Free chapter 路 Read without an account

Chapter 1

by Gidan Iko 路 GARWASHI

_Da ace bawa yana da ikon zabo kaddara, to da wasu mutane da yaww basu zabo kaddarar da take tasu ba_



........"Kaddara sunanta guda Daya ne Amma ma anarta da harsunan ta sunfi gaban a kidaya bare a iyakance. A yadda na fahimci kaddara da Kuma sunanta sai na kalli Duniya da abinda ke cikinta duk a matsayin kaddara. Idan nace kaddara to Ina nufin kaddara. Sai dai yadda Ni na fahimci kaddara akaran kaina ba Haka sauran mutane suke kallon kaddarar ba. Domin ko mun samu banbanci kwarai da gaske. A gareni kaddara itace  komai ya samu bawa kaddara ne Dadi da wuya. Samu da Rashi Rayuwa da mutuwa ita kanta DUNIYA da abinda ke cikin ta kaddara ne . Zuwan bawa Duniya ma kaddara ne Amma sai na fahimci mutane Abu guda Daya Tak suke Kira sa kaddara shine wani Abu da ya samesu marar Dadi shine kawai kaddara ban sani ba Ni fahimtar da nayiwa kaddarar ko don ya kasance gaba Daya Rayuwa ta kaddarorin ne sukayi Mata zobe ne yasa na fahimceta Haka? Koko nawa zaton ne dai Haka ? Oho.

A wannan labarin ma da Zan baku ma babu komai a cikin sa sai tarin kaddarorin da suka faru akaina da iyayena da ma Yan uwana kwara biyu da muka Rayu a wannan kuntatacciyar Duniyar marar tagogin da zasu bamu iskan da zamu Shaka bare mugane Yan cin dake cikin Duniya Wanda har na kirawa kanmu GARWASHI domin ko gara zama a cikin GARWASHIN WUTA da irin kaddarar da kaddarar ta Miko Mana dolen mu kuma muka Mika hannu muka karba har ma muka bita da godiya duk da babu murmushi yayin godiyar sai ma tarin HAWAYE Mai radadi a garemu musamman ma Ni yarinya Fatima Zahra da duka duka shekaruna Sha biyar ne kacal Amma kaddara Bata tausayawa kuruciya ta ba kamar yadda bata tausayawa mahaifiyata ba Akan Rashin dangi da Yan uwa tayi aikin ta Akan mu馃槶

Ku shirya ku Kuma gyara Zama kuji yadda kaddara tayi sukuwa ta kumayi zamiya Akan mu Wanda karfin imani ne ya Hana mu hadiyar zuciya mu kauce daga cikin Duniya da Rayuwa...........

*** *** **** **** ***

Karfe 12:09 am ta buga Mana muna tsakiyar filin jirgin marigayi malam Umar Musa yar Adua a garin katsina motar da mahaifiya ta ke ja kirar marcendy ce 3400 muka SHIGA filin jirgin Wanda yayi daidai da Jin Rigugin jirgin AZAMAN Yana Shirin sauka Alamar dai ba wani dogon jira zamuyi ba Daddyn zai iso nayi murmushi Mai sauti yayin da ammi ta tayani wurin fadin 

"Munzo a daidai ga abin Sona Nan Zuwa 
Ta fada itama tana Kara fadada murmushin ta Wanda yayi daidai da parking din motar da tayi a daidai parking space da sauri na balle murfin motar na fito ina daga kaina sama Ina kallon jirgin da Yake shawagin sauka kasa cikin wani salo Wanda ya dauki hankali na 
Na daga tafin hannun na Ina Kare Ranar dake kashe min ido don na kalli jirgin da Wai buwar da yakeyi idan zai sauka da kyau har ma in bawa Yan uwana labarin da nagani

Ammi tana Raba Mana kallo Ni da jirgin da ya dauko abin sonta cikin murna da farin ciki har zuwa lokacin da jirgin ya Soma saukowa kasa Yana tsillawa aguje kamar ba sauka zaiyi ba kafin ya zuro tayoyin shi da nagan su ya mitsimitsi kafin ya diresu a kasa fankokin shi na wulwulawa inda kuma wata mota Mai dauke tsani wato kwarangar da matafiyan zasu tako zuwa kasa


Na finciki hannun Ammi Wai ta taho itama da sauri ta biyo Ni inda Kuma Naga kamar bata sauri don Haka na saki hannun ta na sheka aguje da nufin idan Daddyn ya fito in fada jikin shi na Rungume shi nayi mishi oyoyo shi Kuma ya sureni yayi sama Dani Yana cillawa sama. don gaskiya Ina son Daddy na fiye da ammi don shi Kam biye min Yake Kuma duk abinda nake so shima shi Yake so yayi wasa Dani yayi dariya in fada mishi damuwa ta yayi min magani akasin ammi da ta Fi bawa Yan uwa na maza kulawa musamman Yaya Abdullahi da kanena sulaiman muhimmanci fiye Dani Ni Kuma Daddy yafi bani muhimmanci abinda ban sani ba shine kaddarar farko kenan da Zan Soma dandan Akan harshena da idanuna da Kuma zuciya ta Akan Daddy na Mai bani kulawa

Muna tsaye muna jiran a bude kofar jirgin don inyi ido Hudu da Daddy na koma in fada jikin shi muji dumin ya da mahaifi da nafi kowa muradin hakan

Kofar jirgin ta bude inda na Fara ganin aminin Daddyn ya Fara fitowa fuskar shi Babu sassauci kafin wani mutum ya biyo bayan shi sai Kuma wasu fuskoki da ban San su ba ban taba ganin su ba suka fito suka dauke da wani Abu Mai kamar gadon tura marasa lafiya wani Abu Wanda aka nade cikin farin yanki kwance Akan gadon kamar gawa........


Gabana naji yayi wata irin sarawa har naji kaina na neman daukar ciwo na juyo Ina kallon Amma wadda ta taho aguje tana bude fuskar Wanda ke kwance Akan gadon Nan fuskar was Zan gani? Daddy na ne babu Alamar motsi ko numfashi a tare dashi

Kafin na tambayi aminin Daddyn wato Alh Mustafa abinda ke faruwa Akan Daddy na sai Jin kukan mahaifiyata ammi naji cikin wata murya da ban zaci Tata bace...........


Kar ku Bari abar ku baya 


Gidan iko shine sunanan ke cewa saduwar ALHERI馃グ

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol