Free chapter · Read without an account
A FARMILIAR NAME
Duk saurin da take be hana ta tarar da mama ta tuqa tuwon ta ba, bayan ta mata mitar bata batta tayi ba suka dora da fira kafin ta kwanta ta gayama mama gobe daurin auren 10am ne don haka zataje da wuri gidansu safiya inda zaayi yinin bikin. Mama tace “Allah ya kae mu kuma ya bada zaman lfia”
Bayan ta shiga daki ta kwanta, se tunanin safiyya ya fado mata ta, tun farkon haduwar su wurin karbar confirmation Usman Danfodiyo University.
TWO YEARS AGO
Maryam na tsaye cikin layin karbar confirmation dinta na shiga jamia, ga gajia da yunwa duk sun dame ta, sauqin ta guda mutum biyu ne gaban ta daga su se ita, tana tunanin in ta samu ta karba gida zata wuce duk abunda yayi saura ya jira se gobe dan tagaji sosae, tana cikin tunanin taji ana taba ta tare da yi mata sallama “salamu alaikum, suna na safiyya, don Allah inaso in tambayeki course dinda aka baki, Inata neman yan course dinmu da zamu riqa yin Abubuwan school tare” Maryam ta juya ta kalli wadda tace sunan ta safiyya sannan ta ansa mata “wa alaikis slam suna na maryam an bani international relations amma ban sani ba ko in ni shiga wurin ansar confirmation din a chanja mini” safiyya ta zaro ido “baki son course din hln?” Maryam ta gyara tsayuwar ta “Aa inaso, nahi wasu suna chewa ana chanza musu in sun shiga” nan safiya tayi murmushi tare da sauke ajiyar zuciya “Alhamdulillah tundazu nika bidar masu international relations amma ban samu ba, Allah yasa kar su chanza miki, ni kinga na ansa tawa” ta dago ta tana nuna ma maryam takardar hannun ta sannan ta chigaba “kinga bari ma in jira ki can in kin ansa se ki sameni, ko da mota kikazo?” Maryam tayi murmushi don ta gane safiya irin Mutanen nan ne masu saurin sabo da sakewa da mutum babu ruwanta ta arzikin su she’s so simple and humble, ta kalli inda take nuna mata wata mota baka me kyau da alama motar tace sannan ta amsa “Aa banzo da mota ba” “okay naga layin ma ya kusa zuwa kan ki mutum guda ne gaban ki” maryam tayi murmushi “toh shikenan in na karba zanzo”. Babu dadewa na gabanta ya shiga ya karbo tashi sannan itama ta shiga, Tana Karbowa ta nufi Motar tun kafin ta isa safiya ta fito motar tana tambayar ta “shi aka baki ko? Allah yasa baa chanja miki ba” maryam tayi dariya ta miqa mata confirmation din tana dubawa taga baa chanza ba, da qarfi ta furta “yeyyy, Allah na gode maka na samu abukkiya coursemate dina” maryam se murmushi take safiya ta chigaba gaskiya naji daadi sosae nasamu Abukkiya kyakkyawa” Maryam tayi dariya “Ai kin fini kyau” sukayi dariya duka sannan safiyya ta bude wurin driver ta shiga maryam ma ta shiga dayan bangaren suka kama haryar barin makaranta, seda suka dan yi nisa sun fita second gate sannan safiyya ta kalli maryam kadan tana sake maida idon kan titi “wace shiyya kike?”
Maryam ta amsa “arkilla”
safiyya ta gyada kae “okay ni sama road nike bari in ajeki sannan in wuche”
maryam ta ansa da sauri “Aa ba se kin kaini gida ba, ki ajeni wurin gidan man ada zan samu Napep tunda ba hanyar mu guda ba”
“Ai inaso inga gidan ku tunda mun riga mun zama qawaye aiko?” Ta fada tareda dan kallon maryam din,
maryam tayi murmushi
“tho shikenan nima wata rana zanje naku gidan in shaa Allah”
suna tafiya safiya tanata yima maryam hira, duk da maryam ba me yawan surutu bace amma ta sake da safiya sosae sukayi labarin secondary school din da kowace tayi, da yar hirar su ta mata har suka isa gidan, maryam na ganin kofar gida rufe amma babu padlock yasa maryam tayi tunanin mama tashiga gidan su imran kenan, dan nan ne kadae wurin zuwanta, sedae taso mama taga sabuwar qawartata, bayan sun zauna ta bata ruwa tasha maryam ta kalli safiya “inagan mamata ta shiga maqwabta bari in kirata a waya”
“kar ki damu Bari kawai in wuche ai naga gida watarana zan dawo in shaa Allah, ranar Monday zamu fara lecture ki shirya dawuri se mu hadu gidan man ada mu wuche”
Maryam tayi mata godiya sosae sannan ta raka ta mota.
Tana komawa ciki tayi wanka tayi sallah sannan taci abincin da tagani kichen, ko baa gaya mata ba tasan nata ne mama ta aje mata, tana cikin cin abincin mama ta dawo, ai kam nan ta bata labrin qawarta safiya, mama tayi dariya ganin yadda maryama ta sake da wannan qawar tareda yi mata nisiha akan karatu da kuma kula da tarbiya.
Ranar Monday maryam ta shirya ta ci abnci Tayi ma mama sallama ta tafi ta jira safiya cen gidan man ada kamar yadda sukayi, maryam bata dade da zuwa ba sega safiya, nan ta dauke ta suka kama hanyar makaranta, yau safiya labarin Siblings dinta taba maryam, itace Auta tana da yanne maza biyu, se mace daya wadda hr tayi Aure yaranta biyu namiji da mace Areef da Afnan.
Sun fara karatu lafiya kuma cikin saa, dayake basu sa wasa ba abunda ya kaisu shi sukeyi, kuma a nan safiya ta fahimci maryam tanada qoqari sosai, ta fahimci maryam irin Mutanen nan ne da karatu baya basu wahala da sun karanta abu yana zaunawa daram a kansu, ta dalilin haka abuttar su tayi qarfi sosai saboda maryam tana yima safiya tutorial tayi mata bayani sosae inda bata gane ba, nan suka samu qarin qawa, bahijja, nan qawancen ya qara qarfi saboda dukansu masu son karatu ne, hakan yasa abuttar tayi qarfi sosai dan gidan su safiya babu wanda besan maryama ba tun sunajin maryama a baki hr ta zama yar gida, mama ma ta san safiya sosae dan yawanci itake kae maryama gida, kullum kuma mama seta yimusu nasiha tare da jan kunne game da karatu da kula da tarbiyar su.
Karatu na tafia musu lfia an gama 1st semester an shiga second wani lecturer dinsu Dr mukhtar Talba wanda ya daukesu course din international law da sukayi borrowing a faculty of law ya nuna interest kan safiya, kyakkyawan matashin lecturer kuma lawyer me ji da kudi da kuruciya ga ilimi don har ya kai matakin PhD a shekaru kadan, ya Gaya mata tun first semester yake ganin ta kuma yaji yana sonta, amma bayason mutane suyi misunderstanding shiyasa seda ya bari an qare first semester din sun riga sun gama borrowing course dinshi sannan ya sameta da zanchen, tunda sun riga sun gama borrowing course dinshi mutane bazasu yi zargin komai gameda alaqar su ba. Safiya ta amincce amma tache idan da gaske yake yaje gida ya samu babanta, ya nuna mata da gasken yake saboda yaje ya Sami babanta Alh Usman maitambari ya nemi izinin magana da ita, kuma babanta ya bashi dama abu kamar wasa soyayya takullu tsakanin dr muktar da safiya wanda ynzu ga matakin aure sun taka.
Maryam taja numfashi sannan tashi zaune tana tunanin ko Yaushe tata alaqar da imran zata kaisu ga matakin aure? Kwanakki da kawun ta yace an bashi dama ya turo babu wata amsar me gamsarwa daya bata, gashi jiya da kawun nata yazo gidan seda ya tambaye ta ya ake ciki dan beji mama tace mishi komi ba.
Tashi tayi ta shiga toilet tayi arwallah ta fara sallar nafila, Tayi adduoi bayan ta qare sannan ta kwanta.
Washegari Da safe ta tashi cikin lokaci ta gyara waken da zata yima mama kosai da kunu, ta kai gidansu imran saboda innaa mamar imran tana niqa, bayan an gama take gaya mata ai imran ya fita tun da safe akwai inda aka kirashi zeyi wani delivery, ta kira qanen imran “auta zo ka kaima maryam niqan nan nata gida” ya fito daga dan dakinsu ya gaida maryam sannan ya dauki bucket din ya fita, maryam na binshi a baya, bayan ta iso gida ta hada kosai ta soya tasa ma mama nata a food warmer tasa kunun a flask ita kuma tasa nata a cup da plate ta zauna ta chi a natse sannan ta wanke kayan tayi wanka ta shirya cikin atampar ta purple me stars a jiki, ta dauki qaramar handbag dinta ta shafa kwalli a Idonta da lipgloss a dan Qaramin lips dinta ta fito, har zata kira imran se ta tuna inna tache ya tafi delivery se kawai tayi sallama da mama ta fita ta shiga keke napep ta nufi unguwar su safiya.
An daura auren safiyya da Angonta mukhtar Talba a masallacin jumua na sultan Abubakar III wanda dimbin Jamaa suka samu halarta, daga nan ango da abokan shi suka nufi gidansu safiya domin daukar pictures.
An yimusu iso a babban parlorn da amarya da qawayenta suke ciki sunata nishadi suna jiran isowar su, anata hotuna da raha, idon fahad yana kan maryam a zuciyar shi yana yaba kyaun ta da kuma tsantsar kamar ta da Aisha wadda ya sani tun ýan shekarun baya. Ango da abokan shi sun gama hotuna sun tafi se kuma yamma dangin ango sukazo daukar amarya Safiyya zuwa gidanta, safiyya tasha kukan rabuwa da mamanta hajiya Ruqaiya, bayan nasiha me ratsa jikin da uwayen Safiyya suka yimata aka dauki amarya zuwa gidanta cikin convoy.
An yi sayen baki bisa al’ada an ba yanmatan amarya kuddin su, daga nan kuma aka tashi ana yima ango da amarya sallama
“Allah ya ba ku zaman lafiya,” maryam ta faɗa a hankali a lokacin da take rungume da safiyya tana dan bubbuga bayanta Alamar rarrashi, Safiyya se kuka take maryam na bata hakuri “kiyi hakuri mana matar dr ai nan da one week zaki fara fitowa mu hadu school” daqyar sukayi sallama ta fito, koda ta fito motocin duk sun cika saboda ta tsaya rarrashin Safiyya, tsaye take tana tunanin ko ta kira imran? Amma bata sani ba ko ya koma gida ynxu? Inma ya koma tasan gajiye yake dukda ya kirata ya gaya mata in ta qare ta kirashi amma batason tayita saka shi dawainiya, Ta sauke ajiyar zuciya, ko dae napep zata nema amma kuma dare yayi, tana cikin tunanin mafita wata mota qirar Mercedes GLB class ta tsaya a gabanta aka sauke glass se taga wannan matashin ne da ke Binta da ido tun jiya, kuma a dd lokacin wayarta ta fara ringing ta duba, mama ke kiran ta itama tasan mama ta fara damuwa saboda dare ya fara yi qarfe 9pm tayi, Sallama yayi mata yana dan murmushi se ta ansa tana sauke kanta qasa,
“suna na Fahad Balarabe, kizo in sauke ki gida”, tayi shuru Tana dan nazarin yanayin fahad din ganin haka ya sake cewa “please ki shigo muje kinga dare yana yi”
“aa Nagode zan samu abun hawa a titi”
se kawai ya fito ya zagayo ya bude mata qofa “please get in”
a dd nan kuma wayarta ta sake qara a karo na biyu ta kalla, mama che ke sake kira, a hankali tana karanto addu’o’in tsari a ranta tayi bismillah ta shiga ta zauna, rufe motar yayi sannan ya juya ya shiga ya kama hanya.
Sun hau main road ya juyo ya kalleta
“wace unguwa zamuje?”
“arkilla” ta amsa a takaice
“okay”
Tafiya sukayi shiru na dan wani lokaci
“Baki Gayamin sunan ki ba”
“maryam”
se ya maimaita sunan
“Maryam.”
Ta dan juyo
“Na’am?”
Fahad ya yi murmushi.
“Ina son in tambaye ki wani abu please”
A hankali ta kalleshi
Ya ɗan yi shiru kafin ya fara magana
“Kin taɓa jin wani ya ce kina kama da wata?”
Maryam ta ɗan yi mamaki.
“Wata?”
“Eh.”
“A’a babu”
Fahad ya kalle ta na ɗan lokaci.
“Akwai wata da na taɓa sani wacce take da kama dake sosai .”
Maryam ta ɗaga gira.
“Wacece?”
Fahad ya yi kamar yana tunani. Sannan ya amsa
“Sunanta Aisha.”
Rass gaban Maryam ya buga numfanshinta ya tsaya na yan sakanni
“Aisha?” Ta tambaya
Fahad ya lura da canjin yanayin ta kafin ya ansa
“Eh.”
Maryam ta daga kai ta kalle shi.
“Aisha?” Ta sake maimaitawa
Fahad yayi shuru Kamar me tariyo abunda ya faru sannan ya amsa
“Na san wata Aisha me kama da ke”
Zuciyar Maryam ta fara bugawa da sauri.
Shekaru fiye da uku kenan ba ta ji wani mutum daga waje yana magana game da Aisha ba.
“Tana ina ne kuma Kanada picture dinta?”
Fahad ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Na daɗe ban gan ta ba.”
Maryam ta kalle shi sosai.
“A ina ka san ta?”
Fahad ya yi murmushi kaɗan.
“Ina aiki da kampanin Northern Crest Holdings Abuja branch, itama haka amma ita a sokoto branch take.”
Sai ya sauya maganar da sauri
“Amma kina kama da ita sosai gaskiya.”
Shuru maryam tayi bata sake magana ba tana tabbatar da yar uwarta che jin ya ambaci northern crest
Shi yayi breaking silence din da chewa
“Zaki damu idan na dan tsaya gawon nama in dauki Mammi?”
“Mammi?” Ta maimaita da sigar tambaya
“Mahaifiyata.” Ya amsa
Maryam ta ɗan yi shuru don batason matar tayi mata wata fassara.
“To.” Ta amsa bayan dan lokaci
Sunyi parking bakin gate din wani gida, ya kira mammi a waya ya sanar da ita yana waje, after few minutes ta fito
Fitowa yayi ya bude ma mammi kofar motar ta shiga maryam ta sadda kanta qasa ta gaishe ta,
Matar ta kalli Maryam da murmushi ta ansa gaisuwar sannan ta kalli fahad
“Itache kache zaka nuna min?”
Fahad ya yi dariya, maryam kuma se ta fara mamaki “me ke faruwa?” Tayi tambayar a ranta
“Eh, ita ce nache miki na gani jiya”
Maryam ta sake gaishe da ita cikin ladabi, tana mamaki toh me yache ma maman shi game da ita? Mammi ta ansa da fara’arta
“Allah ya albarkace ki.”
Da “Amin” ta ansa amma aranta tanata tunani
Sun dan yi nisa fahad ya fara magana
“maryam ai ya kamata ki bani number ki mu riqa gaisawa idan na shigo sokoto”, bataso bashi ba amma ganin mahaifiyar sa tana cikin motar se Tayi shiru batache komi ba, wayar shi ya miqo mata, a ranta tana mamaki toh baya jin kunyar mahaifiyar sa kodai ba ita ta haife shi ba?
Ta karba ta saka number dinta ko ba komai zata sake tambayar shi game da Aisha don ta tabbatar yayarta che tunda ya ambaci sunan kampanin
Sun sauketa gida lfya tayi godiya sosai cikin natsuwa da ladabi fahad nata kallon kofar gidansu har ta shige sannan yayi saving number dinta a take yana cikin driving ya shiga WhatsApp yayi searching sunan ta ya shiga profile ya kalli dp dinta, dam dam kirjinsa ya buga yana kallon picture din da ita da yayar ta Aisha ne, Yayi mata massage
“Ya gajiyar biki?, kiyi saving number na, Fuhad ne”
Koda ya shigo gida ta gaida mama suka zauna sunata firar uwa da ya, Seda ta qare fira da mama tana bata labarin yadda bikin ya kasance mama ta amsa mata “ai nima na tahi yinin bikin amma ina cikin gidan chan sashen mahaifiyar safiya kuma tun bayan la’asar niddawo gida”
maryam ta bude baki “laa mama missa baki kirani ba in taho wurinki? Mu muna chan parlorn baqi”
mama ta dan kalleta “in kiraki ki taho kiyi min mi?”
maryam tayi dariya, daga haka ta tashi Tayi wanka Tayi shirin baccee, tazo kwanciya ta dauko wayarta ta shiga WhatsApp tana duba messages se taga na fahad, Batayi replying dinshi ba se kawai tayi mishi tambayar da keta damunta ganin yana online
“Fahad?”
“Naam?”
“Ka ce ka san Aisha…”
Fahad ya dade beyi replying ba kafin yache .
“Na ce na taɓa sanin wata Aisha me kama dake, tayi aiki a northern crest holdings”
“Me ya sa ka ce ina kama da ita?”
Fahad ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Wani lokaci mutum yana ganin wani abu a fuskar mutum se ya tuna masa da wanda ya taɓa sani.”
Maryam ba ta gamsu da amsar ba.
Amma bata sake chewa komai ba ta kashe data kawai ta kwanta da tunani iri iri a ranta.
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***