Free chapter · Read without an account

CHAPTER 18

by HAERMEEBRAERH✍️✨ · ZAWARA.

ZAWARA.







NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ 








PAGE 18.





"Ni Baba babu wanda nake da burin aure a yanzu,karatu nake so na yi mai zurfi ko kuma idan na gama secondary school ka buɗe min saloon,ka ga shikenan sai na ci gaba da sana'ar kitso da ƙunshi....."

"Nasibah kin ƙunshe min bakinki kin adana shi ko sai ƙunsa miki duka a cikinsa da daren nan? Ke wai wace iriyar yarinya ce ana gabas kina yamma? Ke! Tashi ki je ki kwanta tun kafin ki jawo na kamu da ciwon hawan jini,Allah Ya tashe mu lafiya."

Tura baki Nasibah ta yi ta hau ƙunƙuni kafin ta miƙe ta shige ɗakinsu. Ƙwafa makaɗi ya yi ya ce.

"Wannan yarinya Nasibah Allah Ka shirya min ita. Ki sa a ranki auren Samir kamar kin yi kin gama,idan ma abinda ya fi saloon ne idan kun yi auren ya buɗe miki a can."

Da wannan maganganun Malam Sanda ya gyara kwanciyarsa a tsakar gidan ya ja babbar rigarsa da ta gaji da duniya ya rufa. A can cikin ɗakin Kilishi kuwa tana zaune tana gyangyaɗi saboda ta yi alƙawarin komai dare idan Malam Sanda ya shigo sai ta yi masa magana akan lamarin Nasibah. Cikin dare ta farka ta ga ɗakin daga ita sai halinta Malam Sanda bai shigo ba. Salati ta yi tare da zabga hamma ta sauka daga saman kujera ta fito tsakar gida. Kwance ta ganshi har ya fara sakin munshari hankalinsa kwance. Haɓa Kilishi ta kama ta ce.

"Au Allah! Ni ina can ina jiransa ashe shi yana nan ya hangame baki yana bacci a tsakar gida sauro na walima da jininsa. To ai shikenan Allah Ya tashe mu lafiya."

Ɗaki ta koma ta saka sakata ta yi kwanciyarta tana tunanin rayuwar gidan mijin nasu mai murɗaɗɗen hali.

Washegari da safe Malam Sanda da ƙyar ya je masallaci sallar asuba ya dawo saboda zazzaɓi mai zafi da ya tashi da shi,kai tsaye ɗakin Kilishin da ya yi wa yaji ya nufa ya haye gadonta mai rumfa ya ja bargo ya rufe har kansa,shiga goma fita goma Kilishi sai ta kalle shi ta ƙunshe dariya,domin ko sannu ta kasa yi masa gudun kada ta yi dariya ya ce ta raina shi. Daga ƙarshe duk yanda ta so ta ja bakinta ta yi shiru kasa wa ta yi sai da ta yi dariya ta ce.

"To ai shi Allah ba azzalumin Sarki bane. Mu je dai zuwa wai mahaukaci ya hau kura."

Muryar Malam Sanda a shaƙe yana maƙyarƙyatar sanyi ya kalli Kilishi ya ce.

"Allah Ya sa dai ba da ni kike ba."

"To Malam ai duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake yi ko? Sannan wanda ya saurara idan ya tsargu da shi ake yi ai babu mai iya sauya masa ra'ayi. Ni dai Malam ina mai baka shawara ka dinga kyautata wa iyalanka;dan ko babu komai yau idan aka ce babu kai za su yi kuka su tuna alkhairinka a gare su,amma kai ke nan daga ka kori wannan da zuri'arta idan ta zo sai ka fito wa da wannan kwaɗayinka a fili. Yanzu ga ƴar ƙaramar yarinya nan Nasibah ka sako ta a gaba,na kuwa tabbata ba za ka huta ba har sai ka cimma burinka akanta."

Ƙwafa Malam Sanda ya yi yana sake takure kansa a cikin bargo.

"Malam mai son ka ne kaɗai zai iya faɗa maka gaskiya duk dacinta. Yaran nan jikokinka ne,idan basu zo wajenka sun raɓe ka ba wajen wa za su je? Ko so kake yi idan Allah Ya sa suka girma suka zama wani abu a rayuwa su manta da kai? Shi ɗa na kowa ne baka san mai morarsa ba,kuma..."

Wurgi da bargon jikinsa Malam Sanda ya yi jiki na yi masa rawa ya hau dukan ƙirjinsa ya ce.

"Kilishi don Allah gani ki sa kaina gabar ki yanka ki feɗe ni ki ba wa yaran nan su gasa nama na su cinye ƙarewar soyayyar da kike musu. Haba! In banda ke ba kya neman albarkar aure haka kawai zaki saka ni a gaba bani da lafiya kina yi min surutan banza da wofi? Inda Maryama ta fiki kenan,ƴar nan dai tata ce ita ta ɗauki cikinta wata tara da kwanaki sannan ta haifo abarta,na tabbata ta fiki jin zafin duk wani abu da zai same ta,amma kina nan kin zaƙe kina son kai kanki wuta. To ina so ki buɗe kunnuwanki ki jini da kyau,in dai ni Sanda Uba Makaɗi ni na haifi Nasibah,to bata da mijin da ya wuce Samir."

Kalamansa sun yi matuƙar ƙona ran Kilishi,amma sai ta daure ta ce.

"Ko ka ƙi ko ka so Nasibah nima ƴata ce dan haka dole ne na yi magana akan lamarin da ya shafi rayuwarta."

Waje Malam Sanda ya fita cikin tsananin fushi da ɓacin rai zai shiga ɗakin Mama ya ci karo da Nasibah na zaune a saman bokitin ƙarfe ta na ɗaura takalmin makarantarta. Cike da mamaki ya tsaya yana kallonta kafin ya ce.

"Nasibah za ki iya zuwa makarantar kuwa yau?"

Murmushin yaƙe ta sakar masa domin ta ji duk abinda suka tattauna shi da Kilishi. Cikin murya mai cike da rauni ta ce.

"Zani mana Baba,takalmi na nake jiran na ɗaura na je na same ka ka bani kuɗin tara."

Haɗe fuska Makaɗi ya yi ya ce.

"Wai ke jiya baki yi kitso bane da kike jiran na baki kuɗin tara? Me yasa ke baki da tausayi ne Nasibah? Kina fa kallo ko lafiyar arziƙi ban tashi da ita ba,amma babu sannu ballantana Allah sawaƙe zaki ce na baki kuɗin tara."

Ajiyar zuciya Nasibah ta sauke kawai ta saɓa jakarta za ta bar gidan. Da ganin haka sai Makaɗi ya ce.

"Ƙalatacciya zo ki karɓa,ai ke idan baki raba ni da ƴan canjina ba ba kya jin daɗi."

Hannu ta miƙa masa tana danne murmushinta,shi kuwa sai ya dangwara mata kuɗin ya faɗa ɗakin Mama ya haye gadonta ya kwanta. Cike da mamaki Mama ta ce.

"Ah ah! Malam lafiya ka shigo min ɗaki ka kwanta a daidai wannan lokacin;ko dai ka yi makuwa ne, bafa anan kake ba."

Cikin rawar murya ya ce.

"Na sani Maryama bani da lafiya ne,ita kuma waccan ta fi gane ɗora min damuwa akan lallashina."

"Assha Malam sannu, Allah Ya baka lafiya,bari na karɓo maka koko ka sha da zafin sa sai ka sha magani. Amma dai da ɗakin ita Ummahn nasu ka je da ya fi,tinda ita ce ke da girki."

Buɗe kansa Makaɗi ya yi ya kalli Mama da ta miƙe tsaye za ta fita ya ce.

"Shin ko dai na bar muku gidan ne gaba ɗaya?"

Da sauri Mama ta juya ta ce.

"Me ya yi zafi shi ba wuta ba Malam? Ka sha zaman ka Allah Ya baka lafiya."

Kamar yanda Mama ta ce haka ta shiga kitchen ta ɗebo koko mai zafi a kofi ta kai masa da magani,da ƙyar ya iya shan kokon ya kora maganin sannan ya koma ya kwanta. A wannan ranar Makaɗi ko ƙofar gida bai sake fita ba,daga shiga banɗaki sai sallah su ne suka dinga tada shi.

A ɓangaren Nasibah kuwa lokacin da ta je makaranta sai ta ga ƙawayensu na ta kallonta cike da tausayawa. Nan take zuciyarta ta ayyana mata Nawwarah ta basu labarin abinda ya faru. Cikin ranta bata ji daɗi ba,domin ita yarinya ce da bata son mutane su dinga yi mata kallon tausayi ko su ga rauninta. Wannan dalilin ne ya sanya ta sake wa kamar babu abinda ya faru,har ta miƙa wa Nadiyah da ke a takure hannu suka gaisa. Haka Malamai suka dinga shiga suna fita a ajinsu har aka tashi break. Nadiyah da ke a tsarge sai ta je wajen Nasibah ta ce.

"Don Allah Nasibah ina so mu yi magana da ke ta fahimtar juna."

Murmushi Nasibah ta yi ta ce.

"Tooh! Dama ni da ke akwai wata rashin fahimta a tsakaninmu da ban sani ba?"

Numfashi mai ƙarfi Nadiyah ta sauke ta ce.

"Na san kin san akan me nake magana Nasibah. Don Allah ki fahimce ni,na rantse miki da wanda ke busan numfashi ban san Malam Luƙman ne wanda iyayena za su aura min ba,sai da Ummah ta ce na shirya mijin da zan aura zai zo mu gaisa sannan na san shi ne. Amma idan baki yarda ba..."

Kallon da Nasibah ta ƙura wa Nadiyah ne ya sanya ta haɗiye kalamanta na ƙarshe ta ja da baya kaɗan. Ganin tsoro da damuwa tare da tashin hankali a idanuwan Nadiyah kaɗai ya sanyaya zuciyar Nasibah. Nan take ta kawar da ɓacin ranta ta ce.

"Kada ki damu Nadiyah haka ƙaddara ta zana ni da Malam Luƙman za mu yi zazzafar soyayya,amma kuma ba za mu mallaki junanmu ba ke ce za ki zamo matarsa, dan haka bana so na sake jin damuwa a tattare da ke. Ina so ki saki jikinki sosai ki sha soyayya mai tsafta da mijin da za ki aura. Domin shi namiji duk yanda yake son mace da ya samu wadda ta fita yake mantawa da ita. Dan haka ina son ki fini nuna masa soyayya da tarairaya ta yanda zai so ki sama da ni. Kada ki manta akwai sauran shekaru biyu a gabanki kafin nan kafin aurenku."

Kafin Nasibah ta gama magana Nadiyah ta fashe da kuka ta rungume ta. Godiya ta dinga yi mata tana jin ƙaunar Nasibah har cikin ranta. A wannan halin Nawwarah ta zo ta same su,nan take fuskarta ta bayyana rashin jin daɗin ganinsu tare suna fara'a da juna. Ko ta kanta Nasibah bata bi ba ta wuce ta gabanta ta je ta siyo musu wainar flour suka zauna da Nadiyah za su ci,gefe Nawwarah ta koma tana danna wayarta tana cin magani. Basu kula ta ba suka fara cin wainar,dan kanta ta saki ranta ta saka hannu suka ci gaba da cin abincin a tare suna hira jefi-jefi. Suna gama wa da wainar Nadiyah ta yi amfani da kuɗinta ta siyo musu awara. Haka suka yi ta ciye-ciye har aka koma aji.

Lokacin da aka tashi a tare suka fito su uku za su tafi gida kamar yanda suka saba. Su na zuwa bakin gate Nasibah ta ja ta tsaya tana kallon mutumin dake jingine a jikin mota yana danna waya. Sunanta Nadiyah ta kira ta ce.

"Nansy mu je mana ko kin san shi ne?"

Da sauri Nasibah ta kawar da kanta za ta wuce ta ji an ce.

"Nansyy!".......

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol