Free chapter · Read without an account

Chapter 2: The girl who ruined his mood

by Hauwa Jibrin Sulaiman · FADIANA

Aminu Kano International Airport


Hayaniyar jama'a ta cika cikin Aminu Kano International Airport, wasu na tura trolley ɗinsu cike da kaya, wasu suna tsaye suna duba bayanan jirginsu a wayoyinsu, yayin da wasu kuma suka kewaye danginsu da suka zo yi wa rakiya


A cikin wannan hayaniyar, wata kyakkyawar budurwa ce ke bin bayan wani ma'aikacin airport da ke jan trolley ɗin kayanta. Dogayen ƙafafunta suna taka ƙasa cikin sauri, amma hankalinta gaba ɗaya yana kan wayar da ke hannunta, murmushi ne shimfiɗe a fuskarta


Ba irin murmushin da mutum yake yi don kawai ya nuna farin ciki ba, wannan murmushin nata ya fito ne daga cikin zuciyarta, har ya sa dimples ɗinta suka bayyana sosai a kumatunta both side. Duk lokacin da ta karanta wani abu a wayar, sai ta ɗan cije leɓenta na ƙasa tana ƙoƙarin hana kanta dariya, amma daga ƙarshe ta kasa, sai da ta saki dariyar dake cinta a hankali


Fara ce, doguwa, kyakkyawa, kuma tana da wani irin kyau da ba ya buƙatar ado mai yawa kafin ya bayyana


Ta saka doguwar Abaya mai kyau wadda ta zauna a jikinta tayi mata kyau, veil nata kuma ya rufe kanta yadda ya kamata, handbag ɗinta na rataye a kafaɗarta, yayin da ɗayan hannunta ke riƙe da wayar da ta zama kamar ita kaɗai ce take tafiya a wajen…


"Wallahi wannan yarinyar ba za ta taɓa girma ba" ta furta cikin dariya, tana karanta saƙon da ƙawarta ta aiko mata


Ta yi typing da sauri “You people should just rest. I've graduated Alhamdulillah! I don't need your unnecessary drama today” Ta danna send, ta ƙara da wata emojin dariya


A ɗan nesa da inda take, wani saurayi ne tsaye a gefen hanyar da jama'a ke bi, dogayen ƙafafunsa a miƙe, hannunsa na hagu a cikin aljihun wandonsa, yayin da hannunsa na dama ke riƙe da wayar da yake dannawa cikin natsuwa, fuskarsa ba ta nuna wata damuwa ba, amma akwai wani irin tsauri a yanayinsa da zai sa mutum ya yi tunanin cewa ba ya son a dame shi


Handsome guy ne sosai, dogon mutum ne mai faɗin kafaɗu, sanye da kaya masu tsada waɗanda suka nuna irin mutumin da ya saba da rayuwa mai daɗi. Agogo ne a wuyan hannunsa, takalminsa mai tsada ce, Ko da yake yana tsaye a tsakiyar cunkoson jama'a, hankalinsa baya tare da shi balle yasan abin da ke faruwa don wayarsa yake kallo


Bang!!! Rahma ta yi karo da shi da ƙarfi har wayar da ke hannunsa ta sulale ta faɗi ƙasa


Saurayin ya ɗago kansa da sauri


A lokaci guda kuma, Rahma ta ja baya, idanunta ta zaro sakamakon firgicin da ta yi, ta kalli saurayin, sannan ta mayar da kallonta kan wayar da ke kwance a ƙasa


"Oh! I'm so sorry," ta faɗa da sauri, ta ɗaga hannunta cikin neman afuwa "Ban gan ka ba ne, and ka tsaya a hanya, shi ya sa ban kula ba” Ta faɗi hakan ne cikin gaggawa, har ba ta lura da yadda fuskarsa ta sauya ba


Saurayin ya kalli wayarsa dake kwance a ƙasa, sannan ya ɗago ya zuba mata ido, wani irin kallo ne mai cike da mamaki da fushi, kamar bai yarda da abin da kunnuwansa suka ji ba


"Me kika ce?"


Rahma ta lumshe ido ta bude "Na ce sorry fah, ban gan ka ba ne"


Ba amsar da yake son ji ba knn "Kika ce na tsaya a hanya?"


Ta ɗan daure fuska "Eh, saboda ka tsaya a.."


"Ke wace irin dabba ce?" Ya katse ta


Rahma ta bude baki, amma babu sautin da ya fito nan take sbd speechless data zama


Saurayin ya matso da ƙafa ɗaya gaba, yana nuna ta da yatsansa "Babu nutsuwa ko kaɗan a tare da ke! Kina tafiya kamar babu kowa a duniya sai ke, Ko ba kya ganin gabanki ne? Ko kuma yau ne first time da kika shigo airport har kika manta cewa akwai wasu mutane a wurin?"


Rahma ta ɗan buɗe baki, tana kallonsa kamar ba ita yake yi wa magana ba, sai yanzu ma taji zata iya magana, a hankali ta ɗora hannunta a ƙirjinta "Dabba fa ka ce?"


"Kin ji ni sosai ai”


Ta yi wata ‘yar dariya ta rashin yarda, sannan ta girgiza kanta "Are you for real? Ka kira ni dabba saboda na buge ka bisa kuskure?"


"Kin buge ni, wayata ta faɗi, sannan kika tsaya kina gaya min cewa ni ne na tsaya a hanya, kina ganin wannan normal ne?"


"Na ba ka haƙuri fa Malam!"


"Haƙurin da kika bayar tare da zargin ni ne mai laifi?"


Rahma ta ji wani abu ya tokare mata maƙogwaro, ba don ta kasa mayar da magana ba, sai don irin ƙarfin halin da yake yi na cin mutuncinta a gaban jama'a ya ba ta mamaki, ta saba da wasa, rigima da tsokana, amma ba ta saba wai mutum da ba ta taɓa gani ba yana yi mata magana kamar ta aikata wani babban laifi ba


Ta haɗiye yawu, ta daidaita tsayuwarta "Look, mister, I said I'm sorry. Idan ba ka karɓi haƙurin ba, that's your problem. Amma ba ka da ikon kirana dabba bcos of mistake”


Ya ɗan yi murmushi "Oh, I see”


Ya gyara tsayuwarsa, sannan ya sake kallonta daga sama har ƙasa, kallon da ya ƙara sa Rahma jin haushi


"Now I understand the kind of person you are”


Rahma ta ɗaga gira "Really?”


"Na san irin ku”


"Irin mu?"


"Eh. Irin matan nan da suke zuwa airport suna neman attention na maza, za ki buge mutum da gangan, sannan ki fara yi masa magana, kina nuna kamar kuskure kika yi. Maybe kina tunanin zan fara yi miki murmushi ne ko kuma in nemi number ɗinki”


Rahma ta ji kamar an zuba mata ruwan sanyi a kai, abin da ya faɗa ya fi wanda ta yi expecting muni "Excuse me?"


"Ba sai kin yi pretending ba. Isn't it shameful? Kina ganin duk namijin da kika buge sai ya ɗauke ki a matsayin wata kyakkyawar budurwa son kowa?”


Ta buɗe baki, amma ta kasa samun kalmar da za ta fara magana da ita, Idanunta sun fara cika da ƙwalla


Ba don tana tsoron sa ba. A'a amma akwai wani irin ciwo da mutum yake ji idan wani ya raina shi, ya yi masa hukunci ba tare da ya san komai game da shi ba, sannan ya yi hakan a gaban jama'a


Ta ji kunya sannan taji ta tsane sa, Kuma abin da ya fi komai ɓata mata rai shi ne yadda yake kallonta kamar ya san duk abin da ke zuciyarta


"Ka gama?" ta tambaya a ƙarshe, muryarta ta ɗan yi sanyi


Saurayin ya ɗan karkatar da kansa "And?"


"Na ce ka gama zagin da kake yi min?"


Ya yi wani ɗan murmushi "Why? Kina son in ci gaba ne?"


Rahma ta cije leɓenta, tana ƙoƙarin hana ƙwallar da ta taru a idanunta zubowa


Wani ma'aikacin airport da ke kusa da su ya sunkuya ya ɗauki wayar saurayin. Ya duba ta na ɗan lokaci, sannan ya miƙa masa ita cikin ladabi


"Sir, ga wayarka kayi hakuri kawai”


"Thank you” Saurayin ya karɓa


Sai dai da ya kalli screen ɗin wayar, fuskarsa ta sake sauyawa bcos wayar ta tsattsage


Kacakaca kuwa, gashi ya bazu a fuskar screen ɗin, ya juya ta a hannunsa, yana kallonta kamar bai yarda da abin da ya gani ba


Wayar iPhone 18 ce, sabuwar waya da ya saya ba da daɗewa ba


A hankali ya ɗago kansa ya kalli Rahma, wannan karon, fushin da ke fuskarsa ya fi na farko tsanani


"Are you kidding me?"


Rahma ta kalli wayar, sannan ta sake kallonsa "Oh my God! Ta fashe ne?"


Ya zuba mata ido "Are you blind? Ba ki gani ne?"


Ta ja numfashi mai karfi "Look, na riga na ba ka haƙuri. Ban yi da gangan ba. If there's anything I can do…”


"Anything you can do?" Ya katse ta, yana ɗaga wayar "Za ki sayo min wata kenan? Ko za ki biya kuɗin gyaranta?"


Rahma ta rasa abin cewa, ya yi wani irin tsaki da ƙarfi, sannan ya girgiza kansa


"Useless. Ki koyi yadda ake tafiya a cikin mutane. Idan kina son amfani da waya, ki tsaya gefe ki yi amfani da ita, ba wai ki riƙa tafiya kina kallon screen kamar mahaukaciya ba”


Ta ji idanunta sun ƙara cika da ƙwalla, amma ta daure "Ba ni kaɗai nake amfani da waya a nan ba fa”


"Amma kin iya fad’awa kan Maza ai”


"Saboda ka tsaya a…”


"Don't you dare start again!" Muryarsa ta fito da tsawa, har wasu mutane suka fara kallonsu


Rahma ta tsaya cak


Ya matso kaɗan, ya sunkuyar da kansa domin idanunsa su yi daidai da nata


"Ki saurara da kyau. Bana son ganinki a duk hanyar da zan bi, ki yi ƙoƙarin amfani da idanunki kafin ki sake buge wani mutum. Stupid” Ya juya ya tafi ba tare da ya jira amsarta ba


Rahma ta tsaya a wurin, tana kallon bayansa


Babu wanda ya taɓa yi mata irin wannan cin mutuncin a rayuwarta, let’s say tayi kuskure ne ma, toh iyayenta suna gyara mata ne cikin lallabi, ko abokan rigimarta, waɗanda suka san cewa tana da taurin kai, ba su taɓa zagin ta haka ba


Amma wani baƙo, wanda ba ta san sunansa ba, ya tsaya ya kira ta dabba, ya zarge ta da neman attention, sannan ya yi mata magana kamar ba ta da daraja


Ta sauke idanunta, wata ƙwalla ya zubo mata a hankali, ta yi saurin goge ta da bayan hannunta kafin wani ya lura


"Allah ya isa" ta furta cikin ƙasa-ƙasa, ta ɗaga kanta, ta kalli inda saurayin ya bi


"Ban yafe ba” Ta faɗi kalmomin a hankali, amma da wani irin zafi da ya sa ta ji kamar ta ɗauki alkawari ramawa


Sai ta juya da sauri, ta bi bayan ma'aikacin da ke jan kayanta. A yau ranar farin cikinta ce


Ta gama karatunta a Maryam Abacha American University, kuma bayan shekarun karatu, jarabawa, damuwa da rashin bacci, yanzu ta zama graduate Alhamdulillah!


Wannan ya kamata ya zama abin da ya mamaye zuciyarta, ba wani mugun mutum da ya kira ta dabba ba


Ta share fuskarta, ta gyara veil nata, sannan ta yi ƙoƙarin mayar da hankalinta kan tafiyar da take yi


“He doesn't deserve to ruin my day” Ta maimaita hakan a ranta countless times 


Amma wani ɓangare na zuciyarta ya riga ya yanke hukunci


If I ever see that man again, wallahi sai ya ji bakar magana


Bayan ta karɓi kayanta, Rahma ta nufi wurin da ake gudanar da clearance da duba takardun tafiya


Ta fito da passport ɗinta da boarding pass daga cikin handbag, ta miƙa wa jami'in da ke duba takardun. Ya karɓa, ya duba bayanan da ke ciki, sannan ya yi mata wasu tambayoyi kaɗan game da tafiyarta


Ta amsa masa cikin ladabi, ta jira har ya gama duba bayanan, sannan ya mayar mata da takardunta


Daga nan ta bi alamun da ke nuna hanyar zuwa departure lounge


Akwai wurin da ake sake duba kayan hannu da na'urar scanning. Rahma ta cire wasu abubuwan da aka buƙata ta ajiye su a tray, ta bi umarnin jami'an tsaro, sannan ta wuce ta ɗauki kayanta bayan an gama binciken


Ta sake duba boarding pass ɗinta domin tabbatar da gate ɗin da za ta bi, sannan ta nufi wurin jiran jirgi


Duk da ƙoƙarin da take yi na mayar da hankalinta kan tafiyarta, fuskar wancan mutumin ta ci gaba da bayyana mata a rai


Ta yi tsaki "Mtcheew!"


Wata mata da ke zaune kusa da hanyar ta ɗago kai ta kalle ta


Rahma ta yi saurin murmushi "Sorry, ma”


Matar ta yi mata murmushi ita ma, sannan ta mayar da kanta kan wayarta


Rahma ta girgiza kanta, tana yi wa kanta dariyar takaici ‘Rahma, please. Don't let one miserable man ruin your beautiful day’


Ta zaɓi kujera a gefen da ba ta da cunkoso sosai, ta ajiye handbag ɗinta a cinyarta, ta zauna, sannan ta sauke numfashi mai nawi


Sai yanzu ta ji kamar ta samu nutsuwa, ta fito da wayarta, ta buɗe chat ɗin Mammy


Ba ta son wani abu ya sake ɓata mata mood ɗinta. A yau, tana son ta ji daɗin komai, ta gama uni, kuma za ta koma gida ta ga iyayenta, ta huta daga rayuwar students, ta ci abincin da ta daɗe tana mafarkin samu a gida


Ta danna lambar Mammy


Kafin wayar ta yi ringing na dogon lokaci, aka ɗaga "Hello, my baby!"


Fuskar Rahma ta sake nan take da murmushi "Mammyyyy!"


“Rahma ta, ya ake ciki? Kin gama komai?"


"Eh Mammy. Na gama komai, yanzu ina zaune ina jiran boarding"


"Alhamdulillah! Allah ya sauke ki lafiya. Kin ci wani abu kuwa? Ko dai kin sake fita ba tare da kin ci abinci ba?"


Rahma ta ɗan ɗaga gira, kamar Mammy tana kallonta "Mammy please, can we not start with food?"


"To me zan fara da shi? Idan na tambaye ki ko kin ci abinci sai ki ce na dame ki. Idan kuma kika suma a hanya, ni za’a kira a daga min hankali”


Rahma ta fashe da dariya "Mammy wallahi I love you!"


"Ni ma ina sonki, amma ban yarda da wannan halin naki ba, yanzu ki gaya min, me kike son a dafa miki kafin ki dawo?"


Kamar an taɓo wani side farin cikinta, Rahma ta gyara zama "Ah! Finally, the question I've been waiting for!"


Mammy ta yi dariya a ɗayan ɓangaren "Allah ya taimake ki, To faɗa"


"First of all, ina son tuwon shinkafa da miyar kuka amma ba irin wannan miyar kukar da ake yi a ce wai an dafa ba Mammy, Ina son wadda za ki saka nama sosai, bushashshen kifi, sannan ki saka ɗan yaji kaɗan"


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol