Free chapter · Read without an account

Page 16

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU 

BY

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association YOTA 

Book 1 

Page 16

Suna haɗa ido ta maida kanta cikin zanin gadon,Inna Mairamu tace"waye wannan?"
Umma dake lura da Zarah tayi murmushi tace"kishiyar ki ce Inna,ta san kina ganinta za ki rikice shi yasa ta ɓoye kanta".
Inna Mairamu ta taɓe baki tace"in rikice a wani dalili kenan ana zaune kalau,Ita dai ganina ya ɗaga mata hankali shi yasa ta kasa bayyana kanta,idan ba tsoro ba ta fito mana".
Zarah ta turo baki ta sauke zanin gabaɗaya,Inna Mairamu ta bita da kallo ta sake taɓe baki tace"sai dai a nuna min farin fata ba dai wani abu ba".
Mami da Umma suka fashe da dariya, Umma tace"magana ta fito Inna,kinga dai farin fatar ya ɗaga miki hankali kenan".
Zarah ta kalli Inna tace"Ina wuni".
Inna Mairamu tace"Allah na tuba marigayi mahaifin ki ai shima farin fatar gare shi balle ace yau na fara gani".
Zarah ta taɓe baki tana kallonta ƙasa ƙasa.
Inna Mairamu tace"ba don halinki ba dai zan amsa,ya gida ya hanya?"
A hankali tace"lafiya".
Inna tace"ya sunan ki?"
A hankali Zarah tace"Fatima".
"To Madallah,Allah yayi albarka baturiya".
Umma ta miƙe ta kawo mata tuwon shinkafa da miyar taushe ta ajiye kusa da ita.
Inna tace"yanzu zan tafi ajiye tuwon ki,da kika tuƙa tuwo shi angon nawa akwai abinda kika ajiye masa ne?"
Mami tayi murmushi tace"nima sai da nayi mata wannan tambayar Inna,so take kawai ɗana ya kwana da yunwa,amma tunda ina nan ai shikenan".
Inna Mairamu tace"to dama abinda take nufi kenan ai ƴar nan,inda kika san ba ita ta haifi Sadauki ba,tunda ɗaɗewa nace mata idan bata son shi ta kawo min ni ina so".
Umma dai bata ce komai ba ta koma ta zauna,Mami tayi murmushi tace "tana son shi Inna,wani lokaci yaran ne sai da haka".
Inna tace "to ai shikenan".
Washegari su Mami suka tashi da shirin tafiya,duk da taso Sadauki ya tsaya ya kara ko kwana biyu ne amma Baba bai yarda ba.
Inna Mairamu ta aiko da saƙo cikin ƙaton bacco tace a baiwa Mami,Umma duk wani abu da take dashi a ɗakin sai da ta haɗawa Mami cikin kaya.
Ƙarfe bakwai na safe driver ya shigo kauyen daga cikin garin Bauchi,Baba ya fito da buhun gero da wake aka sa mata a mota.
A haka su kayi sallama Umma sai ɗaga musu hannu take har suka bar layin.
Tunda tafiya tayi nisa Zarah ta fara amai,ba ƙaramin galabaita tayi ba kafin su isa Kano.
Ƙarfe biyu na rana suka isa gida,Mami ta dinga bin motocin dake harabar gidan da kallo.
Tana riƙe da hannun Zarah ta nufi ciki Sadauki ya bi bayanta riƙe da akwati.
Zeenah ce kaɗai a parlourn tana kallo,tana ganin Mami ta fasa ihu ta rungumeta.
Mami tace"kar ki yarda ni dan Allah".
A shagwabe tace"Mami naji kewar ku wallahi, especially Chu Chu".
Tayi maganar tana jan kumatun Zarah.
Da sauri ta kara kai hannu jikinta tace"bata da lafiya ne?"
Mami ta nemi wuri ta zauna tace"lafiyar ta ƙalau dogon tafiya ne kawai bata so".
Zeenah ta riƙeta ta zaunar kusa da Mami,a dai dai lokacin Sadauki yayi sallama a bakin kofa.
Mami tace"ka shigo mana Faruq".
Ya tura kofar ya shigo idon shi a kan Zarah ya ajiye mata akwatin.
"Sannu Faruq,ka je ka huta".
A hankali yace"to Mami".
Mami ta kalli Zeenah tace"ina ƴan uwan ki?"
Zeenah tace "Hajja dasu Oum sun zo da safe,suna part ɗinta."
Mami ta gyaɗa kai tana ƙoƙarin miƙewa tace"ki ce manyan baƙi garemu,bari in shiga ciki in watsa ruwa".
Tunda Mami ta shiga ɗaki ba ita ta fito ba sai bayan la'asar,ta fito parlour sanye da dogon hijabinta ta nufi part ɗin Hajja dake can bayan part ɗin mai gidan.
Tun daga waje take jiyo hayaniyar yara,da sallama ta shiga babban parlourn dake dauke da set ɗin kujeru biyu sai tashin kamshi yake tana bin yaran ciki da kallo.
Da sauri Aneesa ta saki Ipad ɗin hannunta ta rungume Mami.
Mami ta shafa kanta tace"Aneesa ke ce kika girma haka?"
Aneesa ta sunkuyar da kai cike da kunya,su Naima da Firdausi da basu san da dawowar Mami ba suka rungumeta cike da farin ciki.
Naima tace"Mami yaushe kika dawo?"
"Ban wani jima ba,ina Hajja?"
Aneesah tace"tana ciki tare da Oum,Mami ina Zarah?"
Mami tace "tana can ɗaki".
Tana gama magana ta wucesu ta nufi ɗakin Hajja.
Tana zaune a bakin gado sanye da wani Arabian dogon riga tamkar ba tsohuwa ba idonta sanye da siririn eye glasses sai fruits dake gabanta tana sha a hankali.
Mami ta ƙaraso dakin dauke da sallama.
Hajja ta gyara glass ɗin idonta ta amsa sallamar tana bin Mami da kallo ƙasa ƙasa.
Mami ta zauna kan carpet ta shiga gaida in law ɗin nata cike da girmamawa.
"Kun dawo ashe,ai a bakin jama'ar gidan nake jin wai ba kya gari,nace shi ganaral bai sanar dake ina nan dawowa daga Canada ɗin bane?"
Mami tayi murmushi tace"wallahi bai sanar min ba Hajja,da na san da zuwan ku da banyi tafiyar ba ai".
Hajja ta ajiye fork ɗin hannunta tace"dama na san baki sani ba ai Hafsah,ba halinki bane hakan,da dai Ramlah ce wannan ƙaramin aikinta ne ta saɓi gyale sai ranar da aka ganta,gashi ke kwana biyu kawai ki kayi kika dawo saboda kina da hankali,Ita kuwa har shekara sai tayi a can ba tare da ta tuna da wani miji ba balle ƴaƴa".
Mami tayi murmushi kawai ta maida dubanta kan Oum dake danna waya tana sauraron conversation ɗinsu da Hajja.
Ta ajiye wayar a nutse tace"welcome Aunty,ya hanya?"
Mami tace"Alhamdulilah Oum,ya naku hanyar,kwana da yawa".
Oum tayi murmushi tace"shekaru da yawa dai Aunty kusan four years fa, wannan yafi ƙarfin kwanaki kam".
Mami tayi murmushi tace"to ai na hausawa na miki".
Kamshin turaren daya karaɗe wurin yasa gabaɗaya suka juya, ƙasa ƙasa yayi sallama ya shigo ɗakin.
Har zai gifta ya hango Mami,ya dawo yana shafa kai ya durƙusa kusa da ita yace"ina wuni Mami".
Mami da sai bin shi da kallo take tace"wai Abdallah ne ya girma haka?"
Hajja tace"shine ya zanƙale kamar poll waya sai rashin kunya filla filla".
Mami tace"gaskiya na kwana biyu ban ga yaran nan ba Oum".
Oum tace"kin san ko wancan zuwan da nayi yana exams shi yasa bai zo ba".
Bai kula Hajja ba ya tafi kusa da Oum ya zauna.
Jidda ta shigo riƙe da wani babban basket ta gaida Oum don ta san karamin aikinta ne ta falleta da mari babu abinda ya sha mata kai.
Ta ƙarasa gefen Hajja ta ajiye basket ɗin tace"Hajja ga abinci in ji Mama".
Hajja ta kyaɓe baki tace"abincin rana ko na dare?"
Jidda tayi shiru tana kallonta,so take ta mata rashin kunya amma idon Oum ya hanata cewa komai don babu ruwan ta da Mami.
Ta gyara glass dinta tace"tafi abin ki sai anjima,sannunta da aiki".
Jidda ta juya ta bar ɗakin tana ƙunƙuni ƙasa ƙasa.
Tabi bayanta da harara tace"karen hauka ya cije ni ne da zanci abincin Ramlah,ashe dana shiga uku".
Babu wanda yace mata komai cikin su sai Abdallah da ya miƙe yana kallon Oum yace"Oum,zan fita sai na dawo".
Da sauri Hajja tace"daga isowar ka ƙasar mutane akwai inda ka sani ne a nan?,ni dai ga wayata saita min alarm ba ruwana da tambaɗewa a garin jama'a,ƙarfe biyar zaka sa min na asuba".
Abdallah ya watsa mata harara ƙasa ƙasa,ganin Oum na kallon shi yasa ya miƙa hannu ya karɓi wayar.
Ya daɗe yana danne danne sannan ya ajiye wayar kusa da ita ya juya zai fita.
Hajja ta ɗauki wayar da sauri tace"ka saita ko baka saita ba?"
Ba tare da ya juyo ba yace"babu data a wayar,idan kinsa data sai in saita miki".
Yana gama magana yayi saurin barin ɗakin,Hajja ta riƙe wayar tabi kofar da kallo kamar an dasata.
Cike da takaici ta kalli Oum tace"wani irin yaro kika haifa Khadijah,dama alarm sai da data ne?"
Oum tace"ki yi hakuri Hajja,zai dawo ya same ni zanyi maganin shi".
A fusace tace"kina dai gani Hafsah,idan nayi magana ace na cika masifa,kwata kwata yaron nan baya mutunta ni,a duk cikin yaran Khadijah shi ya fita daban kamar ba ita ta haife shi ba".
Mami tace "kiyi hakuri Hajja,gaskiya bai kyauta ba,da kaina zanyi magana dashi idan ya dawo".
Ta ajiye wayar ta sauka daga kan gadon tace"ai shikenan,ya je can yaji da mugun halinsa,daɗin abin uwarsa na haifa kinga kuwa babu abinda na haɗa dashi".
Mami dai sai hakuri take bata,Oum bata sake cewa komai ba saboda sanin halin Hajja,sai ta kai sati ɗaya tana maimaita magana ɗaya.
Haka Mami ta lallaɓa ta bar part ɗin ta wuce nata ganin Hajja na kokarin sa mata ciwon kai.
Da daddare ya shigo part ɗin Mami bayan ya idar da sallar Isha,Mami na zaune tare da ƴan matanta suna kallo sai Zarah dake kwance a jikinta.
Ya ƙaraso ya zauna ya gaida Mami,Mami ta rage volume ɗin kallon da take tace"Abdallah ka dawo?"
Yace"ban daɗe da shigowa ba Mami".
Zeenah da sauran ƴan uwanta suka gaishe shi banda Zarah data rufe ido da sauri bayan sun haɗa ido.
Mami tace"ya studies Abdallah,medicine ka keyi ko?"
Ya shafa kai yace"eh Mami".
Tace"wani year kake yanzu?"
A hankali yace"zan shiga year two kenan".
Ta gyaɗa kai tace"Allah ya taimaka ya bada sa'a,me yasa baka saita mata alarm ɗazu ba?"
Yayi guntun murmushi yace"na saita mata Mami,bata duba bane".
Mami tace"raina min uwa kayi kenan ko?"
Murmushi kawai yayi ya mata sallama ya tafi.
Da safe Mami ta haɗa breakfast cikin basket ta mikawa Zarah dake kwance har lokacin tace "ki kaiwa Hajja".
Nan da nan ta ɓata fuska tace"ban ji sauki ba Mami".
Mami ta watsa mata harara tace"za ki tashi ko saina ɓata miki rai,ni kike son jawa magana?"
Zarah ta miƙe tsaye ta shiga ɗaki ta ɗauki hijab,ko kallonta Mami ba tayi ba ta haura sama.
Ta ƙarasa ta ɗauki basket ɗin ta fita,tana ganin kanta a waje ta fashe da kuka.
Sadauki dake tsaye daga can nesa ya juya da sauri,yana ganin ita ce ya ajiye kayan hannun shi ya nufo inda take yace"lafiya,me aka miki?"
Cikin kuka kamar zata shiɗe tace"na cewa Mami ban ji sauki ba tace sai na kaiwa Hajja abinci".
Yayi shiru yana kallonta cike da takaici don tun jiya ya san da Hajja a bakin Iliya mai gadi.
A fusace yace"bar nan kafin in mare ki".
Da sauri ya hadiye kukanta ta juya ta bar wurin da gudu.
Kamar wata ɓarauniya tayi sallama a bakin kofa,tana zaune saman carpet gabanta kayan breakfast ne iri iri da aka kawo daga part ɗin Mama an maida shi gefe sai wanda Oum ta shiga kitchen ta haɗa.
Abdallah na zaune kusa da ita yana cin pepper soup da Mami ta aiko jiya da daddare,suna haɗa ido ta ɗauke kai da sauri har tana tuntube ta isa gaban Hajja ta ajiye basket ɗin ta koma ta zauna tana wasa da yatsun hannunta tace"Hajja ina kwana".
Hajja ta ajiye tea cup ɗin hannunta tace"sai yanzu kika san ina gidan,na ce sai yanzu kika san akwai wata ƴar banza a gidan nan?"
Zarah ta turo baki tace "ai bani da lafiya ne Hajja".
Hajja ta watsa mata wani kallon banza,sai kuma ta gyara glasses ɗin idonta ta juya ta kalli Abdallah tace"dan Allah kalli yarinyar nan Abdullahi,yanzu tayi kama da mara lafiya?"
Ya mata banza kamar ba da shi take ba,cike da takaici ta watsa mishi harara tace"wallahi akwai aiki a gaban Khadijah,yaro sai shegen rashin kunya filla filla?"
Dai dai nan Oum ta shigo parlourn riƙe da plate cike da soyayyen kwai, Zarah ta miƙe da sauri ta karɓi plate ɗin tace"Oum Ina kwana".
Ta shafa kanta tayi murmushi tace"ya kike daughter,na shigo jiya ance kinyi bacci ba kya jin daɗi,ya jikin?"
Zarah ta saci kallon Hajja tace"da sauki".
Oum ta kalli Hajja tace"ina kitchen na jiyo muryar ki Hajja,lafiya?"
"Akwai mai sani magana ne dama a wannan duniyar idan ba ɗanki ba,wallahi ki raba ni dashi ya fita hanyata,kowa yayi takan shi,yaro sai rashin kunya kamar rainon biri".
Rai ɓace Oum tace"what is your problem Abdallah,why do you always try to cause trouble?"
A hankali yace“babu abin da ya faru Oum, I don’t know why she’s always trying to make an issue out of everything I do.”
Oum tace"ranka zai ɓaci wallahi if you keep denying what I know you're capable of doing".
Hajja ta ƙanƙance ido tace"ya isa haka,ba cewa nayi ki sa shi gaba da faɗa kamar wadda yayi sata ba,kwata kwata guda nawa yake da za'a tada jijiyoyin wuya har ana haɗawa da turanci,mata sai balai kawai".
Oum ta koma ta zauna rai ɓace ta shiga danna wayar hannunta, Zarah ta lallaɓa ta ajiye plate ɗin kusa da Hajja ta juya zata fita.
A kausashe cike da ɓacin ran dake cin shi yace"are you sure you're okay,ni sa'an kine,ko kin gaishe ni ne?"
Hajja ta sassauta murya don duk cikin jikokinta idan ka cire Abdallah ba ƙaramin so take yiwa Zarah ba gashi dama takwarar tace.
A hankali tace"kai kuma ka cika bala'i,yarinyar da naji ba lafiya gare ta ba ka kewa wannan ihun?,ina laifin kace dawo ki gaishe ni".
Kamar za tayi kuka ta dawo ta tsaya jikin kujera tace"ina kwana".
Ya watsa mata wani mugun harara ya ɗauke kai.
Hajja maida kwan data ɗebo zata kai baki tace"kaji bala'i,wallahi Abdullahi ka cika jaraba kamar ba daga tsatsona ka fito ba,yanzu ina laifi ta ce maka ina kwana?"
Oum ta miƙe tasa takalminta ta shige ɗaki,Hajja ta bita da kallon ƙasa ƙasa har sai da ta shiga ciki sannan ta juyo ta kalle shi tace"wai nan fushi take don na mata faɗa,to hauka ake zan biyeta ta firgita min kai a banza?"



Oum Rijalain 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.