Free chapter · Read without an account
THE SACRIFICE
Maryam ta shigo gida ta tarar da mama tana zaune tana tilawar Qurani, tayi sallama ta zauna gefen mama tana sauraren yadda mama ke karatun suratul Yusuf cikin ruwayar warsh, seda mama ta qare ta rufe quranin sannan Maryam ta gaisheta tareda chewa “mama wai Yaushe zaki koyi karatu da ruwayar hafs? Tafi daadi fah”
mama tayi murmushi
“tashi kije kiyi wanka ki chi abnci yana nan na aje miki a kitchen tunda bakida abin hwadi” maryam ta tashi Tana dariya zata shiga daki, se taji mama na chewa “in kin chi abnci ki shirya kije gidan kawu yanason magana dake” da “toh” maryam ta ansa ta shiga dakinta.
Da yamma taje gidan kawu, kafin ta fita seda tayita nanata ma mama kada ta daura abncin dare, idan ta dawo ita zatayi, tana shiga gidan kawu yan yaranshi sunata jin daadi ga anty maryam tazo saboda sunsan tana riqo musu yar tsaraba, ai ko nan ta shiga rarraba musu sunata jin daadi, mamansu wadda ake kira da gwaggo A’i tana fadin “maryam ganinki yayi wahala in akayi magana kiche yanayin makaranta alhalin ke kanki bakison zumunci”,
maryam tayi dariya
“In Shaa Allah zan gyara”
Gwaggo A’i tayi mata iso wurin kawu sannan ta tashi ta basu wuri. Bayani kawu Yayi mata daki daki akan maganar da yayi da baban imran, “meramu, sadda Alh Usman yattaho mini da maganar zaidu na hwada mai nicce akwai wani yaro nan maqwabtan ku wanda ka bidar ki don haka su bari se nayi magana da babanai, dama tun kwanakkin baya nibbaki saqo ki hwadi mai ya turo amma naji shuru shiyassa ni isko Shi da kaina, ya yimin gamsashshen bayani Akan ynzu dai imrana beda halin yin aure, ko gidan da suke kega zaman gadi sukai daki biyu na shi imrana da qane nai su ka kwana cikin daki guda, sannan duk kusan komi na nauyin su shi a dauke dashi shiyasa be wani shirin aure, gashi ba tsayayyen aiki gareshi ba se harakar saqon ga da shikai, don haka babu matsala, shi baze ga lehin mu ba in anba wani damar bidar ki, ynzu meramu shawara zan baki, kega dai shekarun ki gaba sukai ba baya ba, inda ache baban imrana ya bamu lokaci yache kamar nan da lokaci kaza za’a shirya kega se mu jira, amma kega babu wata hujja da za’ache ynzu ki zauna zaman jira nai. Shi Alh Usman yache min in dai maganar ta yiwu basu ma son asa lokaci me tsawo saboda so sukai ayi a gama yaro ya koma chan qasar da shike wurin Kasuwanci nai. Maryam bazan tursasa ki ba saboda ba’a yima diya dole amma shawara nika baki, kitai kiyi tunani ki gani, ya kamata ache kinyi aure ynzu, kar ki tsaya jiran lokacin da bamusan sadda zezo ba, inason in sauke wanga babban nauyin da a bisa kaina na hakkin dan uwana in yimiki aure tun inada rai maryama”. Maryam dai babu baki se kunne, ta saurari kawu tsab sannan ta tashi tayi mishi sallama ta fito tsakar gida, tayi sallama da gwaggo A’i zata tafi gida, nan take tambayar me sunanta (maryama qarama) akache ai suna junior waec se yamma take dawowa gida daga makaranta, adduar saa da nasara tayi mata, haka ta fito ta dawo gida wajikinta duk a sanyaye.
Da dare bayan Maryam ta qare girka abncin dare ta shigo dakinta ta yi wanka ta shafa mai sannan ta zauna a kan gadonta tanata tunanin imran, ya zaayi ta rabu dashi? Ina baze yiwu ba, ko shekaru ze dauka kafin ya shirya zata jira shi, ita bata taba son kowa ba se imran, zuciyarta ta imran che bazata iya qara son wani ba, tana tuna tun lokacin da suka fara haduwa dashi suna gaisawa a matsayin maqwabta har wata alaqa ta qullu tsakanin su, imran mutumin kirki ne bazata iya rabuwa dashi ba. Ta dauko takardar da ta taba gani cikin kayan Aisha tana kallo,
Ta sake buɗe ta..
Names, Dates.
Wasu abubuwan da bata fahimta ba, Ta ɗan yamutsa fuska.
“Me kikayi bincike akai ne wai, Aisha?”
Ta tuna lokacin da Aisha take yawan zama da laptop ɗinta tana bincike-bincike.
A lokacin Maryam ba ta damu sosai ba.
Amma yanzu komai yana dawo mata a hankali.
Balarabe.
Ta sake kallon takardar.
Idan da gaske Aisha tayi investigating ɗin wannan family ɗin, to me yasa?
Me yasa kuma ta bache?
Kuma me yasa yaron wannan familyn da take bincike akai ynzu yazo ache wai yanason auren ta?
Maryam ta sauke gwauron numfashi.
“Ya Allah…”
Ta jingina da bangon gadonta
Ita Bata san Zaid ba, amma ai fahad yache mata yasan Aisha, Sau ɗaya ta hadu da zaid.
Taga alamun Zaid mutum ne mai nutsuwa sosai, kuma tunda ya zo gidan jiya, Maryam ta ji kamar tana magana da wani mutum da ya fi ta shekaru da yawa, a hnkali tache “kai wannan ba warina na bane”
Ba wai tana tunanin yana da wani abu mara kyau ba.
A’a.
Amma akwai wani irin nisa tsakaninsu.
Shekarunsu, yanayin rayuwar su. Komai ma ya bambanta.
Maryam ta rufe idanunta.
“Ko dai in yadda da auren wannan mutumin da mukeda tsananin banbanci dashi saboda in gano wani Abu da ban sani ba?”
Tambayar ta tsaya a ranta.
Sai kuma wata tambaya ta biyo bayanta.
“Idan ban aure shi ba fa?”
Idan nache a’a fa?
Zai yiwu in rasa wannan damar gaba ɗaya.
Zai yiwu ba zan taɓa gano abin da Aisha ta gano ba, ko kuma inda take ynzu
Ya rabbi ya zanyi da imran? Kawu yache sunje sun samu baban shi sun mishi bayani kuma ya fahimce su tunda imran be tashi aure ynzu ba, yache kar su damu ze yima imran bayani, amma tana tunanin anya imran ze fahimce ta?
Maryam ta yi shiru.
Ta kalli hoton Aisha da ke kan ƙaramin shelf ɗinta.
“Ki yafe mini Aisha.”
Ta ɗaga hoton.
“Amma zan yi.”
Zan gano me kika boye min kuma zan gano inda kike in shaa Allah
Ta shiga toilet tayi arwallah ta fito ta fara jera nafiloli tana addua tana neman zabin Allah, batayi baccee ba se bayan da Tayi sallar Asuba, Tayi azkar dinta na safe sannan ta dan kwanta tunda dama batada lecture din safe.
Washegari da safe, Mama na zaune a kitchen zata fara fere dankalin Hausa se ga Maryam ta shigo a hankali.
“Mama ina kwana”
“Hmm, kina lfya kuwa maryam? Kin ga idonki? Kuka kikayi?”
Mama ta kalleta.
“Zo ki zauna.”
Maryam ta zauna kusa da ita ta karbi dankalin da wuqar
Mama ta fara yimata magana
“Kin yi tunani akan maganar ku da kawu?”
Maryam ta yi shiru.
“Eh mama”
Mama ta kalleta.
“To me kika yanke?”
Maryam ta sauke idanu.
“Duk yadda kuka che dd ne mama, jiya nayi sallar dare sosai kuma na roqi Allah ya yimin zabi na alheri.”
Mama ta tsaya.
“Kin tabbata maryam?”
Maryam ta ɗaga kai.
“Eh in shaa Allah”
Mama ta sauke numfashi, don ta lura da yadda Maryam take.
“Amma kina farin ciki maryam? Bnso a yimiki dole”
Maryam ta ɗan yi murmushi.
“Eh, Mama.”
“Maryam.”
“Naam” ta amsa cikin muryar kuka
“Ki faɗa min gaskiya.”
Maryam ta yi shiru.
Mama ta ajiye abin da ke hannunta.
“Ba dole ki amince ba saboda ba wanda ze zauna miki dashi. Idan baki son shi, ki faɗI”
Maryam ta kalli mahaifiyarta, ya zaayi tache mata ta amince saboda taje tayi bincike? Inaa se kawai ta girgiza kai
“Mama, ba matsala in shaa Allah”
“To miye na kuka kuma?”
Maryam bata san abin da za ta ce ba.
Ina son in aure shi ne saboda ina tunanin family ɗinsu suna da alaƙa da batan Aisha.
A’a, Ba yanzu ba.
Ta sauke numfashi.
Mama ta kalleta na ɗan lokaci.
“Kin san zaid din kafin yanzu?”
Maryam ta girgiza kai.
“A’a.”
“Kin taɓa magana da shi sosai?”
“Aa”
“Bayan da yazo nan kun taba magana a waya?”
“Aa”
“Shi ma kinga bai san ki ba, Ynzu ne zaku san juna ku karanci halin juna”
Mama ta yi shiru.
“Maryam, aure ba ƙaramin abu bane Shi ya sa nake tambayarki.”
Maryam ta ɗaga kai.
“Mama, ki chigaba da yimin adduar da kika saba”
Mama ta kalleta sosai.
“Allah ya zaɓa miki mafi alheri, addua kullun cikin yinta nike”
“Ameen.”
Amma a zuciyar Maryam, ta riga ta yanke hukunci.
Za ta shiga gidan Balarabe.
Ba don tana son Zaid ba.
Ba don kuɗinsa ba.
Ba don matsayinsa ba.
Sai saboda Aisha.
Idan akwai wani abu da ya haɗa wannan family da batan Aisha, tana roqon Allah ya bata ikon ta gano shi
Ko da kuwa hakan yana nufin ta shiga rayuwar mutumin da bata sani ba.
Ko da kuwa za ta yi aure da zuciyarta cike da tambayoyi da waswasi
Za ta yi.
Saboda Aisha.
A Abuja kuwa, Zaid yana zaune a Qaramin study office ɗinsa da ke part dinsa
A gabansa akwai wasu documents, amma hankalinsa bai kan su, Ya ɗauki wayarsa se yaga Mammi ta turo mishi saqo
“Mun fara shirin abubuwan aure, nawa zaka bayar a hada lefe? Kuma nache ka karbi number yarinyar nan wurin fahad ku fara gaisawa, ka karba?”
Zaid ya karanta message ɗin.
Sai da ya ɗan bata fuska sannan Yayi mata reply
“har kun fara shirye shirye? Ni da keson in koma Amsterdam kwanakin nan?”
Ya ajiye wayar ba tareda ya bata amsar ko suna gaisawa da maryam din ba
Ya jingina da kujerarsa.
Maryam ta sake dawo masa a rai.
Yarinya ce mai shekara ashirin da uku.
Shi kuma yana da arba’in da biyu.
Shekaru goma sha tara ya bata fah
Zaid ya daure fuska, Shi wallahi bayason raini, ya za’ache ya karbi number yarinya ya kira ta?
Ba wai yana ganin Maryam ba ta dace da shi ba.
Ba haka bane.
Abin da yake damunsa shi ne shekarunta.
“Yar yarinya che fah.”
Ya furta a hankali.
“Anya Anyi mata adalci ta auri wanda seda ya shekara 19 a duniya kafin aka haifeta?”
Ya yi shiru.
Bai san rayuwarta ba.
Bai san me take so ba.
Bai san irin rayuwar da take son yi a gaba ba.
Kuma yanzu ana shirin haɗa rayuwarta da tasa.
Zaid ya shafa gemunsa.
Anya ba’ayi sauri ba kuwa? Kar dai dole za’a yima yarinyar nan fah tunda tanada saurayin ta, kar dai rabata da saurayinta akayi akasa ta dole ta aure shi? Ko dai yache ya fasa ne?
Amma sai ya tuna Mammi daga gefe daya, Shekaru da yawa tana magana akan aurensa.
Kullum tana cewa ya yi aure shi kuma Kullum yana zillewa
Ynzu gashi yakai forty-two.
Maybe lokacin auren Yayi
Ya ɗauki wayarsa ya kira Mammi.
“Hello, Mammi.”
“Na’am, Zaid.”
“Nasan aurena shine abin da kike so amma kina ganin maryam ta dache dani?”
Mammi ta yi dariya.
“Ni zanyi auren ko kai? Ko Baka ganta ba?”
Zaid ya yi shiru.
“Zaid, ba zan tilasta maka aure ba. Amma ka dade kana gudun wannan magana.”
“Na sani mammi.”
“Umm..that..girl..is too..too small and..and innocent..” ya fadi a rarrabe
Mammi ta yi murmushi a ɗayan ɓangaren.
“Don Allah kada ka fara overthinking dinnan naka, wannan ba work project bane, kabar ma Allah komi kayita addua kawai tunda biyayya kayi min bazaka taba faduwa ba”
“In shaa Allah mammi na”
Se ya yi ɗan murmushi.
“Toh in shaa Allah”
Mammi ta yi farin ciki yanaji daga muryar ta
“Allah ya albarkace ku.”
“Ameen.”
Suka yi sallama, har ze ajiye wayar yaji tana chewa
“nasa fahad ya turo maka number ta, don nasan baka kirata ba, zaid ka kirata please”
“okay mammi zan kira”
Zaid ya ajiye wayar.
Ya sake kallon documents ɗin da ke gabansa.
A wannan karon, ya ɗauki pen.
Amma kafin ya fara aiki, ya sake tuna Maryam.
Shi fah ya fara zama confused, Yasan ba sonta yake ba, kuma Bai san ko zai iya zama mijinta yadda ya kamata ba, shi saboda mammi kawai zeyi auren, kuma yarinyar nan qarama che yana tausayin ta Gaskiya, Anya yayi mata adalci kuwa? Ya aureta kawai bayan ita anche akwai wanda takeso?
Amma ya yanke shawara.
Zai yi auren
Idan yayi Mammi za ta daina matsa masa.
Kuma watakila…watakila komai zai daidaita da kansa ya gani ko ze fara iya zama da ita
Abin da Zaid bai sani ba shi ne Maryam ma ta yanke shawara.
Amma nata dalilin ya sha bamban da nasa.
Ta yarda da auren ne domin ta gano gaskiyar da Aisha ta bari a baya.
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***