Free chapter · Read without an account

Page 15

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU 

BY

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1 

Page 15 
Umma na fita ta ɗora ruwa a kan wuta ta haɗa garin kunu ta dama mata kunun tsamiya ta koma ɗakin,har lokacin Zarah na kwance jikin Mami.
Ta zuba sugar cikin kunun ta ajiye kusa da Mami.
Mami tace"sannu da aiki".
Umma tace"ku da kuka sha hanya ai ku za'a yiwa sannu,idan yayi sanyi sai ta sha".
Mami ta ɗauki kunun ta riƙe a hannu tana kallon Zarah dake kwance ta ɗan shafa kanta face"sannu autan Mami,daure ki tashi ki sha kunu kin ji?"
Da taimakon Umma Zarah ta sha kunun Mami ta bata magani da kyar ta koma ta kwanta.
Umma ta fita waje ta cigaba da aikinta ba tare da ta kula Inna Yalwati dake faman zarya a tsakar gidan tana habaice habaice ba.
Ta leƙa waje ta samo yaro ta bashi saƙon cefane ta dawo.
Kafin a kira sallar magriba ta gama dafa farar shinkafa da miyar stew data juye gabaɗaya kazarta a ciki.
Sai da ta juyewa Mami ruwan zafi ta kai banɗaki sannan ta shiga daki.
Mami dake danna waya ta ɗago tace "sannu da aiki".
Umma tayi murmushi tace"na kai miki ruwan wanka,idan kin fito sai auta ta shiga,ya sunanta?"
Mami tayi dariya tace "sunanta Fatima,ana kiranta Zarah".
Umma tace"ki ce takwara ce,lallai wannan dai autar Umma ce na ƙwace ta a hannun ki".
Mami ta miƙe tsaye tana murmushi tace"babu damuwa,in dai Zarah ce na bar miki ita,kukan banzan ta ma kawai ya ishi mutum,a barni da Umar".
Umma tace"wannan ɗanki ne ai,babu mai shiga tsakaninku".
Mami tace"Wanda ya shiga shi keda jin kunya ai".
Umma tayi murmushi ta zauna inda Mami ta tashi ta taɓa wuyan Zarah,jin zafin ya ɗan ragu yasa ta gyara mata riga tabi bayan Mami.
Ana idar da sallah Sadauki ya shigo gidan,ya gaida Umma dake kimtsa inda tayi aiki ya shiga ɗakin,ya ƙarasa inda Zarah ke kwance ya ɗurkusa yana kallon fuskarta.
A hankali ya kai hannu ya shafa wuyarta, Zarah ta buɗe ido da sauri don dama ba bacci take ba.
Ya sauke hannun kamar ba shi ba yace"Mimie".
Tayi shiru tana kallon shi don ba ta san sunan waye hakan ba.
Ganin yadda take bin shi da kallo yasa shi cewa"baki amsa ba".
A hankali tace"waye Mimie?"
Yace"Ni da waye a nan?"
Tayi shiru tana kallon shi,ya katse mata tunanin da take da cewa"ya jikin?"
A hankali tace"da sauki".
"Mami ta baki magani?"
Ta gyaɗa kai a hankali tana kallon shi,ya miƙe ya ɗauko ledan da ya shigo dashi ya ƙarasa gaban kwanonin Umma ya ɗauko roba ya juye mata soyayyen doya da ƙwai da ake soyawa a ƙauyen sanin tana son doya sosai.
Ya ƙaraso har gabanta ya ajiye ya ɗebo ruwa ya dawo ba tare da ya kalle ta ba yace"ki tashi ki ci".
Ta turo baki tace "ni dai bana jin yunwa".
"Zan tafi masallaci,ki tabbatar kin cinye kafin in dawo".
Bai jira cewar ta ba ya ɗaga labulen ɗakin ya fita, ya koma gefe da sauri ganin Mami  dake kokarin shiga ɗakin.
Mami tace"Faruq ka shigo ashe?"
Kanshi a ƙasa yace"ban daɗe da shigowa ba Mami".
Ya bata hanya ta shiga ciki sannan ya fita ya bar gidan.
Tana shiga ta tarar da Zarah ta zubawa plate ɗin doyar ido.
"Ke kuma fa,ina kika samo doya?"
Ta ɓata rai tace"Yaya F ya kawo min kuma bana jin yunwa Mami".
Mami tace"ki ci ko babu yawa mana Zarah,ke baki san abin arziki ba?"
Dai dai lokacin Umma ta shigo ɗakin ta hau jera kulolin abinci,idonta na sauka kan Zarah tace"ina kika sami doya takwara?"
Zarah tace"Yaya F ya kawo min".
Mami ta mata wani kallo tace"ta san miki wani Yaya F?bana son iyayi Zarah".
Umma tayi murmushi tace"menene abin faɗa yanzu,yi hakuri autan Umma ki ci abincinki".
Sai da Mami ta idar da sallar Isha sannan ta zauna cin abinci,idan ka gansu tare da Umma zaka ɗauka sun daɗe da sanin juna,babu nuna ɗagawa ko fifiko ko kaɗan a wurin Mami,hira suke sosai tamkar sun daɗe da sanin juna.
Sadauki yayi sallama a bakin kofa aka bashi izinin shiga,ya sake gaida Mami sannan ya gaida Umma dake bin shi da kallo.
Ta gefen ido ya kalli Zarah dake zaune rike da plate ɗin shinkafa ta kasa ci.
Umma ta nuna mishi wani kula dake can gefe tace"ga abincin ka can a kula".
Ya miƙe ya ɗauki kulan ya musu sallama ya bar ɗakin.
Mami tayi murmushi tana kallon Umma tace"Faruq kenan,ba dai natsuwa ba".
Umma tayi shiru na ɗan lokaci kafin ta ɗago tace"ban san da wani irin baki zan miki godiya ba,kin riƙe Sadauki tamkar ɗan cikin ki,babu ƙyashi ko mugunta,Allah ya cigaba da dafa miki ya shirya miki zuri'a".
Mami ta dauki kofin ruwan dake kusa da ita ta ɗan kurɓa sannan ta ajiye,a nutse tace"babu godiya tsakanin mu,Allah ne ya haɗa ni da Sadauki,idan ban riƙe shi tsakani da Allah ba kaina na cuta,nima na haifa,na san inda zasu tsinci kansu watarana?
"Yau kawai muka sani bamu san gobe ba, Sadauki yaro ne da kowa zai so zama dashi don yaro ne mai hankali da natsuwa".
Umma ta sauke numfashi tace"duk da haka,na san ba ke ce mutum ta farko da ta fara haduwa da Sadauki ba amma a cikinsu ke ce kika rungume shi tamkar ɗa,Allah ya saka da alkhairi ya kara arziki mai albarka ya raba ki da dukkan sharri".
A hankali Mami tace"Amin".
Cike da nutsuwa tace"babban dalilin zuwa na nan shine maganar karatun Sadauki,ban sani ba ko kuna da labarin Sadauki ya cigaba da karatu?"
Umma tace"Sadauki ya taɓa sanar dani kun maida shi makaranta bayan ya bani labarin ku,amma mahaifin sa bai sani ba gaskiya".
Mami tace"Allah yasa ba za'a sami matsala daga wurin sa ba".
Umma zata bata amsa Baba yayi sallama a bakin kofa don dama tun ɗazu ta aika a sanar dashi zuwan baƙi.
Mami ta gyara mayafin dake kanta suka amsa mishi ya shigo.
Ya zauna kusa da Umma dake zaune kan tabarma suka gaisa da Mami sannan Zarah ta gaishe shi ya amsa da fara'a.
Mami ta juya ta kalleta tace"ki zauna ta waje Zarah".
Umma tace"da kin kyale ta akwai sauro a wajen nan".
Mami tace"barta taje,idan an gama sai ta shigo".
Zarah ta ɗauki mayafi ta yafa ta fita waje,Sadauki na zaune karkashin bishiyar da suka saba zama da Sani ya hangota.
Tana tsaye a bakin kofa tana bin tsakar gidan da kallo har idonta ya sauka a kan shi,ta taka a nutse ta nufi inda yake.
Ta cire takalmin kafarta ta zauna kan tabarmar dake shinfiɗe a wurin.
Ya dauke kai a kanta ya jingina bayan shi jikin bishiyar ya lumshe ido,tunda ya sa kafar shi cikin gidan memories da su kayi sharing tare da ɗan uwansa ke dawo masa daki daki.
Shi ya san ba zai iya cire tunanin Sani a ranshi ba, wannan wani space ne da babu wanda zai iya cike masa shi har ya bar duniya.
A can ɗaki bayan sun sake gaisawa Mami ta koro mishi bayani tun daga farko,a nutse Baba ke sauraronta harta kai ƙarshen maganarta.
Mami ta sauke numfashi tace"dalilin da yasa mai gidana yace in zo har gida in sanar da iyayen Faruq abinda ke faruwa kenan,duk da ya hana a sanar da malamin makarantar su amma an zo wani gaɓa da dole a daina ɓoye ɓoye,idan ya hana a sanar da zuwan shi School wannan dole ne a sani".
Baba ya gyaɗa kai tace"wannan shine abinda yafi dacewa,da farko dai zan fara da godiya bisa irin riƙon da kuka yiwa Sadauki tamkar ɗan cikin ku,bamu da bakin godiya,amma zancen cigaba da karatu da kuke son tura shi,karatun ma na soja don Allah kuyi hakuri,ba wai naƙi bane amma abin zai yi yawa aka ce shege da hauka,babu abinda muka haɗa daku sai addininnu da yazo ɗaya,ko wannan ɗinma mun gode Allah ya saka da alkhairi".
Mami tayi murmushi tace"kar ka rusawa ɗana burinsa,na san kun daɗe da sanin hakan mafarkinsa ne,dan Allah kar ku hanasa,muna neman wannan alfarmar".
Mami ta ƙarasa maganar tana kallon Umma.
Umma ta share hawayen dake son gangaro mata jin kalaman dake fitowa daga bakin Mami,a hankali ta kalli Baba tace"Malam kayi hakuri kar ka ce za ka hana Sadauki cika wannan burin,ni da kai dama kowa da yasan waye Sadauki a wannan kauyen ya san babban burinsa kenan,a lokacin cewa ka ke ba ka da wannan hanyar saboda yanayin lalacewar kasar tamu,yanzu ga damar ta samu bai kamata ka ƙi lamarin ba".
Baba ya girgiza kai yace"assha Fatime,ba wai naƙi lamarin bane kamar yadda kuke tunani,naga kar abin yayi yawa ne daga taimako".
Mami tayi murmushi tace"har yanzu baka fahimci matsayin Umar a wurin mu ni da mai gidana ba,na ɗauke shi tamkar ɗa namijin da ban haifa bane a cikina, wannan abinda muke kokarin yi ba wai taimako bane ko alfarma,tamkar hakki ne da muke son saukewa a kan ɗan da muka haifa".
Umma ta kasa cewa komai sai kallon da take bin Mami dashi.
Baba ya sauke numfashi yace"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ya sawa karatun albarka".
Mami tace"Amin Amin,mun gode".
Baba yace"mune da godiya,tunda nake ban taɓa ganin mutane masu karamci kamar ku ba,Allah ya saka muku da gidan aljanna".
Mami ta amsa da Amin.
Zarah ta juya ta sake kallon Sadauki ganin ko motsawa bai yi ba tace"Yaya F".
Ya buɗe ido a hankali ya kalleta,da mamaki take kallon shi ganin yadda idon shi ya kaɗa,ta ɗan matso kusa dashi a hankali tace"Yaya F,baka da lafiya ne?"
Ya mata kallo ɗaya ya maida idon ya rufe,ta bata rai ta koma inda take zaune.
Kamar a mafarki taji abu ya hau jikinta,ta fasa ihu da ƙarfin gaske ta cukwuikuye Sadauki da ya buɗe ido ba shiri.
Kokarin finciketa yake daga jikin shi amma ta kasa bashi wannan damar.
Yabi wurin da kallo ya hango ƙaton beran da ya fito daga rumbu.
Ya riko fuskarta da sauri ya hau jijjigata ganin yadda gabaɗaya jikinta ya saki yace"Mimie,kalle ni Please".
Lokaci ɗaya gabaɗaya mutanen gidan suka fito,Sadauki ya kwantar da ita kan tabarma da sauri ya wuce ya ɗauki cup ya ɗebo ruwa.
Umma ta ƙarasa wurin Zarah dake kwance tace"lafiya Sadauki,me ya sameta haka?"
Sadauki yace"ɓera ne ya hau jikinta Umma".
Hankali tashe Umma tace"garin yaya ka bar hakan ya faru Sadauki?"
Ta karbi kofin hannun Sadauki ta ɗebi ruwa kaɗan ta shafa mata amma ko motsi ba tayi ba,kana ganin Umma kasan hankalinta a tashe yake.
Mami ta ƙaraso wurin a nutse tana kallon Umma tace"ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane,kawai tsorata tayi,autar ta ki ce matsoraciya komai tsoro yake bata".
Ta karbi kofin ganin gabaɗaya Umma a rikice take ta watsa mata a fuska,lokaci ɗaya ta ja numfashi sai kuma ta fashe da kuka ta rungume Mami tace"wayyo Yaya F ka taimake ni kar ya kamani".
Mami ta shafa kanta tace"calm down Zarah,buɗe ido ki gani babu komai".
A hankali ta buɗe ido ta shiga bin mutanen wurin da kallo,Baba yayi murmushi yace"a shiga da ita ciki ta samu ta huta".
Umma ta riƙe mata hannu suka bar wurin, Inna Yalwati dake tsaye kusa da ɗakinta ta taɓe baki ta juya ta shiga ciki.
Sadauki ya bi bayan su Umma da kallo har suka shige daki ya sauke numfashi ya koma ya zauna.
Washegari Umma ta dama kunun tsamiya ta aika aka siyo mata alala da mai da yaji,sosai Mami taji daɗin kunun har ta kasa ɓoye hakan tace"kunun nan yayi daɗi gaskiya,gabaɗaya kamshi ya cika min hanci".
Umma tayi dariya tace"abin ki da mutanen ƙauye,kayan kamshi ake haɗa masa sosai".
Bayan an idar da sallar magriba Inna Mairamu ta shigo gidan, za ta iya ƙirga sau nawa ta taka kafarta a cikin gidan tun bayan auren Umma.
Rabonta da gidan tun wani jinya da Umman tayi lokacin Sadauki bai fi shekaru biyar a duniya ba sai kuma lokacin da aka nemi Sani aka rasa a birni ta shigo har ɗakin Inna Yalwati ta mata gaisuwa.
Ta ƙarasa bakin kofar Inna Yalwati tayi sallama,bayan an amsa ta shiga har ciki.
Inna Yalwati ba ƙaramin mamakin ganinta tayi ba.
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Yalwati mun wuni lafiya?"
Da sauri Inna Yalwati tace"Ina wuni Inna ya gida?"
"Lafiya kalau Yalwati,ya hakuri da juna kuma?ku cigaba da hakuri da juna,ku zauna tsakani da Allah watarana sai labari,na zauna da yar uwata shekaru hamsin babu wanda ya taɓa jin tsakanin mu harta koma ga Allah,gashi yanzu sai dai in ba da labari,Allah ya shiga lamarin ku ya kaɗe fitina".
Inna Yalwati ta amsa da Amin ta bita da kallon ƙasa ƙasa harta fita,ta taɓe baki ta ture ɗanƙwalinta gaban goshi tace"tsohuwa sai kinibibin tsiya,to kar nake kallon ku wallahi,ni dai an gama cutata tunda an haɗa ni kishi da dangin matsafa".
Inna Mairamu tayi sallama a kofar ɗakin Umma,Mami da Umma suka amsa ta shiga tana sake kwaɗa wani sallamar.
Mami tayi murmushi ta gaisheta da girmamawa don kallo ɗaya za ka mata ka hango tsananin kamar dake tsakaninta da Umma.
Umma ta miƙe ta bata wuri ta zauna tace"sannu da zuwa Inna".
Inna Mairamu tace"yawwa,ai ana sanar dani nace ana shiga Masallaci zan fito,to kin ganni sai yanzu,sannunku da zuwa".
Tayi maganar tana kallon Mami.
Mami tayi murmushi tace"sannu Inna,ai da kinyi zaman ki zan zo har gida in gaishe ki".
Inna Mairamu tace"haba dai,ke da kika yi tattaki tun daga Kano ai ke ya kamata a tarar ƴar nan,ya gida ya hanya?"
Mami tace"lafiya Alhamdulilah Inna".
Zarah dake kwance ta rufe gabaɗaya jikinta da zani ta ɗan leƙo tana kallon Inna.



Oum Rijalain 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.