Free chapter · Read without an account
BABI NA GOMA SHA BIYU
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
BAYAN DUK ƴan sanda sun gama binciken su sun kama wacce ake tuhuma da jiwa Nana Asma'u ciwo a baya. Dama tun kafin ƴan sanda su shigo ciki mun gama reviewing case din mun san akwai hujjojin da ze sa se an shiga kotu. Nayi magana da makwabtan su akan duk wani abu wanda suka sani akan lamarin Nana Asma'u a cikin gidan. Mahaifin ta shi kuma be taɓa lura da irin abinda ake yiwa ƴar shi ba. Yace baya zama amma a nawa dubi koda baya zama, idan ya kula da ƴar shi ze san akwai abubuwa da dama da be kamata ayi mata ba. Da yaji maganar shiga kotu yace ayi haƙuri ze magance matsalar gidan shi. Wani banzan kallo na mishi tare da faɗa mishi za'a iya bashi nashi hukunci daban idan yace za'a binne wannan maganar. Ran shi be so ba amma kuma be sake cewa wani abu ba.
Nayi drafting charge sheet ina tuhumar matar uban da assault wanda ya jawo mummunan ciwo a jikin ƙaramar yarinya. A ranar da muka shiga kotu har likitan da yayi mata gyaran ciwo na taho dashi da makwabtan su da suka ji ihun yarinya da kuma wuƙar da aka sa mata a baya a matsayin hujjoji.
Da aka shiga kotu ba se matar uban ta ƙaryata abinda ake zargin ta dashi ba. Na yarda da abinda nake na kuma yarda da gaskiya, indai har na yarda da wannan then I can go to any length to see that justice is served. Tunda tace ba itace tayi ba, nace tunda tace haka kuma yarinyar a hannun ta take tana kula da ita, kuma tace ba ita ta aikata ba, ta faɗi yadda ta samu ciwon tunda a gabanta take itace me kula da dukkanin lammuran ta. Baseless hujjoji ta fara badawa.
Justice yayi duban takardu ya yanke mata hukuncin zama gidan yari tsawon shekaru biyu tare da cin ta tarar dubu ɗari uku a kula da ciwon da ta ji wa Nana Asma'u.
Satisfaction naji a raina akan hukuncin da aka mata. Inaga ko a mafarki ba zata yi tunanin yiwa wani ɗan Adam irin wannan ba. Haka kuma, mata masu hali irin nata idan suka ga abinda ya faru da ita, ze sa suyi hankali akan ƴaƴan da aka bar musu amana. Akwai wata uwa wacce zata so ta tafi wani wuri ta bar yaron ta ne? Ba duk ƙaddarori ne ke sa mahaifa suyi nesa da yaran su ba? Ina maganar wanda suka tafi kuma baza su dawo ba? Mutane basa tunanin su ma zasu iya barin nasu yara ko za'a yi zalunci akan nasu yaran? Mesa mutum ba ze fara kallon kanshi ba kafin yayi zalunci?
Bayan duk komai ya wuce na case ɗin su Nana Asma'u, aka yi publishing littafin Yaya Hauwa. A Chelsea hotel akayi launching nashi. Abokai da kuma ƴan uwa duk sun tafi har yan uwansu wanda ban taɓa gani ba duk na gani Yaya Hauwa tana introducing namu da juna. Yaya Hauwa ta haɗu da makarantan littafan ta sun nuna mata so da ƙauna. Tayi Q&A session inda suke tambayar ta abubuwa tana basu amsa. Daga ƙarshe kuma tayi signing copies na littafan wa masoyan ta. Anyi snacks da homemade drinks an rabawa jama'a komai yayi kyau. A cikin copy na wanda na siye a farkon page ta min signing ta kuma rubuta, ’To my amazing sister in-law, Hadiza Tahir.’ Ta rubuta date harda wurin da akayi event ɗin. 4th July, 2023. Abuja. I find the ‘amazing’ a bit disturbing because what's amazing about me nida ko abinda ɗan uwanta yake so bana mishi. Ya akayi na zama amazing then? Ina tunanin tayi ne saboda Zaid, saboda shi kaɗai amma ba saboda ina amazing da gaske ba.
Covern da ta nuna mana daga ƙarshe shine aka sa mata na zane wanda ya fito da kyau kuma yayi kyau. Sunan littafin kuma ‘Dust and Destiny.’ Ba'a watse a Chelsea hotel ba se bayan Maghrib and I enjoyed what I had there. It felt lively.
___________________
A wurin aiki ina zaune a kujerar desk ɗina nake jin Hanna da colleague namu, Adam, suna magana akan abinda ke faruwa a Nigeria. Bance komai ba se sauraren su da nake amma kuma ba kallon su nake ba.
“I wouldn't mind ayi coup a ƙasar nan” Hanna ta faɗa carelessly.
Akan abinda tace yasa na ɗaga kaina na kalla hoton shugaban ƙasa da yake kan wall ɗin office ɗin mu. Saukar da kaina nayi ina kallon magazine da nake dubawa.
“Kinsan yadda mulkin soji yake kuwa? Babu freedom fa”
“Yanzu da kake maganar freedom, ka faɗa min freedom da muke dashi bayan kuma ba sojoji ne suke mulkar mu ba. I want you to understand Adams“ Hanna tace tana kallon shi. Nasan tana nuna kamar tana son shi tun ba yanzu ba ban san shi ko yana jin haka game da ita ba saboda shi mutum ne me wuyar ganewa “Ba saboda mu bama wahala bane ze sa ace ba'a wahala a ƙasar nan”
“I'm surprised that an Abuja girl cares about other less privileged people” Adam yace
“Me kake nufi Adam?”
“Girls brought up in Abuja are different. It seems like they only care about themselves and they think everyone else is enjoying life the way they are”
“Im an exception because I don't think like that. Kamar yadda nasan yatsun mu ba ɗaya ba haka nasan rayuwarmu ba ɗaya ba”
“Uhmm!” Adam yayi “That's impressive”
Shiru Hanna tayi daga ganin alama ranta ya ɓaci akan abinda Adam yace. A kodayaushe ita taken ta na daban ne saboda tana ganin mutane duk ɗaya, babu wani wanda yafi zama special. And I believe she thinks like this because she's from a wealthy family. When one is born into wealth, tunanin shi na daban ne ze dinga tunanin meyasa kowa ba ze zama ɗaya ba saboda basu san abinda wanda ba irin su yake ji ba . Me yasa se an nuna wannan yafi wannan muhimmanci bayan kuma duk ɗaya muke da juna.
“I have heard about this case” Adam yace tare da rufe desktop ɗin shi yana kallon Hanna. Hankalin ta ta maida wurin shi “What about?”
“Ance ya faru a Kano ne. Wata mata ta ƙona uwargidan mijinta. Me yasa wasu mata basu da hankali? Me yasa suke sa kansu a masifa a dalilin namiji? Me yasa suke nuna sun fi son maza akan kansu?”
“Why are you asking me all these questions?”
“Maybe you have an answer to them”
Idanun ta ta kawo a direction ɗina “Maybe Hadiza can answer them since she's a married woman”
“Hadiza” Adam ya kira sunana. Ɗago kai nayi ina kallon shi. “Kina jin abinda muke faɗa?”
Gyaɗa kaina nayi saboda su nake sauraro. “Hanna tace zaki iya bada amsar abinda nake tambaya”
Shiru nayi ina tunanin tambayoyin shi su kuma sun tsareni da idanun su. “Bana tunanin nasan amsar tambayoyinka. Kowa da yadda yake tunani. Amma kuma tana tunanin ƙarin auren mijinta cin amana ne a wurin ta shiyasa ta kasa ba zuciyar ta haƙuri ta aikata abinda ta aikata”
“Ƙarin aure cin amana ne?” Adam ya faɗa
“A wurin wasu mata” Hanna ta amsa shi.
Wani irin ajiyar zuciya Adam ya sauke yace “Me kike tunanin za'a iya yiwa irin wannan matan?”
My eyes were so sharp akan tambayar da yayi “Rai be fi rai ba. Idan aka ƙonata, ze tura saƙo a cikin kawunan matan da suke da tunani irin nata”
“Ah Hadiza!” Hanna tayi saurin cewa
“Don't be emotional Hanna. She deserves it. A life for a life”
“Yes, you understand Adam”
“Hukuncin yayi tsauri dayawa. Don't you think the woman is mad and she needs a rehabilitation center?”
“C'mon Hanna! A rehabilitation center? You got to be kidding” Ina faɗin haka na gyara cabinet files nawa na tashi tsaye tare da ɗaukar jaka ta da magazine na musu sallama.
A hanya ta na dawowa Shahida ta kira ni. Ban ɗaga wayar ba se da na kawo gate na gida. Ina kiranta take faɗa min shigowa zata yi ne ta dawo daga kasuwa siyen kayan miya ko ina nan. Amsa mata nayi da yanzu na dawo tazo se take ce min gata a baya na. Juyawa baya nayi naga motar ta, na shiga ciki na bata wuri ta shigo itama.
Tare da me aikinsu take. Ganin ta se ya tuna min da faɗan da ake yiwa Khalifa da ya dawo kan Zaid. Kallon yarinyar nake da ta gaishe ni na kasa kama sunan ta.
“Aunty ke ma likita ce irin Yaya Hauwa?” ta tambaye ni tana kallona da idanun ta innocently
“Yaya Hadiza zaki ce ba aunty ba” Shahida ta faɗa mata
“Yaya Hadiza” yarinyar ta faɗa. Ƙaramar yarinya ce in tayi shekara goma sha biyar.
Murmushi nayi nace “A'a, ni barrister ce ba likita ba”
“Ohh!” tayi “Wanda nake gani a cikin kotu suna magana?”
“Eh su”
Gyaɗa kai tayi da murmushi akan fuskar ta. “Wannan mutanen masu kai masu laifi a kotu”
“Ke ya isa ki dena yiwa Yaya wannan tambayoyin. Baki ga yanzu ta dawo daga wurin aiki ba. Yaya yunwa nake ji fa”
“Ga kitchen ki shiga kiyi abinci”
“Bari Rahama ta shiga ta mana” Shahida tace. Nan kuma na kama sunan yarinyar da sakawa a cikin raina ba zan ƙara mantawa ba
“A'a, indai ke kike jin yunwa ke zaki shiga ki dafa abincin ki”
“Na fa gaji nima Yaya”
“Itama ta gaji ne Shahida. Ina ce ba tare kuka je kasuwar ba?”
“Bari ta tayani. Macaroni ce zan dafa”
“Shikenan ni zan shiga ciki”