Free chapter · Read without an account
SCARS BENEATH HER STRENGTH 2
by Saddiqah M · NURI
Da sauri ta girgiza kanta tana hade hannayenta waje daya... Jin kamar tana shirin hada hawaye tayi saurin daga kanta sama trying hard kar hawayen ya zubo. Bata son tunawa dashi sam.... Bata son tuna komai daya shafeshi... Amman har dai wani zai tareta da kalmar so shine wanda yake fara zuwa kanta....
Bathroom din dake dakin tayi saurin shiga ta rufe tana jingina da bango. Kanta ta hau girgizawa sosai tana so ta dawo hayyacinta kar tayi kuka... Qarasawa wajen mudubin dake bandakin tayi ta tsaya tana kallon kanta.. Nuri was no longer Nuri... The Nuri standing before the mirror had changed completely. Tayi baqi ta rame da kana gani zaka shaida hakan indai ka santa da. Gaba daya a firgice take da kana kallonta zaka fahimci yadda take cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali.
Hannu tasa ta dungure kanta tana furta "Bai furta cewa yana sonki ba ke kike haukanki.." kanta ta hau gyadawa da sauri ka ganta atime din sai ka tausaya mata like gaba daya abinda yake faruwa da ita duk da tana mugun qoqarin kame kanta daga barin damuwa kamar ya fara tabata mentally.
Juyawa tayi ta bawa mudubin baya tana dafe hannunta jikin sink din ta baya. Wuri daya ta samu ta kafawa ido tana son ta ture duk wani tunani nasa da yake zuwa kanta.. tana son ta manta da komai daya shafeshi daga ranar data fara ganinsa zuwa ranarsu na qarshe..bayan tayi convincing din kanta cewa shi baya sonta, baice yana sonta ba... Kawai itace take sonsa.. Kuma cikin wannan shekara biyun ta kasa goge tunaninsa akanta...akanshi ta fara so, akanshi tasan mene so and it was hard for her to forget him because he was her first love...shi ya koya mata son kuma ya gudu ya barta da shi..duk lokacn da tayi zurfi a irin wannan tunanin tana qoqarin fahimtar da kanta shi fa baice yana sonta ba kawai wannan shine nashi kalar kulawar... It was obvious cewa ita nata son ta fara da son wanda baya sonta wanda bai ma san tana yi ba.. maybe yana da mata!!!!
Da wani kalar sauri ta nufi hanyar fita daga bandakin bayan tayi wannan tunanin da bata taba yin irinsa ba. He has a wife! That must be why he couldn't love her! Ta zata duk kalar abinda take gani a idonsa a wancan lokacin so ne! Idan haka ne kenan kulawa ce, wannan shine nashi hanyar nuna kulawa deep da zai sa wani ya soshi...idan kuwa haka ne ta tabbatar duk matan da yayi mu'amala dasu suna sona..then.. she was just a victim!
Bata tarar da ZAID ba, mai gidan daya shigo dakin hakan yasa tayi saurin daukar 'yar ledar data shigo da ita ta fice duk kuwa da tasan bata kammala aikinta na ranar ba kawai tana son ta koma gida ne kawai taji kanta yana juya mata.
Gidan yana da nisa da bakin titi sosai haka ta tako da kafa sai dai har tazo bakin titi tunani kawai take bama tasan tazo ba sai jin horn tayi ana cewa "ke yarinya matsa.." da sauri ta ja baya sai dai ta makara wani mai babur daya kauce mata ya bugeta. Faduwa qasa tayi ta gaba shi kuma wanda ya bugeta ya fadi dashi da abin hawan nasa.
In no time, people gathered around them, everyone exclaiming and reciting prayers they didn't need at that moment. Nuri taji ciwo a goshi ne kawai sai few scratches da kuma tsoro da yasa tayi passing out.. motorcyclist din shine wanda ya bugu sosai don jini sosai yake zubarwa ta baki da hanci.
Wani mai mota ne yayi volunteer aka sakasu a motarsa suka kaisu nearby hospital. Suna zuwa aka amshesu ganin condition din wancan kamar yana tsananta don yanzu har ta kunnesa jini yake fita. While Nuri had only just been taken into the A&E, she regained consciousness not long after. The medical staff dressed her wounds leaving her with nothing but a stinging sensation across her body.
Da kallo kawai take bin likitocin dake yawo kanta suna qarasa saka mata bandage a various places da taji ciwo. Rufe idonta tayi tana jin dama ta mutu ne ta huta maybe ta rabauta da Aljanna da babu wannan kalar rayuwar sai tsantsar jindadi.
"Akwai inda yake miki ciwo?" Ba tare data kalleshi ba ta girgiza masa kanta.. babu inda yake mata ciwo da ya wuce zuciyarta wani irin radadi take ji tana yi mata.. Kuma ta tabbatar na komai daya shafi rayuwar tane.. ku gane.. rayuwarta gaba daya ba tayi shi cikin jindadi ba tun bayan batan abbansu time din tana early 19yrs dinta.. tazo daga wannan sai wannan har zuwa yanzu da take 22yrs and babu wanda ta samu tayi confiding with ta bar komai a zuciyarta yana ta damunta don ma ahaka wani lokacin da dare tana tashi tayi kuka ko za taji sanyi even though the tears never took away her worries, she believed they could at least bring her heart some relief...
Nuri tana ganin kamar duk duniya babu wanda jarabawarsa ya kai nata.. tana ganin kamar nata yafi na kowa tsanani.. Mamanta tana raye amman basa tare... Waya ma suna dadewa basuyi ba.. they're not in touch with each other.. Dan uwanta yana raye amman yana wata duniyar though shi kusan kullum suna yin waya... Bata da qawa, qawarta Zara tayi nisa da ita they're no more contacting each other... Inna kawai ta rage mata, matar da duk duniya take jin tafi tsana sama da kowa amman she was bound to living with her.. ta tsani Inna amman ta rasa mene yasa take damuwa da abinda ya shafi Innar wanda yake nuna mata tana sonta duk kuwa da tsanar da tayi mata... Kamar wannan yafi damunta so da qi a lokaci daya...Abbansu duk hope din dawo musu da take dashi a ranta yanzu babu ta tabbatar da Abba yana raye zai nemesu ba zai manta dasu ba..karatunta! Da take bala'in so, tun tana JSS take son zama scientist that's why ta nemi medical laboratory science and by Allah's Grace ta samu ashe ba zata qarasa ba.... sai kuma kwatsam zuciyarta ya dauko mata sabon aikin da yafi komai bata mata rai idan ta tuna which was Love!! Love din ma she's the only one in it... In fact, wanda take son ma bata san ina yake ba...kamar zuciyarta duka yayi qanqanta da handling wadannan... rashin someone that will comfort her akusa da ita ya qara mata wani sabon raunin... Dawainiyar Inna da aikin da take yi yana qara mata wani pressure da suke takurawa kwalwalwarta.
"Bamu number mu kira gida mu sanar musu halin da ake ciki..." Har yanzu babu wanda ta kalla ta amsa da "basu da waya.." kallonta likitan yayi sosai kamin ya sake cewa "kwata-kwata babu mai waya?"
Kai ta gyada masa kawai tana rufe idonta alamar ya takura mata tana son a bata space.. tana son kasancewa ita kadai... She wanted to be alone.
Kamar likitan ya gane sai ya juya ya fita yana rufo qofar dakin tana jin fitarsa ta bude ido tana hararar qofar kamar itace ta takura mata. Time din alokacin around 12:30 ne Kuma cikin alluran da aka mata akwai na bacci hakan yasa ta fara baccin da bata farka ba sai 4.
Ahankali ya bude idanunta tana bin dakin da kallo kamin ta sauke idonta kan ruwan da ake qara mata daya qare. Miqewa tayi ta saka hannu ta cire sannan ta miqe tsaye ta qarasa inda taga an ajiye mata hijab ta dauka tana mitar ko wanne riqaqqen ne ya cire nata oho.. with all the injuries she had sustained, she still had the strength to complain.
Hijab din ta saka sannan ta juya ahankali ta fara takawa tana dan dafe kanta da yake mata ciwo. Fita tayi tana addu'ar Allah yasa kar ta hadu da kowa don ba zata zauna anan ba. Qasa tayi da kanta tana qarfafa kanta da kyar tayi tafiya kamar normal mutane ba marasa lafiya ba duk saboda kada a ganeta har ta samu ta fita daga asibitin ba tare data waiga ko sau daya ba.
Tafiya ta cigaba dayi har sai data yi nisa sosai sannan ta samu waje ta zauna tana haki kamar wata wadda tayi gudu ga ciwon kan nata sosai yake qaruwa. Minti kusan goma ta bata a zaune anan tana bin hanyar da kallo.
Idonta ya sauka kan wasu da suke tahowa su hudu, mata da yaranta guda uku kowa sai surutu yake mata yana riqe hannunta if she can hear them well ma taji suna cewa "Maama don Allāh mu ba sai kin kaimu wajen aunty ba munfi son zama dake..."
Qura musu idanu tayi, yaran duka mata ne kyawawa kuma baqaqe. She felt emptier than ever at that moment. Binsu ta rinqa yi da kallo har suka bace mata tana jin sun burgeta, taji dama itace daya daga cikinsu at least duk da bata san wannan quncin rayuwar ba. Ta rasa da zuciyarta da kwakwalwarta wanne yafi mata ciwo. One thing she knew for certain was that if someone examined her physically and mentally they would discover that she was unwell.
Miqewa tayi da kyar tana tattaro dan sauran kwarin gwiwar daya mata saura ta cigaba da tafiya. Duk wannan saurin da take gida take son komawa.. kuma saboda Inna, tasan ta barota bata da lafiya so bata san a wanne yanayi take ba shisa take so taje ta dubata, ta barota ita kadai kuma babu wanda zai kula da ita. After all, mai gidan hayan nasu ya jawo mata tsana daga kowa dake gidan plus ita kanta bata bari a rabesu kamar ta gama believing cewa babu wanda zai iya taimaka musu kaf duniya ciki harda Inna, so duk kalar ciwon da zasuyi komai tsananinsa babu wanda zai kawo musu dauki shi yasa duk rintsi duk wuya ko tana jinta bata da lafiya bata taba bari ta kwanta ba.
Tana shiga layin nasu takalminta ya tsinke hakan yasa ta tsaya tana dubawa taga ko da akwai dabarar da za tayi masa ta qarasa tafiya don daga bakin layin zuwa gidan shima wata sabuwar tafiyar ce. Takalmin ya mugun gajiya da ita don ita kanta ta manta yaushe aka siyo kawai dai tasan ya mugun dadewa. Haqura tayi ta cire ta riqe ahannu duka biyun sanin babu kyau tafiya da takalmi guda daya. Gashi yamma ne qasar wajen zafi saboda yadda rana ta gama dukanta ahaka ta cigaba da daurewa tana tafiya.
Sai da tayi tsakiyar layin taji kamar ta taka abu mai zafi daya sakata runtse ido da qarfi tana jin zafin yana ratsawa cikin kanta. Tsugunnawa tayi ta duba just to find out that qusa ta taka ga jini sai fitowa yake. Zaman dirshan kawai tayi awajen tana kallon qafarta without any hope. Duk dauriyarta da dakiyar da take mugun arowa kanta ranar sunyi nasu wajen abinka da dama halin aro ne.. kuka ta fashe dashi tana dafe qafarta anan kan hanya bata damu da duk wanda suke kallonta ba, kukan tasan shi kadai ne zai rage mata quncin da take ciki da kuma zafin da zuciyarta yake mata wanda yake damunta. Abu daya ne yake ringing akanta alokacin shine "bani da kowa arayuwar nan duk kuwa da cewa ban rasa kowa ba!!!!"
like, comment & share