Free chapter · Read without an account
ARE WE DESTINED TO MEET?
Tun daga wajen event Centre Maryam ta tabbatar da lallai bikin qawarta babban biki ne, manyan motoci ne bila adadin wa’inda da ka gansu kasan masu su sunchi sun tada wuya da kudi
An shirya wurin da kwalliya mai qayatarwa sosae, indae ka kalla to dole zaka sake kallo, An rataye fitilu a wurare daban-daban, an jera kujeru round da table, daga gefe kuma an jera wasu in a rectangle shape suna facing juna, sune na yan matan amarya da abokan ango, planners kuma suna ta kai kawo suna shirya abubuwan da suka rage kafin lokacin fara bikin ya yi.
Maryam ta tsaya tana dan dube duben inda zata ga sauran qawayen su.
“Maryam! Maryama!!”
Taji anata kwala mata kira
Ta yi murmushi a hnkali tache “bahijja” don tasan ita kadai che zata iya yimata irin wannan kiran a wannan lokacin
Seda tazo dab da ita sannan ta fara magana “zo mu tahi ga dakin da anka ware muna cen inda zamu zauna kahin kahin ango da abukkai nai su taho se ayi entrance tare, munata jiranki ki taho har safiyya ma tana chewa a kiraki”, a daidai nan suka iso kofar suka bude, Amaryar na zaune cikin ɗakin da aka ware mata tare da wasu ƙawayenta. Ta yi kyau sosai cikin kayan wankin amarya, hannayenta sun sha lalle, fuskarta kuma tana dauke da annurin Amarci da farin ciki.
Tana dago kai ta kalli maryam ta tsuke fuska “Ke kuma se yanzu kinka taho?”
Maryam ta shiga tana dariya tana kama kunnuwanta alamar ban hakuri
Safiya ta kalle ta daga sama zuwa ƙasa.
“Keda kinkache mini zaki taho da wuri?”
“Aikin gida ya riƙe ni, yi hankuri”
“Karya kike yi.”
Maryam ta zauna kusa da ita.
“Wallahi Mama ta aike ni yar kasuwa kahin in hito”
Safiya ta girgiza kai.
“Ke kullum Mama this, Mama that.”
“Kin san ni ka mata Aikin gida”
Dukansu suka yi dariya.
Wata daga cikin ƙawayen Safiya ta kalli Maryam.
“Maryam, kin sha kyau, wlhy kinyi kyau sosae, kinsan dama ke kayi ma kaya kyau”
Maryam ta yi murmushi.
“Nagode.”
Safiya ta matso Tayi mata rada a kunne “amma maryama biki na guda Kin zo daga ke se lip gloss kawai? Na dauka tunda aurena ne yau zanyi nasarar ganin kin shahwa ko powder che saboda ni”
Maryam ta yi dariya.
“Eh.”
“Missa baki son makeup?”
Safiya ta kalli fuskarta wani madubi da ke tsaye a dakin
“Kai, wallahi wasu mutane Allah Ya yi musu rahama, don kinga hwa kinada kyau ne, indama imran ze hito ayi auren nan kahin late comer yazo yayi mai wuff dake”
Maryam ta bugi kafadarta.
“Ke bari dan Allah.”
“Mi zan bari? Hwadin gaskiyar?.”
Maryam ta yi dariya tache ‘’ai yau ke in angonki yaggane ki nasan sedae a ruhe mai baki”
Safiya tache “toh ya ranki? Ni kam yau amarya ce. Dole in hi ki kyau.”
“To ai kin hi”
Safiyya ta rungume ta.
“Zanyi missing dinki qawata.”
Maryam tayi murmushi me sanyi itama tana rumgume ta
“Nima zanyi missing dinki”
Safiya ta sake kallon Maryam
“Amma fah…gaskiya… kin yi kyau sosai.”
Maryam ma murmushin ta sakar mata “kai Amarya safiyya ko bar zolaya ta haka”
Wata daga cikin yan matan ta shigo ɗakin da sauri.
“Safiyya! Anche mu shirya mu hito gasu nan sun iso.”
Safiyya ta mike.
“To gamu nan amma bari me makeup dinnan ta gyara min veil dinnan yadda ze ruhe huska ta”
Haka suka shirya suka fito amarya tana tsakiya tun daga wajen ake tashin qamshin turaren wuta na alfarma daya cika ko ina. Wata irin hadaddiyar mota akayi parking daedae kofar entrance din ango ya fito tare da sauran Abokan shi sun saka dakakkin shaddodi, haka suka jera da amarya da ango da abokan ango da yan matan amarya, suka shiga ciki ana buga kidan kwarya irin na al’ada, suna takawa a hnkali har amarya da ango suka zauna sannan suma suka zauna wurin da aka tanadar musu.
Yau maryam Tana cikin farin ciki sosae safiyya Babbar Aminiyarta zatayi aure, sedae tana iya kacin kokarin ta ganin tunanin yar uwarta Aisha be hanata sake wa ba, amma tunane-tunane basa tambayar izini kafin su shigo, nan ta tuna wani lokacin, shekaru da suka wuce, lokacin da Aisha na qoqarin yi mata kwalliya zasu je wani biki.
“Ki tsaya manah Maryam.”
“Aisha, zamu bata lokaci hwa”
“Ba zamu bata ba.”
“Ke kullun in zamu hita se kin tsaya kwalliya.”
Aisha ta yi dariya.
“In dai kin yi kyau ai shikenan babu wani maganar bata lokaci.”
Maryam ta yi murmushi kamar Aishar tana gaban ta, a hankali kuma murmushi ya rage har ya bar fuskarta tuna cewa har yanzu babu Aisha, babu labarinta.
“Maryam?”
Ta ji muryar bahijja.
“Naam?”
“Mi kika tunani? Kinsan ko so nawa nikkira ki? Tashi muje anche abukkan amarya suje su dan tattaka”
Maryam ta girgiza kai.
“Banson rawa. Bahijja”
Tashi muje ai ba se kinyi rawar ba muje dai wurin, a hnkali take tafiya har suka isa tsakiyar wurin, yanmata sunata rawa abunsu wasu suna pictures wasu suna videos, maryam ta tsaya dan gefe tana kallon su, kana ganin ta kasan a takure take, badon takurar bahijja ba da babu abunda ze taso ta daga wurinta.
Daga side din abokan ango kuma Fahad ya tsayar da idon sa a kanta ya na tunanin inda yasan fuskar, tun lokacin da suka fito da amarya zasuyi entrance yake kallon ta, tanada kyau sosai kuma yanada tabbacin yasan wata kema da ita.
Fahad ya qureta da ido sosai har seda jikinta yabata kamar ana kallonta, tana juyawa karab suka hada ido tayi sauri ta sauke idonta kasa tareda jin faduwar gaba, fahad na sanye da kaftan da babbar riga cream color mai kyau, tasha dinki, simple and yet classy.
Ya riƙe wayarsa da hannu ɗaya, yana magana da wani friend din su amma idonshi na kanta
Bayan ya gama maganar, wani yaro yazo cikin kunne ya rada mishi
“Fahad Mammi tache kazo ka bata mint zatayi liqi!”
Fahad ya yi murmushi.
“To ka ce mata gani nan zuwa.”
Yaron ya juya da gudu.
Fahad ya kalli wurin da yake cike da mutane ya sake qure maryam da ido yanajin bugun zuciyar shi na sauyawa da abubuwa da kuma tunani kala kala akan yarinyar, ya tashi ya nufi wurin table din uwayen ango inda mammi take da sauran manyan mata. Jin idon fahad din sun ragu akanta yasa ta jin wani relief tare da neman hanyar komawa wurin zaman ta dan ba yin rawar zatayi ba, tana kallo Fahad ya juyo ze bar wurin mammi Wata ƙaramar yarinya ta yi karo da shi.
Ya riqota da sauri don kar ta fadi
“Sannu. Kin ji ciwo?”
Yarinyar ta girgiza kai.
Fahad ya yi murmushi.
“To ki daina gudu haka kar ki fadi kinga akwai mutane”
Yarinyar ta yi dariya ta gudu. Maryam tayi murmushin ta me kyau tana kallon yarinyar, fahad ya sake bin maryam da kallo, idanuwansa suka haɗu da na Maryam na ɗan lokaci kafin ta sauke kanta qasa, a zuciyar shi yache “batada hayaniya ita kadai che bata shiga Tayi rawa ba”
Babu wata magana, Babu wata alama, Babu wani abu da zai sa Maryam ta yi tunanin cewa wannan mutumin zai zama wani mutum da ze shigo rayuwarta.
Sai dai…
Lokacin da Fahad ya dan yi nisa, ya sake juyawa.
Ya kalli Maryam na ɗan lokaci ba tareda ta lura ba, Sai ya juya ya ci gaba da tafiya.
Akwai wani abu a fuskarta da ya sa ya tsaya tunani. Ba kyau kaɗai ba Akwai wani abu da ya tuna masa da wata, Wata wadda bai yi tunanin zai sake tunawa da ita ba har abadah! Aisha!
Fahad ya runtse idanunsa na ɗan lokaci.
Sai ya ci gaba da tafiya kamar babu abin da ya faru. maryam na gefe da wayarta tana yiwa yan mata masu rawa video, sedae a karon farko ta hadu da fahad, wanda ya riga ya san abubuwa da ita bata sani ba.
Tana zaune tana kallon videos din da tayi ma abokan su da kuma amarya da ango se kawai wani tunanin ya fado kanta, babanta ya rasu a accident din da take kyautata zaton akwai wani abu saboda ana tsakiyar wani hargitsi a kampanin da yake aiki, shekaru biyu bayan nan maryam ta samu aiki a kampanin kuma bata rufe shekara biyu tana aiki a kampanin ba ta bache bat, babu ita babu labarin ta, kai Anya kuwa?
Daga nan ta fadah tunanin rayuwar baban ta
SHEKARU MASU YAWA DA SUKA WUCHE
Bashir (mahaifin su maryam) an haifeshi kuma ya girma a unguwar masallacin shehu da ke tsakiyar birnin sokoto. Babanshi ana kiranshi da Alh Atiku me fata saboda sana’ar fatar da yakeyi a majema. Yana sarrafa fata zuwa abubuwa daban daban kama daga jikkuna irin na fata na wanzamai dinnan, da tintimi da sauran su, Bashir yana da qane guda daya wanda tun a lokacin ake kiranshi da kawu saboda sunan Qanen alh atiku da ya rasu aka mayar mishi wato suleiman, suna rayuwa cikin kwanciyar hnkali da wadatar zucci se kwatsam watarana suna kwanche gobara ta tashi daga gidan maqota har ta kama gidan su, da yake lokacin sanyi ne iska na kadawa sosai kafin yan kwana kwana su iso wutar tayi nisa, daqyar aka fitar da bashir da kawu ta window, suna ji suna gani haka uwayen su suka qone a wutar, koda yan kwana kwana sukayi nasarar kashe wutar sedai gawar su aka fitar. A lokacin ne yaran suka shiga cikin damuwa da matsatsi sosai har aka kore su daga makaranta saboda rashin biyan kuddin makarantar. Haka dai suke rayuwa cikin kangon gidan su maqota suna yammusu abnci, watarana kawai Bashir ya tashi ya shiga kasuwa ya rinqa taya mutane daukar kayan sayayyar su yana kai musu mota suna biyan shi, da haka ya fara sabawa da kasuwar har wani bawan Allah da ke sayen tintimi wurin baban su ya ganshi a kasuwa yache yazo ze dauke shi yaron shago. Ya fara zama shagon mutumin cikin aminci yana kula da amanar shagon kuma mutumin yana bashi kuddin albashi masu dan tsoka wanda da kuddin yayi amfani ya maida kawu makaranta shi kuma yanata zama kasuwa, mutumin da ya aminta dashi sosai ya sakar mishi ragamar shagon shi kuma yana kula dashi bisa amana, har kwatsam Allah ya yima mutumin rasuwa, yaran shi kuma suka raba gado suka sayar da shago amma sun yi mishi ihsani sun bashi kuddi, wanda yayi amfani da wannan kuddin ya fara tashi sanaa ya Gina kanshi, har ya koma makaranta yayi yaqi da jahilci saboda kasuwancin yafi tafiya in Kanada ilimi. Yayi karatu tareda sanaa kuma sosai Allah ya bude mishi har ya fara yawon qasashen su Niger da Cotonou yana kasuwancin shi, a chan Niger ne Allah ya hadashi da mamar su maryam wadda ya auro ta ya kawo ta Nigeria. Kuma yayi nasarar kammala karatun shi wanda har ya samu aiki da kampanin northern crest holdings a wancan lokacin.
Maryam ta nisa ta sauke ajiyar zuciya, Batason dare yayi bata koma gida ba don haka ynzu duk hankalinta yana kan yadda zata bar wurin ba tareda safiya ta sani ba, batason mama ta tuqa tuwon nan tafison taje tayi, don haka ta dauko wayarta ta kira imran ringing biyu ya dauka “hello my beautiful kin qare inzo in dauke ki?” “Eh don Allah”
Yana isowa kofar wurin ya kirata, ta kalli safiya taga hankalinta ya dauku anata pictures, ta sulale ta fito ta hau mashin din imran suna tafiya suna hirar su ta masoya har suka isa gida tayi mishi seda safe ta shige.
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***