Free chapter · Read without an account
BABI NA GOMA SHA HUƊU
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
YAU WATAN Ibrahim huɗu da sati uku zuwa Maiduguri domin aiki. Kafin su tafi, ya faɗa min ance wata biyar zasu yi su dawo amma ba yau aka saba faɗan irin haka ba kuma be zama gaskiya ba. Idan suka tafi irin wannan aikin se kuma sun dawo zaka san tsawon lokacin da suka ɗauka basa gida. Gaba-ɗaya dani kaɗai se ƴaƴanmu muke waya dashi idan ya tafi irin wannan aikin. Nima watarana muyi waya ne watarana har sati ɗaya mu kan yi babu waya. Juna biyun da nake ɗauke dashi kuma watan shi uku daidai duk ɗauka ta irin wancan abu na rana ɗaya kafin ya wuce ba ze sa na samu ciki ba amma kuma gashi. Cikina dama ba me fitowa bane ba. Cikin yarana ba wanda yasan ina da ciki su Ahmad da Baffa dama a hostel suke zama se idan anyi hutu suke dawowa.
Albashin shi yanzu yana hannuna saboda baya nan amma kuma a ciki nake taimakawa yarana masu karatu a jami'a kuma ciki muke ci da sha da duka lalurorin mu na rayuwa. Amma duk kuma yanda za'a yi ban taɓa bari abinci koda shinkafa ce ta yanke mana ba.
Yau ya kasance satin mu biyu bamu yi waya da Ibrahim ba. Zaune nake duk damuwa ta ishe ni ina ta tunanin ko yana raye ko kuma akasin haka duk da nasan da baya raye da yanzu an sanar damu. Sallama na fara ji na tashi da sauri jin muryar Ahmad da Baffa. Ina fitowa daga cikin ɗakina ina amsa musu. Ban san lokacin da nayi murmushi ba ganin ƴaƴa na biyu sun dawo gida da ƴar jaka a hannun su na kayan su wanda daga gani basu da yawa nasan sun bar saura a chan hostel tunda ba hutu bane me yawa ba.
“Har kun gama jarabawar Ahmad?” nace ina kallon Ahmad na kuma maida dubana ga Baffa “Baffa sannun ku da zuwa”
“Tun satin chan na gama na jira shi mu dawo gida tare”
“Kai da ƙanin ka! Ai kuwa ka kyauta Ahmad. Sannun ku da zuwa”
“Duba Umma kamar wasu baƙi. Ke dai kinyi kewar ƴaƴan ki”
“Dube yaron nan! Kaga laifina nida ƴaƴana. Kuzo ku huta gidan yayi min shiru dama gashi nan wani iri”
“Daddy baya nan ai dole zaki ce gida yayi shiru”
Murmushi Ahmad yayi ya shiga ciki da jakar shi shima Baffa ya wuce. Bayan sun aje kayan su suka dawo parlour muka yi zaune muna yin hira. Anan ne nake faɗa musu yau sati biyu bamu yi waya da mahaifin su ba. Ajiyar zuciya Baffa ya sauke. “Wannan aikin da wahala yake. Iyalan ka ba zasu taɓa samun kwanciyar hankali ba idan baku tare da juna”
“Abinda Daddy yake so yayi kenan kuma shi baya duban haka”
“Yanzu kuna gani ance da sunyi wata biyar zasu dawo kuma yau saura sati ɗaya amma nasan se sun wuce wannan lokacin. Tsorona kar ace har se anyi shekara saboda hawan jini na yana iya tashi bana iya jure wannan tashin hankalin”
“Kuma idan shekara ne ai haka zasu yi su dawo lafiya. Ko tafiyar da yayi Malawi ai sunyi shekara biyu kafin su dawo” inji Ahmad
“Ahmad kaga wannan gida ne tunda duk Nigeria ne amma ina jin tsoron case na Maiduguri”
Tashi Baffa yayi ya fita saboda baya son irin wannan maganar kuma baya son nuna damuwa akan damuwar da muke.
“Ki dena damuwa. Shine abinda zan faɗa miki a kodayaushe. Mu godewa Allah da har yanzu Daddy yana nan ko bayan tafiye-tafiyen da yake”
“Ba zaka gane abinda ke tsakanin mata da miji bane da kuma irin wannan haɗarin abubuwan, Ahmad. Ina ƙoƙari na kwantar da hankalina amma wani lokaci zuciya ta tana fin ƙarfina”
“Kiyi haƙuri Umma. Ai ya kusa dawowa gida mu ma mu koma gida dukan mu”
Shiru nayi ban ƙara cewa wani abu ba.
___________
Kwana biyu bamu samu abincin da zamu ci ba muna zama a cikin daji na Maiduguri a cikin wasu rumfuna. Ruwan dake gefe na na ɗauka na sha cikin gajiya ina ƙoƙarin danne wahala ta. Daga cikin sojojin da muke tare dasu maciji ya cije wani daga cikinmu ana bashi medical treatment. Nasan zafin da yake ji ne yasa shi yin ihu yana son riƙe kafar shi inda aka ciza. Combat Boots nashi duk an cire mishi da duk wani abu wanda ya matse shi a jiki.
“You gon be alright” military medical officer ya faɗa mishi.
Haƙoran shi ya gimtse wuri ɗaya ya ƙara yin wani ihu saboda babu antivenom da za'a kashe cizon macijin amma kuma an bada sanarwa za'a kawo daga cikin gari. Tsaye nayi ina kallon shi da kwatanta irin ciwon da yake ciki.
Muna nan tsaye aka kawo antivenom na maciji a cikin gari nan take aka mishi abinda ya kamata. Cikin ƙanƙanin lokaci duk ihun da yake ya dena se bacci ya kwashe shi yana sauke ajiyar zuciya.
A lokacin ne kuma aka kawo mana abinci. Kowa yunwa yake ji kowa ya fara cin abinci kamar wanda suka yi sati basu ci abinci ba.