Free chapter 路 Read without an account
Chapter 3
*_Lokaci bak'o ne, zuwan sa da tafiyar sa duk baya sallama, Sai dai kuma yana zama alkalin yanke hukunci, ina ma ace bawa ya San abinda zai faru a gobe? Wata kil da ya gyara kuskuren sa, wata kil kuma da yayi nadamar mugun aikin sa,_*
.........Jikin ammi yayi matukar sanyi ganin Yaya Abdullahi ba sanarwa . Ni kuwa kuka na ne ya bayyana mishi wani Abu ya faru ko Kuma zai faru. Ina durkushe Agaban shi Ina faman Rera kuka na kasa dago Kai na dubeshi kamar yadda ya kasa Rarrashi na ya kuma kasa tambaya ta ba asin kukana.
Ammi ta zuba Mana ido tana Raba Mana kallo itama ta kasa tsayar da nata HAWAYE
Sulaiman ne yake fasawa Yaya Abdullahi Rasuwar Daddyn Kan shi tsaye Kuma ya fadin hakan saboda kuruciya Kuma shi tunda yayi kuka lokacin da za a fitar da gawar Daddy Bai Kuma sai dai ya kalle mu munayi Ni da Amma har wani lokacin nake tambayar kaina juriya ce ga sulaiman koko kuruciya? Sai na Gane jaruman Duniya sune Wanda basa taba Barin damuwa ta kassara musu farin ciki ta hanyar nuna komai ba komai bane . Sune Kuma Basu yarda damuwa ta kawo musu cikas ko tazgaro ba don suna ganin abinda ya faru ya faru babu Kuma me iya dawo da bara ta dawo bana in ba Allah ba sai su murje komai ya Zama ba komai ba su fuskanci abinda ke gaban su manta da wani tabo da kaddara ta kawo musu in ma kaga sun tuna to sun waiga baya ne don hango wani abun ba wancan ba sai yayi clation da shi
Duk juriyar da nasan Yaya Abdullahi da ita da jarumta irin ta maza Amma kukan da yakeyi Ni kaina sai da na tausaya mishi domin ko kalaman da Yake fada ne Dole su saka Mai imani zubar HAWAYE mussamman da na tuna burin mahaifin mu Bai wuce ya inganta Rayuwar mu da ilimin da zamu zamo abin alfahari ba mu Kuma zamo ya fita hakkin mu da kowane irin gata da gatantawa
"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Yake ta maimaitawa Yana fadin
"Shikenan Rayuwa ta juya Mana baya burina na son karatu ya Rushe duk yadda nake son karatun Nan Dole Zan barshi
"Shikenan SHIGA UKU ta samemu ammi Ina tausayin kaina Ina tausaya Miki.
Maganganun da Yake fada ne ya tabbatar min da lallai baya cikin hayyacin shi domin ko sambatu yake tayi Kuma Ni da ammi an kasa samun Wanda zai Mika mishi wata kalmar da ta danganci hakuri ko Rarrashi
Duk juriyar sulaiman sai da ya Rungume Yaya Abdullahi Yana Taya shi kuka Koko tausayin shi ne ya Kama shi oho
Bai tsinke ba sai da yaji abinda Alh Mustafa da Yan uwan mahaifin mu sukayi na karbe duk kaddarorin Daddyn. Ya kasa tankawa ammi akan wannan Rashin mutuncin kamar yadda ya kasa tsayar da hawayen shi.
Tun daga wannan Rana sai Rayuwa tayi Mana wani irin sauyi me yawa sauyin da yazo da kaddarori kala kala domin ko Yaya Abdullahi Bai samu zarafin komawa Egypt ba Domin ko kudin da ake biya mishi ba kadan bane Dole ma karatun ya tsaya ya dawo gida ya zauna muke Rungume da hannuwa in da muka tsira da gidan da muke ciki da Kuma motocin da Daddy Yake Hawa har guda uku sai ta ammi guda Daya don haka ammi ta taramu nida Yaya Abdullahi take fada Mana cewa zata siyar da Tata motar ta nemi wani kasuwanci ta Rika yi saboda mu samu na cin abinci inda Kuma yaya Abdullahi ya kawo shawarar a siyar da duka motocin sai a siyi babbar mota wadda zata Rika yin sufuri ana bamu kudin muna yin lalurar mu.
Ammi tace A a Kar a siyar da na Daddyn Wai hakkin mune Kar suzo su shige a banza Amma Tata ko ta shige a wurin hidimta Mana batajin komai Akasin ace gadon da mahaifin mu ya bar Mana ya salwance bamu Mori komai ba don ta San cewa abinda su kawu madu suka karbe da sunan Adana Mana sun dai fada ne kawai Amma ba adanawar zasuyi ba
Abdullahi ya tambayi Ammi har da kudin Daddyn na account din banki duk sun kwace?
Tace har fa abincin dake store Basu Bari ba sun Jude Kai sururun shi ma da komai na dakin shi Basu Bari ba sun kwashe Wanda Bai bar wannan ba yaushe zai iya Rike Amanar maraya? Ni dai Nagode wa Allah na Kuma godewa uban ku da yayi silar kawo Ni cikin hasken musulunci ba Kuma Zan butulcewa Ubangiji ba don wasu daga cikin bayin shi suna goranta min Ni din tuba nayi . Na yarda na Kuma Amince da musulunci shine karbabben addini wurin Allah na Kuma gode da ya Azurta Ni da samun ku a cikin musulunci sai dai Yan uwan uban ku da suke zagina da aibata Ni Akan tuba na Kuma ko su zanyi musu uzurin jahilci don aganina irin karbar da Dan uwan su yayi min irin ta ya kamata ace sunyi min kasancewar shi musulmi Dan uwan musulmi ne sai suka nuna min har abada shi Wanda ba musulmi ba in ya shigo cikin musulmi bashi da muhalli sai gori sai kyara da hantara. To babu komai in ma sunce ba zasu karbe ku a matsayin Ya'yan Dan uwan su ba Ni ina son ku tunda Kuma na hakura da Yan uwana da iyayena da gatana na baiwa komai da kowa baya Suma Zan iya Barin su tunda nayi Ruko da igiyar Ubangiji nasan ba zata tsinke ba sai mu Riki Allah Ni da ku nasan ya ishemu a ko ina Kuma ko yaushe
Mun Sha kuka da Jin wannan magana ta ammi Domin ko Bata taba fada Mana wani Abu da ya girgiza zukatan mu kwatankwacin irin wannan ba inda Kuma muka hakikance lalli Wanda yayi Rashi irin namu shine ya San dacin da ke akwai cikin Duniya Kuma Wanda Bai Rasa Uwa ko Uba ba hakika Bai San wani bakin ciki Mai yawa ba
Rayuwa tayi Mana sauyi hatta da irin cimar da muka Saba da ita ta sauya sabulun wanka ma ya sauya daga porrin zuwa Dan gida Nigeria. Makwanci ya sauya sutura ta sauya a komai mun samu sauyi kamar yadda sauyin Rashin Daddyn ya same mu Haka sauyin komai ya nuna kanshi a garemu
Tuni aka siyar da motar ammi aka siyi karamar motar gwalp wadda kuma ta Rasa Wanda zata dankawa Amanar ta don ba kowa ta sani ba inda ta tuntubi mama ko za a cigita Wanda zai karba yayi Mata sufuri ita Kuma mama tace zatayiwa mijin ta magana ya samo Mai Amana. Yaya Abdullahi yacewa ammi shi zai Rika Jan motar Yana zuwa Kano kaduna da sauran Yan garuruwan da ke kusa Wanda zai iya Amma Ammi tace Bata yarda ba don ba sabawa yayi ba Kuma ma Bata yarda ba wahala ce tukin mota . Duk nacin da yayi ya Kuma nuna Mata duk Wanda za a samo ba zai Kai ya shi ba Amma Ammi tace Bata yarda ba gara ta bude mishi shago ta zuba mishi Yan kayan treda ya zauna anan seet room din Daddy Wanda kofar shi ke kofar gidan
Haka Kuma akayi Yan sauran kudin da ta Rage na ragowar kudin motar ta su ta zubawa Yaya Abdullahi kayan treda Kuma cikin ikon Allah Asirin mu ya Rufu a ciki muke samun na hidimar gida har ma ayi Mana hidimar karatun mu Ni da sulaiman dake makarantar kayalwa dake kofar durbi Ni Kuma Ina makarantar scondry ta government college Yar kutungu
Muna ta Rayuwa a Haka cikin ikon Ubangiji da kallon komai Akan idanun mu da zukatan mu da Kuma godewa Allah a ko yaushe Kuma kowane irin hali da Kuma Mika hannu mu karbi ko wace irin kaddara kaddarar ta Miko Mana zamu karba mu Kuma godewa Allah tare da neman sauki acikin kaddarar da kaddara ta Miko Mana
Wata hudu da kwana goma da Rasuwar Daddyn mu ta fita takaba inda lissafin hakan da Kuma kwanakin mahaifina a kasa Bai taba kubce min ba a kullum dai nayi alkawarin Raka shi da ADDU A zuwa makwancin sa wadda na tabbatar ita kadai ce gatan da zanyi mishi shigen Wanda yayi min
Na dawo makaranta kenan na Tara's da ammi tayi wanka tayi Yar kwalliyar ta kadaran kadahan cikin wata atamfa me saukin farashi wadda mama ce ta siya Mata ita ta kumayi lalle abinda ta Dade batayi ba tunda Daddyn mu ya kwanta Dama tayi sallama da ko Mai Mai kamshi bare lalle sai dai Kuma duk da wannan Yar kwalliya da tayi maimakon Naga tana murna sai na Tara's tana kuka abinda ba sai an fada min ba tuno Daddy ne yasa ta kuka
Ta tusa aya da gyadar da ta soya zata Rabawa makota Amma sai Kuma take inda ta karya zuciya ta Nima sai na soke kaina cikin cinyoyi na Ina tuno Daddy da Kuma kalubalen da Rashin sa ya bar Mana wanda shi Allah baya barin wani don wani yaji Dadi. Lallai da Ubangiji na barin wani don wani yaji Dadi to da lallai muna daga cikin wadan da ba zasu taba zubar da HAWAYE don bakin ciki ba sai dai kukan Dadi irin na Ya'yan gata Domin kuwa na tabbatar Daddy zaiyi iyakar kokarin shi don ganin bamuyi kuka don Bakin ciki ba sai dai kukan Dadi
Haka Ammi ta bawa zuciyar ta hakuri Nima na bawa tawa muka share hawayen mu ta kulla ayar da gyadar ta bani na Rabawa makota gida gida har wasun su sukan Aiko Mata da Yan kudi Wai sadaka ce wasu Kuma abinci danye sai gashi ta samu kudi masu yawa da abinci
washe gari sai ga Yan uwan Daddy su kawu gide da yagana da kawu madu sun diro gidan suna zare idanu Alamar dai Rashin mutunci ne ya kawo su.............
Salon labarin nan daban yake da sauran da kuka sani, Kar ku sake ayi Babu ku bare abaku labari
Gidan iko ne sunana *** nake ke cewa saduwar ALHERI馃拑馃徔
Godiya marar adadin karshe ga masu sharing na labarin nan ina ganin Ku ina gode muku Allah ya bar tare 馃グ馃檹馃徎