Free chapter · Read without an account
THE LAST NIGHT
SOKOTO — WEDDING DAY
Da asubah, gidan su Maryam da hayaniya aka tashi tun kafin asuba
Yau ce ranar Sa Lalle.
Tun kafin rana ta fito sosai, mata suka fara shiga da fita. Wasu suna ɗauko kayan da aka tanada da zaayi amfani dasu, wasu suna shirya abinci, wasu kuma suna zaune a tsakar gida suna hira suna dariya.
Maryam kuwa tun da safe anty maimouna da gwaggo A’i suka tashe ta.
“Amarya, tashi”
Ta buɗe ido a hankali.
“Na tashi ai”
Anty maimouna ta yi dariya.
“Kin tashi ne kawai? Yau ba ranar kwanciya bacci bace kinji yarinya, tashi kiyi brush ga madarar nan da zafin ta ki shanye ki bani cup” maryam ta tashi tayi brush ta karba ta shanye ta miqa ma anty cup din
Anty da gwaggo A’i suka rangada guda me qarfi har sauran matan da ke tsakar gida suma sukaji suka fara yi daga chan
Maryam ta yi murmushi, Ta tabbatar yau babu gudu babu ja da baya, Ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai sunan ya sake bayyana a zuciyar ta
Zaid Rahman Balarabe.
Sai kuma takardar nan
KADA KI AURI ZAID BALARABE.
Ta danne tunanin, Ba yau ba, Ta tashi ta shiga toilet, Tayi zaman ta a ciki ta bata lokaci sosai
Tanata tunanin imran, ko ya yakeji ynzu? Me yake ciki? Ko yana chin abnci? Shin yana yimata kallon maciyar amana? Tana saqe saqe daban daban cikin ran ta, hawaye ko se aikin zarya suke, ta chigaba da tunanin shin wannan auren da tasa kanta ko yaya shi mijin ze zauna da ita? Ko yaya zaman su ze kasance? Ta dade sosai a toilet tanata kuka se taji Safiyya na buga mata qofa tana fadin “ke wai duk gyaran jikin da aka yimiki be isa bane? Wannan wane irin wanka kikeyi ko dai chanja fatar kikeyi ne, tundazu mukazo kina wanka haryanzu baki qare ba?” Bata amsa mata ba haka Tayi wankan ta fito ta tarar da safiyya da bahijja da hauwa koulu da wasu qawayenta duk suna zaune cikin daki har an kawo musu abnci suna chi suna fira cikin nishadi, se ta fara tunani “wai anya idan tache da zarar da qare binciken da ze kaita zata bar auren nan Tayi ma mama adalci? Tayi ma duk wa’innan da keta farin ciki adalci? Ache Tayi aure da manufa amma yan uwa da abokan arziki sunata jin daadi saboda basu san tanada manufa ba, amma kuma ai bazata iya chigaba da zama da zaid ba tabar imran tunda tasan shi zaid ba sonta yakeyi ba
chan taji bahijja ta taba ta “ke wai ya akayi ne? kinyi tsaye kinata kallon mu kuma ana miki magana bakiji ba halan tunanin mi kikai? Ko kin matsu a daura ne?”
Sauran suka fashe da dariya maryam ma tayi murmushi ta zauna kan gado ta dauko man da masu gyaran jikin suka bata sukache dashi zata rinqa amfani
Seda ta qare shafawa se safiya ta miqe tsaye “bari inje dakin mama in dauko kayan da zakisa cikin wa’inda aka kawo na salalle da wankin amarya” ta fita daga dakin tana ratsa Mutane har taje dakin mama, bata tarar da mama a ciki ba se gwaggo A’i, Itache ta nuna mata wurin da kayan suke taje ta bude ta dauko wa’inda maryam zatasa sannan ta fita daga dakin ta koma chan dakin maryam, ita da bahijja suka taya Maryam tasa kayan sannan suka shafa mata powder da dan jambaki Kadan, bahijja ta daura mata dankwali sannan suka yafa mata gyale a kai
SA LALLE
A wajen tsakar gida kuwa, a riga an fara shirya ruwan lalle.
Babban baho ne aka ajiye gaban inna ladi
An kawo niqaqqen lalle da kuma ganyen lallen, an ajiye manya manyan kwalabe na designer oil perfumes da su hajiya ruqaiya suka kawo
An dauko lallen da aka nika shi sosai. Aka zuba shi cikin wani babban baho, sannan aka zuba ruwa a hankali ana juyawa har sai da ruwan suka koma ja sosai
Daga nan kowa se ya tashi ya debi ganyen lallen yayi addua sannan ya zuba cikin ruwan, se kuma Su dauki kwalba daya cikin kwalaben da ke ajiye na designer oils perfumes din su bude su zuba a cikin ruwa se su koma su zauna
Haka akayita yi duk wanda yazo zeje gaban inna ladi yayi addua ya sa lalle, ana haka dangin ango suka iso, su hajiya Ruqaiya da su hajiya raliya da anty Hafsat da anty Hadiza da sauran su, suma suka sa lalle sannan akayi wasu abubuwan al’ada anata guda kafin suka wuche se kuma yamma zasu dawo wankin amarya
Wasu daga cikin matan nan masu gyaran jiki suka ƙara kayan ƙamshi da aka saba amfani da su domin lallen ya kama jikin amarya kuma ya bar ƙamshi a jikinta
Aka ci gaba da juyawa.
Bayan an gama haɗawa, aka rufe kwanon aka ajiye shi domin ya jika da kyau ya kuma kwanta yadda ake so kafin ayi amfani da shi.
Inna ladi ta shiga dakin Maryam tana ta rangada guda ta fito da ita daga daki safiya da bahijja na riqe da hannuwanta, se aka zaunar da ita tsakiyar qawayen ta, aka zana mata lallen amare baqi da ja, ya zauna a hannunta kamar da engine akayi shi, Qawayenta ma duka aka zana musu dd dd, da Lallen ya bushe masu Lallen suka chire mata suka wanke suka shafa mata kayan qamshi sannan suka tashi, mata kuwa aka yita waqoqin Amare irin na al’ada Ana taba hannuwa “ayye mama ayye mama, mamaye iye, ayye mama labo labo, mamaye iye, da aure yana raka aure mamaye iye da na biki mun tafi tare mamaye iye” chan kuma se a fara “tazama tazama tazama, tazama dauko riga, tazama dauko hulla” haka dai aka yini har yamma
Da rana ta fara lafawa, aka fara shirye shiryen wankin amarya, Bayan sallar magrib dangin zaid suka iso, su hajiya ruqaiya, su hajiya raliya da sauran matan da sukazo bikin, Akasa maryam a tsakiya Matan suna kewaye da ita, zaune take a inda aka shirya mata, suka fara shafa mata lalle a hannuwa da ƙafafu, seda suka murza mata shi a jiki sosai sannan sauran matan gida da kowa sukazo suma sukayi, har a fuska da gashi seda aka murza mata shi ko’ina, jikinta se tashin qamshi yake, tayi jawur abunka da farin mutum, anayi ana raha, wasu suna yin magana, wasu suna dariya, wasu kuma suna yi mata nasiha, wasu na addua
“Allah ya baku zaman lafiya.”
“Amin.”
“Allah ya sa aure ya zama alheri gareki”
“Amin.”
“Allah ya baku zuri’a ta gari.”
“Amin.”
Ana addua mutane suna ansawa
Amma duk lokacin da aka ambaci aure zuciyar maryam se ta yi wani irin tsalle, Ta kalli lallen dake hannunta.
Aisha.
Sunanta ya sake bayyana a zuciyarta.
Se taji inna ladi ta kira sunan ta
“ke Maryam?”
Ta ɗago kai.
“Na’am?”
“Hnkalin ki ya tafi ina ne?”
Maryam ta yi murmushi.
Hajiya Raliya ta kalle ta na ɗan lokaci, kamar ta lura da wani abu, amma batache komi ba se inna ladi ta chigaba da magana “ruwan lallen nan Anya zakiyi wankan nan dakyau ko dai se anyi miki?”
Maryam ta sunkuyar da kai batache Komi ba,
bayan an gama chin abinci da sauran shirye-shirye, gidan ya sake canza yanayi.
Ruwan lallen da aka shirya tun safe sun riga sun jiqu yadda ake so, aka kawo su, Ƙamshinsu ya cika wajen, aka dauka aka kai toilet inda aka tanadar mata, inna ladi ta shiga tare da ita, ta fara mata wanka da ruwan lallen nan, Tana zuba su a jikinta a hankali, ana wanke ta kamar yadda al’adar wankin amarya take, Ta kuma ci gaba da amfani da turare da sauran kayan da aka tanada domin ranar.
Maryam tana zaune kan kujera a toilet din cikin nutsuwa, Ta rufe idanunta, tanajin yadda kidan qwarya ke tashi daga waje, A wannan lokacin, hayaniyar wajen ta fara yi mata nisa daga cikin kanta, Ta fara tunani.
Gobe, Gobe za a daura aurenta, Gobe za ta tashi daga wannan gidan a matsayin matar wani, Matar Zaid.
Sai zuciyarta ta matse a qirjin ta, Ta tuna Imran.
Ta tuna yadda ya kalle ta ranar da ta gaya masa komai, Ta tuna kalamansa
“Kin riga kin yanke hukunci ai.”
Idanunsa, Murmushinsa mai ɗauke da ciwo da rauni, Maryam ta sauke ajiyar zuciya.
“Ya Allah…”
Ta bude idanunta.
“Ka taimake ni.”
Ba ta san abin da gobe za ta zo da shi ba.
Amma ta san dalilin da ya sa ta yarda da wannan auren
Aisha.
Bayan an gama wankan inna ladi da fito da ita, aka shirya ta tsab cikin atampa yellow and brown aka fito da ita waje tana lullube da fuskar ta. Masu kidan kwarya suka kara karfin kidi abokan maryam suka taso suka kewaye ta sunata taka rawa, dangin zaid kuwa suma suka tashi anata yima amarya ruwan kuddi, ita dai tana tsaye kanta a kasa, seda aka gama wannan shagalin aka mayar da Maryam ɗakinta.
Ta saka kaya masu sauƙi, ta zauna a gefen gadonta, nan safiya da bahijja suka yimata sallama suka tafi
Gidan har yanzu cike yake da mutane.
Ana dariya, Ana fira, Ana shirya abubuwan gobe, daurin aure da walima
Ta kalli mirror, taga fuskar ta da tasha gyara, da lallen ta, da gashinta da aka gyara amma baayi kitso ba saboda santsin shi, amma a badini duk bashi take gani ba
Tunani take wannan shine daren qarshe da zata kwana a gidan su
A gidan hajiya Ruqaiya kuwa, sashen da aka saukar da dangin angon, Zaid ma bai yi bacci ba.
Yana zaune shi kaɗai, Wayarsa tana hannunsa,
Yana duba hotunan wankin amarya da mammi da fahad sukayi posting a status dinsu, yanata kallon maryam, ta qara zama cute kuma kamar ta dan rame ta rage girma
Ya buɗe chat ɗinshi da ita, blank page, basu taba magana ta WhatsApp ba
“Ko in tura mata message ne?”
Sai ya dakata.
Bai san abin da zai ce ba.
“Ya gajiyar biki zeche?”
Ya ɗan yi murmushi yache no kar in takura yarinya, bari in qyaleta kawai”
Ya ajiye wayar, Ya tashi ya yi alwala.
Gobe zan zama mijin Maryam, gara in kwana ina sallah Allah yasa wannan hukuncin da na yanke na yadda da auren ya zamar min alheri, Shi ma har yanzu yana ƙoƙarin fahimtar yadda komai ya faru cikin sauri.
Ya hau kan carpet, Ya tsaya, Ya ɗaga hannuwansa sama
“Ya Allah…se ya kasa furta komai”
Se kawai ya kabbarta sallah, ya dade yanayi sannan Ya yi addu’a.
Allah ka tsaya min, Allah kasa kada in zalunci yarinyar mutane, Allah ka bani ikon zama mijin da ya kamata, Allah ka kare mu daga abin da ba mu sani ba.
Tabbas Idan ka sallama ma ubangiji lamarinka, toh ze dauki ragamar kaf al’amarin kuma ya shige maka gaba. Abnda zaid be sani ba, Allah ya karba mishi adduar shi, kuma ze shige mishi gaba.
A ɗayan gidan kuwa, Maryam ma ta yi sallah.
Ta zauna a kan sallayarta bayan ta gama, Ta ɗaga hannuwanta.
“Ya Allah, idan wannan aure alheri ne a gare ni, ka bani ikon jurewa ka taimakeni akan abnda zanyi”
Ta yi shiru, Sai hawaye suka cika idanunta.
“Ka kuma taimake ni in gano gaskiyar abunda ya faru da Aisha.”
Ta goge hawayen.
Ta tuna takardar da ta ɓoye.
KADA KI AURI ZAID BALARABE.
Sai ta jingina da gadon
A wannan daren, babu wanda ya san abin da gobe za ta zo da shi.
Kuma babu wanda yasan chewa Allah ya karba musu adduar su
Gobe ba kawai ranar da za a daura aure ba ce.
Gobe ce ranar da Maryam za ta kama hanyar shiga cikin gidan da ta yi imanin chewa yana ɗauke da amsar tambayar da ta shafe shekaru tana nema.
Kuma Zaid…Zaid zai shiga wannan auren ba tare da sanin cewa matar da zai aura ta zo da wani sirri nata ba.
Sirrin Aisha.
Sirrin Balarabe.
Da kuma wata gaskiya da har yanzu babu ɗayansu da ya shirya fuskanta.
Follow this link to join my WhatsApp group: ***