Free chapter · Read without an account
CHAPTER 17
by HAERMEEBRAERH✍️✨ · ZAWARA.
ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️
PAGE 17.
Ganin yanda Nasibah ta fito daga ɗaki a gigice kamar wata mahaukaciya sabon kamu,sai yaran da take yi wa kitso suka takure waje guda suna zare ido. Kilishi dake bakin makwarara tana wanke maburgi da muciyar da ta gama amfani da su sai ta saki soson hannunta ta kalli Nawwarah ta ce.
"Ke me yake faruwa na ganta a haka?"
Cike da matsananciyar damuwa Nawwarah ta ɗora hannuwanta a ka ta kasa furta komai sai nuna wa Kilishi hanyar waje da Nansy ta ɗauka take yi. Tsallake kwanukan dake wajen Kilishi ta yi ta nufi ɗakinta da gudu ta zaro mayafinta dake a saman ƙyauren ɗakin ta bi bayan Nawwarah da ta fita da gudu tana kiran Nasibah.
Nasibah kuwa tinda ta yi mummunan gamo da masoyinta na yi wa ƙawarta tsadadden murmushin da ita kaɗai yake yi wa irinsa ta dena fahimtar komai. Babban fata da burin ta bai wuce ta ganta a gaban Nadiya ba a wannan lokacin. Duk inda ta wuce mutane sai sun tofa albarkacin bakinsu a kanta,musamman ma da suka ganta babu mayafi ko hijabi, ballantana ƙafarta ta samu arzikin takalmi.
Tun daga nesa Nasibah ta hango Malam Luƙman a jingine a ƙofar gidan su Nadiya,nan take wani irin abu mai matuƙar nauyi da zafi ya soki zuciyarta, ba tare da tunanin komai ba ta rage saurin da take yi ta ƙarasa har jikin gidan su Nadiya. Muryar Malam Luƙman ɗinta ce ta sake tarwatsa duk wani sauran buri da ƙwarin guiwar da take da shi akansa. Cikin wani irin salo Malam Luƙman ya ci gaba da cewa.
"....dan haka na faɗa miki ki saki jikinki a yi wannan lamarin a gama cikin sirri. Ni na tabbata idan muka roƙi Nawwarah kada ta faɗa mata komai har sai an gama biki to ba za ta sanar da ita ba,ni kuma ta ɓangare na dama tuni na yanke duk wata alaƙa da ita,kuma ko ɗaurin aure ne ma zan roƙi Baba na ce ayi idan yaso da kun yi candy sai a yi walima a tare ba shikenan ba?."
Muryar Nadiya na rawa ta ce.
"A gaskiya ni dai ina jin tsoro,ka fa san halin Nasibah sarai da jidali da tashin hankali. Na rantse har yanzu zuciyata bugawa take yi dan na zaci Nawwarah ta gammu ɗazu. Kai ni fa gani nake yi kamar wani zai gammu tare ya je ya sanar da ita. Ni dai don Allah ka dena zuwa da rana,ka dinga bari sai dare ya yi sosai,ko kuma mu dinga yin waya kawai."
Tafi Nansy ta hau yi tare da ƙarasa wa gaban Nadiya dake maƙale a cikin soron gidansu. Nadiya na yin ido huɗu da Nasibah sai ta faɗa cikin soron gaba ɗaya ta manne a bango tana kuka mara sauti. Malam Luƙman kuwa suna haɗa ido da Nansy ya sauke kansa ƙasa yana kallon ƙafar Nasibah da ta yi fururu kamar wadda ta yi tafiya a cikin sahara. Majina Nasibah ta sha ta ce.
"Ki kwantar da hankalinki Nadiya ki auri Malam Luƙman ba tare da fargabar komai ba;domin ni Nasibah idan har na haifu cikin Maryama da Sanda Uba Makaɗi na barka kenan bari na har abada Luƙman. Na yi zaton kana so na, na yi zaton ni ce mahaɗin rayuwarka kamar yanda kake faɗa min a kullum,na yi zaton ni ce bugun zuciyarka Luƙman,ashe dama ƙarya kake yi min ashe dama kai mayaudari ne? Ashe dama...."
Wani irin kuka ne ya ƙwace mata sosai har sai da ta duƙar da kanta ta rufe bakinta da hannunta na dama. Hannu Malam Luƙman ya ɗaga zai riƙe wa Nasibah hannu,cikin sauri ta ja da baya tana watsa masa wani irin kallo mai wuyar fassara, ƙwalla ta gani a kwance a cikin idanuwansa. Dariya ta yi mai sauti hawaye na zuba daga idanuwanta ta ce.
"Ai murna za ka yi tinda ni Nasibah na san abinda kake lulluɓe wa. Ina so ka sani na so ka Luƙman,ina son ka har yanzu,amma ni Nasibah zuciyata bata da gwani,a yau idan na ga dama zan iya maye gurbin ka da duk wanda na so,kada ka yi tunanin soyayyar ka numfashi na ce da idan babu ita ba zan rayu ba. A yau na tabbatar da karin maganar Bahaushe da ya ce Namiji ƙanin ajali ne. To ni dai Nasibah na fi ƙarfin namiji ya yi ajalina sai dai ni na yi ajalinsa. Ina son ka sani ba a banza ake kirana da Nansy Ƙaya ba,na yi maka alƙawarin sai soyayyata ta maƙale maka a zuciyarka kamar yanda ƙaya ke maƙalewa a maƙoshi."
Kilishi na ƙarasowa wajen sai ta yi turus tana kallon ikon Allah. Nawwarah kuwa dama tinda ta iso ƙofar gidansu ta je ta tsaya tana hango yanda Nansy ke magana ta na kuka,ga Malam Luƙman tsaye ya shiga cikin matsananciyar damuwa. Jikinta har rawa yake yi zuciyarta na tabbatar mata da rashin kyautawa akan abinda ta aikata na ɗaukar hoton Luƙman da Nadiyah a ɓoye ta nuna wa Nasibah.
A ɓangaren Nasibah kuwa juyawa ta yi za ta tafi ta ji kalaman Malam Luƙman a cikin dodon kunnuwanta.
"Kada ki ga laifina Nasibah ke kin sani babu macen da na taɓa so a kaf ƴan matan da suka nuna min so sai ke kaɗai. Ke ce macen da ni na gani da idanuwana na kamu da soyayyarta a kallon farko. Nasibah na so ki tun baki gama sanin menene kalmar so ba. Ina so ki sani duk son da nake yi miki idan aka taɓa martabar iyayena dole ne na haƙura dake. Mahaifinki ya faɗa min kalaman da ko ni shege ne dole zan ji zafi ballantana ina da uwa da uba a raye."
Murmushi Nasibah ta sakar wa Luƙman da Nadiyah wadda har a wannan lokacin take manne da bango tana kuka. Cikin dasasshiyar murya ta ce.
"Ina yi muku fatan alkhairi."
Tana gama magana ta yi gaba tana tafiya cikin rangaji kamar ƴar maye. Da sauri Kilishi ta bi bayanta ta rungume ta tana jin matsanancin tausayin Nasibah na ratsa zuciyarta. A haka suka isa gida Nasibah na sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci. Kai tsaye ɗakinsu ta wuce ta haye gado ta kwanta ta rushe da wani irin kuka mai firgitarwa. Mama da ta jima a tsaye ita da Rabi tun bayan fitar Nasibah da Kilishi a hargitse sai suka ɗunguma zuwa cikin ɗakin suka hau tambayar Nasibah abinda ya same ta. Kasa furta musu komai ta yi,dan babu wata kalma da za ta iya fasalta abinda take ji a cikin zuciyarta. Faihah Kilishi ta kira ta aika maƙota ta siyo mata ruwan sanyi guda biyu. Tana kawo wa ta karɓa ta shiga ɗakin ta zauna a kusa da Nasibah ta ɗaga ta zaune ta ɓula ledar ruwan ta kafa mata a baki. Cikin sauri Nasibah ta hau kwankwaɗar ruwan har sai da ledar ta ƙare. Jikinta na rawa ta karɓi ɗayan ta miƙe tsaye ta fasa ta hau kwarawa jikinta. A ƙasan wajen ta zube tana kuka ta ce.
"Ummah zuciyata zafi take yi min. Ummah Malam Luƙman ya ci amanar soyayyarsa da na jima ina riritawa a zuciyata. Da na san irin cin amanar da zai yi min kenan da na bi maganar Baba na cire shi a raina tun da wuri."
"Ki yi shiru ki dena kukan haka ya isa,bari Baban naki ya dawo wannan abubuwan da yake yi sun isa haka."
Mama da ta kula babu mai bata amsa sai ta yi ajiyar zuciya ta ce.
"Allah Ya kyauta Ya kawo mafita."
Daga nan ta sa kai ta bar ɗakin. Sai dai duk da cewa ta bar ɗakin amma gaba ɗaya hankalinta yana kan ƴar tata tana hango irin matsananciyar damuwar da take ɗauke da ita. Da ƙyar Kilishi ta lallaɓa Nasibah ta fita ta ɗaura alwalar sallar magariba. Ko da ta dawo ɗaki sai ta sauya kayan jikinta ta saka hijabi ta tayar da sallah. Tana idarwa Makaɗi na dawowa gidan. Fuskarsa a sake ya shiga gidan yana yi wa su Najlah wasa. Idanuwansa ya dinga jefa wa a tsakar gidan amma bai hango ƴar rigimar tasa ba. Murmushi ya yi ya ce.
"Ke Faihah ina rigimatun gidan take ne yau na ji ko ina tsit kamar an yi rasuwa?"
Cikin fushi Kilishi ta fito daga ɗakinta sanye da hijabi ta ce.
"Ba dole ka ji ko ina tsit ba tinda kana neman ka jefa yarinya ƙarama a cikin mawuyacin hali? Wai kai don Allah Malam in tambaye ka mana. Shin me kake da shi a lokacin da ka je gidan iyayenmu neman aurenmu gaba ɗaya? Ina ce a wancan lokacin banda ruƙon ganga babu abinda kake yi wa mahaifinka? Da kuɗin kiɗa aka aura maka uwar su Hauwa ni kuwa...."
Kafin Kilishi ta ƙarasa maganarta Malam Sanda ya katse ta cikin wani irin matsanancin fushin da bata taɓa ganinsa a cikinsa ba ya ce.
"Ke dakata min Malama! Me yake faruwa a gidan da har za ki zauna kina neman zagar min asali da yi min gorin arziƙi?"
"Yo meye ma bai faru ba Malam? Garin leƙen jar miya a maƙota kana neman ka babbake taka tallen. Ina so ka sani a auren yanzu ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi ba wai auren je ki dangwalo wa dangi arziƙi ba,shi kansa yaron nan da kake maitar haɗa Nasibah aure da shi baka da tabbacin iyayensa za su yarda ya auri ƴar mai facin taya jinin makaɗa."
Jinjina kai Malam Sanda ya yi ya ce.
"Afff tohh! Yanzu na gane inda maganganunki suka dosa. To ina son ki buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau Kilishi. Ko na mutu na bar wasiyya wa ƴan'uwana da abokaina Nasibah bata da wani mijin da ya wuce Alhaji Samir,dan haka ki adana duk wasu kalamanki na rashin arziƙi da kika tanada domina."
"Au haka ma za ka ce Malam?"
"Haka kuma za a yi ba."
"Malam wannan yaron ne fa Lukman zai auri aminiyar Nasibah."
"Allah Ya basu zaman lafiya. Itama idan tana so wani satin sai a ɗaura nata auren da Alhaji Samir."
Shiru gidan ya ɗauka,banda kukan Nasibah da ke tashi baka jin komai. Mama na ɗaki ta zabga tagumi tana jin kamar ta je ta tunkari Makaɗi a yi wadda za a yi. Muryar Kilishi da ke sake yi wa Makaɗi magana ce ta sanya ta zama saboda kar ta nuna rashin kara. Haka Kilishi da Makaɗi suka yi ta sa-in-sa a tsakaninsu har ya fusata ya fita ya bar gidan. Tinda ya sa kai ya bar gidan bai dawo ba yana can wajen mai shayin dake saman layi yana hira da abokansa.
Fitarsa ke da wuya su Mama da Kilishi har da rabi da Usman sai suka zauna a tsakar gida suka hau tattaunawa akan lamarin Nasibah da Malam Luƙman. Mama ta ce bata ga laifin Malam Luƙman ba domin Malam Sanda da kansa ya kore sa ya yi masa iyaka da ƴarsa. Ita kuma Kilishi ta ce dama can baya son Nasibah tinda ya yarda da auren aminiyarta ba tare da ya ji shakkar yin hakan ba. Rabi kuwa sai ta ce to da dikkan alamu dama can yana son Nadiyah faɗa ne bai yi ba,jira yake yi sai ya auri Nasibah daga baya ya yo mata kishiya da Nadiyah. Usman kuwa kukan da Nasibah ke yi ne ya ɗaga masa hankali har ya kasa cewa kanzil a lamarin,daga sauke ajiyar zuciya sai dogon tsaki ya dinga ja har taron nasu ya tashi kowa ya nufi makwancinsa.
Malam Sanda bai dawo gida ba sai da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare,fuskar nan a murtuke ya shiga gidan da ita gudun kada ma Kilishi ta ga ƙofar kawo masa wata maganar mara tushe da amfani. Jin gidan shiru alamun kowa ya yi bacci ne ya sanya shi ajiye ledar da ke riƙe a hannunsa a saman randar tsakar gida ya ɗauki buta ya zaga bayan gida. Ya na fitowa ya ɗauki kofi da plate a kwandon wanke-wanke ya juye shayi da soyayyar indomie da kwai sannan ya nufi ɗakin su Nasibah da yake a buɗe. Kai tsaye gaban gado ya zauna a inda Nasibah ke kwanciya ya ce.
"Tinda na shigo na ji alamun idanuwanki biyu ƴar Baba, taso mu je ki ci abinci ki kora da shayi haɗin kauri dan na san baki ci abinci ba kika kwanta."
Hawaye Nasibah ta share ta juya wa Makaɗi baya ba tare da ta ce masa komai ba. Makaɗi kuwa bai sare ba sai ya ci gaba da lallashin Nasibah har sai da ta sakko daga gadon ta na kuka suka fito tsakar gida suka zauna a shimfiɗarsa. Da ƙyar take shan shayin dan kuwa ko da wasa bata gwada kai Indomie bakinta ba. Sai da Makaɗi ya gama cinye indomien tass sannan ya murje hannuwansa ya yi gyatsa ya ce.
“Nasiban Baba ina so ki buɗe kunnuwanki ki saurari dalilin da ya sa na zaɓar miki miji kamar Alhaji Samir. Na farko dai ni na san ba kya ƙaunar kishiya a rayuwarki duba da yanda kike rayuwa da ƴan'uwanki a cikin gidan nan. To shi kuwa wa talakan Malam Bahaushe babu wanda ya kai sa yawan aure. Amma idan kika auri mai kuɗi,kyau da cikakkiyar nasaba kamar Alhaji Samir za ki tsira da talauci da kishiya,ga shi uwa uba zaki dinga taimaka wa iyayenki da duk abinda kika samu a ƙarƙashin mijinki. Idan kuma ki na ganin zaɓina bai yi miki ba Nasibah ni Malam Sanda a yau na yi miki alƙawari zan aura miki duk kalar mijin da kike so."
Shiru Nasibah ta yi tana kallon kofin dake riƙe a hannunta kamar tana son hango maƙerin kofin. A hankali ta yi ajiyar zuciya ta ɗaga kai ta kalli Malam Sanda ta ce..........