Free chapter · Read without an account

THE REASON

by Nihaal Maalik · KIRAN KADDARA

Maryam ta shigo dakinta da dare bayan ta qare fira da mama da niyyar zata dan yi karatu kafin ta kwanta, amma se ta zauna a gefen gadonta, tana kallon ceiling, hankalinta yana wani wuri daban.

Tun bayan da Zaid da Fahad suka tafi, maganar da sukayi ɗin nan ta kasa fita daga ranta.

Ba wai saboda Zaid ba ne, Sai dai saboda yadda komai ke faruwa 

Bataga alamar Zaid ze aureta ba amma meyasa yazo ganinta tun daga Abuja har sokoto?  bayan ta kula da chewa rayuwar su ta sha ban ban da juna, meyasa ze zo? Ai wannan yafi qarfin ta. 

Jiya warhaka bata ma san cewa akwai wani Zaid ba, Yau kuma se gashi yazo wai ganinta 

Ta sauke numfashi a hankali.

“Hmm.” 

Ta dauko wayarta, ta duba screen ɗin, sannan ta ajiye.

Akwai wani abu da yake damunta.

Sunan Rahman balarabe! 

 Fahad yache mata sunan shi fahad rahman balarabe sunan yayan shi zaid Rahman barabe

Maryam ta ɗan tsaya.


“Rahman balarabe…”

Ta maimaita sunan a hankali.

Sai kwatsam wani abu ya zo mata a rai.

Aisha.

Maryam ta miƙe daga kan gadon.

“Subhanallah…”

Ta zauna kuma.

Aisha ta taɓa yin magana akan sunan wannan familyn, shin ta sansu ne?

Shekaru da suka wuce ne.

Maryam tana junior secondary lokacin, kuma a lokacin bata taɓa ganin maganar a matsayin wani abu mai muhimmanci ba.

Amma yanzu…

Ta fara tunawa.

Aisha ta kasance tana yawan zama da laptop ɗinta, tayita rubuce-rubuce, tana waya da mutane, wani lokacin kuma idan Maryam ta shigo ɗaki sai tayi sauri ta rufe wayarta.

A lokacin Maryam ta ɗauka kawai yanayin aikin Aisha ne.

Amma wata rana…ta tambayeta 

“Aisha, me kike ta bincika haka?”

Aisha ta kalleta sannan ta yi murmushi.

“Ba komai. Wani family nike bincike.”

Maryam ta yi dariya a lokacin.

“Wane family kuma?”

Aisha bata amsa nan take ba seda ta dauki dan lokaci

“Wani lokaci bazaki gane wasu abubuwa ba se kin girma”

Maryam ta yi dariya “idan na girma so kike in zama detective ne? Kema dai ki aje wani bincike kiyita aikin ki kawai”

A lokacin bata fahimci komai ba.

Amma yanzu…

Ta ji zuciyarta ta fara bugawa da sauri.

Wane family ne Aisha take bincike?

Rahman Balarabe family, Toh meyasa?

Maryam ta buɗe idanunta.

Ta furta sunayen a hankali.

Zaid Rahman Balarabe.

Fahad Rahman Balarabe.

Ta zauna shiru.

Wani irin sanyi ya ratsa jikinta.

“Kar dai…”

Ta kasa ƙarasa maganar.

Amma yanzu wani abu ya fara haɗuwa a kanta.

Babanta ya samu issue da northern crest holdings wanda na Rahman Balarabe family ne, ana cikin binciken issue din ya rasu,

Aisha tana investigating family din rahman Balarabe, Aisha ta ɓace.

Shekaru sun wuce.

Yanzu kuma ita, Maryam Bashir Misalati, ana tunanin aurar da ita cikin wannan family.

Ta tashi ta nufi ƙaramin wardrobe ɗinta.

Ta fara bincika wasu tsofaffin abubuwan Aisha

Tsohon diary da wasu Wasu papers se Hotuna.

Maryam ta zauna a ƙasa tana dubawa ɗaya bayan ɗaya.

Babu komai.

Se chan ta ga wata tsohuwar takarda da aka nannade cikin wani littafi, Ta buɗe ta.

Ba ta fahimci abin da ke ciki ba.

Akwai wasu sunaye da dates da Aisha ta rubuta da handwriting ɗinta, Maryam tanata kallon paper din sosai.

Amma kafin ta samu wani abu mai ma’ana, sai taji Mama ta qwalo mata kira daga waje.

“Ke Mayrama!”

Maryam ta yi saurin ɓoye takardar.

“Na’am Mama!”

“Zo nan”

“Gani nan zuwa.”

Ta mayar da takardar inda ta same ta.

Amma dai tunanin zuciyarta ya riga ya fara canzawa


Abuja, Nigeria.

A ɗayan ɓangaren kuma, Zaid yana zaune a ɗakinsa an Abuja.

Laptop ɗinsa tana ajiye a coffee table a gabansa.

Wasu emails suna loading, Wasu documents suna gabansa.

Amma hankalinsa baya kan aikin gabadaya, Ya ɗaga kai daga kallon laptop ɗin.

Maryam!

Sunanta kawai ya zo masa a rai.

Ya ɗan yamutsa fuska.

“Meyasa nike tunanin ta?”

Ya dan jingina da kujerar sa

Bai san ta sosai ba.

Basuyi magana ba gaisawa kawai sukayi, se ya tuna da yanayin maganar ta, hausar ta na bashi dariya sosai, yayi murmushi da ya tuna yadda ta furta “awo”

“Maryam Bashir me salati” ya fadi sunan 

“Bashir me Salati” ya sake fadi sannan yayi shuru

Ya ɗauki wayarsa ya duba lokaci 

Sai ya ga missed call daga Mammi, Ya kira ta.

“Assalamu alaikum, Mammi.”

“Wa alaikumussalam. Kana gida?”

“Eh.”

“Ka qi shigowa don kar in maka magana ko zaid? Shiyasa abncin ma kache a aika maka a part Dinka ko? Don kar ka ganni”

Yache “aa mammi ina dan aiki ne, kinsan ko Ina nan dole in yita duba abubuwa”

Mammi tache

“Yayi kyau, Toh Ka yanke shawara?

Zaid ya yi shiru na ɗan lokaci.

“Bakaji ba ne? Nache kayi tunani?”

“Eh nayi”

“Me ka yanke?”

Zaid ya sauke numfashi.

“Zan yi” Zaid yaji amsar ta fito bakin shi kamar an tunkudo ta da qarfi”

Mammi ta yi shiru kamar ba ta yarda da abin da ta ji ba.

“Da gaske?”

“Eh, Mammi.”

“Zaid, Allah ya saka maka da alheri.”

Zaid ya ɗan yi murmushi.

“Ameen  Mammi na, Mammi Anya banyi saurin yanke hukunci ba? Ina jin kamar banyi dd ba.”

Mammi ta yi dariya.

“Ba dole sai ka san komai yanzu ba, a hnkali zaka gane nufi na, chewa nayi ka yi aure ba chewa nayi za’a kaika prison ba.”

Zaid ya yi ɗan murmushi.

“Okay.”

“Allah ya nuna mini ranar auranka.”

“Ameen.”

Suka yi sallama.

Zaid ya ajiye wayar. Ya fara tunani? Meyasa nache zanyi? Inaga saboda kawai idan nayi auren mammi zata dena damuna da maganar auren, kuma yarinyar ma ai zan iya wucewa Amsterdam in batta a nan kawai

Ya kalli laptop ɗinsa.

Har wannan karon ma bai buɗe emails ɗin ba.

Ya yi tunani na ɗan lokaci.

Maybe da gaskiyar mammi, ya kamata ache yanada mata ynzu, Maybe lokacin auren yayi

Ba wai saboda yana son Maryam ba, A’a.

Shi ina shi ina soyayya kuma da yarinya qarama ma kamar maryam, Amma watakila lokaci ya yi da zai daina barin aiki ya mamaye komai a rayuwarsa, Watakila auren zai kawo masa wani sabon abu.

Ya sake ɗaukar laptop ɗinsa

Se ya tuna yadda tache “awo” ai kawai dariya ta kubce mishi Yayi smiling ya maida hnkali kan aikin shi

Amma shi ma bai san cewa Maryam ta riga ta fara neman amsar wata tambaya da za ta canza komai ba.

Aisha tayi binciken Balarabe family, saboda me?


Sokoto 

Washegari da safe maryam ta shirya bayan ta qare aikache aikachen da zata yima mama, tayi mata sallama ta tafi makaranta. Har zata tsaya gidan man Ada ta jira Safiyya se kuma kawai Tayi tunanin ba lallai safiya tazo ba kuma tun da aka kaita bata samun ta a waya don haka se kawai ta wuche bus stop ta shiga bus, takawa Tayi daga bus stop zuwa department dinsu se ga wata mota Tayi parking kusa da ita, tasan motar, motar dr muktar Talba che, Safiyya ta fito daga ciki, Ihu sukayi suna rungume juna sannan maryam ta saketa tana Binta da ido 

“qawata aure yayi daadi hadda kashe waya ko? Ai Ban aza zaki shigo school yau ba, kuma Inata kiran wayar ki bata shiga” 

safiya ta sauke ajiyar zucciya

“ke tun lokacin bikin nan hwa Wayata ta bache, kuma ba dole in shigo school ba qila mutumin nan zeyi test kinsan ya iya daukar mutane by surprise”

Maryam ta gyada kai

 “Ana Biki anka sache wayar amarya amma dai barawon nan ya cika, wallahi kuwa prof na iya yimuna test kedai zo mu shiga ciki mu dan yi karatu, wai kinsan jiya har shigowa daki niyyi zanyi karatu amma wani abu ya dauke min hankali, ke kan ai nasan dr zesa ki karatun dole amma se ya gama angwanci tukunna”

Safiya tayi dariya 

“Bakida m maryam, bari in gyara parking dinnan se mu shiga” ta fadi tana komawa ta zauna cikin motar

Maryam tayi murmushi

“kaga matar dr har an fara tuqa motar dr”. Safiyya ta wuche tana gyara parking Tana dariya. 

A ciki suka hadu da bahijja, maimakon karatun da sukache zasuyi se suka bige da fira, sunata fira suna tsokanar safiyya wai har tayi kumatu, a haka har lecturer din ya shigo, saukin su daya beyi musu test din da suke tsammani ba

Bayan sun qare lecture suka fito suna takawa zuwa wurin da safiya tayi parking suna firar su,

Safiyya ta kallai Maryam 

“ke akwai wani cousin dina fahad, ya kira mama yanason magana dani wai ya kasa samuna a waya, se mama ta tura mishi number din dr ya kira bayan da suka gaisa yache dani yakeson magana, dr ya bani, se yayita yimin tambayoyi akan ki, ni fah na dauka ma sonki yake, se da mukaje gidanmu mu gaida su mama shekaraniya se nike gayama mama se tache wai aa yayan shi zaid akeso a hada dake, inata Allah Allah in kira in gaya miki amma bnda waya, har zanche mama ta Turomin number ki ta wayar dr se nache bari dai mu hadu ido da ido firar se tafi daadi a fili. 

Maryam tayi murmushin yaqe

“hmm, Kedai har sunzo gidan mu jiya shi da Fahad din”

Safiyya da Bahijja a tare suka zaro ido waje

“kinga zaid din? Cousin dina ne fah amma bnsan ma ya fuskar shi take ba, rabon da in ganshi an dade sosai, yana chan qasar waje beson zama Nigeria, ina dai iya tuna yadda yanayin shi yake lokacin ina qarama sosai yayita daure min fuska wai shi baya wasa da yara” 

Bahijja ta fashe da dariya “toh ai in maryam ta auri irin wannan mijin shikenan ba wanda zeje gidansu, ita bata saurin sakin jiki da Mutane shi kuma yana daure fuska, duk wanda yaje gidansu so daya baze sake komawa ba”

Maryam tayi dariya sosai “ai ko jiya da nigganai haryanzu ma be dariyar”

Safiyya ta gyada kai “ai dama daqyar ya chnja tunda halin shu ne haka yake, amma kin amince? Don Allah ki auri cousin dina kinsan ya hadu, ko sadda muna yara duk family dinmu ba Wanda ya kaishi kyau, gashi kema ki kalli yadda kike, zaku haiho muna cute babies fah”

Bahijja na bude baki alamar mamaki tana kallon safiyya “in kinada hoton shi nuna min in gani, ai dama hadadde me kyau ya dache da maryam saboda mu samu yara masu kama da larabawa”

Maryam ta riqe baki “Tabb lallai ma sannun ku, ni zan auri wannan me fuskar shanu? Wai kun manta da imran dina hala? Zan hwada mai duk abnda kuke chewa”

Safiyya ta dan bata fuska, don Allah kakki hwada mai kinsan imran na ganin mutuncin mu, kuma duk inda anka hito ai mu ka kare mishi ke daga mazan ka kawo miki hari, amma hwa wanga dan uwana na dole inyi mai campaign”

“Bahijja ta gyada kai alamar gamsuwa “nima dai inaga zan bi Safiyya muyi campaign don kamar imran be tashi aure ba ynzu”

Maryam ta bude baki “don yana dan uwanki ai ba sona yakai ba, dole anka sashi yazo ya ganni, amma imran yana so na”

Safiyya ta kalleta 

“ke ai da kun dan saba dole ya hwara son ki, ko don kyaun ki da gashin ki, ina tuna lokacin muna qanana in mun tahi Abuja hutu gidansu, be wasa damu ko Kadan, amma weekends se yazo yache ma mammi wai ta bari ya gyara muna gashi in yasso in an kaimu saloon kitso kawai za’a yimuna”

Maryam ta fashe dariya 

“wa yaga namiji da gyaran gashi” bahijja ma na tayata dariyar 

Safiyya tayi murmushi 

“wallahi kuma lfya yake gyara muna shi ya wanke, kitso kawai ne be iya ba kuma shima yana chema mammi ta bari ya gwada se tache aa kar yasa kan mu yayi ciwo”

A dd nan suka iso kofar gidan su maryam ta sauka tana yi musu se anjima tana chewa ku tahi zuwa bidar ma yayanki mata nikam kinga inda zaa kaini chan, ta fadi tana nuna qofar gidan su imran 

Safiyya tayi dariya 

“ai indai campaign ne ynzu ni hwara yima yayana se na tabbatar da ya shiga ran ki don haka ki shirya hwara son shi kawai 


Join our WhatsApp group 


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


7ECA89C6-EF8F-4DB9-98CF-FDD365D7B74F.png

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol