Free chapter · Read without an account

CHAPTER 20.

by HAERMEEBRAERH✍️✨ · ZAWARA.

ZAWARA.








NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ 




*A karanta wannan saƙon yana da muhimmanci.*


*Ina kuke masoya littattafan marubuciya Hadiza D. Auta? Ku matso kusa ga wata dama ta samu. Ta fitar da promo na kwana uku kacal. Littafin da ke 1000 ya koma 700, na 700 ya koma 500.*

1. Abokin Aikina 1000
2. Baƙon Yanayi 1000
3. Dakan Ɗaka 1000
4. Gidan Aure 700
5. Dije ƙarangiya 700
6. Shagalalliya 1000
7. Bakan Gizo 1000
8. Jiki da Jini (A'isha) 1000
9. Ruwa Da Kankara 1000
10. Gidan Aure 700
11. Zubar Hawayena 500
12. Dace da Juna 700
13. Amfanin Fitila 1000
14. Tartsatsi 1000
15. Fansar Ƙauna 1000
16. Idan Rana Ta Fitowa 500
17. Umarnin Zuciya 1500
18. Kisan Mummuƙe. 1000

*9032685442 Opay Hadiza Ɗan Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lamba: ***.*


*LAST FREE PAGE.*



*Saƙo zuwa ga duk wani mai son cigaban labarin ZAWARA,a tura 700 a satin farko da fara yin payment ta 9031416423 Hamidah Sanusi Ahmad Opay,sai a tura shaidar biya ta ***. Satin farko na wucewa littafin zai koma 1k.*


PAGE 20.


Sanye take da wando irin na sojoji wanda ya yi matuƙar ɗame ta ta sama,ta ƙasa kuma ya saki sannan ya tsuke tsintsiyar ƙafarta mai sanye da rufaffun takalma. Rigar jikinta baƙa ce ta ɗame duk wani lungu da saƙo na jikinta,kanta babu ɗankwali sai tulin natural hair ɗinta da ya sha gyara ta fito daga cikin motar da ta ajiye ta a bakin gate ɗin gidan Alhaji Yusha'u Gwamnati. Ƙwanƙwasa gate ɗin gidan ta yi da ƙarfi kamar za ta ɓalla ƙofar ta shiga. Da gudu Lawi ya isa bakin gate ɗin ya leƙa ta jikin ƙaramar ƙofa ya hango Munirah tsaye tana huci kamar kububuwa,jiki na rawa ya buɗe mata tare da ja da baya yana karkarwa. A fusace Munirah ta ɗaga hannu ta wanka wa Lawi mari sannan ta ce masa.

"What took you so long to open the gate for me you fool."

(Me ya ɗaukeka tsawon lokaci kafin ka buɗe min gate ɗin kai wawa.)

Shiru kawai Lawi ya yi domin ba safai yake gane irin turancin Munirah da Samir ba. Cikin gidan ta shiga ta na ƙwala wa Samir kira,sai dai shiru babu wanda ya amsa mata. Har ta ɗauki hanyar shiga sashensa ta kula da Sakinah zaune a kujera tana danna wayarta hankalinta kwance. Cike da masifa Munirah ta isa gabanta ta ce.

"Ke! Meye ma sunan ki? Whatever barshi ba sai kin faɗa ba,dan ko kin faɗa ba riƙe wa zan yi ba. Wato dan wulaƙanci kina ji ina neman yayanki shine ba za ki kula ni ba ko?"

Kai Sakinah ta ɗaga ta kalli Munirah daga sama har ƙasa ta watsar;tare da ci gaba da latsa wayarta. Rai a matuƙar ɓace Munirah ta kai hannu za ta fizge wayar, cikin zafin nama Sakinah ta riƙe wayarta tare da miƙe wa tsaye ta nuna Munirah da yatsa ta ce.

"Ke! Mahaukaciya ki nutsu,kada ki kuskura ki yi gangancin yi min wannan haukan naki da kika saba,ina so ki dinga tunawa Hajjah ce kawai ke iya tolerating wannan nonsense ɗinki,sai kuma shi wanda kike baro gidan iyayenki kika biyo shi kamar ba mace ba."

Sosai kalaman Sakinah suka ƙona ran Munirah. Da ƙyar ta shanye ɓacin ranta ta ce.

"Yeh a ƙalla gwara ni ina da masoyin da nake zuwa wajensa,ke kuma da baki da kowa sai shegen baƙin hali fa?"

Nan take hayaniya ta kaure a tsakanin su kowa na ƙoƙarin nemo kalaman da za ta yi amfani da su wajen baƙanta wa ƴar'uwarta. A haka Hajjah Barirah da Samirah suka riske su. Tsawa Hajjah ta daka musu ta rufe su da faɗa. Sakinah ko ƙala bata sake cewa ba ta koma saman kujerar da ta tashi ta cigaba da latsa wayarta. Ita kuwa Munirah sai ta fashe da kuka ta faɗa jikin Hajjah ta ce.

"Hajjah don Allah ki sa Samir ya aure ni,na gaji da wulaƙancin da yake yi min a koda yaushe. Yaushe ma ya je Abujan da har zai kamo hanya ya taho ba tare da ya sanar da ni ba?"

Tsaki Samirah ta ja ta ce.

"To sannu uwarsa,haka kawai sai ya tsaya sai kin amince masa sannan zai dawo gida ko? Ko dama dan ke yake zuwa Abuja ba aikinsa ba?"

Hannu Hajjah ta ɗaga musu gaba ɗayansu kafin ta ce.

"Wai kina mufin shi Samir ɗin ne ya baro Abuja a yau? To ina yake kenan dan ni ban gan shi ba."

"Hajjah da gaske nake yi ya dawo,ina samun labari a wajen Nuh na sayi ticket na biyo bayansa."

Dariya Sakinah ta fashe da ita ta miƙe daga saman kujera ta wuce su Hajjah tana faɗin.

"Wa ya ga bindi,ko kunya bata ji wai na biyo shi."

Ta ƙarasa maganarta tare da karkace baki tana yanga kamar yanda Munirah ta yi.

Zama Hajjah Barirah ta yi a kujera tare da buɗe password ɗin wayarta ta nemo Lambar Samir wanda a daidai wannan lokacin yake tsaye a bakin motarsa yana riƙe da murfin ƙofa yana jiran Nasibah ta fito. Ringing wayar ta dinga yi amma Samir ya ƙi ɗaukan wayar. Nasibah na fitowa daga motar ya ce mata.

"Mu je ciki."

Juya wa ta yi tana harararsa ta ce.

"Ban gane mu je ciki ba. Ka ga Malam ka fa dena shigar mana gida kai tsaye kamar ɗakinka,akwai matan aure da ƴan matan da ba muharraman ka ba,that is in ka san menene ma'anar muharrami."

Nasibah ta ƙarasa maganarta tare da shigewa cikin gida. Ta na shiga ta ga ƙannenta suna ta bada labarin yanda Baban nasu ya zauna ya cinye kazar da Samir ya kai masa shi kaɗai bai bawa kowa ba,yana gamawa ya sha magani ya buga babur ɗinsa ya bar gidan. Cike da takaici ta shige ɗaki ta zauna a bakin gadon ɗakinsu tana hango irin kallon da Giɗaɗo ke wurga mata ta madubi. Kalamansa masu nuna tsantsar kulawa sai amsa kuwwa suke yi mata a cikin dodon kunnenta. Hannu ta saka ta toshe kunnen sannan ta miƙe ta kwanta da kyau a gado. Muryar Samir ta jiyo a tsakar gida suna magana shi da Kilishi tana sanar da shi Malam Sanda baya nan. Cike da matsananciyar damuwa Samir ya ce.

"Don Allah a sanar da shi gobe zan dawo da azahar wajensa;za mu yi wata muhimmiyar magana da ni da shi."

"To shikenan in Allah Ya yarda zan sanar da shi da zarar ya dawo."

Cikin sauri Samir ya fito daga gidan yana danna Lambobin wayar Malam Sanda ko zai same shi ya sanar da shi inda yake sai ya je su haɗu. Sai dai cikin rashin sa'a baturiya ta tabbatar masa da cewa wayar a kashe take. Tsaki ya ja zai shiga motarsa kenan ya hango motar Giɗaɗo na shigowa layin. Nan take zuciyarsa ta hau bugawa da ƙarfi yana jin kamar ya yi bindiga saboda damuwa da takaici. Gani ya yi motar ta tsaya na wani ɗan lokaci kafin daga baya ta juya da sauri ta bar layin a guje kamar za ta tashi sama. Wata iriyar wawuyar ajiyar zuciya Samir ya saki tare da jingina a jikin motarsa ya fashe da dariyar farinciki. Cike da ba wa kansa ƙwarin guiwa da yaƙini ya ce.

"In dai kuɗi na mallaka wa mutum abinda yake so;to Nasibah bata da miji a duniya sai ni Samir Yusha'u Gwamnati."

Yana gama magana ya buɗe motarsa ya tayar da ita sannan ya fara tafiya yana jijjiga kai tare da bin waƙar dake tashi a cikin motarsa,a hankali ya sa hannu ya ɗakko sigari a mazaunin da ya yi mata na musamman a motar ya kunna ya hau zuƙa cike da nishaɗi. Har cikin ransa yake jin son Nasibah,kuma a wannan lokacin ya yi wa kansa alƙawarin aurenta a gobe,domin ba zai bari zuciyar Makaɗi ta karkata zuwa kan Giɗaɗo ba ya rasa ta.

A ɓangaren su Giɗaɗo kuwa suna gab da zuwa gidan su Nasibah wayarsa ta fara ruri,ya na duba wa sai ya ga lambar Goggoji na yawo a saman screen ɗinsa,jiki a mace ya amsa kiran. Muryar Hajiyah Yalwa ya ji cikin kuka tana faɗin.

'Ka yi sauri ka zo asibiti Goggoji ta faɗi Giɗaɗo.'

A rikice Giɗaɗo ya tashi zaune da kyau ya ce.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,garin yaya ta faɗi Hajiyah?"

'To ni ma dai ban sani ba,amma mu na zargin sugar ko hawan jininta ne ya hau kwarai da gaske,gata nan likita ya sa an shigar da ita emergency room,don Allah ka zo da wuri i am helpless Giɗaɗo.'

Hajiyah Yalwa ta ƙarasa maganarta tare da rushewa da wani sabon kukan. Cikin sauri Giɗaɗo ya yi wa Malam Sadi umarnin su juya su je asibitin da aka saba duba Goggojin. 

Ko da suka isa asibitin sai Giɗaɗo ya fito daga cikin mota da sauri ya shiga cikin asibitin. Kai tsaye emergency room ya nufa,a bakin dakin ya tarar da Hajiyah Yalwa,Yansmin da Yusrah suna ta kuka. Hajiyah Yalwa na ganinsa ta nufe shi ta faɗa jikinsa tana mai rushewa da kuka. Cikin kuka ta ce.

"Giɗaɗo bana so na rasa Goggoji ita nake gani a matsayin uwa da ubana nake jin daɗi."

Idanuwansa ya rintse yana jin ƙirjinsa na bugawa,Goggoji ita ce rauninsa,kuma duk wani masoyi da maƙiyinsa ya san da hakan. Cikin wata iriyar murya mara karsashi Giɗaɗo ya ce.

"Me ta ci a wajen partyn ko kuma me aka yi mata da ya tada hankalinta jininta ya hau? Shi yasa na ce bana so a yi wannan bidi'ar kuka ce abu ne na ɗan lokaci."

Kai Hajiyah Yalwa ta sadda ƙasa ta ce.

"Shi yasa zan ƙare sauran rayuwata ina nadamar tursasawrar da na dinga yi a yi partyn nan. Da na san abinda zai faru kenan da ban matsa ba."

Fuskar Giɗaɗo da ta ji jawur ya shafa ya ce.

"Me ta ci!"

A razane Hajiyah Yalwa ta ja baya saboda tsorata da furucin Giɗaɗo ta ce.

"Ca...ca..cake ta ci. Tsaya ka ji kowa na gani sai da na hana ta,ita ta matsa ta ce ɗan kaɗan za ta ci."

Wajen Giɗaɗo ya bari ya isa daf da bakin ƙofar emergency room inda su Yasmin suke tsaye ya dinga leƙe ko zai iya hango Goggoji. Bai jima da tsayuwa ba likita ya fito,tafiya suka fara yi da Giɗaɗo yana yi masa bayanin yanayin sugar ɗin Goggoji da ya hau fiye da ƙima. Cike da damuwa Giɗaɗo ya ce.

"To yanzu likita ya ake ciki?"

"Alhamdu lillah tinda sugar ne kaɗai jininta bai hau ba,mun samu Allah Ya bata ikon farfaɗowa,sannan mun bata duk taimakon da ya kamata,sai dai fa ina mai tabbatar maka da cewa idan har ba a kula da cimar Hajiyah Goggoji ba da kuma yawaita motsa jikin da na ce muku tun farko tana yi akwai matsala."

"In Sha Allahu babu wata matsala da za a sake samu. Na gode Dr. Don Allah a cigaba da bata kulawar da ta dace. Kada kuma a bawa kowa izinin ganinta har sai na buƙaci hakan ."

Hannu suka miƙa wa juna Giɗaɗo ya nufi wajen Hajiyah Yalwa ya ce musu duk su tafi gida ita da yaran nurses za su kula da Goggoji. A shagwaɓe Yusrah ta isa gabansa ta ce.

"Haba Hubby ta yaya za mu tafi gaba ɗaya mu barta sai kace wata marar gata?"

Ransa a matuƙar ɓace ya ce.

"Da tana da gata da ba a barta ta ci abinda zai zame mata illa a gangar jikinta ba. Bayan haka ma ni da kaina na bada order ɗin cake ɗin ai,sai da na tabbatar da cewa na sanar kada a saka normal sugar a yi amfani da brown sugar da flour alkama,to a ta yaya ma cin cake kaɗai zai tayar mata da ciwonta har haka?"

Ido Hajiyah Yalwa ta hau matsewa tana kuka,kallonta kawai Giɗaɗo ya yi ya fuskanci tabbas akwai wata a ƙasa. Ƙwafa ya yi ya ce.

"Just go home,zan zauna har ta farka,idan na dawo zan yi bincike na gano abinda aka saka a cikin cake ɗin. Duk wanda na samu da hannu a cikin jefa Goggoji a cikin wannan mawuyacin halin ba zan raga masa ba,ko wanene!"

Giɗaɗo ya ƙarasa maganarsa a tsawace. Da sauri Yusrah ta kama hannun Hajiyah Yalwa suka fara tafiya,Yasmin da ta ci kuka ta gode Allah sai ta kalli Giɗaɗo cike da rauni ta ce.

"Yah Giɗaɗo ka yafe min,na san ina da laifi a wannan abun da ya faru saboda na matsa maka a haɗa mata grand party."

Murmushi Giɗaɗo ya sakar mata sannan ya rungume ta a gefensa na hagu. Ba tare da ya ce mata komai ba ya samu waje suka zauna suka yi shiru suna jiran tsammani. Haka suka kwashi kusan mintuna arba'in kafin Goggoji ta farfaɗo. Ana fito da ita daga emergency room suka bi likita da nurses dake tura gadon da take kai har ɗakin da aka canja mata. Sai da aka ɗaura mata ruwa sannan nurses suka fita suka bar Giɗaɗo da Yasmin suna rige-rigen zuwa wajen Goggoji. Hannuwanta kowannensu ya riƙe suka hau jera mata sannu. Da ido take bin su da kallo,a hankali ta furta.

"Ku dena..damuwa..na ji sauƙi."

Murmushi Giɗaɗo ya sakar mata tare da sumbatar hannunta ya ce.

"Za dai ki ji sauƙi Goggoji. Allah Ya baki lafiya Ya raba ki da yawan kwaɗayi."

A hankali ta saki murmushi mai sauti sannan ta ce.

"Amin Giɗaɗo am. Ke ƴar fara...duk kin koɗe saboda kuka...ya isa haka kukan...na ji sauƙi."

Kwantar da kanta Yasmin ta yi a jikin Goggoji tana matse guntuwar ƙwallar da ta taru a idonta. Shi kuwa Giɗaɗo sai ya miƙe tsaye ya ce.

"Na ga alamun bacci kike ji,bari mu tafi ki samu ki huta ok? Na san har da gajiya ma a tattare da ke;tinda yau kika dawo daga umra kuma aka tsiri wannan shirmen."

Kallonsa ya mayar kan Yasmin da bata da niyyar tashi su tafi ya sassauta muryarsa cike da kulawa da lallashi ya ce.

"Taso mu tafi gida ko? I promise you i will bring you back tomorrow."

Kafaɗa Yasmin ta maƙale masa,dan bata son tafiya ta bar Goggoji,haka kawai take ganin da ta tafi za su rasa ta. Ganin za ta kawo masa taurin kai sai ya fito mata a Giɗaɗonsa,nan take ta miƙe ta yi waje tana sharɓen kuka. Sallama ya sake yi wa Goggoji sannan ya bi bayan Yasmin yana jin tausayinta ƙwarai da gaske a cikin ransa. A hanya tunanin Nasibah ne danƙare a cikin ransa,sosai yake son ganin mahaifinta saboda ya miƙa ƙoƙon bararsa ko zai samu dacewa ta zamo rabonsa.



*************************

Da misalin takwas da kwata Malam Luƙman ya isa gidan su Nadiya hira. Kafin ya isa Nadiyah ta sha ado sosai tare da sanya turare,sai ta saka dogon hijabi akan shigar tata ta fita. A tsaye suka tsaya suna hira sama-sama. Babu jimawa wayar Nadiyah ta fara ringing,ko duba wa bata yi ba ta ƙi amsa kiran saboda ta gane Nawwarah ce ke kira daga kiɗan da ta saka mata. Kallonta Malam Luƙman ya yi cike da ayar tambaya. Nadiyah na ganin haka sai ta yi murmushi ta bi bayan kiran. Nawwarah na ɗaukan wayar sai ta ce.

'Ke fa ƴar wulaƙanci ce Nadiyah. Tin dazu nake ta kiranki in faɗa miki damuwata amma kina gani kika ƙi ɗaga wa.'

"Subhanallah me ya same ki Nawwarah?"

Nadiyah ta faɗa cike da kulawa. Ajiyar zuciya Nawwarah ta sauke sannan ta ce.

'Ni na rasa me maza suke gani a jikin Nansy wanda bamu da shi Nadiyah. Ke dai gashi nan ragowarta za ki aura,ni kuma da alama wanda na ƙwallafa raina akansa ba ya ganin kowa sama da ita. Ko kin san cewa Yah Giɗaɗon su Yasmin ita yake ta kallo tinda muka taho ta madubi?'

"Kin ga Nawwarah ki bari zan kira ki anjima,yanzu ina yin wani abu ne."

Cikin sauri Nadiyah ta kashe kiran tana kallon Malam Luƙman wanda ya yi zurfi a cikin kogin tunanin Nasibah. Cikin ransa yake ayyana.

'Bayan wancan nunar ranar har da kuma wani ne yake kai wa Nasibahta hari? Anya zan iya haƙura da ita kuwa? Kaii ina,a gaskiya ba zan iya jure ganin Nasibah a gidan wani namijin ba ni ba.'

Ba tare da Malam Luƙman ya yi wa Nadiyah sallama ba, kawai ya sa kai ya wuce gida......


*Shin tsakanin Yunus (Yah Giɗaɗo) da Samir,da kuma Malam Luƙman masoyin yarinta wanene zai samu nasarar auren Nasibah?*

"Tsakanin Nasibah,Nadiyah,Nawwarah da Rabi wacece za ta zamo ZAWARA a wannan labari namu?*

*Wace manufa Hajiyah Yalwa ke son cimmawa a gidan Gwani Ibrahim Yunus?*

*Mutuminku Malam Sanda Uba Makaɗi zai samu irin arziƙi da dukiyar da yake fata da burin samu ta hanyar aurar da ƴarsa da ya fi so a gidan masu kuɗi?*

*Ku biyo ni a wannan labari mai cike da cakwalkwalin cakwakiya na ZAWARA dan jin yanda zata kasance.*

*Assalamu alaikum Masoya karanta litattafaina. Kada ku manta ina da labarai masu daɗi da nishaɗantarwa tare da faɗakarwa. Duk mai so ta neme ni a wannan lambar ***. Ga waɗanda ke son a yi wannan tafiyar da su kuma,a sati na farko da fara yin payment ɗin novel ɗin ZAWARA za ku saka 700 kacal a 9031416423 Hamidah Sanusi Ahmad opay. Sai ku tura shaidar biya ta ***.*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol