Free chapter · Read without an account

37. ...RORAH...🖊️

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)

37. ...RORAH...🖊️


Ta window na hango su biyun suna tafiya inda ake ajiye motoci Khalil na magana duk da ban jin abinda yake faɗa,ya ɗaura hannunshi a kafaɗar Romo,ture hannun yayi gaba Khalil na dariya daga baya.. Leonardo ya iso wurin da akwatin Romo yasa a baya,shi kuma ya zauna driver seat sun daɗe suna magana da Khalil kafin Romo ya shiga motar suka wuce Khalil na masu bye bye...


ajiyar zuciya na sauke na koma na zauna babu wani abu a zuciyata. ba daɗewa Khalil ya shigo da ɗaya daga cikin ma'aikatan. Safara'u ta kalle ni ta taɓe baki kamar taga kashi...bawai ta dameni bane ai...

can saiga Hajiya Momma da wasu daga cikin yan matan sun shigo sashen lokacin nida Khalil muna wasar cingum cingum yace '' wacece ma tace ita ba sunanta chidera ba kuma bazata yi ƙawance da masu kuɗi ba?" Ya ɗage gira idonshi a kaina

'' wallahi wata yarinya wai sunan ta Tuwo...kaji fa wani suna wai tuwo...'' murmushin gefen baki ya saki nayi dariya..can ya damƙo hannuna '' kuma kina kama da ita ..kodai kece?"

Zaro ido nayi ina jan hannun nace '' kai ina!! aini sunana Abeedah ba tuwo ba!" 

'' oh really...'' 


'' iyye!!!!...'' dukan mu muka juyo da sauri, Hajiya Momma dasu Seraphina ne suna kallon mu ido waje, Hajiya Momma ke bina da wani matsiyacin kallo

 '' lallai Ibrahimu,abin yayi ƙamari wato har da jawota jikinka ko? Da bamu zoba Allah kaɗai yasan abinda zai faru!" Khalil ya sake ni, kanshi a ƙasa..nikam nabi matar da kallo,me take nufi? 


'' ke kuma mayya.. kina bina da wannan shegun idon naki na maita,to nafi ƙarfin ki! shi Ibrahim ɗin da kika lashe shima dan dolenki ki sake shi wallahi...''

Tayi maganar tare da wasgo hannu na kamar zata katse shi.da sauri Khalil ya miƙe ya cire hannuna daga nata ya mayar dani bayan shi .Hajiya Momma da yan matan mamaki ya kusan gamawa dasu a wurin,wasun su kamar zasuyi kuka..

.'' aunty kitten bata min komai ba,and you're causing scene here. Dan Allah ku tafi...'' ya nuna masu hanya... idonsu suka kasa tsayuwa wuri ɗaya sai kallona suke suna kallon shi


'' lallai Ibrahimu ka girma! Yanzu ni kake kora saboda wannan? shikenan...'' sai ta kalle ni ta ƙifta yatsanta '' ke kuma zaki gani wallahi!"

Ita da muƙarabanta da badan sun soba suka kwasa riiii sukayi gaba...Juyowa Khalil yayi ya riƙo hannu na data kusa katsewa'' I'm sorry kitten!" girgiza kaina nayi...ina jin ba daɗi a raina...

****

Da ƙarfe biyu jirginsu Roman ya sauka Abuja... jawo hular baƙar rigar jikinshi yayi ya rufe rabin fuskarshi yana jan akwati... tafiyar shi a wani irin sluggish yanayi kamar an zare mashi laka,the emptiness he often feels ya fara mamaye shi...ajiyar zuciya ya sauke daga can gaba wasu mata da mijine da ya'yan su twins mace da namiji masu tsananin kama...dukansu chocolate complexions ne dasu...har ake kiransu da Chocolate family... Alhaji Safwan da matar shi Aisha sai yayan su Amnah da Ameen yan kimanin shekaru sha bakwai... yaran na hango Roman suka fara ɗaga mashi hannu kafin suka ruga da gudu zuwa inda yake...


Tsayawa Roman yayi har suka iso,ya ware masu hannayen shi suka rungume shi a tare cikin nishaɗi da farin ciki...kaɗan corner bakin shi yaɗan ɗage alamun murmushi...

'' ya ARMAN we missed you so much!" Macen ta faɗa. shafa kan namijin yayi yace '' yanzu gani a nan...'' suka gyaɗa kai kafin namijin ya cigaba da jan akwatin macen ta riƙe hannun Roman tana murmushi kamar gonar auduga har suka iso inda matar da mijinta suke tsaye


Cikin girmamawa da mutuntawa Roman ya gaishe dasu...Alhaji Safwan da matarshi sai murmushi suke '' Mallam Arman,ka kuwa ga yanda ka ƙara zama babban mutum?" Alhaji yayi maganar yana bubbuga kafaɗun Roman da yayi ƙasa da kanshi

Hajiya A'ishah tace '' come on,kada ku damar min yaro..ku barshi yasha iska...'' sai kowa yayi dariya banda Roman dayayi ɗan murmushin daba murmushi ba...


Mota biyu suka zo da ita,Hajiya A'ishah da mijinta da kuma Amnah a ɗaya, Roman da Ameen a ɗayan motar..suka bar airport ɗin

Cikin motar su Roman babu abinda Ameen yake sai zuba Roman na sauraren shi with keen interest '' oh..ba'a dafa komai a gida ba,amma an tanadi abubuwa idan kazo sai ka yi mana tiramisu wannan abun mai daɗi...'' Roman ya ɗage gira, cike da farin ciki Ameen ya cigaba da faɗin '' da gaske nake..kuma tun safe ban ci komai ba,kai nake jira idan kazo sai ka dafa mana...amma ai dai baka gaji ba ko?"

'' da ƙafa nayi tafiyar?" Roman ya mayar mashi da tambayar...sosa ƙeyarshi Ameen yayi...Roman ya sake shafa kan yaron... runtse ido guda Ameen yayi yana jin daɗin affection ɗin Roman.. 

Bayan kusan awa ɗaya suka iso wani babban gida a life camp...gate aka buɗe masu suka shigo, bayan sunyi parking su Roman suka fito... Ameen yake jan akwatin Roman su duka suka ɗunguma zuwa parlorn..Roman yake bin ko ina da kallo...sosai yaga gidan ya canja mashi,can ya hangi painting da suka taɓa yi 7yrs back shi da ita, slowly ya miƙe daga zaunen da yake ya fara zuwa wurin maƙogaron shi na up and down...mutanen parlorn suka bishi da ido

slowly ya kai hannun shi ya shafa painting ɗin na wasu yara mace da namiji suna wasa a park..daga ƙasan painting ɗin akwai signatures guda biyu..nashi da kuma nata...

Sai kuma sunan su da suka rubuta a tsakiya... RORAH.. farkon sunan shi wato Ro...da kuma ƙarshen sunan ta Rah.. 

'' saboda ina so ka rayu ka samu farin ciki'' maganarta ta ƙarshe ta maimaitu a kunnen shi


“Non avresti mai dovuto lasciarmi(You should have never left me)” yayi maganar ƙasan maƙoshi idon shi yayi ja

''“E tu non avresti dovuto sacrificarti per me.( And you shouldn't have sacrificed yourself for me)” yayi whispering tareda sumbatar gefen da yarinyar take,ya kwantar da kanshi a wurin haɗe da lumshe ido

Alhaji Safwan da Hajiya A'isha suke bin shi da kallon tausayi,su Amnah a gefe 

a hankali Alhaji Safwan ya matso kusa dashi ya ɗaura hannun shi a kafaɗar Roman yana bubbuga '' she's in a better place'' Alhaji Safwan ya furta murya ƙasa

'' I know!!" Roman ya amsa batareda ya ɗago daga position ɗin da yake ba

After a while ya ɗago tare da sauke ajiyar zuciya, Alhaji Safwan ya zaunar dashi saman kujera,nan suka sake gaisawa da kyau kafin a dawo maganar abinci 

'' ku barshi ya huta kada ku cika shi da surutu...'' Hajiya A'isha tayi dariya jin yanda suke ta santin girkin Roman 


shidai Roman sai binsu da ido yake fuska a sake

'' ga abubuwa can ma an ajiye a kitchen'' Amnah ta faɗa tana turo baki,

''.nima kwana biyu nayi missing abincin nan naku na yan Italiya...yau dai banci komai ba ina jiran naka!" Alhaji Safwan ya faɗa da dariya kaɗan Roman yayi murmushi kafin ya miƙe ya nufi upstairs... Amnah tabi bayanshi da kallo,sauran kuma suka cigaba da hira


Tura ƙofar ɗakin yayi ya tsaya daga bakin ƙofa yana ƙarewa ɗakin kallo...komai na ciki fari ne,sai ƙatuwar glass window dake buɗe ta inda yake hango zirga xirgar mutane can baya...kallon gefen gadon yayi

A memories ɗin shi,wata rana yana zaune a wurin, lokacin shekarun shi sha takwas yana zane akan sketching pad yaji an jefe shi da wani abu... carefully ya ajiye sketching pad ɗin ya isa bakin tagar ya leƙa... yarinyar cikin painting ɗin downstairs ce, rabin fuskarta rufe da farin mayafi tsaye a wurin hannu riƙe da ƙugu...tana ganin shi ta ɗaure fuska kafin ta matso kusa kusa,ta ɗaga kanta tace '' ina so in shigo ciki...''roman bai matsa ba, baice komai ba ya cigaba da kallonta..sai data maimaita maganar sannan yabar wurin,bayan kusan minti biyar ya sako mata blanket mai kauri


Kamawa tayi ta fara hawa ko tsoro bataji kada ya gaji ya saketa ta faɗo daga ciki kuwa fuskar Roman tayi ja dan ba ƙaramin ƙarfi yayi amfani dashi ba sanda ta iso sama sama,ya riƙo hannunta ya iyarda jawo ta ciki su biyun suka faɗi ƙasa ita a saman shi...

Tana hararar shi tace '' R-man baka da mutunci...kullum ni nake zuwa inda kake baka zuwa wurina..kai baka damu dani ba ko?" Kafeta yayi da ido batareda yace komai ba ta fashe da kuka.. simply ya saukar da ita daga jikinshi ya miƙe tsaye ya kakkaɓe kayanshi ya koma ya cigaba da abinda yake yi...


Pillow ta ɗauka ta jefe shi dashi...sai kuma ta ƙaraso wurin tana jan gashin shi '' sai ka bani haƙuri...!" Bai tureta ba yake ƙoƙarin cire hannun ta daga gashin shi kawai...ganin ya kasa fuskar shi tayi pink yace '' sorry ...'' sai lokacin ta sake shi

Tana huci...shafa kanshi ya shiga yi feeling disoriented...littafin dake saman cinyarshi ta ɗauke hannunta riƙe da fuskarsa tana murmushi'' idan munyi aure ya'ya nawa kake so R- man?" Ɗan waro fararen idonshi yayi...kunnen shi yayi zafi, kumatun shi suka yi pink...yarinyar tana kallon shi tayi dariya tace

'' You look hot when you blush...mwhah!" tayi mashi kiss a kumatu..

Hakan ya ƙara intensifying zafin da yake ji fuskar shi ta ƙara rinewa...

'' Ya Arman har yanzu kana nan?" Muryar Ameen ta dawo dashi daga tunanin daya shiga... Kyakkyawan murmushin dake fuskarshi ya ragu.. amma bai ɓace duka ba..it was genuine,daga zuciyar shi


Shiga ɗakin yayi ya rufo ƙofar Ameen ya wuce nashi... baye Roman ya shiga yayi wanka ya fito ɗaure da towel jikinshi na ɗigar ruwa...yasa kaya,ya tsane gashin shi..yayi Sallah... yana nan zaune wayar shi tayi ringing... Khalil ne,sai da wayar ta kusa katsewa ya ɗauka...ba wata magana mai tsawo sukayi ba kafin kiran ya ƙare...ya wuce kitchen bayan nan..

Kamar yanda Ameen ya faɗa komai a shirye...sai daya sake wanke abubuwan da aka wanke...su Amnah suka shigo amma babu wanda ya taɓa wani abu daga cikinsu, Amnah baki kamar zai katse tsabar yanda take murmushi

'' you have a crush on him...'' Ameen yayi whispering a kunnen ta, matsawa tayi nesa dashi tana kame kame...rufe bakin shi yayi yana dariya .. fuskar Amnah ta tsuke 

Roman ya ɗaura apron ya jawo tukunya ya ɗora a kan wuta ba tare da ya ce uffan ba, ya shiga aiki kamar professional cook

soon ƙamshin albasa da sauran spices ya game kitchen ɗin

Amnah da Ameen kamar babu su a wurin, duk da shidai Ameen yaga nawar a gama a zuba mashi, Amnah kuwa kallon Roman take kamar zata haɗiye shi da idon ta...

'' ya Arman meye wannan ka haɗa?" Ameen ya matso kusa yana bin abincin da ido yawun shi sun tsinke '' Risotto..'' ya bashi amsa...'' oh.. tiramisu ɗin fa?" '' yanzu xan haɗa

Roman ya ɗora ƙaramin bowl a kan counter ya zuba mascarpone cheese a ciki. A gefe kuma ya fara bugun whipping cream har ta yi kauri... 

Ameen dai kamar zai ciro idonshi ya jefa cikin bowl ɗin tsabar yanda yake bin kowane motsi na Roman da ido 



" Risotto and Tiramisu ready!" Ya furta,wani irin tsalle Ameen ya daka har da yar ƙaramar rawa, Roman ya ɗauko tiramisu ɗin ya miƙa mashi with a low smile...da sauri ya karɓa..yawun shi suka faɗa sama... hakan yasa murmushin Roman faɗaɗa..

Sai ya kalli Amnah datake kallon shi kamar ta samu TV, itama ya miƙa mata ɗaya...da sauri ta iso wurin ta karɓa da murmushi '' na gode...''

Suna nan tsaye hajiya A'ishah da Alhaji Safwan suka shigo '' a'a party ake banda mu?" 

Ƙarasowa tayi ta ɗauka,hakama Alhaji Safwan..suna ta santi...

'' oh harda risotto..bari muzo muci abincin chef Arman...'' zama sukayi a dining ɗin kitchen ya ɗauko komai ya ajiye masu...

Kowa yayi serving kanshi sai santi suke..shima kujera ɗaya ya zauna ya zuba nashi suna ci tare...

yafi jin kanshi a gida cikin wa'yannan mutanen sama da dangin shi na jini...

Wa'yannan adoptive parents ɗin shi ne,akwai sanda yayi zama a gidan marayu shiba maraya ba...rayuwar shi bata kasancewa mai sauƙi ba bayan rasuwar mahaifiyar shi da kuma...Ita wacce ba'a kiran sunanta!!

lowering idonshi yayi yana kallon su ta ƙasa yanda iyayen ke taraiyar ya'yan nasu...he felt the void

Wani memory ne ya sake dawo mashi.. lokacin shekarun shi shida...yana gudu a cikin meadow da yamma Maman shi biye dashi '' Mano ka tsaya fa..nace ka tsaya...'' take faɗa da italy

Amma bai tsaya ba,ya cigaba da bibiyar bilbilaye itama tana biye dashi...Saida ya kama bilbili ɗaya sannan ya tsaya ta kamashi

'' kai kana so ka dinga wahalar dani ko?" Ta tambaya tana dungure mashi kai...yayi murmushi tare da girgiza kanshi abinda yakan daɗe bai yiba,hakan ba ƙaramin ɗumama zuciyar ta yayi ba,ƙwalla ta taru a idonta '' na kama!" Ya nuna mata...


'' ina son ka sosai ɗana..''

''.ina sonki nima Mama...'' ya furta sai ta rungume shi... regardless of condition ɗinshi na zama autistic,ko sau ɗaya Mamanshi bata taɓa nuna gajiyawa ba...tana son shi sosai..yet an samu wa'yanda suka ɗauke masa ita...

Bai masan da cewa ya dena cin abincin ba,sai maƙogaron shi dake kaikawo hannun shi yayi fari jijiyoyin sun fito

'' Arman!" Hajiya A'ishah ta kira da ɗan ƙarfi..sai lokacin ya dawo hayyacin shi fuskarshi kamar an jaye jini...ya ajiye cokalin shi '' excuse me..'' ya tashi ya bar wurin ..suka bishi da kallo Amnah kamar ta bishi kallon da Hajiya A'ishah ta jefa matane yasa ta koma ta zauna ...

Da daddare bayan sun gama hira kowa ya shige ɗakin shi wurin kwanciya...tsaye Roman yayi daga bakin window yana kallon nesa da nisa...hannunshi na shafa pendant ɗin dake maƙale a wuyan shi...ɗakin ba haske sai wanda ke fitowa daga na'urar Ac,wanda ya kasance blue light...

Can ya sauke ajiyar zuciya ya dawo ya kwanta bayan yayi addu'ar bacci... badaɗewa ba bacci mai nauyi ya ɗauke shi ya faɗa duniyar mafarki


Wannan karon yana zaune a ƙarƙashin bishiya da littafin shi a hannu,wurin babu kowa sai shi kaɗai da kuma kukan tsuntsayen dake dajin...yarinyar ɗazu ce ta rugo da gudu fuskarta in a blur ta durƙusa gaban shi..ɗagowa yayi daga littafin shi ya kalleta da ƙaton murmushi a fuskarta tace '' na kawo maka kyauta...'' ta zaro pendant daga cikin aljihunta ta nuna mashi...yabi pendant ɗin da kallo babu wani reaction a fuskar shi...itama murmushin fuskar ta ya ɓace,ɗauke littafin tayi daga saman cinyarshi ta shiga tsakanin ƙafafunshi ta ɗan durƙusa kaɗan ta maƙala mashi a wuya...sai ta kamo a hannunta ta sumbaci saphire blue stone ɗin...ya bita da kallo...zaunar da kanta tayi saman cinyarshi.. fuskar shi tayi ja da sauri,ya kasa kallon ta however with a serious tone tace '' tunda kai baka iya siya ma mutane kyauta ba,ni na siya ma and you'' have to keep it ''

Ya kalli cikin idonta da kalar su take blurred,komai ma a mafalkin ba clear bane

 '' I hope to live in your heart forever..''ta faɗa tana shafa ƙirjin shi saitin Zuciyarshi, hannun shi ya kai ya shafa gashinta batareda yace komai ba


Hakan ya daɗaɗa mata, ta rungume shi'' ina sonka sosai R-man...'' sai ta ɗago ta haɗe bakinsu in a quick kiss

Da sauri ta miƙe daga jikinshi tana kallon fuskar shi har zuwa ƙirjin shi da sukayi ja tace '' idan ka cigaba da blushing haka...zan sauya maka suna zuwa tumatur...'' ta kashe mashi ido ya kawar da kanshi gefe yana ta ƙifta idon shi dake zare 


Ta bar wurin tana kiran '' tumatur...ɗina...''

Da ƙaton murmushi Roman ya buɗe idonshi...har safiya ta waye,ya tashi zaune yana share gashin shi zuwa baya har lokacin murmushin manne a fuskar shi,yana kallon ko ina na ɗakin kamar yana neman hanyar komawa cikin mafalkin...ya riƙe saphire pendant ɗinshi..ya kai baki ya sumbata'' you're unique'' ya furta with a low deep voice...


🍁🍁: kodai Abeedah ce?😳

Roman: wace ce ita?

🍁🍁: matarka.. budurwarka?

Roman:🤬 yaushe ta zama matata? yaushe nace ina sonta?

🍁🍁: well,koda yaushe kana kula ta...

Roman: 🤦 I expected you to be smarter...
any ways if she keeps throwing herself at me ya zanyi?


🍁🍁: sai ka share ta 

Roman: it's impossible..

🍁🍁:🥰🥹

Roman: don't look at me like that... 

🍁🍁: ko dai akwai wani abu a ranka?

Roman: I ain't telling you shit...nan gaba zaki sani...chop chop out you go!!!


🍁🍁: at least ka faɗa ma...

Roman: ni ba ita bane da zan buɗe baki ina faɗa maki abinda ke raina...nan gaba zaki sani..

Bang! 

Ya rufe ƙofar... toh ku masu shipping Abeedah da Roman ashe Abeedatu bata da gurbi a zuciyarsa wata ta riga ☹️😔

____

Khalil na zaune a parlor'n shi saye da farin glasses riƙe da littafi yana karantawa idonshi ya sauka akan Diyaam dake ta leƙen shi,a hankali yayi murmushi 

'' Oh... it's Sofia...'' jin ya kira sunan ta yasa ta ja baya zuciyarta na bugu da ƙarfi a ƙirjinta , sai ta kai hannunta a baki tana cizar yatsa,tana tsaka da wannan tunanin taga ya buɗe ƙofar duka...ƙare mata kallo yayi,kayan jikinta doguwar riga baƙa mai glitters da yawa akai sai baƙin hijabi data ɗaura sama,sosai tayi kyau kamar ba yar Nigeria ba,ganin yanda ta koma yar ƙarama gaban shi yaji abun ya bashi dariya,ga kuma yanda tayi hiri hiri da manyan idonta kamar wacce tayi ma sarki ƙarya



'' You' here for me friend?" Ya tambaya with a hint of amusement a muryar shi

sai da Diyaam ta haɗiye yawu sannan ta gyaɗa kai,sai kuma tayi ƙasa da idon ta bayan sun sauka cikin nashi,wani irin kunya ya kamata 


'' thank God wani ya tuna dani, shigo ciki.'' ya ware mata ƙofar da faffaɗan murmushi a fuskar shi,jin yanda yayi maganar yasa ta ɗago ta kalle shi,shima ita yake kallo da sauri tayi ƙasa da kanta ta wuce ciki tana tafiya kamar zata faɗi

“Hol ko waɗi maa Diyaam?(Meyake damunki Diyaam)” ta ɗanyi maganar da ƙarfi tana facepalming kanta,Khalil dai yayi murmushi jin abinda ta faɗa duk da bai san ma'anar hakan ba

slowly ta zauna saman rug ta tanƙwashe ƙafafunta duk da yace ta zauna saman kujera ta girgiza kai

miƙa mata remote yayi ta karɓa da godiya tasa tashar cartoons 


sosai ta mayarda hankali tana kallo ko motsi bata yi,ita harta Ma manta da Khalil na wurin,daga lokaci zuwa lokaci yake kallon sashenta...ita da Abeedah suna matuƙar son cartoons ya lura

Diyaam na ganin za'a fara Sofia da first ta wani iri gyara zama baki washe dan tana matuƙar son cartoons ɗin ana fara waƙar itama ta wage baki tana bi

🎶 I was a girl in the village doing alright
     Then I became a princess over night    
      Now I gotta figure out how to do it 
         Right,so much to learn and see


       Up in the castle with my new family 
        and a school that's just for royalty 🎶


Khalil ya ɗago daga littafin shi yana sauraren yanda take bin waƙar bata missing ko harafi, kamar ita tayi waƙar her voice sounds better than the actual singer,ajiye littafin gefe yayi ya tallafo haɓarsa yana kallon TV'n 
 
    

    🎶A whole enchanted world is waiting for me.. I'm so excited to be...

Sofia the first 

I'm finding out what being Royal's all about 

Sofia the first 

Making my way it's an adventure every day..

  Sofia!


Sofiaaaaa!!.... 🎶

da sauri ta juyo bayan Khalil yayi whispering sunan ta yana bin waƙar shima ya sakar mata Murmushin daya sa tayi ƙasa da fuskarta da sauri tana cizon lower lip ɗinta dan hana kanta murmushi 


🎶It's gonna be my time..to show them all that I'm Sofia the firsssst 🎶

Khalil ya iyar tare da TV'n, Diyaam ta kasa ɗagowa 

a hankali dariyar sa mai daɗin sauti ta ratsa kunnenta kafin taji yace '' You blush quite alot..'' 

sai ta rufe fuskarta da hijabi tana dariyar farin ciki...he noticed 

  🌹 ❤️📖✨



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️












































 








Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.