ma baya iya yinsa,kullum yana gida abinsa yana cima mai kyau duk da ɗanɗanon abinci ya fara janyewa daga bakinsa saboda tsufa,itama Gwaggo ladi tsufan ya taso mata amma bai kai na Baba ba don tana iya ƴan aikace-aikace amma ba sosai ba,Allah yasa ma harda mai aiki aka kawo musu saboda tsufan da sukayi.


Ƴar yaya dai ana nan ana girbar abinda aka shuka,susa take ko'ina a jikinta babu ji babu gani tanayi tana ihu saboda azabar da take ji a jikinta,Allah kenan taso Umman Sa'eeda ta dawwama a irin wannan halin ashe ita ta zabarma kanta huƙubar ta take so Ubangiji ya hukunta ta dashi tun kan aje lahira,ƴarta ce ke taimakonta ta gyare-gyare domin ɗaki guda aka ware mata ita kaɗai don ko ƴarta ma sai idan zata bata abinci ko kuma gyaran gidan take zuwa ɗakin.Gashi tsabar susan da take duk jikinta yayi *bororo*,ya kar-kar ce saboda susa.


Umman Sa'eeda ta aikoma Mairo da Na'ima jari mai tsoka wanda zasu dinga juyawa,sosai suka shiga yi mata godiya akan wannan alkhairin da ta musu.Wannan kenan.


          @@@@@@@@@@@@


A ɓangaren *REAL AND GENUIE LOVE BIRDS* 🕊️🕊️🕊️ wato *Sadam da Sa'eeda* rayuwa tana tafiyar musu yadda ya kamata,kullum suna manne da junansu,wani lokacin idan Sadam zaiyi tafiya zuwa ƙasar waje harda Sa'eeda yake tafiya saboda yanzu jinta yake kamar jinin jikinsa,kullum wutar so da ƙaunarta ƙara ruruwa take a cikin zuciyarsa.

Ƴan kwanakin nan Sa'eeda na fama da yawan bacci da zaɓen abinci, ga shegen ci kamar *Gara* har cikin dare tashi take taci abinci,da safe ta karya amma da anjima tayi zata ce yunwa taje,abincin yarbawa ta koma ci musamman *Amala da Ewedu soup haɗi da ganda* wanda abincin yana ma Sa'eeda daɗi sosai,tun Sadam na ɗaukar abin da wasa har yanzu ya koma bashi mamaki,har ya gaji ya ce suje asibiti a dubu meke damunta,ada taso yi masa jayayya wai ita lafiyarta ƙalau amma daya kafe akan sai anje asibiti,haka ta miƙe tana turo baki ta dauko hijab suka tafi zuwa asibiti.


Shi da kansa yayi driving zuwa wata asibitin kuɗi,kasancewar babu wani layi haka suka shiga ganin likita,Sadam bai ɓoye ma likitan abubuwan da Sa'eeda take ba wanda hakan na bashi tsoro ko wani rashin lafiya ne zai sameta,tun sanda Sadam yake bama likita bayanin abubuwan da Sa'eeda takeyi Likitan ya fara murmushi domin ya *harbo jirgin* su dai ne basu gano ba,ce ma Sa'eeda yayi ta kwanta a saman patients bed,saida ta turo baki tana kallon Sadam kafin ta wuce ta hau saman bed ɗin,ɗibar jininta yayi wanda kan ya ɗiba saida Sadam ya taimaka masa wurin riƙeta saboda tsoran allura take sosai,ta wayar tafi da gidanka ya kira wata ƴar lab ta amsa jinin tare faɗa mata test din da zatayi,su kuma suka dawo wurin kujerunsu tare da zama,rumgume Sa'eeda Sadam yayi babu kunya tare da mata raɗa a kunne wanda lokaci guda tayi dariya tana kallonsa sannan ta ce

"Da gask...................





*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.