Free chapter · Read without an account

THE WARNING

by Nihaal Maalik · KIRAN KADDARA

SOKOTO — 2 DAYS TO THE WEDDING


Tun ranar da dangin Mama suka zo, Maryam ba ta sake yin wani aiki na gida ba, Gaba ɗaya an ɗauke ta mata komai.

Kamar yadda aka saba yima Amare idan za a yi aure, tun lokacin aka fara mata gyaran jiki tun daga kanta har zuwa ƙafafunta.

Tun safe har dare, ɗakin Maryam ya zama ƙaramin wajen gyaran amarya.

Matan da suka zo daga Niger musamman don gyaran jikin ta suna tare da ita kullun a daki, 

Wata tana gyara mata gashi, wata tana shafa mata abubuwan da za su sa fatarta ta qara laushi, wata kuma tana shirya mata ruwan wanka, har safiya da bahijja baa bari baya ba, don chewa sukeyi suna hauwa koulu tayi musu tunda ta iya, ayita yima bajijja tsiya ana chewa safiya tanada miji amma ita ko Tayi gyaran ze tafi a iska ne kawai, se Tayi dariya tana chewa ai baa sani ba ko wurin bikin maryam itama ta samu nata.

Ana yima maryam dilka a hankali saboda yanayin fatar ta yanada laushi sosai, daga nan se ayi halawa, ana cire mata gashin jikinta a hnkali, ana kula da dukkan jikinta sosai.

Maryam kam dai kullun zaune kawai take tana karɓar kulawa ta musamman.

Tana jin daadi idan su bahijja da safiya sunzo ayita wasa da dariya, sun zama kamar sun saba da masu gyaran jikin da sauran yan uwan mama, don su safiya kam ba daga nan ba in dai wurin sakin jiki ne da saurin sabo. 

Safiyya na tsokanar maryam 

“Amarya kin shirya kuwa? Kinsan yayana tsohon tuzuru ne gwara muyi miki shiri na musamman”

Aka kwashe da dariya a dakin 

Maryam ta sunkuyar da kanta.

“Allah dai ta shirya ki Safiyya, kyale ni ban sani ba”

“Ba ki sani ba?” ɗaya daga cikin matan ta yi dariya. “Kwana biyu ya rage fah, wannan gyaran da muke miki dole ki shirya yarinya”

Duk suka yi dariya.

Maryam ma ta yi murmushi.

Amma cikin zuciyarta akwai wani abu da babu wanda ya sani.

Ta san abin da ke jiranta.

Auren Zaid.

Da kuma sirrin Aisha.

Kullun idan Anyi mata gyaran jiki an gama mata wanka, sai a turara mata jikinta da turaren wuta na jiki me qamshin gaske, ynzu ma shine aka dauko, Ƙamshin turaren ya Riga ya cika ɗakin, ya manne a jikinta da kayanta duka, Maryam ta rufe idanunta na ɗan lokaci tana jin yadda ƙamshin yake ratsa hancinta da jikin ta

Kuma kullun Bayan an qare turare ake kawo mata madarar raqumi da aka tafasa mai ɗumi, Ba madara kawai ba ce, An tafasa ta da abubuwa masu amfani domin a ƙara mata wasu abubuwan amfani a jikinta da kuma kula da jikinta. Kullum ana bata safe da dare 

“Sha,” Anty maimona ta miqa mata.

Maryam ta karɓa.

“Ki shanye ta duka.”.

Kullum haka.

Abinci, madara, wanka, gyaran jiki, turare, hira da matan gida da abokan ta

Babu wani aiki da aka bari Maryam ta yi.

Ko wayar ta bata wani tabawa se da dare kafin Tayi baccee wani lokacin se ta dan duba. 

Yau bayan Tayi sallar maghrib ta zauna Tayi azkar har akayi isha ta tashi Tayi sannan Tayi shafa’i amma batayi witr ba saboda tanaso Tayi sallar dare anjima. matan da suke yini tare da Maryam tun safe suna mata gyara sun riga sun fita daga ɗakin, Wasu sun koma tsakar gida suna hira, wasu kuma sun tafi ɗakunan da aka ba su sun kwanta.

Maryam tana zaune a kan gadonta, jikinta a rufe da wani shawl mara kauri sosai, tana jin ƙamshin turaren da ake turara mata da ya riga yanzu ya kama jikinta.

Sai aka buɗe ƙofar a hankali.

Mama ta shigo.

“Maryam.”

“Na’am Mama.”

Mama ta zo ta zauna kusa da ita.

Ta kalli ɗiyar tata na ɗan lokaci.

“Kin gaji ko?”

Maryam ta ɗan yi murmushi.

“Kaɗan.”

Mama ta yi dariya.

“Kaɗan? Kullun ayi ta murza jikin ki tun sahe ana ta yi miki abu guda har yanzu baki gaji ba, nasan halinki baki qaunar abnda ze taba miki jiki”

Maryam ta yi murmushi.

“Sun hana ni yin komi ai sedai gyaran”

“Haka ya kamata dama”

Mama ta gyara mata hijabin da yake kan kafadarta sannan ta chi gaba

“Yanzu ke amarya ce, Ba a barin amarya tana aiki.”

Maryam ta sunkuyar da kanta kawai

Mama ta kalle ta sosai.

“Maryam…”

“Naam?”

“Kina hwarin ciki da auren ga ko?”

Ta ɗaga kai ta kalli Mama 

“Mamana”

Mama bata ansa ba, ta yi shiru na ɗan lokaci tana kallonta

“Mayrama Naga tun da aka fara maganar auren nan, kina yawan yin shiru sosai, in akwai wata matsala ki hwada mini”

Maryam ta sauke idanunta.

“Babu komi mama”

“Kin tabbata?”

“Eh in shaa Allah”

Mama ta kama hannunta.

Maryam ta kalli hannun Mama da ke riƙe da nata 

“Mama…” 

“Abin da nake so kawai shi ne ki samu zaman lafiya mayrama”

Maryam ta yi shiru.

Mama ta ci gaba da magana a hankali.

“Na san komi ya hwaru da sauri. Kuma na san ba ki daɗe da sanin Zaid ba.”

Maryam ta haɗiye yawu.

“Ba komi Mama, na yi istikhara.”

Mama ta gyada kai.

“Na sani, shiyasa Hankalina ya kwanta kuma ina miki addua kullun”

“Nimq na roƙi Allah ya zaɓa min abin da ya fi alheri.”

Mama ta matse hannunta.

“Shi ya sa na yarda da ke nasan duk inda kike bazaki yi watsi da Ibadar ki ba”

Maryam ta ɗan yi murmushi.

Mama ta kalli fuskarta.

“Amma akwai abu guda da nika son ki sani.”

“Toh”

“Ko me ya hwaru a gidan mijinki, kakki ji tsoron magana da ni, banche sirrin ku na aure ba, kinsan dai wannan tsakanin ku ne, Bnson kai qara, in wani abu ya hada ku gara ku sasanta kanku ba se kowa yaji ba, amma in kinga wani abu da baki iya jurewa ki hwadamin”. Tayi shuru sannan ta chigaba “maryam ba lallai daga ynzu mu sake samun lokaci mu zauna irin haka ba har zuwa sadda za’a wuche dake dakin ki, shiyasa nikason muyi magana, maryam kisa ga ranki ibadah kinka tahi yi, kiyi hankuri, shi aure gabadaya dan hankuri ne, bautar Allah ne don haka kisa Allah tsakiyar al’amurran ki in shaa Allahu bazaki tabe ba, kiyi ma mijinki biyayya kuma duk abnda kigga beso Toh kiyi qoqarin bari, ki kula da mamatai sosai ki dauketa kamar ni, kiyi mata biyayya, kakki daga mai murya, ko hwada yaka yimiki akan abnda a ba lehinki ba kakki maida martani ki bari se ya huche sannan kiyi mai bayani, sannan abnci, kakkiyi wasa da abncin mijin ki, ki lura da abncin ya yahhi so ki dage sosai wurin fannin cikin mijin ki. Sannan ina qara jaddadaa miki..in kinka kasa daure Abu..”

Maryam ta ɗaga kai taga mama na hawaye

“Ki kira ni. Ki faɗa min komai. Kada ki riƙe abu a zuciyarki saboda kina ganin za ki dame ni.”

Maryam ta ji wani abu ya tsaya mata a ƙirji, ta daga hannu tana goge hawayen mama, itama nata sunka fara fitowa kamar an kunna pampo,

Ta kusa faɗa mata, Ta kusa cewa akwai wani abu da take ɓoyewa wanda shine dalilin da yasa zatayi auren

Amma sai ta tuna komai.

Aisha.

Da auren Zaid.

Ta kasa fadi 

“Maryam?”

Ta dawo daga tunaninta.

“Na’am?”

Mama ta yi murmushi.

“Ki yi haƙuri ki rage damuwa kinji?”

Maryam ta yi dariya kaɗan.

Mama ta rungume ta.

“Allah ya yi miki albarka.”

Maryam ta lumshe idanunta a jikin Mama.

“Amin.”

Mama ta sumbaci goshinta.

“Allah yayi miki zabi mafi kyau a rayuwar ki. Allah ya sa ku zauna lafiya. Allah ya ba ki farin ciki fiye da wanda kike tunani.”

Hawayen Maryam suka chigaba da gangarowa

“Amin, Mama.”

Mama ta tashi zata wuche 

Maryam ta dan riqo hannunta “mama..”

Mama ta juyo tana kallon ta

Tayi shuru se mama ta dawo ta zauna “maryam akwai wani abu ne?”

“mama imran” se hawayen ta suka sauko 

Ta chigaba “mama kar yaga kamar nachi amana tai, ranar da yazo nan gidan na kasa chewa komi chemai dai niyyi da yadda da auren” 

Mama ta rungumeta

“Kar ki damu ai kinsan kawu yayi maganar fahimta da babanai, kuma ko jiya ba kina ji inna tai ta shigo nan gidan ba? Da ita aka komi, kuma su kaka ladi suna magana da ita suna jajanta mata tacce Habah ai aure yin Allah ne kuma ko ita adda diya macce irin haka ya faru dole zata ba diyarta shawarar tayi aure da wanda ya tashi” maryam ta girgiza kai

“mama ni shi nikeso ya fahimce ni” 

mama ta rungume ta

“kar ki damu in shaa Allahu in an gama komi zansa a kiramin shi ya taho in yi magana dashi” maryam ta gyada kai, mama ta shafa bayanta a hankali sannan ta tashi ta fita tana chewa

“Ki huta, Gobe ma akwai sauran gyaran shine na qarshe ina ga”

Maryam ta yi dan guntun murmushi kadan 

“Again goben ma zaayi?”

Mama ta yi dariya.

“Amarya ce ke nan.”

Ta fita ta rufe ƙofar.

Maryam ta zauna ita kaɗai.

Murmushin da ke fuskarta ya ragu a hankali.

Ta qura ma qofar da mama ta rufe idanu

“Allah ya sa komai ya zama alheri.”

Se Ta kwanta a kan gadonta tana kallon ceiling.

Kwana biyu.

Kwana biyu kacal.

Suka rage ta zama matar Zaid Balarabe.

Maryam ta juya gefe.

Ta kalli jakar da ta ajiye a gefen gadonta.

A ciki akwai takardar da ta karɓa dazu da wani yaro cikin yaran dangin mamanta ya shigo daki ya bata “Anty maryam gashi inji wani mutumi da ya rufe fuska yache a baki”

Tun da ta karanta Takardar ba ta faɗawa kowa ba.

Ta sake tuna kalmomin da ke rubuce a ciki

KADA KI AURI ZAID BALARABE.

Zuciyarta ta buga da ƙarfi.

Ta ɗauki pillow ta matse a jikinta.

Waye ya aiko mata da ita?

Me ya sa?

Kuma…

Maryam ta zauna dakyau 

Ta kalli ƙofar ɗakinta, Sai ta sauke numfashi, A waje, ana ta dariya, Ana shirye-shiryen aure.

Ana jiran ranar da amarya za ta tafi.

Se ta jawo jakar ta bude ta dauko takardar ta sake karanta ta, kamar tana neman taga wani Abu da bata gani dazu ba 

Maryam ta sake kallon takardar da ke hannunta.

Ta karanta kalmomin a karo na uku.

KADA KI AURI ZAID BALARABE.

Ta sauke takardar a hankali.

Me ya sa?

Me ya sa wani zai so ya hana ta auren Zaid?

Shin mutumin ya san Zaid ne?

Ko kuma ya san wani abu ne game da danginsa?

Maryam ta dafe goshinta.

Sai tunanin Aisha ya sake dawo mata.

Aisha ma ta taɓa yin irin wannan tunani tunanin ko dai ina zurfafa tunani ne? Ta tuna dai tana ganinta tana ta binciken Rahman balarabe family 

Ta yi ta rubuce-rubuce.

Ta kasance tana yawan ɓoye wayar ta lokacin

Tana yin wasu wayoyi da ba ta so kowa ya ji.

Kwatsam Sai kuma ta ɓace…

Maryam ta lumshe idanunta.

“Ko ba’aso ne in gano abin da Aisha ta gano?”

Ta buɗe idanunta

A’a! Banida tabbacin komai.

Wataƙila mutumin yana ƙoƙarin tsoratar da ni ne kawai.

Wataƙila wani ne da ba ya son auren ya faru saboda wani dalili nasa.

Amma idan haka ne…

ta yaya ya san ni? Ya yasan ni che zaid ze aura?

Koda yake maganar duniya bata boyuwa balle su da family dinsu yake da suna cikin Nigeria 

Maryam ta ɗauki envelope ɗin ta sake kallonsa.

Babu suna, ba address 

Babu komai da zai nuna wanda ya aiko shi.

Sai kawai wannan saƙon.

KADA KI AURI ZAID BALARABE.

Maryam ta yi shiru.

Ta tuna ranar da ta fara ganin Zaid.

Nutsuwarsa.

Yadda ya taimaka mata lokacin da ta kusa zubar da tray din abnci 

Har yanzu ba ta ga wani abu a tare da shi da zai sa ta ji tsoro ba.

“Toh me yasa?”

Ta tambayi kanta.

“Me yasa zaa che kar in aure shi?”

Ta ɗan yi shiru.

Sai wata magana ta dawo mata daga zuciyarta.

Ba wai Zaid kaɗai ake magana ba…

ana magana ne akan Rahman Balarabe family 

Maryam ta kalli takardar.

Aisha ta yi binciken Balarabe family 

Yanzu kuma wani da ban sani ba yana gargadina kada in auri wani daga cikin Balarabe family 

Wannan ba zai zama coincidence ba ai ko?

Zuciyarta ta fara bugawa da sauri.

Ta ɗauki takardar ta ninke ta.

A wannan karon, ba ta saka ta cikin jakarta ba.

Ta ɓoye ta a wani wuri da babu wanda zai iya ganinta.

Ta tsaya a tsakiyar ɗakin.

Sai ta kalli kanta a madubin da ke gabanta.

“Maryam…”

Ta furta sunanta a hankali.

“Me kika shigar da kanki?”

Ta kasa amsawa.

Amma abu ɗaya ta sani.

Ba za ta fasa auren nan ba.

Bayan duk abin da ta take ganin zata gano game da Aisha.

Idan akwai wani abu da ke ɓoye a gidan Balarabe…

za ta shiga ta gano shi da kanta.

Maryam ta sauke numfashi, ta tashi ta dauro alwala ta fara qiyamul lail

Wannan daren, ba ta kwanta ba sam

Zuciyarta da tunaninta suna wani wuri

Wurin Aisha.

Wurin Zaid.

Wurin Balarabe family.

Wurin kuma wannan mutumin me ban mamaki wanda ya gargade ta

Join our WhatsApp group 


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


7A917E60-936D-455D-AC0D-3E09A04279B5.png

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol