Free chapter · Read without an account

BOOK ONE CHAPTER 14

by Hindatu Auwal · ƘYAURE KARIYAR GIDA


Ta ɗan yi shiru alamar tinani. Daƙiƙa ɗaya...biyu...uku sai ta kallesa cikin idanu ta furta

"Mu cigaba da zama a haka...nauyin zai sauka a zuciyata."


Ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen bakinsa.

Batare da ta janye idanunta acikin nasa ba ta motsa laɓɓanta, ƙaramin sauti mai ratsa zuciya ta fito.

"Yes!"

Ya ɗan ɓata fuska.

"Me?"

"Ga shi."

"Me?"

"Na sa ka yi murmushi."

Ya girgiza kai.

"Allah ya shirya min ke..."

Ta yi dariya. Ya sauke kai yana murmushi. Sai ya ɗago ya kalleta.

"Kin san wani lokaci kina da ban mamaki?"

Ta ɗan ɗaga gira.

"Ban mamaki mai kyau ko mara kyau?"

Rayyan ya yi dariya a hankali.

"Ban sani ba."

"To sai ka bincika."

Ya sake dariya.

A wannan karon dariyar ta fito da nishadi fiye da wadda yake yi tun shigowarsa gidan.

Aliya ta kalle shi a hankali. Zuciyar ta na cikada jin dadin ganin nasa zuciyar ta sami natsuwa.

Hakan yasan yata gabatar masa da abincin data girka, batare da musuba ya tashi suka je dining.



Seda suka kammala cin abincin yake gaya mata sun hadu da Yaya Rafiq ya gaya mai centern makarantar su ta kirasa akan tom print ɗin WAEC ɗin ta, tashirya gobe taje ƙarfe 11: 00am.

Aliya tai shiru tana sauraron sa. Bazata taɓa mantawa da ranar da tadawo daga makaranta na ƙarshe ba. Ranar da Jamila ta rusa gidanta, tai zaɓi a rayuwar ta. Ranar da mahaifinta yai kuka ta share masa hawaye da kalaman ta. Kalaman da suka sauya rayuwarta. Kalaman da suka kawo ta wannan sabuwar rayuwar. Kalaman da suka mallaka mata Ustaz Rayyan ayanzu.



Ta ɗago idanuwanta ta kallesa tana jin wani abu na ratsa ta. Ta lumshe murfin idanunta ruwa mai ɗumi ya sauka akan kuma tun ta. Ta kai hannu ta share dasauri kada Ustaz Rayyan yagani.




*Jamila*

Tun ranar da Raihan ya shigo ɗakin ta sukai kallo atare zuciyar ta ta soma dokamai. 


Se awashe gari da suka haɗu a dining ta fito break fast yake gaya mata ya dawo gidan da zama, kayan sa na ɗayan part din dake nata.


Tun yana mata hira tana jin nauyin amsa masa zuciyar ta na gaya mata kada tai sabo dashi bai dace ba, harammun ne a musulunci, ta ƙetare wannan maganar ta saki jiki sosai dashi.


A yanda ta fahimci Raihan samm bayada girman kai ko jin shi wanine kamar yanda yara matasa masu kudi su keyi.



Yanada wata baiwa na fahimtar halin da mutane ke ciki, zaka rantse da Allah yana kallon cikin zuciyar mutum afili shiyasa yake karan tata kai tsaye. 



Tun abin na bama Jamila tsoro, ya koma mamaki, ayanzu ya zame mata jiki ta saba da wannan side din nashi.



A kace sabo turken wawa to hakan ne ta faru da Jamila. Raihan ya zame mata aboki, ƙawa, abin ɗebe kewa agareta.




Unin da take yi a online tana chart da kewayen ta duk ta watsar. Shi kanshi Samir ta daina kiran sa.



A duniyar Jamila yanzu Raihan ne kawai. Yanda yake bata kulawa abin na matukar yin mata daɗi, musamman ranar da suka je shopping a Jabi Lake Mall, Jamila ta fahimci cewa Raihan ya bambanta da yadda ta fara ɗaukarsa.

Ba wai don yana da kuɗin sayen duk abin da ta nuna masa ba ne, sai don yadda yake ba ta damar zaɓar abin da take so ba tare da ya matsa mata ba.

A gajiye liss!suka dawo zuciyoyinsu cike da farin cikin moment din da sukai spending a tare.


Bayan kwanaki biyu ya ɗauke ta suka je suka gaida Mimi. wata mace mai dattako da mutunci, ga fara'a da wayewa don Jamila tayi zaton Mimi zatai ma Raihan fada akan yanda yake kai hannu jikinta don ko magana zeyi mata sai ya riƙo hannun ta cikin nasa, ko ya lakato kumatunta, awasu lokutan har jan mata hanci yake yi.



Jamila ta ƙara tabbatar da wayayyun mutane ƴan gayu basada matsala arayuwa. Ba ruwansu da duhun kai ko ƙorafe-ƙorafe akan abubuwan da basada muhimmanci.



Haka sukai uni zungur ranar a gidan Mimi sai dare suka koma gida.



Haka rayuwar ta cigaba da tafiya. A cikin duk lokutan da suka shuɗe sau daya tak sukai wayada Samir shima ta sanadin Raihan.



Farin ciki da ɗaukin da take tinanin zataji idan sukai wayada Samir samm bata ji shiba. Abinda yasan yata ta dinga mamakin kanta da son sanin dalilin haka.




*Zainab*

"Please Mami....dan Allah ke ko ki taimaka kibani imbanda ke banida kuwwa ke kadai ce gatana a duniya, im bakeba banida kuwwa...."



 "Kinga malama ki shiru ba jinki takeyi ba."



Anis ya katse magiyar da Ramlat take ma Zainab.



Kaman ba zatai shirun ba, se kuma taɗaga narkakkun idanunta ta sauke akan Zainab data dora pillow akan side face dinta ta toshe kunnuwanta yanda bazata jiyo ta ba.



Cikeda naci Ramlat tamike ta koma kusada ita ta janye pillown tana magana:



"Haba uwata, gatana abin alfahari na, idan baki minba wazai min! Kece gatana kwalliyar nan innayi ke za'a yaba mawa in banyi ba ke za'a zaga."



"Ni banaso a yabe Ni gwara dai a zageni."


Zainab tai maganar tana kallon ta, dan ita wasu lokutan har mamakin son kwalliya irin na Ramlat take yi, duk abinda ya shafi kwalliya da ƙyale-ƙyale tana ciki.



Inda suka sha banban da Khadija kenan, ita duk irin wadannan abubuwan ba ruwanta dasu, yanzu ma ko magana ba wani damunta yake yiba. Da suka fara exam na WAEC kuwa sai tazama busy, kodayaushe tana daki tana karatu, ko yanzu da ake wannan maganar tana daki abinta tana karatu.



Anis yace"indai akan kayan kwalliyar kine ai gwara a zageta bata siyaba da yanda wa'innan masu dogon wuyar suke biyoki in zamuje makaranta. Kuma wallahi Mami haka Sheikh Hafiz yace dan sace zuciyar samarin khairul anwar kawai Aunty Ramlat ke zuwa makaran..."



"To parrot dalla yi mana shiru, Annabi ma yace kafadi alkhairi ko kai shiru."




Zainab tace"aike baki san abinda yake fadi shine alkhairin ba. Mai sonki shike miki fada arayuwa. Ranar naka aise naka."


Ƙwata Ramlat tai ta ballarama Anis harara tana turo baki gaba.



Khalid ne yai sallama yashigo. Suduka sukai mai sanda zuwa harda Ramlat dake kumbura fuska.



"Sissy yane....waya taɓa min ke?"


Me niman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Ramlat ta narke fuska hawaye na saukar mata.



Khalid ya jawo ta jikinsa da fadin"Subhanallah wannan hawaye haka....gaya min waye ne yataɓa ki, muje mudaku Ni dashi."



"Da kudi zaku daku a shagon mai cosmetics."




Dariyar maganar Anis ce takama Khalid yagimtse. Ya share mata hawayen da cewa"yanzu Sissy akan banza cosmetics kike kuka bari innaje wurin aiki na ɗan sami kudi se muje a siyo."




"Kadama ka soma, agidannan dai mungama raka asarar da ayyiriri. Bame ƙara siyan miki kayan kwalliya."




Baki Ramlat ta buɗe zatai magana Khalid ya ƙyafta mata idanu alamar tai shiru. Shirun kuwa tayi tana ajiyar zuciya. Tasan tunda yace zai siyan mata to yana samun kudin ze siya. Dan ma wurin aikinnasu na mechanics ba wani biya mai kyau yake yin musuba.




Du-du-du asati befi yabashi dubu ɗaya ba, se uban sa aiki kamar mai gidan jaki.



Duk idan Khalid din yasoma ƙorafi se Zainab ta hanashi, ta kance"Ni pha bana kaika wurin aikinnan dan kudi bane, kai ma kasani. Kawai bana son barinka a anguwar nan kana yawo da rashin jine, aita niman magana tarbiyya na gurɓacewa, dan haka kai shiru kawai, kaci gabada aikin ka, albashina ya ishe mu komai."



Idan tafaɗi haka a dole yake shiru. Iyanzu Zainab itace komai na rayuwar su, idan sunci itaa, idan sun sha itaa, idan sunyi wanka da wanki duk itace.


*


Misalin ƙarfe 4:10pm tafito daga wurin aikinta. Tana tafiya cikin natsuwar ta kamar kodayaushe.



Alh.Haruna dake zaune a driver seat yaja iska ta ƙofofin siririn hancinsa yana kallon bayanta da ta wuce ta mirrow.



Alh.Mahbub dake gefensa ya kallesa yana kallon ta shima da cewa:



"Abokina wai tsawon wani lokaci zaka ɗauka kana dakon yarinyar nan azuciyar ka."



"Nima ban sani ba. Wata ƙila shekara daya. Shekara biyu.....



"Ko har ƙarshen rayuwar ka ba."



Alhaji Mahbub ya ƙari kama Alhaji Haruna maganar sa a ƙufule cikin gajiya da ƙosawa.



Se da yaga ta ɓacema ganinsa sannan ya maido da dubansa ga Alhaji Mahbub.



"Zuciya ta bata gayamin zan jira watannan yarinyar har ƙarshen rayuwa ta. With time zan mallake ta. Kamar yadda nake mallakar duk wani abu da nake so."



"Tayaya zaka mallake ta bayan ko magana baka iya mata. Na gaya maka da siyasa, da kuɗi, zaka iya mallakar ta. Idan kuma zatai maka taurin kai kasanya ai maka kidnapped dinta kabiya buƙatar ka a wuce wurin."



Kai Alhaji Haruna ya girgiza "Ba rapping dinta na keson nayi ba. Daɗi nake son naji da ita. And kaima kasani daga Ni har kai babu mai courage ɗin da zai iya tun kararta yai mata magana. Wani abune atare da Zainab mai girma wanda ke hana kuwwa dun kararta."




Shiru Alhaji Mahbub yayi. Shi kanshi da yake cewa aima Zainab magana baze iya ba. Yarinyar nada wani baiwa na cika ido. Ko ƙwayannin idanuwan ta bazasu iya kalloba balle har sui mata magana.




Tun ranar da Alhaji Haruna ya ɗora idanunshi akan Zainab zuciyar sa ta jarabtu da ita.



Kullum sai yashirya tun kararta yai mata magana se yakasa. Mata dayawa sukan yaudare su da kudi, kayan ciye-ciye da sauransu.



Ga Zainab kam abin ba haka yake ba. Baiwa gareta na musamman. Idan ka kalleta sai kaji kamar anɗora maka nauyin duniya akanka. Shi yasa ko gaidasa tayi daƙyar yake iya bude baki ya amsa.





Kamar kullum acikin watanni hudun da suka shafe suna bibiyar Zainab. Alhaji Haruna yema motarsa key suka bar restaurant din.



✨✨✨


Tsaye take a tsakar gidan ta tana kallon Khadija da Ramlat dake ƙarika wake-waken da sukai amfani dashi yau da safe.




Jikinsu sanyeda uniform na makaranta. Wanda ita Khadija yau zasu rubuta final exam din su na WAEC sui candy.



Juyowan da Ramlat za tayi sai taga Zainab da sukai sallama tun ɗazu tana tsaye a'inda take.




"Mami wai baki tafi ba."



Murmushi Zainab tayi tana jijjiga kanta.



"Kinga Mami gaya min menene?"



Ramlat ta fada tana tsame hannun ta daga ruwan wanke-wanken.


"No karki taso yanzu zan tafi. Kada dai Ki manta inna dawo za muje kasuwa musiyo kayan abinci...."



"da kayan kwalliya na."



Ramlat ta ƙarke mata maganar da take yi. Baki Khadija ta buɗe za tai magana, fitowar Khalid da Anis yasan yata yin shiru tana ɓoye Anis dake niman mafaka abayan ta.




"Mami dama baki tafi ba?..."



"Ban ta fi ba. Amma ban gaya maka ka daina dukan yaron nan kamar wani sa'an kaba?."



"Rashin kunya fa ye mun."



"Ai dama haka zakace. Kullum kaida Ramlat ba kuda abinyin da yafi wannan. Ka bari Allah ya dawo dani lafiya. Zamu haɗe ne, dan ƙafar wando ɗaya zamu saka daku akan Auta na." Kai kuma... Ta koma kan Anis"idan ka cigaba da abinda ka keyi, da kaina zan sanya bulala in zane ka."




Shiru sukayi suna sauron ta. Seda ta gama fadar, ta kuma yin musu sallama adaki na uku ta fita.



Khalid ya fesar da iska ta bakinshi"oh! Allah wannan faɗa haka kamar ruwan sama mai feshi."




Dariya Ramlat tayi tana kallon Anis dake kumbura fuska.




Ita kam Khadija ba ruwanta dasu. Ta ɗauki basket din wanke wanke ta shige dashi ciki.


_*_



Kai tsaye wurin aikinta ta nufa. Tana shiga ta soma tar ban customers. Ko minti talatin ba tayi ba wayarta tai ringing ta ciro ta daga aljihun wandonta tana tsayawa a reception ta ɗauka da sallama duk da numbern ba suna.




Muryan wani na miji ne yayi sallama. Ta amsa jikinta na ɗan saki sakamakon sheshsheƙar kukan Ramlat da taji.




"Ina magana da maman....Kai menene sunan ka?!" Aka saki maganar da akeyi da ita.



Muryan Khalid taji yana bashi amsa. Itama baki na rawa tace"mahaifiyar Khalid ne."



"Tom Madam sai hakuri Sister ɗin shice ta sami accident anan rasha road.."


Gaban tane ya faɗi. Zuciyar ta ta tsinke. Jikinta na ɗaukan wani irin kyarma na tashin hankali.




Idanu arufe ta nufi bakin ƙofa. Har ta kai verandan fita daga wurin taji muryan Alh.Haruna a tsakiyar kanta.



"Malama Zainab lafiya?."



Batare da ta ko kalleshi ba ta amsa shi"Ɗiya tace ta sami accident."



Ganin tayi gaba yasan yashi taranta yana cewa"Subhanallah muje na kaiki."



Inda acikin hayyacin ta take da ba zata hau ba. Sedai ayanzu idanunta sun rufe. Ji takeyi kamar tai tsuntsuwa ta ganta a gaban yaranta .




Tun bayan gaya mai inda akai accident din bata ƙara ce mai komai ba. Tafiya sukeyi babu mai ceda ɗan uwansa. Zuciya dasauri sai Zainab ta raina gudun da motan keyi. Shi yasa ko packing ɗin arziki bai yiba agefen titin da mutane sukai chaa...ta ɓalle murfin motar ta fita. Alh.Haruna ya biyo ta abaya.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.