Free chapter · Read without an account
Chapter 35
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 35
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
DR Waahab tun da uwarsa ta haife sa bai taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba, da ƙyar ya zauna kan kujera, don ji yake duniyar na juya ma, tun da ya girma yake tare da hankalinsa bai fuskanci abin da ya girgiza sa ba irin na yau, ya yi da ya sanin zuwa Tumbin Giwa, da ya sani da ya bari daga baya sai ya yi wishing Angel birthday. Ji ya yi kansa na sara masa, tabbas in ya ci gaba da zama a wajen zuciyar sa za ta yi bindiga, don haka da ƙyar ya mik'e yake tafiya ya tunkaro ƙofar fita...
Zuciyar sa ta buga a lokacin da ya tuna da mafarkan da ya yi da Angel har sau biyu tana neman taimakon sa, a hankali ya juyo ya kura mata idanu, ya hango tashin hankali a tare da ita, tabbas bai dace ya bari ayi mata haka ba, yana tunanin hanyar da zai samu mafita ya kuɓutar da ita. Cikin ƴan minti dabara ta faɗo masa ya tunkaro cikin taron...
Abraham dake tsaye sabar murna da farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha haka yake ji, wai shi ne za ayi baikonsa da Angel, yarinyar da yake burin mallakar ta. Ya fiddo da zoben alƙawari a lokacin pastor dake tare dasu a Tumbin Giwa ya taho suka iso inda Angel ke zaune ta nemi kuka ta rasa, wani abu ya tokare mata zuciya, ashe kuka ma rahama ce...
ALAJA ta miƙar da ita tsaye, tare da cewa Abraham ya sanya mata zobe pastor ya sanya albarka, da murna Abraham ya kai hannu zai riƙe hannu Angel Dr Waahab ya shiga tsakani ya dakatar da shi, da mamaki suke kallon sa, Angel ta dube shi fuskar nan a ɗaure timau kamar sabon kumurci ransa a ɓace yake don haka ta sudda kai tare da runtse idanunta...
ALAJA da mamaki ta ce
"Yallaɓai kake likita ko engineer, baka ganin abin da ake yi ne za ka shigo sakani"
Ya dube ta da jajayen idanunsa da suka sanya ta yi baya, ta sora sai ka ce tsohon soja, ya kalli Abraham tare da nuna sa da yatsa ya ce
"Angel ba mallakinka ba ce, kuma banga ta inda za ka mallake ta ba"
Abraham bai yi mamakin ganin sa ba, don ya san dole sai ya halarci birthday party na Angel, kuma yana so ya nuna masa iyakarsa, yana ji yana gani zai aure ta, ya daidaita tsayuwar ya ce
"Waye kai da za ka hana na mallake ta? Kana ji kana gani zan aure ta"
"Ba za ayi wannan baikon ba, sai dai kai kana ji kana gani za ka rasa ta"
Abraham cikin ɓacin rai ya ɗauki kwalba ya fasa yayo kan Dr Waahab pastor ya hana, tare da cewa
"Kai bawan Allah, me yasa za ka hana wannan baikon?"
"Shi ba musulmi bane, ba zai yu ya aure ta ba"
"Amma ai mu matan mu Cristian suna auran mazan musulmi"
"Tare da girmamawa na ce, mu ba zayyu ba"
Cewar Dr Waahab, Alaja ta hassala ta ce
"Kai ka fice min daga gida"
DR Waahab ya juyo kanta ya ce
"Wannan ki ke kira da gida, kina yaɗa baɗala da alfasha a unguwa ki ce gida, sannan kina ƙoƙarin tilasta yarinya ta auri wanda bata so kuma addinin su ba ɗaya ba, ƴan haka ya saɓawa addini, to babu inda zan je"
"Ya ishe ka, duk waɗan nan da kake gani babu wacce take zama na duk haya suke yi, suna biya na, ba ni ce na tara su ba. Don sun yi abin da su ke so ai ba laifi na bane, sannan batun baiko sai an yi kuma yanzu anan"
Sauke numfashi Dr Waahab ya yi da ƙarfi ya ce
"Ba zan bari hakan ya faru ba"
"Ku barni na ɓurma masa wannan kwalbar yanzu ya san da waye yake ja"
Cewar Abraham, sai hakuri ake ba shi, pastor ya kalli Dr Waahab tare da cewa
"Batun auren su ba laifi bane, tun da ku ma kuna auran addinan da ba naku ba, kaga in aka yi auren sai kowa ya yi addinin sa"
"Tabbas addini mu ya halatta auran wasu Addinin amma maza kawai za su iya ba mata ba"
"Na ga kai faɗa kake nema, ana sasanci kana kawo rigima, tun da kowanta ya amince ina ruwanka"
DR Waahab bai sake cewa komai ba, ka kalli fuskar Angel da ta sudda kanta ƙasa ta runtse idanunta ya ce
"Ki wuce cikin gida"
Jikinta ya soma rawa, hankalin ta a tashi ta yi steps ɗaya biyu ALAJA ta dakatar da ita ta hanyar cewa
"Is he your father?"
Ta dakata ta tsaya, Alaja ta ci gaba da cewa
"Na ce shi ubanki ne da zai ba ki umurnin tafiya, ki dawo nan ki tsaya Abraham za ki aura ko za ki mutu"
"ALAJA me yasa za ki yanke hukunci ba tare da kin nemi shawarar mamata ba? kuma ba ki ji daga ba ki na ba? Me na yi miki kike...
Wani wawan mari Alaja ta kwashe ta da shi, ta nuna ta da yatsa tare da cewa
"Har kin isa, wacce ke da zan yi abu ki soma min baki?"
Pastor ya gyara tsayuwar ya ce
"Madam ba ki yi daidai ba, ban san cewa bata son Abraham ba, da ban zo yin wannan baikon ba"
"Ƙarya take yi, tana so na, wannan munafikin ne ya zugata"
DR Waahab ya ji marin da Alaja ta yi wa Angel, shi ya fi komai ba shi haushi, ya taɓa masa ransa ya ce da ita
"Wannan shi ne na ƙarshe da za ki mare ta"
So al'ajabi ma suke yi, wai menene na shi don Abraham ya auri Angel. Sosai ake yin hayaniya me bakin sigari da gudu ya fita nemo limamin masallacin unguwar su, wanda shi ke ɗaura duk wani aure da ya shafi tubabbun karuwan Tumbin Giwa, don ba haka ba ya san yau za ayi kisan kai, ba ƙaramin aikin Abraham bane ya kashe wannan mutumin dake shiga sakanin baikon.
Babu jimawa suka shigo, kai tsaye Malliman ya tambayi Alaja
"Me yake faruwa anan?"
Kai tsaye ta ce
"Bikin sanya ranar aure"
"Auren waye?"
"Na Bilqees da ɗana ABRAHAM"
"Amma Alaja SA'ADEEY ba mun zauna mun kawo ƙarshen ire-iren waɗannan tashin hankalin ba?"
"To shi kenan Liman ba zan yi abin da ya dace ba, ina ruwan wannan saurayin da abin da ya shafe mu"
Liman ya juya ya kalli Dr Waahab da tun shigowar sa ya kura masa idanu yana son jin ƙarin bayani daga gare shi, ya ce
"Kai saurayi yaya sunanka?"
"Sunana Abdulwahab"
"Barakallah, labari ya zo min kana shirin hana baikon yarinyar nan"
"Eh haka ne"
"Saboda menene?"
"Ita musulmace shi kuma ba musulmi bane"
Da mamaki Liman ya dubi ALAJA tare da cewa
"ALAJA SA'ADEEY gaskiya ne yake faɗi?"
"Eh"
"Wa'iyazubillah! Wannan sai an samu zama"
A lokacin aka gyara kujerun da za su zauna, kowannen su ya zauna sannan Liman ya ya ce
"ALAJA SA'ADEEY ina kin karɓi musulunci da jimawa"
"Haka ne Liman"
"To me ya sa ki ke son saɓawa ubangiji?"
"Abin da yasa na dage sai an yi wannan bikin shi ne, na farko yarona yana mutuwar son Bilqees, har yau yake nemo budurwa ya aura ya kudurci ita zai aura, shi ne nake so na aura masa farin cikinsa"
Ta sauke numfashi ta ce gaba da magana
"Sai kuma akwai yarjejeniya a sakanina da Mamanta"
"Wane irin yarjejeniya?"
Cewar Liman, ta gyara zamanta ta ce
"Ina bin ta kuɗin haya na shekaru 22 bata bani ba, da wasu kuɗaɗen da nake bata aro"
"Ki ci gaba muna jinki"
Cewar Malliman, duk suka zuba mata ido suna sauraron ta, ta ci gaba da cewa
"Shi ne muka zauna mu ka yi magana da ni da ita akan zata dawo min dasu nan ba da jimawa ba, in kuma bata dawo da su ba zan aura mata duk wanda ya dawo min da kuɗaɗena"
"Ikon Allah ALAJA SA'ADEEY to ai wannan haɗin da ki ke shirya yinsa ba yi ba, kuma babu ilimi a cikin sa"
"To ai naga kuɗaɗena ba za su fito ba, shi ne kawai naga gara na ɗaurawa auren da yarona"
"Shin Abraham ya musulunta ne?"
"A'a bai koma addinin musulunci ba"
"To ya shirya komawa?"
Aka tambaye shi kai tsaye ya ce
"A'a ina nan akan addini mahaifina"
"To wannan auren ba zayyu da kai ba, kai Abdulwahab kana son Bilqees ne?"
Shiru aka yi, kansa a ƙasa, yana jin tattaunawar su, tambayar da Liman ya yi masa ne ya ɗan sanya shi cikin tunani. Bilqees jin an tambayi ya yi Uncle yana sonta ne ko a'a yasa ta ɗan kalli shi cikin sanyin jiki, tana tsoron amsar da zai bada...
"Zan bada kuɗaɗen da ake bin Maman Angel duk zan biya, a lissafa min su"
Da mamaki suke dubansa, musamman ALAJA Yallaɓai likita zai dawo mata da kuɗaɗen da take bin Maman Bilqees ta ɗan sauƙo ta ce
"Da yawa fah?"
"Eh zan biya amma da sharaɗi"
"Menene sharaɗin ka?"
"Tun da an warware wannan yarjejeniyar, daga yau ALAJA bata da iko akan Bilqees, za ta barta ta yi rayuwa cikin kwanciyar hankali, ko yatsa ba za ta nuna mata ba"
"Ba ka da matsala"
Malliman ya sake cewa
"Za ka iya auranta?"
"Eh"
Cewar Dr Waahab sai da Bilqees ta yi shock da jin abin da ya ce, ko dai ko dai don an matsa masa da tambayoyi ne ya amsa da haka..
"Ina sonta zan aure ta"
Cewar Dr Waahab, Malliman ya ce
"To ma sha Allah, ni ne limamin masallacin unguwar nan, kuma ni ke bada auren duk macen dake gidan nan in ta tashi dawowa hanya madaidaiciya, to in dai Bilqees ta dawo kan hanya za ta yi istibra'i sannan ayi aure"
"A'a malam yarinya ce, bata taɓa sanin ɗa namiji ba"
"To hamdallah, sai ka turo iyayenka"
"Ni ba ɗan nan ƙasar ba ce, ɗan ƙasar Nigeria ne, aiki ne ya kawo ni, na wasu organisations kuma muna dab da kammalawa, a bani lokaci na yi magana da iyaye na"
"Amma za a dawo min da kuɗaɗena kamin lokacin"
"Eh bani list ɗin su"
"Suna restaurant gobe ka je cen sai mu yi magana"
"To"
Abraham ya tada tarzoma shi an cuce shi an nuna masa, don shi ba musulmi bane, waya mutu waya tashi, Malliman ya fice Dr Waahab ya yi wa Bilqees rakiya zasu shiga cikin ALAJA ta ce
"Dakata ina za ta shiga?"
"Ciki mana wajan mahaifiyarta"
"Babu in da zata je sai an biya ni sannan ta shigo cikin gidan"
Dr Waahab ya sauke numfashi, ya yanke shawarar tafiya da ita hotel don bai san me zai faru anjima ba, kada wawan nan ya illata ta..
"Ba damu wa, Angel mu tafi zuwa gobe sai ki dawo"
Bata so bin shi ba, tana so ta yi magana da Mamanta, amma kuma tafiyar ita ce mafita, haka suka fito, Abraham kam sai ife² da zagi yake yi yana kudunduma ruwan ashariya, suna fita ya kama musu mashin biyu suka hau ya kawo su hotel. Angel jiki duk a sanyaye suka shigo, a lokacin har lokacin sallah magrib ya gota, ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya fice, Bilqees ta rasa ya za ta yi sallah don bata da hijabi, tana nan zaune har bayan ishai sannan ya shigo, ɗauke da leda, ya miƙa mata tare da cewa
"Akwai kayan sakawa a ciki, ki shiga toilet ki watsa ruwa"
Sudda kanta ƙasa, ta yi, ta kasa karɓa, tana tunanin ta yaya za ta shiga wanka yana cikin ɗaki, ya miƙa mata key ya ce
"Ki rufe ɗakin, zan je waje na jira ki"
Ya ajiye mukullin ya fice, ta mik'e ta sanya key ta rufe ƙofar sannan ta dawo da ƙyar ta watsa ruwa ta sauya kaya, zuwa farar Abaya tayi rolling ta yi mata kyau sosai, ta idar da sallah magrib da ishai sannan taji ana nocking, ta iso bakin kofar ta kasa buɗe wa tsoro take ji kada ta buɗe taga ba Uncle bane
"Angel ki buɗe ni ne"
Ta sauke ajiyar zuciya da ƙarfi ta buɗe, ya shigo ya kura mata idanu ta yi saurin sauƙe kanta jikinta ya soma rawa, yaga tayi matukar kyau cikin farar Abaya ta amshi jikinta sosai, ai wannan shigar ya fi akan wanda ta yi ɗazu...
"Mu je ko"
Da mamaki ta dube shi ya nuna mata hanyar fita alamun ta wuce gaba, bata musa ba, ta fito shi ma ya fito ya sanya wa ƙofar key suka fito, taga sun wuce parking space, ya iso wajen haɗaɗɗiyar mota, ya buɗe mata mazaunin gaba yana kallon ta, jiki a sanyaye ta yi yadda yake so, ta shiga ta zauna, ya shigo ya zauna a mazaunin driver ya ja suka bar cikin hotel ɗin, kai tsaye ya wuce da ita babban titi suka tsaya a wani kayataccen wajen cin abinci, ya buɗe mata motar ta fito suka shiga ciki, wani ɓangare ya kaita sai dai a lokacin da ta iso wajen babu haske sai deep light don haka bata iya kallon duk abin da ke wajen, ya nuna mata in da za ta tsaya, ta tsaya ya ɗan sauƙo da fuskarsa suna kallon juna ya ce
"Close your eyes"
Kuri ta yi masa, ta kasa rufe wa, sai da ya yi mata alama da ta rufe sannan ta rufe, jin kaɗan ya ce
"Ki buɗe"
Ta buɗe haske ya gauraye wajen an ƙayata in da suke da wasu furanni da kyallaye masu ɗaukan ido, tana bin wajen da kallo, dining table ne da kujeru guda biyu an shirya musu abin taɓawa, sai kuma idanunta su kai kan, decorations da aka yi a jikin bango an rubuta happy birthday Angel...
Ta dube shi, ya sauke numfashi a hankali ya ce
"Ki ƙarashe farin cikin ki anan, tun da an ɓata na cen"
Idanunta suka ciko da ƙwalla tana tuna lokacin da yake cewa yana sonta...
"Saboda ki yi murmushi na kawo ki nan, bana son ganin hawaye"
Ta haɗiye kukan, ya yi mata nuni da su ƙarisa wajen, sai da ta matso daf taga ɗan ƙaramin tebur ɗauke da madaidaicin cake na birthday, a hankali ya ce
"Happy birthday Angel"
Ta sauke numfashi tare da cewa
"Thank you"
Cikin nutsuwa da dabara yake yi mata wasu abubuwan yana sawa tana manta tashin hankali da aka yi ɗazu, har ta yanka cake ta miƙa masa ya karɓa ya kusura, sannan suka dawo dining sai dai bata ci komai ba, shi ne ya ɗan ci, ya fahimci kunya take ji kuma yasan bata ci abinci ba, dole yasa ta ɗan taɓa sannan suka dawo hotel, kamar yadda suka tafi. A palour ta zauna shi kuma a ɗaki tana ji ya shige toilet ya watsa ruwa, har ya fito bata yi bacci ba, sai tunanin irin hidimar da Uncle ya yi mata kusan wasanni biyu, tana ji yana waya, har ya gama ya kwanta ta kwanta kan carpet ta takure jikinta guri guda saboda sanyi da take ji, shiru ya ratsa taji taku a hankali an shigo ta runtse idanunta zuciyar ta na bugawa, taji ya haska ta da hasken wayar sa, ta kasa motsi ta yi shiru, taji ya sauke numfashi tare da rufeta da duvet ya bar palour, ta sauke ajiyar zuciya tana jin ɗumi bacci ya ɗauke ta....
Dr Waahab kusan kasa bacci ya yi, yana tunanin irin rayuwar da Angel ke ciki, ya kasa gane kanta, me yasa Mamanta ta zaɓi zama a cikin Tumbin Giwa bayan ta san yadda wajen yake? Sannan yadda ya fahimta babu alaƙa ta ƴan'uwan taka sakanin Angel da ALAJA, kuma bata san mahaifin ta ba, duk da baya so ya yi zargin komai dangane da rayuwar su amma wasu abubuwa suna yi masa yawo akai...
Yana wannan tunanin ne bacci ya ɗauke shi...
WASHE GARI
A hankali ta buɗe idanunta, da ƙyar ta tashi ta zauna, karatun Alqur'ani taji ana yi, ta miƙa ta iso bakin kofar taga Uncle ne, ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito zuwa palour ta idar da sallah, sannan ta zauna tana addu'a daga zaune bacci ya ci ƙarfinta ta jingina da jikin kujera bacci ya ɗauke ta.
Dr Waahab jin shiru babu motsin ta yasa ya taso ya shigo ya tadda tana bacci abin ta, a hankali ya sauke numfashi ya kurawa fuskar idanu, sai yaga kamar murmushi take yi, shi ma murmushi ya yi, sai dai jin motsi yasa ta buɗe idanunta ta sauke su cikin na Uncle, ta yi saurin gyara zamanta ta ce
"Barka da safiya"
"Angel kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah"
"Ma sha Allah"
Ya fito zuwa ɗakin sa, ya zauna bakin bed ya kira Dr Faisal a waya, babu jimawa ya shigo tare da cewa
"Special doctor morning"
"Morning Sir, naga kira da safen nan"
"Yanzu ne safe kusan 8:00 am"
Dr Faisal ya ɗan sosa keyarsa, ya ce
"Bab bata tashi ba"
"Magana nake so mu yi"
"Ok ba damuwa ina jin ka"
"Akwai yarinya a cikin palour, anan ta kwana akan ta za mu yi magana"
Dr Faisal ya gyara zamansa cike da mamaki ya ce
"Ka kwana da mace!"
"Kai ka saurari me nake cewa, anan ta kwana"
"To Sir tare ku ka kwana kenan"
"Faisal"
"Na'am"
"Don't judge me"
"Ok Sir, anan ta kwana"
"Yawwa abar maganar a haka"
"To an bari"
"Ina neman alfarma, za ka hakura da side naka, ka dawo nan ita kuma wannan yarinyar ta koma cen wajen Beb taka na kwana biyu kawai"
"Sir kwana biyu ba kawai bane"
Ya faɗa yana sosa keyarsa, Dr Waahab ya ce
"Ah menene a ciki kuma kullum kuna tare don kwana biyu kun ɗan bada rata shi ne abin damuwa"
"Ba za ka gane bane Sir, ba kowanne magidanci bane zai jure haka"
"Kaga kada ka yi min gori shi kenan ka yi tafiyar ka"
"Sorry sir na amince"
"Ka yi shawara da matarka"
"No ni namiji ne ai a tsaye nake a gidana, an gama magana"
Ɗan murmushi Dr Waahab ya yi, ya sauke numfashi, wannan ita ce mafita a gare shi.....
Ayi hakuri da typing errors
Comment and share fisabilillah