Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Rukayyat · RIKON KA'KA

RIKON KAKA

By 

Rukayyat (Rukyelmuaz)

YOUNG TALENT ASSOCIATION WRITER'S (YOTA)

Book 1

Chapter 10

FLASH BACK 

WASU SHEKARU DA SUKA GABATA(1907)

Malam Sule mai almajirai ya kasance Malami ne mai tarin almajira a garin Batsari saboda yawan almajiran da yake da su da ƙyar ka ambaci sunan shi bakasamu wanda ya san shi ba. Almajira kuwa har daga makwaftan ƙasashenmu ana kawo yara almajiranci.

Malam Sule ya kasance Yana da mata biyu Ramu uwar gida Badiyya amarya sai dai duka matan duk wacce ta haihu yaran basa zama komawa suke .

Kullum cikin rokon Allah ya bashi zuri'a mai albarka wacce zaiyi alfahari da su ya ke. 

Rayuwa tanata tafiya kullum cikin aikin karantarwar shi ya ke bai cire ran wata rana zaiga gudan jinin shi a duniya ba.

Zaman Ramu da Badiyya gwanin sha'awa zaka rantse ba kishiya da kishiya bane kamar wasu aminan juna ne.

Kullum cikin hidimtawa almajirai suke domin su da kansu suke girki a zubama almajirai, don Malam Sule almajiran shi basa bara saidai in yaro kunnan ƙashi gare shi.

Ya kan haɗa da abin da iyayen yara suka kawo da Kuma abinda ya noma dasu ake anfani a sarrafa.

Hakan ya saka wasu daga cikin almajiran nashi Baba suke kiran shi wasu suce Baba Malam.

Manyan almajiran da sukayi hadda da kanshi yake fara kaisu gurin koyan sana'a, wanda hakan yasa mafi akasarin manyan almajiran shi suna taimakawa sosai gurin bada gudun mawa na ciyar da sauran almajirai.

Wata ranar litinin da safe hantsi ya fara fitowa almajiran nata karatu kowa ya ɗauki allo masu biya karatu nayi masu rubutu nayi wasu na gaban Malam yana duba musu allo wani ba'agadez yazo da ƙaramin yaro kyakkyawa sumar kanshi baƙa ce wuluk ta kwanta a kan shi anyi mishi gayu da wani yadi riga da ban wando da ban gashi kayan sunyi masa yawa da gani bashi kwancan kayan akayi.

Gurin da Malam Sule ke zaune ya nufa da yaron ganin shi ya sa Malam Sule sallamar almajiran shi da ke kusa da shi. Yaba wannan Ba'agadez ɗin damar zama akan sallayar dake kusa da shi yaron na tsaye rungume da Ghana masgo. Malam Sule ya ce. "Yarona samu guri ka zauna can gefe ka ji"

Gurin da zai zauna ya nuna masa baiyi musu ba ya je ya samu guri ya zauna nesa da su.

Wannan Ba'agadez ɗin yace sunana Mahi ni ɗan Niger ne ya yi ma Malam Sule baya ni akan ce wa. Shifa ya kawo yaron shi makaranta ne amma baya son a barshi yazo gida da kan shi zai zo ya maidashi a duk lokacin da aka samu hutu.

Malam Sule ya ce babu damuwa amma zanyi ma wasu tambayoyi tukunnan ina son amsar su.

"Wannan yaro shekaran shi nawa? Kaine mahaifin shi meye sunan shi?"

"A wani gari kuke mai ya sa ka zabi kawo shi almajiranci me ye sunan ɗalibin?"

"Shekaran shi goma ne ina son ya hadda ce alqur'ani mai girma sunan shi Ahmad Basam Mahi."

" Nine mahaifin shi ni Tuareg Agadez ne"

Sai dai niɗin ba mazauni ba ne ina tafiya cira ni a kai a kai bana son rashina kusa dashi yasa ya fara bin yaran da basu da tarbiyya."

Malam Sule ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Ina mahaifiyar shi?"

"Allah ya yi mata rasuwa tun yana jinjiri"

Ya ba Malam amsa cikin fuskar tausayi idonshi ya kawo ƙwalla.

"Shikenan, amma kasani ci da shayarwar duk yana kan mahaifi ne."

Malam Sule ya faɗawa Mahaifin yaron

"Babu damuwa Malam duk zan iya ɗauka."

"Ya sunan yaron ka ce?"

"Sunan shi Ahmed Basam Mahi"

A haka suka gama komi da wannan Ba'agadez ɗin gashi babu waya bare ya amsa number ɗin shi domin jin buƙatun yaron shi da lafiyar shi zai tafi ya ciro kuɗin ya bayar da wani ƙaramar sarka yace gashi na yaron ne a aje mishi kar a bashi a hannun shi saboda zai iya salwantar wa.

Kuɗi masu yawa ya bada wanda za'a ringa kula da Ahmad kafin ya sake dawowa ya yi sallama ya tafi.

Tun daga wannan ranar bai sake waiwayar yaron da ya kawo almajiranci ba.

Har Ahmad ya kusan sauke Alqur'ani ya yi girma don yanzu ya kusa shekara sha biyar 

Kyaun shi da wayon shi duk sun bayyana Malam Sule ya maida shi tamkar yaron da ya haifa Ahmad bai nemi komi ya rasa ba a rayuwa don har makaranta ya ke tura shi wasu garuruwan don ƙarin ilimi Badiyya ke kula da shi kamar ɗanta na cikinta har ya fara kiran ta da mama ita ce ta hana shi don ita a tunanin ta ko yau she za'a iya raba ta da shi gwara karya saba ma ta domin a duk lokacin da aka raba su zata ji ƙunar abun fiye da kima.

Ahmad baya iya cin abu bai kawo ma Badiyya ba Allah ya saka mishi tausayin ta da son ta a zuciyar shi.

Badiyya na zaune a kitchen tana girkin abincin rana taji zuciyarta na tashi ta fita da gudu daga kitchen ɗin ta fara amai hakan yasa sai dai Ramu ce ta amshi girkin ta yi.

Tun daga wannan lokacin ta ɗau lokaci mai tsayi bata son ƙamshin komi wannan dalilin ya sa Ramu ce ta ke girkin gida ganin abun na Badiyya ƙara gaba yake hakan ya saka Malam Sule ya ce Ramu ta raka Badiyya su je asibiti bayan sunje asibiti aka tabbatar Badiyya na da ciki har na wata ukku.

Ramu ta yi farin ciki kamar ita ce ke da cikin haka a ɓarayin Malam Sule ya yi farin ciki sosai. 

Tunda Ahmad ya san Badiyya na da ciki ya ke murna za'a yi mishi ƙanwa.

Haka suka ci gaba da rainon cikin tare Ramu ta bata kulawa Malam Sule ya ba ta kulawa komi basa son ya samu Badiyya.

Cikin ya shiga watannin haihuwa wata ranar Litinin Badiyya ta tashi da ciwon mara sosai hakan ya saka Malam Sule ya ce kar ayi wasa a tafi asibiti suna isa aka ce haihuwa ce amma bazata iya haihuwa da kan ta ba dole ayi ma ta aiki ana buƙatar Malam Sule ya saka hannun an yi komi an gama za'a shiga da ita operation room ta ce a tsaya ta na da magana da Malam da Ramu babu gaddama aka kira ma ta su bayan sun zo ne Badiyya ta fara magana..

"Malam ko da ace rai ya yi halin shi don Allah ku yafe min ban sani ba ko zamu sake zama tare da ku"
"Ni dai na yafe muku duk da baku yi min laifin komi ba amma ko tsakanin harshe da haƙori ana samun matsala ko akasi" 
"Sannan ko da ace ban samu damar fitowa ba in har abinda ke cikina ya rayu don Allah kar aba kowa yarona na ba Ramu ita nike son ta kulamin da abinda na haifa ta bashi tarbiyya irin wacce uwa ta ke ba yaronta"

Dukan su jikin su ya yi sanyi Malam ya kasa magana tasbihi kawai ya ke daurewa ya ke zuciyarshi karyewa ta ke tunani da ban da ban su na zuwa cikin kwakwalwar shi amma bayada damar hana su tambayoyi da dama sun zo zuciyarshi amma ba ya da amsar su.

Ramu ta fa ra hawaye jikinta duk ya yi sanyi duk wa ta walwalarta da annashuwa sun ɓace daga fuskarta.

"Wace irin magana kike yi waye ya ce miki mutuwa za kiyi zaki dawo mucigaba da rayuwa mu raini abinda zaki haifa"

Ramu tayi maganar tana share hawayen da ke zubowa da ga fuskarta.

"Ni dai don Allah ku ce kun yafe min"

"Na yafe miki wallahi bakimin laifin komi ba ko da kinyi min na yafe miki"

"Nagode sosai Ramu. Malam kai ba zaka yafe min ba?"

"Na yafe miki Badiyya"

"Nagode Malam in mace na haifa sunanta Hafsat don Allah ku sa ma ta wannan sunan na roƙi wannan alfarmar tun inada rai"

Tana kaiwa nan aka shiga da ita ciki an ɗauki lokaci kafin wutar ɗakin ta mutu alamar angama aikin. Badiyya ta haihu ɗiya mace amma saidai a wannan karon Allah baisa taga abinda ta haifa ba.

Ramu tafi kowa shiga damuwa duk maganar da Badiyya tayi mu su ta dinga dawo ma ta ashe dama wasiyya ta ke bar musu.

Lokacin da Badiyya ta rasu Ahmad baya gari Malam ya tura shi ƙaro karatu Barno bayan ya dawo ya samu labarin rasuwar ta Ahmad ya shiga cikin wani halin tashin hankali duk rayuwarsa ta canja ta zama sai a hankali har ciwo saida ya kwanta kullum yana gurin Hafsat ko da kuwa da rarrafe ne bazai iya kwana bai ganta ba.

Kamar yanda Badiyya ta bar wasiyya haka aka yi aka ba Ramu ɗiyar da ta haifa aka saka ma ta suna Hafsat kamar yanda Mahaifiyarta ta ne ma.

Allah ya raya musu ita soyayya suke nuna ma ta sosai kullum Malam Sule cikin yi ma ta siyayya ya ke wani lokacin tana zaune a gefen shi ya ke karantar da almajiran shi.

Tana da shekara bakwai Ramu ta roki Malam da ya kai Hafsat makarantar waje tunda a gida bata maida hankali ya ce sam bazai kai ƴar shi mace wani guri makaranta ba dole babu yanda ta iya haka ta kyale shi Hafsat taci gaba da karatu a makarantar malam.

Ahmed Basam Mahi.

Ya zama ɗan gayu kyakkyawan saurayi ƴan mata duk inda ya shiga ana crushing ɗin shi kamannin shi da ƴan Agadez duk ta sake bayyana ga tsayi ga fari sumar kanshi baƙa ce duk yanda za'a siffanta mai kyau to tabbas yana cikin masu kyau.

Duk lokacin da ya samu hutu yana garin Batsari to yana tare da Hafsat duk soyayyar da yake ma Mahaifiyarta gaba ɗaya ta dawo kanta in zai dawo daga wani garin da ya je tsaraba yake ma ta sosai ya ɗauketa kamar wani nauyi a gare shi wanda ya zama dole ya kula da shi ko ya sauke shi.

Hafsat ta zama budurwa yanzu tana cikin shekara ta goma sha bakwai Ahmad da Hafsat suna zaune suna fira a tsakar gida Ramu ta fito rike da buhu an zuba masara a ciki.

"Ke Hafsat zo ki kai surfe don yau almajiran nan kamar anyi ruwa an ɗauke kinga duk basu shigo ba."

"A'a Inna Ramu kawo ni in je kai Malam Baba baya son tana yawan fita"

"Malam Baba baya so?" Ko dai baka so kun sangarta yarinya, gashinan don Allah ka ba yaro kai ma ba sai kaje da kan ka ba"

Amsar buhun Ahmad ya yi ya fita, ba'a jima ba ya dawo ya kawo ma ta,

"Assalamualaikum warahamatullah"

Sallamar Malam sukaji hakan yasa dukan su suka waiga da fara'a ya ida so zuwa in da suke.

Kai Ahmad ka same ni a soro yanzu babu musu ya bi bayan Malam yana zuwa suka iske taron muta ne Malam ya ce. "Zauna" Ahmad ya samu guri ya zauna Malam ya kalli muta nan da ke zaune a gurin ya ce "Abinda yasa na tara wannan muta nan ina son su zama shaida ni Malam Sule na ba Ahmad Basam Mahi auren ɗiyata Hafsat"
"Amma akan sharaɗi in ya amince da auren in kuma bai amince ba ya yi magana ba za'ayi mishi dole ba"

Kan Ahmad yana ƙasa yama kasa fahimtar wai shi Ahmad ɗin Malam ya ke nufi yama kasa ɗago ido ya kalli Malam to taya hakan zata kasance dama ana aure haka ne ta ya za'a zo da irin wannan maganar a wannan lokacin wannan ba abu bane da hankali zai ɗauka auren wasan yara ne da kawai rana tsaka za'a zo ace ma mutum za'a mishi aure

"Ahmad da kai ake magana kayi shiru ko baka ji maganar da akeyi ba?"

Muryan Malam Sule ya dawo da shi daga saƙar zucin da ya ke

"Na'am Malam me kace"

"Ka amince da auren ko baka amince ba?"


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.