Free chapter · Read without an account

Chapter 35

by Narrnarhh Bukar · NACINA YA JAWO MINI..

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*








NACINA YA JAWO MINI...







THE END
035

Shi da kansa yayi driving zuwa wata asibitin kuɗi,kasancewar babu wani layi haka suka shiga ganin likita,Sadam bai ɓoye ma likitan abubuwan da Sa'eeda take ba wanda hakan na bashi tsoro ko wani rashin lafiya ne zai sameta,tun sanda Sadam yake bama likita bayanin abubuwan da Sa'eeda takeyi Likitan ya fara murmushi domin ya *harbo jirgin* su dai ne basu gano ba,ce ma Sa'eeda yayi ta kwanta a saman patients bed,saida ta turo baki tana kallon Sadam kafin ta wuce ta hau saman bed ɗin,ɗibar jininta yayi wanda kan ya ɗiba saida Sadam ya taimaka masa wurin riƙeta saboda tsoran allura take sosai,ta wayar tafi da gidanka ya kira wata ƴar lab ta amsa jinin tare faɗa mata test din da zatayi,su kuma suka dawo wurin kujerunsu tare da zama,rumgume Sa'eeda Sadam yayi babu kunya tare da mata raɗa a kunne wanda lokaci guda tayi dariya tana kallonsa sannan ta ce

"Da gaske zaka siyamin"

"Sosai ma kuwa  my darling star,daga asitinin nan direct zamu tafi best resturant ɗinki in siya miki amala da ganda,wai tsaya! anya bakiyi jiɓi da yarbawa ba? "

Dariya sosai Sa'eeda tayi tana cewa

"Who knows"

Shidai likita yana kallon ikon Allah,soyayyarsu sukayi mararan babu ko sakayawa,a zuciyarsa yana cewa 'Amma wannan couples ɗin sun birgeni,ji yadda suke nuna so da ƙaunar junansu,maa shaa Allah' ƙwanƙwasa ƙofa akayi,likita ne  ya bada umarnin a shigo.Ƴar lab ɗin da aka ba jinin Sa'eeda tayi test ne ta shigo tare da result a hannunta,miƙa masa tayi sai ta juya ta fita,duba result likitan yayi tare da ɗago idanunsa yana kallonsu,suma shi suke kallon suna jiran suji mai zaice,sayayyan murmushi ya sakar musu sannan ya gyara murya tare da cewa

"Congratulations Mr Sadam,matarka na ɗauke da ciki har na tsawan wata biyu da ƴan wasu kwanaki"

Dummmmmm! haka ƙirjin Sa'eeda ya bada,shi kuma Sadam maganar tazo masa kamar a mafarki,ƙara tabbatar musu likitan yayi,da sauri  Sadam ya miƙe tare da kallon gabas yayi *Sujudus-shukur* don nuna farin cikinsa hadi da godiya ga Allah mai girma da buwaya.Sosai yayi farin ciki yana ƙara godema likita da wannan daddaɗan albishir da yayi masa,kuɗi ya ciro masu yawa wanda shi kansa baisan nawa bane ya miƙama likita yana ƙara godiya a garesa,sosai likitan yaji daɗin wannan kyautar tare da yi musu godiya hadi da adduar Allah ya raba lafiya,cema Sa'eeda yayi suzo su wuce bayan ya amsa paper wanda zai siya magani daga hannun likita,babu musu ta miƙe a hankali kamar wacca ƙwai ya fashe mata,ita fa tun lokacin da likita ya ce tanada ciki ƙwakwalwarta ta tafi wucin gadi na ɗan wasu sakanni daga baya da ƙwaƙwalwar ta dawo daga shock din da tayi sai kuma ta sake lulawa duniyar tunani,a ranta tana cewa 'Ya Raham ni yau nake da ciki a jikina har na wata biyu da ƴan wasu kwanaki amma na gaza ganewa,wait! Yaushe rabon da nayi period ma,tab! amma anyi hotiho wallahi' takaicin kanta take da rashin gane tanada ciki,ko yawan cin abincin da take wanda ya wuce ƙa'ida ai ya kamata ta gane amma kamar an doɗe mata ƙwaƙwalwar fahimta da nazari.Haka suka fito daga office ɗin zuwa pharmacy don siyan magungunan da likita ya ce su siya saboda zai taimaka mata tare da lafiyar yaron dake cikin,bayan sun siya magani tare da biyan kuɗin,tun a wurin Sadam ya kira Mominsa tare da sanar mata cikin Sa'eeda, wayyo daɗi zo kuga yadda Momin Sadam take farin ciki tare da murnar autanta yana gab da zama *Daddy* miƙa ma Sa'eeda wayar yayi,gaisheta tayi Sa'eeda tana ƙasa da kanta alamun maganar da tayi mata taji kunya,sun daɗe suna waya sannan suka kashe kiran,sai a sannan ne suka nufi motarsu,fita sukayi daga asibitin zuwa wani resturant da Sa'eeda take son abincinsu musamman Amala da ganda,takeaway sukayi sannan ya nufo gida,suna isa gidan bayan sunyi parking har sun shiga falo,Sadam baiyi wata-wata ba ya sunkuceta tare da juyi da ita yana cewa

"My Darling Star,my darling star,ina matuƙar farin ciki sosai da wannan cikin,Allah ya raba lafiya"

Murmushi tayi sannan ta ce

"To sauke ni malam tukunna,yunwa nake ji"

Dariya yayi sannan ya sauketa yana cewa

"Wannan ai dole ne my darling star,kici sosai baby na yayi ƙato"

Kwaɓe fuska tayi tana cewa

"Baby ta zaka ce ba baby na ba,nafison mace"

"A'ah wallahi namiji dai My darling star"

Buɗe mata ledar yayi tare da ciro takeaway ya miƙa mata yana cewa

"A gaskiya ki rage cin wannan baƙar amalar kar yarona ya fita ɗan baƙi"

Turo baki tayi cikin shagwaɓa ta ce

"To to to ni laifina ne,ai yaron yake son amala ba ni ba,tunda nake ban taba cin wannan abincin ba saida nazo gidanka,kaga is not from me just blame your son idan ya fito ɗan baƙi"

"Shikenan ai,let me start calling family and friend su tayamu murna har da momina ta ƴan majali....."

Katse mishi maganar tayi da cewa

"Don Allah ya Sadam karka sanarma Ummina wallahi kunya nake ji,koda ka kira Mom ka sanar mata ɗazu banso hakan ba,naso kawai saidai suji na haihu"

Galala yayi yana kallonta sai can yace

"You're kidding beb wallahi babu wanda bazan kira ba,har da Aunty Sadiya da sauran ƴan uwanmu na ƙasar waje duk yau saina sanar musu,abin farin ciki ya samemu saiki hana in faɗa,hmmm yarinya kina ruwa wallahi"

Ajiye amalar tayi a gefe tana turo baki haɗi da diddire ƙafafunta tana cewa cikin shagwaɓa

"Please karka faɗa musu,uhmm uhmm uhmm,don Allah yayana kaji"

"Naƙi wayon,dama kin cigaba da cin abincinki da yafi miki don bazan canja maganata ba"

Haka ta haƙura tana kallon yadda yake kiran ƴan uwa da abokan arziƙi yana sanar musu har harda abokansa.(Auta Sadam manja wanga terere hadi da rawar kai haka😂😂😂).Har Umman Sa'eeda da su Dr. Nabila ya kira ya sanar musu,sosai suka shiga farin ciki da wannan samun cikin Sa'eeda har da Ummanta duk da tana kawaici.

Tun daga wannan ranar wata sabuwar kulawa haɗi da tattali Sadam ya cigaba da yima Sa'eeda,Mominsa kusan kullun cikin kiransu take taji ya suke da babyn sosai hakan yanama Sa'eeda dadi arai domin tayi sa'ar surika mai so da kaunarta,kullum cikin ci take,ta ce wannan ta ce wancan,Sadam baya gajiya wurin aikawa a siyo mata,ko kuma yaje da kansa,yanzu haka ya rage tafiye-tafiya zuwa ƙasashan waje saboda ita,saida  P.A ɗinsa ya wakilcesa inba taro mai muhimmanci ba na ƴan kasuwa.

Tafiya tayi tafiya,tun ana kwanaki har ankoma satuttuka,yanzu ana kiran watanni,cikin Sa'eeda yanzu haka yana cikin watan haihuwa wanda ana saka ran haihuwa yau ko gobe,cikin ya girma sosai ga kyau da ya ƙara mata,ana cewa ciki na ƙarama mace muni amma ita kyau ya ƙara mata da haske,,domin ta koma kamar wata balarabiyar asali,a scanning ɗin da tayi ance ƴan biyu zata haifa mace da namiji sosai suka ƙara farin ciki tare da siyan kayan haihuwa bibbiyu na mace da namiji,Momin Sadam tayi-tayi akan Sa'eeda ta dawo Kebbi state ko wurin Ummanta ta haihu amma Sadam yaƙi,shi wallahi ba za'a rabashi da matarsa ba,a bari idan ta haihu sai ta koma wanka,haka ta haƙura ta kyalesa don tasan tunda ya cije to da wuya ya bari.

A  ranar laraba Sa'eeda ta  tashi da naƙuda,sosai hankalin Sadam ya tashi,kiran driver yayi a waya don bazai iya tuƙi a yadda yake ba,sunkutarta yayi zuwa mota wanda a lokacin har driver ya iso,ajiyeta yayi a bayan mota sannan ya ƙara komawa ciki don ɗaukar kayan haihuwa wanda komai sun saka a babban basket in case haihuwa ta taso,da sauri ya ɗauko lokacin har driver ya tada motar shi kaɗai yake jirs,asibitin da Sa'eeda take awo suka nufa,a cikin motar sai faman jujjuya kai take tana cije lips dinta da ƙarfi,hannunta ɗaya na ƙugunta ta riƙe,idanunta sai juyi kawai suke,shi kuma Sadam sai faman sannun yake mata,ita ko babu bakin magana sai cije lips,a haka har suka isa asibitin, da sauri nurses suka amsheta zuwa labour room,Sadam yaso binsu amma suka hanashi haka ya haƙura,sai can tunanin kiran Mominsa da Ummanta Sa'eeda ya fado masa a rai,wayarsa ya dauko tare da kiran kowa yana sanar musu akan su sakasu a cikin addua akan Allah yasa Sa'eeda ta haihu lafiya,lokacin da ya kira Dr. Nabila yana sanar mata ai tuni ta rikice tana tambayarsa wani asibiti suke,sanar mata yayi asibitin sai tace gata nan zuwa,kasa zama yayi sai   faman kaikawo  yake a wurin labour room ɗin yana addua kala-kala wanda ni kaina wasu addu'o'in a wurinsa na fara jinsu,ba ayi rabin awa ba saiga Dr. Nabila ta iso asibitin har zuwa inda yake,ko gaisawa basuyi ba ta tambayesa har yanzu bata sauka ba,girgiza mata kai kawai yayi don  a yadda yake bai tunanin zai iya furta mata koda harafi ɗaya ne balle bata amsar tambayar da tayi masa.

A cikin labour room likita mace da nurses biyu ne suke taimaka da Sa'eeda,ta daɗe tana naƙuda har likitar tana niyyar fitowa ta faɗama mijinta ko za'a ba CS ne tunda ta galabaita sosai,babies ɗin ma haka,da wani irin saurin likitar ta koma inda Sa'eeda take ganin har kan yaro ya fito,nurses ɗin suke cemata ta ƙara nishi,ai ko sai da ta matse idanunta gammm! Haɗi da tunkule hannayanta sannan tayi wani irin nishi mai ƙarfi sai gashi cikin hukuncin Allah yaro ya fito,da sauri likita ta yanke cibiyar yaron,wata nurse ta amsashi tare da goge masa jiki da olive oil,ba'ayi mintuna huɗu da fitowar yaron ba sai wata sabuwar naƙuda ta sake rike Sa'eeda, nan ma Allah da ikonsa ƴar mace da fito,maa shaa Allah tabarakallah haka ɗaya nurse ɗin ta amshi yarinyar don ta goge mata jiki bayan likita ta yanke mahaɗar cibiyar,kasancewar da kayan haihuwa suka shigo cikin ɗakin haihuwar kayan sanyi suka saka musu tare da fitowa dasu har wurin mahaifinsu wanda tunda yaji kukan jariri na farko ya koma wurin ƙofar ya tsaya,haka itama Dr. Nabila ta koma idan yake ta tsaya,Momin Sadam da Umman Sa'eeda harda da ƴan uwa da abokan arziƙi sai kiran waya suke don jin ko ta sauka amma shiru,buɗe kofar nurse tayi tare da fitowa ɗaya nurse ɗin na biye da ita,bai ma amsa yaran ba ya jefo musu tambaya akan fatan matarsa tana cikin ƙoshin lafiya babu wata matsala,ce masa sukayi Eh likita na can na ƙara dubata don tabbatar da tana cikin ƙoshin lafiya sannan mu kaita ɗakin hutu,sai a sannan ne ya sauke ajiyar zuciya tare da amsa yaron ita kuma Dr. Nabila ta amshi yarinyar,Woooooow! Haka Sadam ya furta ganin yaronsa mai kama dashi kamar yayi kaki ya tofar,komai na yaron kusan iri ɗaya da nasa,haka a ɓangaren Dr. Nabila bayan ta amshi yarinyar cewa tayi *Fatabarakallahu ahsanal khaliqin*  domin yarinyar kyakkyawa ce ga hanci kamar na mamanta,ganin an fito da Sa'eeda a keken marasa lafiya kowannansu ya dawo hankalinsa tare da bin bayan keken zuwa ɗakin hutu,kwantar da ita nurses din sukayi sai suka fita,Sadam zama yayi akan wata kujera wacca take kusa da gadon,ita kuma Dr Nabila ta zauna a ɗayar kujerar,kowannansu waya ya ciro tare da kiran ƴan uwa da abokan arziƙi suna sanar musu da haihuwa Sa'eeda, sosai kowa yayita farin ciki musamman Momin Sadam da Umman Sa'eeda.Kusan awa ɗaya Sa'eeda ta kwashe tana baccin gajiya,sai daga baya ta farka,bin ɗakin tayi da idanu sai can ta buɗe idanunta tar! Akan Sadam wanda ya tsura mata idanun tun lokacin da ta farka,tashi tayi ta zauna a hankali,Dr. Nabila ce ta dawo kusa da ita tana tambayarta ya jiki,kai kawai ta ɗaga mata sai can yaro ya fara kuka,ai kamar jira ƴar uwarsa take,ita ma ta fara kuka

"Gashi ki bashi mama daman ke yake jira" cewar Sadam yana miƙo mata yaron

Turo baki tayi tare da kin amsar yaron tana cewa

"Nifa yunwa nake ji,haba daga fitowarsa duniya zai fara damuna da ci"

Dariya Dr. Nabila tayi tare da miƙewa da ɗauko flask da sauran kayan abinci wanda mai aikinta ta kawo,tea ta haɗa mata mai kauri tare da miƙa mata,amsa tayi tana mata godiya sai tasha kaɗan sannan ta ɗan ci peppe soup din naman rago wanda Dr. Nabila ta sake miƙo mata shima bada yawa ba.Sai a sannan ne ta amsa yaron sai ta buɗe rigarta ta  ciro nonunta tana saka ma yaron a baki,caraf! Ya amshe tare dayi ma nonon wata iriyar zuka,ai da saura Sa'eeda ta ciro nonon daga bakinsa tana cewa

"Wayyo Allah na!!! Wani irin zuka ne haka"

"Tunda ya barki kinci naki abinci ai saiki barsa ya sha nasa,kinsan ya miki haƙuri shida ƴar uwarsa ko"

"Kai yaronka kawai kasani ko,kasan irin zafin da naji ne sanda ya zuko nonon kuwa"

"Niko ina zan sani,malama yaro yunwa yake ji wai bikiga kuka yake bane"

Turo baki tayi waje tana gunguni sannan ta sake saka mishi nonon a baki.Dr. Nabila sai dariya take musu ganin wanga sabon drama haka, likita ce ta shiga tare da wata nurse tana biye da ita,tambayoyi ta mata akan yadda take jin jikin nata amma sai ta ce Alhamdulilliah cikinta ne yake ɗan mata ciwo shima ba sosai ba,farin ciki likitar tayi tare da cewa yau za'a sallameta tunda lafiyarta ƙalau.A ranar aka sallamesu suka nufo  gida.Washe gari gidan Sadam ya fara cika da masu barka har da babbar yayar Sadam ta iso da wasu ƴan uwansu na Kebbi,Aunty Sadiya sai ana gobe suna zata iso Nigeria,haka ƴan uwa da anokan arziƙi suka yita zuwa barka har zuwa ranar suna.

A ranar suna yaro yaci sunan Daddyn Sadam wato Dauda amma ana kiransa da Ameer ita kuma yarinya taci sunan Momin Sadam amma ana kiranta da Ameera,maa shaa Allah anyi bushasha a sunan,anyi ciye-ciye sosai don raguna bibbiyu aka yanka ma yaran haɗi da shanu babba wanda za'ayi hidimar sunan dashi,gidan ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi,Iman ma tazo sunan wacca ita ma tana da ciki amma ƙarami,Maryam da Rahma duk sunzo sunan,da sauran wa'inda Sa'eeda ke mutunci dasu,Maman jummalo da su Nusaiba sune gaba-gaba a sunan,ƴan uwan Abban Sa'eeda na ƙauye ma sunzo,kai kai in takai ce muku kusan kowa yazo sunan nan,har da su mairo da Na'ima ba'a barsu a baya ba,harda ƴan Abuja,Uwar gayya Sa'eeda tasha kyau ita da yaranta,ta saka kaya sunfi kala shida a  ranar kuma masu tsada,ga gold da ke shiƙi a wuyanta wanda set guda ne Sadam ya siyo mata a Dubai.shima Angon ƙarni ba'a barsa a baya ba yayi kyau sosai.Hakiƙa yaran sunyi goshi don sun samu kyaututtuka da dama wurin ƴan uwa da abokan arziƙi, Momin Sadam da Daddyn Sadam sunyi bajinta sosai don kyautar kamfani suka ma yaran kowanne,ita ma uwar yaran anyi mata kyautar kamfani ɗaya daga wurin Daddyn Sadam. Haka taron suna ya watse kowa ya koma gidansa cikin farin ciki tare da abin arziƙi.

Washe garin ranar Sa'eeda ta koma gidan Ummanta wanka,wanda kusan Sadam bacci ne kadai bayayi a gidan kullum yana nanike da yaransa sai in kuma zaiyi tafiya harkar kasuwancinsa shima ko acan sunayin video call da Sa'eeda tana nuna masa yaransa.Wannan kenan.



        @@ @@@@@@@@@@@


Hausawa suka ce *rana bata ƙarya saidai uwar ɗiya taji kunya*  bikinsu Nusaiba da sauran ƴan uwanta yazo wanda baifi saura kwana uku ba,tuni gida ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi,Umman Sa'eeda ma ta dawo gidan sai bayan biki zata koma gidanta,Sa'eeda kuma tana zuwa ta koma gidan idan yamma tayi ita da nannyn yaranta wanda yaran  sun ɗanyi wato ga kyawunsu sai ƙara fitowa yake maa shaa Allah. Ƴan uwan marigayya Umma Kande na Maiduguri sun iso da ƴan uwan Maman jummalo da ƙauye dana baban jummalo duk sun iso,tuni suma ƴan uwan Abban Sa'eeda suka yada zangonsu a gidan tun ana saura kwana biyar biki suka iso,saboda yanzu suna mutunci sosai da matan Ɗan uwansu ba kamar Umma Kande ba.

Haka akayi biki ba tare da wata matsala ko husuma ba kowa ya koma gidan cike da farin ciki da annashuwa,sannan ko wacce amarya aka kaita gidan mijinta cikin nasara da aminci,babu laifi kowaccansu ta samu gida mai kyau daidai gwargwado.

A ɓangaren zamantakewarsu Umman Sa'eeda da abokiyar zaman Maman jummalo kuwa suna  mutunta junansu musamman ma Maman jummalo wani respect na musamman take ba Umman Sa'eeda sannan duk ranar asabar takan je gidan Umman Sa'eeda ziyara,sun haɗe kansu.Abban Sa'eeda yana jin dadin zama dasu sosai,ga kasuwancinsa sai ƙara bunƙasa yake babu abinda za'a ce sai godiyar Allah.

Amare dai suna sha amarcinsu,kowacce tayi sa'an gidan miji ba kamar mazajensu na baya ba,Nusaiba ma tana zaune lafiya da mijinta harda abokiyar zamanta,baka jin wata matsala a tsakaninsu.

Jummalo ce tana zaune ita da mijinta suna kallon labarai a Tv sai taga  mijin marigayya Zaliha da wasu mutane a court ana shari'ah wanda ita ce ta ƙarshe shari'ar kuma an yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kasamu da akayi da tsafi haɗi da cin naman mutane da auran yara don suyi tsafi dasu saboda suyi kuɗi.Sosai tayi farin ciki da wannan hukuncin da aka ma mijin ƴar uwarta koba komai Allah ya saka ma Zaliha tun a nan duniya,mijinta ne ya tambayeta ta sansu ne take farin ciki da hukuncin da aka yanke musu,ce masa tayi akwai mijin ƴar uwarta Zahila wacca ta rasu a sanadiyarsa tare da bashi labarin irin mutuwar da Zaliha tayi,sosai labarin ya girgiza shi tare da yin Allah shi kyauta ya kuma tsaresu daga son abin duniya.Waya Jummalo ta dauka ta kira Mamanta,Nusaiba,Abbansa Sa'eeda da Iklima tana sanar musu ta hukuncin da aka yanke ma mijin Zaliha,sosai suma sukayi farin ciki da wannan hukuncin, Allah ya sakama Zaliha duk da ta rasu amma mijinta ya girba abinda ya shuka a nan duniya.Wannan kenan.


         @@@@@@@@@@@@ 


A ɓangaren *LOVE BIRDS* 🕊️🕊️ Alhamdulillah kawai zamu iya cewa domin suna zaman lafiya babu wata matsala,sannan akwai kyakkyawan fahimta a tsakanin matan har da miji shima.Ga Aikinsa yana tafiya yadda ya kamata domin Sadam ya kara mishi albashi haɗi da allowances sosai  saboda jajircewan da Sauban yake akan Kamfanin,yanzu ma haka haɗadɗen gida Sauban yake ginawa da Rigachikun wanda har ginin yayi nisa yanaso ya dawo shida iyalinsa gidan.Khairat ma cikin nata ya fara tsufa domin tana a wata na takwas,ita kuma Maryam na rainon ƴarta wacca har tayi wayo ta fara tafiya.Wannan kenan.


          @@@@@@@@@@@@@@


*KAUYEN DAMARI*


A ɓangaren su  Gwaggo Ladi da Baba komai yana tafiya a yadda ya kamata saidai tsufan ta sukayi wanda yanzu haka Baba baida wata isassar lafiya,Uncle Hassan da Umman Sa'eeda sunzo sun dubashi don har asibiti suka kaishi amma jikin yaƙi haka suka dawo dashi gida tare da magungunan da zai sha sai suka koma.


Ƴar yaya dai tana nan tana shan wuya domin susar nan babu fashi,duk ilahirin jikinta ya lalace ko'ina ciwo ne saboda susar da take.


Su mairo da Na'ima sai juya jarin da Umman Sa'eeda ta basu suke,gashi sana'arsu ta karɓu sosai.suna cikin kwanciyar hankali da ƙoshin lafiya wannan kenan.


         @ @@@@@@@@@@


*BAYAN SHEKARA BIYU*


a wa'innan shekarun abubuwa da dama sun faru musamman rasuwar da a kaita yi,a ciki Baba Garba na Kebbi  a wa'innan shekarun biyu ya rasu bayan yayi jinyar wata ɗaya,haka Baba na ƙauyan Damari Allah yayi masa cikawa shima,haka ƴar yaya lokaci yayi itama.


A ɓangaren  kasuwancin Sadam sosai yake ƙara bunƙasa ciki da wajen Nigeria don yanzu yana daya daga cikin matasa masu kuɗi a Nigeria,ga matarsa Sa'eeda tana ƙara inganta companies nata guda biyu wanda ƙara habbaka suke sosai.Umman Sa'eeda ma Uncle Hassan yanata juya mata dukiyarta kuma babu laifi dukiya tana ta bunƙasa,ribar direct take shiga account ɗinta.

Abban Sa'eeda ma kasuwancinsa ya ƙara bunƙasa don yanzu shagunansa biyu wanda yake cike da kayan sawa.Rayuwarsu Nusaiba da sauran ƴan uwanta a gidan mazajensu babu laifi suna cikin kwanciyar hankali da wadata domin a shekarun biyu kowaccansu Allah ya bata haihuwa.Kai kai kai in taƙai ce muku a gaskiya komai na rayuwar wa'innan bayan Allah ya sauya.

Gwaggo Ladi tsufa yazo mata sosai don yanzu ƴar aikin take komai a gidan saidai idan su Mairo sun zo gaisheta suka yin wasu aikace-aikacan,suma suna zaman lafiya da mazajensu ga kasuwancinsu a gefe yana ƙara bunƙasa tun jarin da Umman Sa'eeda ta basu.


         @@@@@@@@@@@


A ɓangaren su Sauban tun a shekarar baya ya koma sabon gidansa da matansa,wanda har Khairat ta haihu ta haifi ɗa namiji wanda yaci sunan mahaifin Sauban,ita kuma Maryam har ta yaye ƴarta yanzu tana da ciki ƙarami.Sannan har yanzu suna mutunci da Sa'eeda sosai kuma suna ziyartar junansu.Wannan kenan.


        @@@@@@@@@@@@@


Kasancewar yau Asabar ranar hutu,a yau Sa'eeda ta shirya ita da yaranta zuwa gidan Ummanta don ziyara,wanda har ta yayesu amma bata da ciki.

Suna zaune Ameer da Ameera na   guje-guje a falon sai Umman Sa'eeda ta dubi ƴarta tace

"Sanyin Idaniyata idan na tuna da rayuwar da mukayi baya sai naga abun kamar a mafarki"

Murmushi Sa'eeda tayi sannan ta ce

"Wallahi kuwa,koni nakan tuna rayuwarmu ta baya,yau mu ne a cikin daula haɗi da farin ciki"

"Sosai kuwa Sanyi idaniyata,Allah kenan mai canja abinda yaso a lokacin yaso,kamar bani nayi wankau na kayan mutane tare da sharar titi a baya ba" cewar Umman Sa'eeda tana kai fruit salad wanda yaji kayan haɗi a bakinta.

"Rayuwa kenan gashi duk abubuwan da suka faru damu a baya sun zamo mana labari daman hausawa sunce *MAHAƘURCI MAWADACI*  sannan suka ƙara da cewa *MAI HAƘURI KE DAFA DUTSE HAR YASHA ROMANSA* gashi munyi haƙuri da tawakalli a lokacin da muke cikin tsanani ya wahala,sannan mun dogara ga Allah haɗi da jajircewa,yanzu Allah ya kawo mana mafita haɗi da jin daɗi"

"Wannan haka yake sanyin idaniyata,kema kin cika alƙawarin da kikamin a baya akan zaki a jirjice kuma ki na ce akan karatunki gashi yanzu *NACINKI YA JAWO MANA NASARA A RAYUWA* kin maida hankalinki a karatunki wanda sanadiyar haka Ubangiji ya kawo mana sauyi a rayuwarmu baki ɗaya tare da haɗamu da ahalinmu"

Kiran su Ameer Sa'eeda tayi saboda guje-gujen da suke yayi yawa,natsar dasu tayi sannan ta maida hankalinta ga Ummanta tana cewa

"Ummina bayan *Nacina da jajircewata* ai har da taimakonki,domin kece *Gadon bayan duk wata nasarata a rayuwa" koda nike da naci a karatu idan baki jajirce wurin biyamin kuɗin karatu ba taya zan kai ga gaci,kece kika ɗau wahaloli da dama wurin inganta rayuwata Ummina,ina matukat lafahari da samunki a matsayin uwata"

Faɗada murmushi Umman Sa'eeda tayi jin yadda ɗiyarta ke yabonta sannan ta ce

"Tabbas da taimakona haɗi da jajircewata amma da baki nace akan karatunki ba taya zan samu ƙwarin gwiwar biya miki kuɗin karatunki,kinga kema kin taka muhimmiyar rawa"

"Haka ne Ummina tabbas *NACINA YA JAWO MIN NASARORI DA DAMA A RAYUWATA HAR DA TAKI UMMINA* Allah yayi mana jagora yasa mu dace duniya da lahira"

"Ameen ya Hayyu ya Qayyum,Allah ya iya mana"

Haka suka cigaba da hira sai yamma Sa'eeda ta ɗauki yaranta cikin zazzafar motar sabuwa land Rover suka wuce gida.

Lokacin da suka dawo gida Sadam bai riga da yashigo gida ba,direct ta nufi kitchen haɗi girka musu lafiyayyan dinner wanda sai bayan magrib ta kammala girkin,wanka tayi ita da yaran sannan tayi sallar magrib,bayan ta kammala sallah sannan ta ɗauko food warmer ɗin da ta zuba abinci ta kawosu dinning room tare da jerasu a dining table sannan ta wuce sama don shiryawa don tarbar mai gidanta.


Sai bayan Isha'i Sadam ya dawo gida wanda lokacin har Sa'eeda ta shirya cikin rantsattsan English wear riga milk colour da wando pencil  baƙi wanda ya mata chif! A jiki,gashinta ta bazo dashi waje wanda yasha gyara sai tashin ƙamshi yake,yaran suma bata barsu a baya ba,kwalliya sosai ta musu wanda idan ga gansu zakayi tunani unguwa zasu je,haka dukkaninsu suka wuce dining area.Jollof din taliya tayi wanda taji kifi da kayan lambu sai tashin ƙamshi girkin yake.Sosai Sadam ya baje haɗi da lodama cikinsa,yaranma sunci sosai tare da shan Apple and banana juice wanda Sa'eeda ta haɗa da kanta.

Bayan sun kammala cin abinci suka dawo falo tare da kunna TV suna kallo haɗi da hira har yaran sukayi bacci.Sadam ne ya kai yaran ɗakinsu tare da yi musu adduar bacci sannan ya dawo falon.

Kujerar da take ya zauna tare da rugumota yana mata raɗa kunne yana cewa


"My darling star ya kamata kiyi ma su Ameer ƙanne fa,kinga Kamal yanzu haihuwarsa biyu sannan Sadiq ma haihuwarsa biya,mu ne kawai mukayi ɗaya"

Ɗagowa tayi tana kallonsa sai ta ce


"Kai Ya Sadam yaushe su Ameer sukayi wayo da zanyi musu ƙanne bama ƙani ba"


Sake matseta yayi a jikinsa sannan yace 

"Ki yarda yau kawai nayi farautan ƴan ukuu......."


Ai da wani irin sauri Sa'eeda ta cire hannayan Sadam daga jikin tana ƙare masa kallo da cewa

"Naƙi wayon da yake ba kai zaka haihun ba sannan bakasan wahalar naƙuda ba,mai wayo kawai"

Miƙewa tayi ta ruga da gudu zuwa sama,binta yayi da kallo yana dariya sai can ya miƙe tare da nufar ƙofar falon ya kulle,sannan ya kashe bulbs din falon complete har kitchen sai ya haura saman shima,bedroom ya wuce tare da kashe musu wutar ɗakin.Ni kuma tunda naga an kashe wutar ɗakin sai na tayasu jayo ƙofar ɗakin tare da  yi musu fatan zuri'ah masu albarkha.

TAMMAT BI HAMDULILLAH 

Mu haɗu a wani ƙayataccen littafina FREE BOOK mai suna BA NI DA MADOGARA. Zai zo muku immediately bayan wannan in shaa Allah. Taku har kullum NARRNARHH BUKAR MAI ALƘALAMIN BAN MAMAKI*



*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.