Free chapter · Read without an account
THE BEGINNING
WhatsApp: ***
TikTok: The_unnamed_writers
Instagram: The_unnamed_writers
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيمِ
اللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِي هَذِهِ الْقِصَّةِ، وَاجْعَلْ فِيهَا خَيْرًا وَنُورًا وَعِبْرَةً، وَافْتَحْ لَنَا بِهَا أَبْوَابَ الْفَهْمِ وَالْحِكْمَةِ.
اللَّهُمَّ اجْعَلْ كُلَّ كَلِمَةٍ فِيهَا سَبَبًا لِلْخَيْرِ، وَكُلَّ صَفْحَةٍ فِيهَا تَذْكِيرًا بِأَنَّ مَا كَتَبْتَهُ لَنَا لَا يُخْطِئُنَا، وَمَا لَمْ تَكْتُبْهُ لَنَا لَا يُصِيبُنَا.
رَبَّنَا افْتَحْ لَنَا أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ، وَبَارِكْ فِي هَذَا الْعَمَلِ، وَاجْعَلْهُ خَالِصًا لِوَجْهِكَ الْكَرِيمِ.
آمِين يَا رَبَّ الْعَالَمِينَ 🤲🏽
Da sunan Allah, Mai yawan rahama, Mai jin ƙai
Ya Allah, ka sanya albarka a cikin wannan labari, Ka sanya alheri, haske da darasi a cikinsa, Ka buɗe mana ƙofofin fahimta da hikima ta hanyarsa.
Ya Allah, Ka sanya kowace kalma a cikinsa ta zama sanadin alheri, kuma kowane shafi ya zama tunatarwa cewa abin da Ka ƙaddara mana ba zai taɓa wuce mu ba, kuma abin da ba Ka ƙaddara mana ba ba zai taɓa samun mu ba.
Ya Ubangijinmu, Ka buɗe mana ƙofofin rahamarka, Ka sanya albarka a cikin wannan aiki, Ka kuma sanya shi tsarkakakke domin neman yardarka
KIRAN QADDARA🔥
By: The Unnamed Writers
Chapter 1: THE BEGINNING
PROLOGUE
Gudu takeyi iya qarfin ta, bata sanin inda take jefa kafarta kamar yadda bata ganin gabanta saboda duhu, batasan inda ta dosa ba, kawai addua takeyi Allah ya kubutar da ita kafin azzaluman mutanen da take hannunsu su gane chewa ta gudu, bata ankara be jin tayi ta bugu da wani abu me mugun qarfi kamar icce, seda tayo baya ta fadi qasa da qarfi, lalabawa tayi ta sake miqewa tsaye da qyar saboda yadda gabadaya qafafunta ke ciwo tun daga saman su har zuwa tafin qafar da ta tattaka qayoyi mara adadi sakamakon rashin takalmi a qafar ta, gudun ta chigaba da yi amma ba da sauri ba saboda karfinta da ya fara qarewa da kuma wani irin jiri da ke neman kayar da ita, chan taji muryoyi daga dan nesa kadan “bata isa yin nisa ba tunda akwai duhu kuma batasan hanya ba, ku dudduba ko’ina ku haska fitila dakyau, da zarar muka rasata oga baze chika muna kuddin mu ba”
Ai tanajin haka batasan inda ta sake samo wani qarfi ba ta chigaba da gudun iya ranta, idan batayi qarya ba se tache ma kafin dayar kafar ta sauka qasa take qara daga dayar, batasan ya akayi ba kwatsan taji ta dena taka ciyayi da yashi da qayoyi, kamar kafafunta na sauka akan titi, kafin ta samu damar rage gudunta ta Kalli inda take takawa se wata irin qara taji kamar ana danna horn din mota se kuma taji wani irin qiiiiiiii a kunnuwanta, bata ankara ba taji wani abu ya bugeta seda ta tashi sama sannan ta fado qasa, idanunta suka fara lumshewa a hnkali amma kafin ta qarasa rufesu taji kamar inuwar mutane a kanta da muryoyi.
Sokoto.
Rana ta fara faduwa amma zafin ranar har yanzu yana nan sakamakon wani irin zafi da akeyi a garin, a cikin wani Qaramin daki Maryam che a zaune a gefen karamin gadonta, goshinta na kyalli alamar zufa, a hannunta tana riƙe da wasu tsofaffin hotuna.
Ta qura ma hoto daya ido tanata kallo, A cikin hoton, Maryam ce wadda bata wuce shekara huɗu ba a lokacin, Kumatunta cike suke amma sun lotsa kadan saboda dariyar da takeyi, an raba gashinta gida biyu an ɗaure mata shi da ƙananan ribbon, fuskar ta dauke da murmushin yarinyar da ba ta san komai game da duniya ba, very free and innocent.
A bayanta kuma yayarta Aisha ce, Aisha ta fi ta girma sosai, wadda zatayi shekara goma a lokacin. Hannunta ɗaya yana zagaye da wuyan ƙaramar Maryam, tana riƙe da ita kamar za’a kwache mata ita, fuskar ta dauke da tsantsar farin cikin yanayin da suke ciki, dukda qanqantar shekarun Maryam a lokacin, zaka gane tsantsar kamar da ke tsakaninta da yar uwar ta, sedai banbancin haske don maryam din tafi Aisha hasken fata.
Maryam ta yi murmushi a hankali, Baza ta iya tuna ranar da aka ɗauki hoton ba.
Amma Aisha…
Tana iya tuna yanayin da ta tsinchi kanta a ciki lokacin da akache Aisha ta bache.. tana tuna yadda Aisha take ɗaukar ta duk inda za ta, yadda idan wani abu ya tsorata ta, Aisha take zaunawa kusa da ita tana lallashin ta, yadda Aisha take ɓoye mata nata naman miya ta bata a boye idan sun gama chin abincin, yadda take tsawatar wa duk wanda ya sata kuka.
A wurin Maryam, Aisha ba ’yar uwa kawai ba ce, ta kasance kusan komai, Yar uwa, Mai kare ta, Abokiyar hira, abokiyar shawara, tabbas irin soyayyar da shaquwa da ke tsakaninsu ba qarama bache
Maryam ta juya hoton se ga wani, Aisha ta fi girma a wannan, Sai wani hoto, Sai wani kuma, A hankali ta shimfiɗa hotunan a kan gadonta tana kallo tana hawaye har Idonta ya tsaya akan wani hoto, University graduation din Aisha ne.
Aisha tana tsaye cikin rigar graduation, tana murmushi cikin farin ciki, Mama kuma tana gefenta, Maryam ta tuna ranar. Ranar tafi Aisha farin ciki, Ta tuna yadda ta rungume Aisha tana chewa watarana zaki aramin rigar nan insa inyi hoto nima. Aisha ta yi dariya sannan tache “Allah ya nuna min ranar da zaki fara daukar karatu serious maryama”
Maryam ta yi murmushi da tunanin wannan magana. Amma murmushin ya ɓace a hankali.
Yatsunta suka tsaya kan wani hoto, a nan kam
Aisha ta qara kyau, ga wani irin confidence a Idonta, Ta girma, Ta canza.
A lokacin ne kuma abubuwa suka fara sauyawa.
Bayan Aisha ta gama jami’a, ta samu aiki a matsayin administrative officer a wani babban kamfani mai suna Northern Crest Holdings, sokoto branch dinsu, kamfanin da ke harkar gine-gine, filaye da gidaje, da kuma harkar noma.
Maryam Tayi matuqar murna da wannan aikin da yar uwarta ta samu, mama kam sam bataso Aisha Tayi aiki da wannan kampanin ba saboda a Chan baban su yayi aiki kuma a qarshe abin be qare dakyau ba, har rayuwa ta fara chanja musu, Saboda Aisha ta dauke ma mama kaso 70 bisa 100 da harakar kula da gida, kuma ta tsaya tsayin daka akan karatun maryam.
Amma kafin a rufe shekara daya abubuwa suka fara sauyawa, Aisha ta fara zaunawa tayi shuru kamar me tunani, damuwa ta fara bayyana a fuskar ta, Wani lokaci Maryam za ta zauna kusa da ita tayita mata magana na tsawon mintuna, kafin daga baya ta gane cewa Aisha ba ta ji ko kalma ɗaya daga cikin abin da take fadi ba, Wani lokacin wayarta za ta yi ƙara, sai kawai ta tashi ta fita daga ɗakin wanda sam ba haka suka saba ba, bata saba boye ma maryam komi gameda rayuwar ta ba, lokuta da dama Maryam za ta tambaye ta:
“Aisha, mi anka miki?” “Ko dai Harynzu tunanin baba na yaqi fita kan ki? Muyi hankuri mu dai munsan halin babanmu hiye da kowa munsan abinda ze iya yi da wanda be yi, watarana gaskiya zata hito kiyi hankuri mu bamma Allah komi”
Aisha kuma sai dai tayi murmushi.
“Babu komi Maryam, kakki damu”
Amma akwai wani abu, Maryam ta sani. Tabbas akwae abunda ke damun yar uwar tata amma abunda ba ta sani ba shi ne menene?. Maganar baban nasu che ko wani abu daban?
Sai wata rana… kwatsam
Akache Aisha ta ɓace.
Ba wani bayani.
Ba bankwana
Kawai…Wai ta bache..se kache wasu takalmi
Maryam tayi kuka, Tayi bakin ciki ta fita daga hayyacin ta har ta kwanta ciwo me tsanani seda mama ta tashi tsaye akanta tunda dai ynzu ita kadai che ta rage gabanta kar itama ta rasa ta, Maryam dai tasa ma kanta dangana daga baya, amma bata yadda da ake chewa wai qila Aisha ta rasu ba, ta lura mamansu ma ta yadda chewa Aisha ta rasu in ba haka ba ai da ta dawo gida, amma maryam naji a jikinta Aisha tana raye.
Kwanaki sun wuce, watanni ma haka har aka fara lissafin Shekaru, amma Maryam ta kasa yarda cewa Aisha ta rasu, Ta kasa yadda chewa Aisha zata tafi tabarta bayan ta saba mata da rayuwa da ita, kuma itama Aishar batada kowa se su kadai, ta kasa yarda da duk shaquwarsu Aisha zata tafi ta barta, dole akwae dalili, dole akwae wani abu da ya faru kuma tana da tabbacin tana raye in shaa Allah.
Ta share hawayen da suka zubo mata,Wasu suka sake gangarowa, Da sauri ta share su Sai ta ji muryar Mama daga waje cikin hausar su ta sakkwatawa tana yimata magana
“Meramu!”
Maryam ba ta amsa ba, saboda tana qoqarin gyara muryarta da fuskarta da duk hawaye suka bata
“Meramu! Kina ina? Taho kiyi min chehwane, sannan ki shirya ki tahi wankin amaryar ko kin hwasa zuwa?”
Ta ja numfashi, ta fara tattara hotunan da ke kan gadon, Sannan ta ansa
“Gani nan tahe Mama!”
“Kina tahowa ki yimin chehwanen Ko sai na iskoki ɗakin? ke zahi be ma damun ki kullun kina daki se kace Amaryar kunshe”
Maryam ta sake kallon hoton hannunta Na ɗan lokaci, ta yi shuru hotuna mabanbanta na haskowa a kwakwalwar ta, suna qara zuwa mata cikin kai, sannan ta saka hotunan a hankali cikin drawer, kamar me bankwana da su
Ta miƙe ta fito tanata chewa “mama yi hankuri gyaran daki na nikae, gani”
“To kina sawo min ko sena aiki wani?”
“Aa mama gani, dami dami zaa sawo miki?” Maryam ta fada tana murmushi dan sake boye damuwar fuskar ta dan kar mama ta lura da yau ma tayi kuka.
Mama ta ɗauko kuɗi ta ɗora su a tafin hannun Maryam.
“Ga shi nan, Ki sayo min tattasai na 300, Tarugu na 200 Albasa kuma ta 300 sanna ki sawo min garin kuka ta 200”
Maryam ta kalli Mama ta zumburo baki wanda hakan kamar dabi’artane
“Haba, Mama! Yau ma miyar kaďi zakiyi muna?”
Mama ta ɗago kai tare da hararar ta “in baki ci ki bari ae babu dole”
“A’a, inaci mama”
“To ki yi maza ki dawo kin san kinada biki ko?”
“Toh .” Maryam tache sannan ta miqe ta saka takalmi ta fita, a hankali take tafiya har ta isa yar kasuwar unguwar su, Ta sayi tattasai, tarugu, albasa, da garin kuka, sannan ta dauki hanyar zuwa gida, a hanyar ta hadu da imran suka gaisa “mama ta aiko ki hala?”
“Eh amma na qare zan koma gida ne”
“Toh hau muje nima na qare kai saqunan yau, gida zan tahi ynzu”, imran maqocin su ne yana harkar delivery yana taimaka ma iyayen shi, kuma duk cikin samarin da ke tururuwar yima maryam Zanchen soyayya shi kadai take magana dashi, shima saboda kirkin shi da kuma yadda mahaifiyar shi ke mutunci da mama
Lokacin da imran ya sauke Maryam kofar gidan su ta shigo cikin gida, rana ta fara karkata zuwa yamma.
Ta miƙa wa Mama kayan.
“Gasu mama”
Mama ta qarba tareda bude ledar
“Kin sawo komi da komi ko?”
“Awo mama bude ki gani”
“Toh Sannu Allah yayi albarka”
“Amin amma ki bari in dawo se in tuqa tuwon banson kina wahala”
Mama Tayi murmushi tana Jin qaunar yar tata sam maryam bata son tana aikin wahala.
Daga nan Maryam ta yi sauri ta shiga ɗakinta ta cire kayan jikin ta daura Zane ta shiga toilet, Tayi wanka ta fara shiryawa cikin sauri sauri saboda lokaci ya fara qure mata, Kuma imran yache in ta shirya ta kirashi ya ajeta wurin bikin, Ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗan tsaya tana kallon kayan da ke ciki kafin ta dauko ankon su na yammatan amarya ta saka, ta tsaya gaban madubi tana duba abunda zata dan yima fuskarta dan ita ba gwanar kwalliya bache, kwalli kawai ta zizara ma dara daran idanunta sannan ta shafa lipgloss a dan karami bakin ta, Ta saka ƙananan ’yan kunne,da bracelet a hannunta, sannan ta daura agogon hannunta.
Gashinta yana da cika da tsayi kuma yana da curls sosai shiyasa ma bata kitso saboda tanayi yana walwalewa, tattaro shi tayi ta kama ta daure da ribbon amma koda ta dauko dankwali zata daura se ga curls din gaban gashinta ta sun fito bayan duk wahalar da tasha wurin daure su, dariya kawai tayi ta daura dankwalin ta, Wasu suka fito ta gefen goshinta da kusa da kunnenta, Ta tura su baya da hannunta, suka sake dawowa, ganin zasu qara bata mata lokaci ta haqura.
Maryam ta yi dariya tana kallon kanta ta madubin, Fuskarta tayi fresh, fatarta tana da haske, haske irin me kyaun nan da daukar ido, idanuwanta kuma farare tas se baqin idon ta me duhu ne sosae irin me sa nutsuwa, Tana da irin kyawun da ba ya neman wata kwaskwarima amma yana jan hankalin me kallonta
A takaice kallo daya zaka yimata kasan maryam kyakkyawa che ajin farko, ta karkatar da kanta kaɗan. Ta yi wa kanta murmushi a cikin madubi tana fadin
“Kin yi kyau meramun mama.”
Daga waje Mama ta sake kira.
“Meramu! Kin shirya?”
“Na shirya! Mama”
“To ki hito hakanan marece na yi”
Maryam ta ɗauki ƙaramin handbag ɗinta ta fito.
“Mama, zan tahi, imran ze kaini”
“Allah ya tsare, ki kula don Allah, kuma kakkiyi dare”
“Amin mama, in shaa Allah”
Maryam ta fita daga gidan tana murmushi ta jira shi qofar gida, dama ta kira shi kafin ta fito, minti biyu basu cika ba imran yazo ya dauketa suka kama hanya.
Sedae Abunda bata sani ba shine wannan ranar zata zama ɗaya daga cikin ranakun da za su fi kowane muhimmanci a rayuwarta, wannan bikin ze zama bikin daze zama wani bangare na rayuwarta, Ba ta san cewa wani wanda ba ta taɓa haɗuwa da shi ba zai shiga rayuwarta, Har ya zama silan samun abunda ta dade tana nema, Kuma ba ta san cewa dangin da take shirin haɗuwa da su suna da dadaddiyar alaƙa da iyalinta ba tun kafinta zo duniya.
Abin da ta sani kawai shi ne
Zata bikin Safiyya, bestyn ta.
A chan hidima event Centre kuwa, anata ci gaba da shirye-shiryen wankin amarya, taro ne wanda zaayi in a traditional modern way Wanda maza da mata zasu yi attending kamar kamu, wurin yasha kwalliya me kyau da tsari ga kuma traditional and modern kayan ciye ciye da abubuwan sha kala kala tundaga kan treats, chops, drinks, mocktails da abincin kala kala, da ganin wurin kasan bikin na masu qasa ne.
Join our WhatsApp group
Message ***