Free chapter · Read without an account

06

by Umaimah Ado Gaya · SARƘAƘIYA

Chapter 6 page 11

     Fukhee ta fito daga ɗakin Ultrasound a hankali, hannunta riƙe da ƙaramin takardar da aka ba ta. Suna hada idanu da M.d, wanda yake tsaye a bakin ƙofar kamar bai taɓa motsawa daga inda ta bar shi ba.Yayi saurin ƙaraso wa gare ta.

"Babe..." Ya fada yana karɓar takardar daga hannunta kafin ya dubi fuskarta.

"Yaya kika ji?Ba dai wahala ko?"Ya fada cike da kula wa hannunsa cikin nata.

Ta yi ƙoƙarin yafito murmushi tace "Da sauƙi Alhamdulillah."

Sai dai M.d ya fahimci murmushin nata ba har zuciya ba ne.Ya lura idanunta sun cika da tsoro da firgici a yanzu fiye da baya.. Kafin su karasa gurin likitan ta kasa jurewa ta furta abin da ya tsaya mata a rai, "Me ya sa likitar da ta mini scannin ba ta gaya mini komai ba?"

M.d ya ɗan yi shiru kafin ya amsa cikin natsuwa.
"Saboda ba aikinta ba ne."

Ta sauke idanunta. "Amma..." Sai kuma ta yi shiru.

Ya ɗan sake matse ta a jikinsa sannan yace 
Ki kwantar da hankalinki,ko me yake da akwai soon insha Allah za mu ji shi.Amma me kika gani a fuskarta da har ya firgita mini ke?"

Fukhee ta haɗiye yawu. "Da farko tana murmushi..."

Ta ɗaga idanunta ta kalle shi.

"...amma daga baya sai ta yi shiru."

M.d bai amsa ba.

Ba don bai fahimci abin da take nufi ba ne.

Sai don baya so ya ƙara ɗora mata wani nauyin tunani.

---

Sai da suka koma sashen gwaje-gwaje domin jiran sakamakon jinin da aka ɗauka.

An sanar da su cewa wasu gwaje-gwajen za su ɗauki lokaci kafin su kammala.

Saboda haka suka zauna a wani sashe na masu jira.Yayin da Lokaci yake tafiya a hankali,bugun zuciyoyinsu kuma da sauri.Mutane sai shige da fice suke yi wasu na shigowa yayin da wasu ke fita.Nurses na kiran sunaye,suna tura kowa dakin da aka tura sakamakon test dinsa.

 Ga M.d ji yake tamkar lokaci ya tsaya cak,Ya waiwaya ya kalli Fukhee da ta jingina kanta da bango, idanunta a lumshe.

"Kina son ruwa?"

Ta buɗe ido ta girgiza kai.

"Juice fa?"

"A'a."

"Coffee?"

Ta ɗan yi dariya.

"Ni lafiya nake ko za ka buɗe mini restaurant ne?"

Ya ɗan saki murmushi.

"In dai hakan zai sa ki ci wani abu, zan buɗe guda goma."

Ta girgiza kai tana kallonsa.

"Wani lokaci kana bani mamaki."

"Wani irin mamaki?"

"Yadda kake kula da ni."

Ya yi shiru.

Bayan wasu daƙiƙu ya ce,

"Ba kula da ke nake yi ba."

Ta ɗago gira.

"To me kake yi?"

Ya kama hannunta cikin natsuwa.

"Ina kula da zuciyata ne."

Ta ɗan haɗe fuska.

"Ban gane ba."

Ya yi murmushi mai laushi.

"Saboda zuciyata tana zaune ne a jikinki."

Fukhee ta zuba masa ido.

Kalaman suka tsaya mata a rai.

A hankali ta matsa kusa da shi ta jingina kanta a kafaɗarsa.

Ba ta ce komai ba.

Shi ma bai ƙara magana ba.

Wani lokacin shiru yana faɗin abubuwan da kalmomi ba za su iya faɗa ba.

---

Kimanin mintuna arba'in bayan haka...

Wata nurse ta fito da fayil a hannu.

Ta ɗan ɗaga murya.

"Mrs. Fukhaihat..."

Dukansu suka miƙe lokaci guda.

Nurse ta yi musu murmushi.

"Doctor would like to see you."

Kalaman ba su da wani abu mai ban tsoro.

Amma yadda ta faɗe su...

Ya sa zuciyar M.d ta buga da ƙarfi.

Ya kalli Fukhee, a wannan karon bai kira ta da babe kamar yadda ya fi yawan kiranta da shi ba idan yana cikin soyayya,sai dai a hankali ya kama hannunta.

"Fukhaihat..." Ya kira cikin wata murya mara amo.

Ta ɗago ta kalle shi.

Ya yi murmushi domin ya kwantar mata da hankali.
Sai dai murmushin bai kai cikin idanunsa ba,ballantana kuma cikin zuciyarsa 

Ba tare da sun ƙara cewa komai ba...

Suka bi bayan nurse zuwa ofishin likitan.

Kowanne daga cikinsu na tafiya da wani irin nauyi a zuciya.

  Sau uku M.d yana buɗe ƙofar ofishin, amma sun kasa shiga sai a na ukun sannan ya tsaya gefe ya bari Fukhaihat ta fara shiga.

Likitan ya ɗago kansa daga takardun da ke gabansa.

"Please... have your seats."

Suka zauna cikin nutsuwa.

A wannan karon, ofishin ya yi shiru fiye da da.

Likitan ya ɗauki sakamakon gwaje-gwajen jinin da suka fito ya fara dubawa a hankali. Wani lokaci yakan tsaya ya sake kallon wata takarda, sannan ya kwatanta da rahoton Ultrasound.

M.d ya lura da hakan.

Tun da ya shigo, bai ga likitan ya yi gaggawar magana ba.

Sai dai yadda yake nazarin sakamakon ya fara ƙara masa damuwa.

A ƙarshe likitan ya ajiye biro.

Ya ɗago idanunsa ya kalli Fukhaihat.

"Yaya kike ji yanzu?"

Ta gyara zamanta.

"Har yanzu ina jin kasala... sannan tashin zuciyar bai daina ba."

Likitan ya gyada kai.

"Na fahimta."

Ya sake kallon takardun.

"Na duba sakamakon gwaje-gwajenki."

Dukansu suka mayar da hankali kansa.

"Akwai wasu abubuwa da suka fito da ba su yi yadda muke so ba."

Zuciyar M.d ta buga.

"Wane irin abubuwa ne, Doctor?" ya tambaya cikin nutsuwa.

Likitan ya juya takardar gabansu.

"Gwajin ya nuna cewa wasu sinadarai da ke nuna yadda hanta ke aiki sun yi sama da yadda ya kamata."

Ya nuna wani ɓangare na sakamakon.

"Sannan akwai ƙarin bilirubin, wanda zai iya bayyana dalilin da ya sa idanunki suka fara ɗaukar launin rawaya."

Fukhaihat ta sauke idanunta kan takardar, amma ba ta fahimci lambobin da ke ciki ba.

Ta ɗaga kai.

"Doctor..."

"Na'am?" Ya amsa kiran da tai masa yana dubanta.

"Wannan yana nufin ina da ciwon hanta kenan?"

Likitan bai yi saurin amsawa ba.

Ya haɗa hannayensa a saman tebur.

"A'a... ba zan iya faɗin haka yanzu ba."

M.d ya ɗan numfasa, amma har yanzu damuwa ba ta gushe ba.

Likitan ya ci gaba.

"Akwai cututtuka daban-daban da kan sa irin wannan sakamakon. Wasu ana magance su cikin sauƙi, wasu kuma suna buƙatar ƙarin bincike."

Ya ɗan yi shiru, sannan ya ci gaba da magana cikin sanyin murya.

"Abin da zan faɗa muku yanzu shi ne... akwai alamun cewa hantar Fukhaihat tana cikin matsala. Amma ban san musabbabin matsalar ba tukuna."

Kalmar "matsala" kaɗai ta isa ta sa Fukhaihat jin wani iri.

Ta kalli M.d.

A wannan karon shi ma bai san abin da zai ce mata ba.

Likitan ya ci gaba.

"Ina son ku ga ƙwararren likitan cututtukan hanta. Shi ne zai gudanar da wasu ƙarin gwaje-gwaje domin mu gano ainihin abin da ke faruwa."

Ya fara rubuta takardar tura mara lafiya.

"Ba na son ku firgita. Kun zo da wuri, kuma wannan abu ne mai muhimmanci. Mataki na gaba shi ne mu gano dalilin matsalar, sannan mu fara maganin da ya dace."

M.d ya karɓi takardar cikin hannunsa.

"Za mu iya ganin specialist ɗin yau?"

Likitan ya ɗan yi murmushi.

"Na yi muku magana da ofishinsa. Idan ya gama duba marasa lafiyan da yake ciki, zai karɓe ku."

M.d ya sauke numfashi.

"Mun gode, Doctor."

Likitan ya kalli Fukhaihat.

"Ki yi ƙoƙari ki kwantar da hankalinki. Kada ki yanke hukunci kafin mu kammala bincike."

Fukhaihat ta gyada kai.

Amma zuciyarta ta riga ta fara komawa shekaru baya...

Lokacin da Daddy ya taɓa riƙe hannunta yana cewa:

"Ki riƙa addu'a kullum. Akwai wasu cututtuka da ba a son a ji sunansu sai an yi haƙuri da ƙaddara."

Ba ta taɓa fahimtar dalilin da ya sa ya faɗi hakan ba.

Sai yau...

Da ta ji kalmar "hanta."

MUBARAK:

"Mai ya sa na kasa mantawa da ita?"

Mubarak, wanda yake zaune a falon gidansa da yake sauka a Kano, ya tambayi kansa bayan ya sauke wani gajeren numfashi. Ya jingina bayansa da kujerar, sannan ya ɗora hannunsa a kan goshinsa yana ƙoƙarin fahimtar abin da yake faruwa da shi.

"She is so beautiful, I know. Amma na tabbatar ba wannan ne ya sa take yawan faɗo mini a rai ba."

Ya sake furta hakan a hankali, yana gyara zamansa a kan kujerar.

Kwanaki huɗu kenan da idanuwansa suka yi arba da kyakkyawar surar Fujeerat, amma abin mamaki, duk ƙoƙarin da yake yi na cire ta daga tunaninsa ya ci tura. Duk lokacin da ya samu kansa cikin shiru, sai tunaninta ya kutso cikin zuciyarsa ba tare da izininsa ba.

Wani lokaci har murmushi yake yi shi kaɗai idan ya tuna yadda suka haɗu, amma da zarar ya ankara da kansa, sai ya ɗaure fuska tamkar wanda aka kama yana aikata wani laifi.

"Anya kuwa ita mutum ce?"

A take ya zabura daga kan kujerar, yana zare idanuwansa.

"Yeah! Tabbas gamo na yi. Idan ba haka ba, ta yaya za a ce na kasa mantawa da ita daga kallo ɗaya kawai? What exactly wrong with me?"

Ya girgiza kansa, kamar yana son kawar da tunanin nata daga kwakwalwarsa.

"Allah Ya tsare ni daga dukkan wani abun cutar wa."

Ya ɗauki T-shirt ɗinsa da ke shimfiɗe a kan kujerar gefe, ya sanya a jikinsa bisa Three-quarter ɗin wandonsa. Daga nan ya nufi tsakiyar falon, inda ya ɗauki makullin motarsa da ke kan center table.

Bai damu da sauya silifas ɗin da ke ƙafafunsa ba, domin a yanzu abin da yake buƙata kawai shi ne ya fita ya ɗan zagaya, ko hakan zai taimaka wajen kwantar masa da hankalinsa.

Ya fice daga gidan, ya buɗe motarsa, ya shiga, sannan ya kunna motar ya fice daga harabar gidan.

A hankali yake tuƙi a cikin garin Kano, yana kallon yadda mutane ke kai-komo a kan tituna. Sai dai hankalinsa bai cika kasancewa a kan abin da yake gani ba, domin zuciyarsa na wani wuri dabam.

A cikin zuciyarsa kuwa, yana ta jero addu'o'in neman tsari daga sharrin dukkan halittu, yana fatan Allah Ya kare shi daga duk wani abu da zai iya jefa shi cikin damuwa.

Sai dai ina!Addu'ar da yake yi ba tayi tasiri akan ainihin abin da yake damunsa ba.Domin ko kamar wanda aka bashi umarnin juya wa,sai ya karkatar da kansa zuwa gefen titi.

A take kuwa, ya ji wani abu ya tsaya masa cak a zuciya.

Ita ce!

Fujeerat!

Tana tsaye a gefen titi tana ƙoƙarin tare abin hawa, sanye cikin wata riga da wando na material masu kyau, waɗanda aka yi musu ɗinkin falazu. Ta naɗe ƙaramin mayafinta mai launin light blue a kanta, wanda ya yi matuƙar dacewa da shigarta.

Fuskarta na sheƙi cikin kwalliya mai sauƙi, wadda ba ta wuce ɗan hoda ba, da kuma kwallin da ta yi wa idanuwanta. A leɓenta kuwa, ta shafa lip gloss mai ɗan sheƙi, wanda ya ƙara fito da kyawun fuskarta.

Mubarak ya rage gudun motarsa, yana kallonta tamkar wanda ya ga wani abin al'ajabi.

Ya lumshe idanuwansa, sannan ya sake buɗe su.

Tana nan!

Ya sake lumshe idanunsa a karo na biyu, yana mai tabbatarwa kansa cewa ba mafarki yake yi ba.

"Subhanallah!"

Ya furta a hankali, yana kallonta.

"Is this for real?"

A yanzu Fujeerat ta samu wani mai napep da ya tsaya a gabanta. Tana magana da shi, kamar tana masa bayanin inda take son zuwa.

Ba tare da wani dogon tunani ba, Mubarak ya kashe motarsa, ya buɗe ƙofa, sannan ya fita da sauri.

Kai tsaye ya nufi inda take tsaye.

Fujeerat ba ta lura da shi ba sai da ya tsaya a gabanta. Ta ɗago kai domin kallon wanda ya tare mata hanya, amma kafin ta fahimci komai, ya zura hannu cikin aljihunsa, ya ciro wasu kuɗi, ya miƙa wa mai napep ɗin.

"Jeka kawai."

Mai napep ɗin ya kalli kuɗin, ya kalli Mubarak, sannan ya kalli Fujeerat.

Da alama yana so ya tambayi dalilin da ya sa aka dakatar da shi daga aikin da ya zo yi, amma ganin yadda Mubarak ya miƙa masa kuɗin, sai ya karɓa.

"To, Allah Ya kiyaye."

Ya yi musu sallama, sannan ya ja napep ɗinsa ya bar wurin.

Fujeerat kuwa, ta buɗe baki da hanci tana kallon Mubarak.

"Excuse me?"

Ta furta a hankali, amma shi ko kallonta sosai bai yi ba. Ya kamo hannunta ya fara jan ta zuwa inda motarsa take.

A take zuciyarta ta fara bugawa da wani irin sauri. Ta kasa fahimtar abin da ke faruwa, balle ta san irin matakin da ya kamata ta ɗauka.

'Anya kuwa mutum ne wannan?'

Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta.

Tun bayan haduwarsu ta farko, ita ma ba ta samun cikakken sukuni. Sau da yawa takan tsinci kanta tana tunanin fuskarsa, maganganunsa, da yanayin da suka rabu. Amma duk da haka, ba ta taɓa tsammanin za ta sake ganinsa cikin wannan yanayin ba.

Abin da ya fi ɗaure mata kai shi ne yadda yake jan ta kamar sun daɗe da sanin juna.

Ta sauke dubanta zuwa hannayensu, sannan ta ɗago ta kalle shi.

"Excuse me, sir! Where are you taking me?"

Amma Mubarak bai amsa ba.

Ya ci gaba da jan ta har suka isa gaban motarsa. Ya buɗe ƙofar gefen direba, sannan ya juya zuwa gare ta, yana ƙoƙarin shigar da ita ciki.

A nan ne hankalinta ya dawo jikinta gaba ɗaya.

Ta ja hannunta da ƙarfi, ta ƙi yarda ta shiga.

"Malam, lafiya kuwa? Me kake ƙoƙarin yi haka?"

A karon farko, Mubarak ya tsaya cak yana kallonta.

Ya zuba mata idanu, yana nazarin fuskarta kamar yana ƙoƙarin karanta wani abu a cikinta. Ya ɗan karkatar da kansa, sannan ya sauke numfashi.

"Why?"

Ya tambaya a hankali.

Fujeerat ta daure fuska.

"Why what?"

"Why are you doing this to me?"

Ta ƙara buɗe idanuwanta.

"Doing what to you?"

Mubarak ya ɗaga hannu ya shafa fuskarsa, sannan ya sake kallonta da wani irin yanayi na damuwa.

"Me ya sa kike bibiyata? Me ya sa kika kasa barina in huta? Me ya sa kika yi mini wannan babbar satar?"

Ya tsaya na ɗan lokaci, yana kallonta kamar yana jiran ta ba shi amsa.

Sai kuma ya girgiza kai, ya furta cikin murya mai ɗauke da ruɗani:

"Dan Allah, wai ke mutum ce ma kuwa?"

Fujeerat ta yi shiru.

Ta kalle shi, sannan ta sake kallonsa, tana ƙoƙarin fahimtar ko wasa yake yi ko kuwa da gaske yake magana.

A ƙarshe ta kasa daurewa.

"Excuse me?!"

Ta furta cikin mamaki.

"Are you okay, sir? Kai kuwa lafiyarka?"

Mubarak bai kula da tambayar da ta yi masa ba. Ya ci gaba da kallonta, har sai da ya ɗan lumshe idanuwansa.

"Fujee, you hearing me, Say something, please!"

Ya ƙarasa maganar cikin wata irin murya mai laushi, wadda ta sha bamban da yanayin da ya fara magana da ita.

Fujeerat ta haɗiye yawu.

Ta rasa abin da za ta ce. A gefe guda, yadda yake kallonta yana sa ta jin kunya, a ɗaya ɓangaren kuma, maganganunsa suna ƙara ruɗa mata kai.

A hankali ta furta:

"To, ni me zan ce? Ban san abin da kake magana a kai ba."

Mubarak ya karyar da wuya, yana kallonta cikin rashin yarda.

"You mean you don't know?"

Ta girgiza kai.

"No, I don't!"

Ya yi shiru na ɗan lokaci.

Daga nan ya kalli ƙofar motar, sannan ya sake kallonta.

"Okay, get in the car. Let's discuss this carefully."

Fujeerat ta dubi motar, ta dubi shi, sannan ta sake kallon motar.

A fili yake cewa ba ta yarda da yanayin da take ciki ba. Amma duk da haka, akwai wani abu game da wannan mutumin da ya hana ta iya juya baya ta bar wurin kai tsaye.

Ta ɗan ja baya.

"Ba za ka fara ja na haka ba, ka ce in shiga motarka ba tare da ka gaya mini ko kai wanene ba."

Mubarak ya ɗaga gira.

"You don't know who I am?"

Ta ɗaga kafada.

"Taya zan sani,alhalin ba ka sanar mini ba?"

Ya buɗe baki zai yi magana, amma sai ya rufe shi.

A karo na farko tun bayan da ya fara magana da ita, ya ji kamar shi ne wanda aka jefa cikin jarabawar tambayoyi.

Ya sauke numfashi, sannan ya gyara tsayuwarsa.

"Fine. My name is Mubarak."

Ta kalle shi.

"Mubarak kawai?"

Ya ɗan yi murmushi.

"Mubarak kawai ya isa a yanzu."

Fujeerat ta kawar da kai, tana ɓoye murmushin da ya kusa subuce mata.

"To, ni kuma Fujeerat. Yanzu da ka san sunana, zan iya tafiya?"

Murmushin da ke fuskar Mubarak ya gushe a hankali.

"No.Ai already na san sunanki,and na kasa manta wa da shi.... Da ke na baki daya."

Ta juyo da sauri.

"Excuse me?"

Ya nuna motar da kansa.

"Please, just get in. I promise I won't hurt you. I only want us to talk."

Fujeerat ta zuba masa idanu, tana nazarin fuskarsa.

Akwai wani irin yanayi a tattare da shi da ba ta iya fassara wa kanta ba. Bai yi kama da wanda yake shirin cutar da ita ba, amma yadda ya fito ya hana ta tafiya, sannan ya kori mai napep ɗin da kuɗinsa, ba ƙaramin abin mamaki ba ne.

Ta cije leɓenta na ƙasa, ta sake kallon hanyar da za ta bi.

A ƙarshe, ta yi kundunbala ta shiga motar.

"Wallahi, idan ka yi wani abu da bai dace ba, sai ka ga yadda zan yi maka!"

Ta faɗa tana nuna shi da yatsa.

Mubarak ya kasa riƙe murmushinsa.

"Noted, madam."

Ya rufe mata ƙofa a hankali, sannan ya zagaya zuwa kujerar direba.

Yana shiga, ya kunna motar, ya ɗaure bel ɗinsa, sannan ya kalli Fujeerat.

Ita kuwa, tana zaune ne a gefensa, hannayenta rungume da ƙirjinta, fuskarta a ɗan ɗaure.

Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, yana kallonta ta gefen ido.

A hankali ya motsa motar, suka bar wajen.

Bayan sun yi tafiya na ɗan lokaci, Fujeerat ta juya ta kalle shi.

"Yanzu dai, ina za mu?"

Mubarak ya ɗan yi murmushi.

"Somewhere quiet."

"Somewhere quiet?"

Ta maimaita maganar cikin rashin yarda.

"Malam Mubarak, ka san ba haka ake yi ba ko? Ka fito daga inda ban sani ba, ka tare ni a hanya, ka sallami mai napep ɗina, ka ce wai ina bibiyarka, yanzu kuma za ka kai ni wani wuri da ban sani ba?"

Ya yi shiru.

Da alama a karon farko yake kallon lamarin daga mahangar Fujeerat. Ya fahimci cewa yadda ya yi mata ba zai sa ta ji daɗi ba, musamman ganin cewa ba su san juna sosai ba.

Ya sauke numfashi.

"You are right. I'm sorry."

Fujeerat ta juya ta kalle shi da sauri.

"Me ka ce?"

Ya waiwayo mata da ido guda, yayin da ɗayan ke kan titi.

"I said I'm sorry."

Ta ɗan buɗe baki, sannan ta rufe.

Da alama ba ta yi tsammanin zai ba ta haƙuri ba,domin a ganin ta ba abin da ya dace yace ba ne yanzu.

Mubarak ya ci gaba da cewa, "Zan kai ki gidan cin abinci da ke nan kusa. Za mu zauna mu yi magana. Idan kin ga ba kya son ci gaba da hirar, zan dawo da ke inda na ɗauke ki. Is that okay?"

Fujeerat ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta amsa:

"Okay."

Sai dai a cikin zuciyarta, ta fara tambayar kanta irin tambayar da Mubarak ya shafe kwanaki yana yi.

Me ya sa duk lokacin da na ga wannan mutumin, nake jin kamar na daɗe da saninsa?

Ta kawar da tunanin daga ranta, ta mayar da dubanta kan titi.

A gefe guda kuwa, Mubarak ya kasa hana murmushin da ke ƙoƙarin bayyana a fuskarsa.

Aƙalla dai, a yau ya samu damar zama kusa da ita.

Amma abin da bai sani ba shi ne, hirar da yake shirin yi da Fujeerat za ta buɗe ƙofar wasu tambayoyi da ba su da amsa a yanzu.

Kuma watakila, ita kanta Fujeerat ba ta san irin sauyin da wannan haɗuwa za ta kawo a rayuwarta ba.


Chapter 6 page 12
    Tafiyar da ba ta wuce mintuna goma ba suka isa wani katafaren gidan cin abinci da ke gefen titi. Mubarak ya faka motarsa a filin ajiye motoci, ya kashe injin ɗin, sannan ya juya ya kalli Fujeerat.

Ita kuwa tana zaune ne shiru, idanuwanta a kan wayarta, kamar ba ta ma san cewa sun iso inda za su je ba.

"Fujee!"

Ya kira sunanta a hankali.

Ba ta amsa ba.

Ya ɗan matsa kusa da ita.

"Fujeerat!"

A wannan karon ta ɗago kai da sauri.

"Na'am?"

Mubarak ya haɗiye dariyar da ta zo masa.

"Mun iso."

Ta dube shi, sannan ta kalli wajen da suka tsaya.

"Oh!"

Ta furta a taƙaice, kafin ta buɗe ƙofar motar domin fita.

Sai dai kafin ta sauka gaba ɗaya, sai ta ji muryarsa.

"Wait!"

Ta tsaya cak, ta juyo ta kalle shi.

"Again? What is it this time?"

Mubarak ya buɗe ƙofar motarsa, ya fito, sannan ya zagaya zuwa inda take tsaye.

"Nothing. Ina nufin, bari na bude miki kofar da kaina."

Ta ɗaga gira.

"Hmm"

Ya ɗan yi murmushi.

"After you, madam."

Fujeerat ta girgiza kai, sannan ta nufi ƙofar gidan cin abincin.

A zahiri, tana ƙoƙarin nuna cewa ba ta damu da kasancewarsa ba, amma a cikin zuciyarta, wani irin yanayi take ji wanda ta kasa fassara wa kanta.

Tana jin kamar duk lokacin da ya kalle ta, zuciyarta tana ƙara bugawa da sauri.

Abin da ya fi ba ta mamaki shi ne yadda ta amince ta shiga motarsa, alhali kuwa da wani ne ya yi mata irin abin da ya yi, da tuni ta yi masa magana mai zafi.

'Allah Ya kyauta mini! Wane irin mutum ne wannan?'

Ta faɗa a cikin zuciyarta.

Suna shiga gidan cin abincin, wani ma'aikaci ya ƙaraso ya gaishe su, sannan ya nuna musu wani teburi a gefe da ba mutane da yawa a wurin.

Mubarak ya jira har Fujeerat ta zauna kafin ya ja kujera ya zauna a gabanta.

Ya cire wayarsa daga aljihu ya ajiye a kan teburin, sannan ya dubi ma'aikacin da ya tsaya kusa da su.

"What would you like to have, sir?"

Mubarak ya juya ga Fujeerat.

"What would you like to eat?"

Ta girgiza kai.

"Nothing, thank you."

Mubarak ya daure fuska.

"Nothing?"

"Yes."

"You mean you don't want anything?"

Ta kalle shi da mamaki.

"Malam Mubarak, ka tambaye ni sau nawa kenan? Na ce maka ba na son komai."

Ya ɗan ɗaga hannu.

"Okay, okay. No need to get angry."

Ta kawar da kai.

"I'm not angry."

Mubarak ya yi murmushi.

"Of course, you're not."

Ta sake kallonsa, amma kafin ta ce wani abu, ya juya ga ma'aikacin.

"Bring us two bottles of water, a plate of fried rice with chicken, and a bottle of fresh juice. Make it quick, please."

"Okay, sir."

Ma'aikacin ya tafi.

Fujeerat ta zuba masa idanu.

"Amma ai na ce ba na son komai."

Mubarak ya jingina bayansa da kujera.

"Na ji. Amma ina da tabbacin cewa idan aka kawo abincin, za ki ci."

Ta buɗe baki da nufin mayar masa da martani, amma sai ta rufe.

Wannan karon murmushinsa ya bayyana sosai.

"See? Na san ba ki da amsa."

Fujeerat ta kaɗa kai.

"Allah Ya kyauta maka!"

Mubarak ya yi dariya a hankali.

"Ameen. Ke ma."

Sai suka yi shiru.

Mubarak ya zuba mata ido, yana nazarin fuskarta. Ya lura cewa kyawunta ba wai kawai a fuskar yake ba ne, har da yanayin yadda take magana, yadda take kallonsa idan ta ji haushi, da yadda take ƙoƙarin nuna cewa ba ta damu da shi ba.

Ya sauke numfashi.

Ya Allah, mene ne wannan?

Ya tambayi kansa.

Kwanaki huɗu yana ƙoƙarin kawar da ita daga tunaninsa, amma duk ƙoƙarinsa ya ci tura. Yau kuma da ya sake ganinta, sai ya ji kamar wani abu da ya ɓace masa ya dawo gabansa.

Abin da ya fi ba shi mamaki shi ne, bai san komai game da ita ba.

Bai san inda take zaune ba, bai san danginta ba, bai ma san ko tana da wanda take so ba.

Amma duk da haka, zuciyarsa ta ƙi ba shi sukuni.

"Fujeerat?"

Ya kira ta a hankali.

Ta ɗago kai.

"Na'am?"

"Can I ask you something?"

Ta gyara zamanta.

"Ka tambaya."

Mubarak ya ɗan yi shiru, yana neman kalmomin da suka dace.

"Do you believe in love at first sight?"

Fujeerat ta zaro ido.

"Me?"

Ya sake maimaita tambayar.

"Do you believe in love at first sight?"

Ta zuba masa idanu na wasu daƙiƙu, sannan ta saki wata dariya ta mamaki.

"Malam Mubarak, lafiya kuwa?"

Ya yi murmushi.

"Why? Is it a bad question?"

Ta girgiza kai.

"A'a, ba tambaya ce mara kyau ba. Amma me ya sa kake tambayata wannan?"

Mubarak ya ɗan karkatar da kansa.

"Just curious."

Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ɗauki kwalbar ruwan da aka kawo musu ta buɗe ta sha kaɗan.

"To, ni ban san ko akwai abin da ake kira love at first sight ba. Amma na san mutum yana iya ganin wani a karon farko, sai ya ji wani irin yanayi a zuciyarsa da ba zai iya bayyanawa ba."

Mubarak ya gyara zamansa.

"What kind of feeling?"

Fujeerat ta ɗaga kafada.

"Ban sani ba. Kai ka fi ni sani, ai kai ne ka yi tambayar."

Ya yi murmushi, amma a cikin zuciyarsa, sai ya ji kamar ta faɗi wani abu da ya taɓa tunaninsa.

"Okay. Let me ask you something else."

Ta ajiye kwalbar ruwan.

"Ka tambaya."

"Since the day we met, have you ever thought about me?"

Tambayar ta zo mata a bazata.

Fujeerat ta yi shiru.

Ta kasa amsawa nan take, domin a zahiri ta san amsar, amma ba ta son ta ba shi gamsasshiyar amsa.

Ta tuna yadda ta shafe kwanakin baya tana tunanin fuskar Mubarak. Ta tuna yadda wani lokaci takan tsinci kanta tana murmushi ita kaɗai, sannan ta yi saurin gyara fuskarta idan ta tuna cewa babu wanda ya kamata ya san abin da ke zuciyarta.

Amma ba za ta taɓa gaya masa hakan ba.Ta ɗan gyara zaman mayafinta.

"Why should I think about you?"

Mubarak ya yi murmushi.

"Because I think about you."

Maganar ta fito daga bakinsa kafin ya samu damar tantance ta, sai kuma ya yi shiru.Shi kansa ya yi mamakin yadda ya furta hakan kai tsaye.

Fujeerat kuwa, ta buɗe baki, ta kasa magana.

Ta kalle shi, sannan ta kawar da kai, tana jin wani irin sanyi yana ratsa fuskarta.

Mubarak ya lura da hakan.

"You're blushing!"

Ta ɗago kai da sauri.

"No, I'm not!"

Ya yi dariya.

"Yes, you are."

"Wallahi ba na jin kunya!"

"Okay, I believe you."

Ya faɗa, amma murmushin da ke fuskarsa ya nuna cewa bai yarda da ita ba ko kaɗan.

Fujeerat ta ɗauki kwalbar ruwan ta sha, domin ta samu abin yi maimakon ci gaba da kallonsa.

A wannan lokacin aka kawo abincin da Mubarak ya yi odar sa.

Ma'aikacin ya ajiye faranti a gabansu, sannan ya tafi.

Mubarak ya matsar da farantin kusa da Fujeerat.

"Eat."

Ta dubi abincin, sannan ta kalle shi.

"Na ce maka ba na jin yunwa."

Ya ɗaga gira.

"Fujeerat, please. Ki ɗan ci wani abu."

Ta yi shiru.

A ƙarshe ta ɗauki cokali ta fara ci, ba tare da ta ƙara cewa komai ba.

Mubarak ya ji daɗi a ransa, amma bai nuna hakan sosai ba.

Ya jira har ta ci kaɗan, sannan ya jingina hannayensa a kan teburin.

"Now, can we talk about something serious?"

Fujeerat ta ɗago kai.

"Like what?"

Mubarak ya zuba mata ido.

"About us."

Cokalin da ke hannunta ya tsaya cak.

Ta ɗago kai a hankali, tana kallonsa kamar ba ta ji abin da ya faɗa daidai ba.

"About who?"

Mubarak ya yi murmushi, amma a wannan karon murmushin nasa yana ɗauke da wani irin tsanani.

"About you and me, Fujeerat."

Ta sauke cokalin a hankali.

"Amma ai babu wani abu a tsakaninmu da za mu tattauna, Mubarak."

A karo na farko, ta kira sunansa ba tare da ƙarin wani suna ko girmamawa ba.

Mubarak ya lura.

Kuma ba don komai ba, wannan ƙaramin abu ya sa zuciyarsa ta yi wani irin tsalle.

Ya ɗan matsa kusa da teburin.

"Are you sure about that?"

Fujeerat ta kalle shi sosai.

"Eh. Tabbas."

Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya tambaye ta:

"To, me ya sa ni ma na kasa mantawa da ke?"

Fujeerat ta ji kamar an ɗauke mata numfashi.

Ta kasa motsi.Ta kasa magana.Domin wannan tambayar ita ma ta daɗe tana yi wa kanta.Sai dai ba ta taɓa tsammanin za ta ji ta daga bakinsa ba.

A hankali ta sauke idanunta zuwa kan teburin.Mubarak ya jira amsarta.Amma kafin ta samu damar magana, wayarta da ke gefenta ta fara ƙara.

Ta kalli allon wayar,sunan wanda yake kiranta ya tilasta wa fuskarta sauya wa.

Mubarak ya lura da canjin da ya samu a yanayinta.

"Is everything okay?"

Fujeerat ba ta amsa ba.

Ta ɗauki wayar, ta miƙe tsaye, sannan ta ce:

"Excuse me. I need to take this call."

Ta matsa daga teburin, ta nufi wani wuri mai nisa kaɗan.

Mubarak ya bi ta da kallo har ta isa, sannan ya sauke numfashi.

A yanzu ya fara fahimtar cewa akwai abubuwa da yawa da bai sani ba game da wannan yarinyar.

Kuma watakila, kafin ya fahimci dalilin da ya sa ta shiga zuciyarsa, zai fara buƙatar sanin ko wanene ita da gaske.

Ya ɗauki kwalbar ruwansa ya sha kaɗan.

Sai dai hankalinsa yana can inda Fujeerat take tsaye, tana magana a waya cikin wata murya da bai taɓa jin ta yi amfani da ita ba tun lokacin da suka haɗu.

Muryar da ta sa ya fara tunanin ko akwai wani ɓangare na rayuwarta da take ɓoyewa daga gare shi.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.