Free chapter · Read without an account

BABI NA GOMA SHA SHIDA

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

KASHE WAYATA nayi gaba-ɗaya jin muryar mace na faɗa wa Ibrahim ba ze shigo suyi wanka a tare ba. Zuciya ta duhu nake ji a cikin ta ban san lokacin da hawaye suka fara fitowa a idanuna ba. Jikina naji ya kasa ɗauka ta yasa na zauna ƙasa a cikin ɗakina. Wani sanyi naji ya fara bin ƙafafuwana. Rufe idanuna nayi ina jin kowane irin emotion a cikin raina. Ibrahim ya rasa yaushe ze min zalunci da cin amana se yanzu da ba yara muke ba?. 
Ina jin yadda jinin ke min zuba sosai a jikina yasa na tashi na shiga ban ɗaki na fara gyara kaina. Zanen da nake daure dashi duk ya lalace da jini. Ganin yana ƙara karfin zuba yasa na fito gida na wuce asibitin Barracks. Taimakon gaggawa aka bani suna ganin miscarriage ne na samu. Kallo nake bin su dashi ɗaɗɗaya. Gani nake kowa ya taru ya yaƙe ni da farin cikina. 
Yadda naga rana haka naga dare a wannan rana. Karfe biyar na koma gida kar Farida ta tashi bana nan. 

Da safe a Bariki se ga senior officer, Imam da military medical officer sun taho. Duk wanda yaga waɗannnan mutanen a kofar gidanshi yasan ya kawo mishi munannen labarin da kowa yake jira yake kuma tsoron sauraro. 
A gidansu Maman Ummi suka shiga. Gabana ya faɗi ganin abokin Ibrahim ne indai aiki ne tare zaka gansu. Kuka aka ji ya karaɗe block ɗin mu da innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Kukan Maman Ummi ake ji tana faɗin “Wanene ze tsaya min nida da ƴaƴa na? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun” 
Chan ma across from us wasu da suke christians ba musulmai ba an tafi musu da pastor aka faɗa musu rashin su. Block ɗin ya karaɗe da kuka yayi tsit kamar anyi ruwa an ɗauke babu hayaniya babu maganganu dayawa se kuka da ake ji da yadda barracks tayi wani irin nauyi na silence wanda bashi da dad'i. 

Zama nayi na kasa yin komai ban san lokacin da na fara kuka tare da masu rashi ba. Jiya-jiya Maman Ummi ke faɗa min ƙarshen wahalar su ya taho saboda gida zasu koma da su Nasir sun dawo daga wannan aikin ashe bada shi za'a dawo ba. Kuka nake taya su akan abinda ya faru dasu idan ya faru dani nima kuma kuka nake akan irin abinda Ibrahim ya min sakayya dashi ya watsar da abinda muka gina tsawon shekara da shekaru da kuma ƴaƴan mu da suka girma. Farida ce tazo tayi zaune gefe na ta sunkuyar da kanta se kuma ta ɗago tana kallo na “Umma lafiya kike kuka? Harda Daddy na ne yana cikin su?” shiru na mata ban bata amsa ba. “Umma, da Daddy?” ta ƙara tambaya idanun ta na cikowa da hawaye itama nan take ta fara kuka. Hannuna nasa a ƙafaɗar ta and we cry together. 

Gama shirya gawawwakin akayi aka musu sutura aka ɗaura ƙyalle me taken flag na Nigeria akan saman jikinsu. Respect aka ba gawawwakin su tukuna aka kai su sabon gidajensu. Tsaye nayi ina kallo ana sa ƙasa ga jikin Nasir har ta rufe jikin shi gaba-ɗaya ba'a ganin shi. _“Yana yiwuwa na koma gida na dena wannan aikin saboda a gaskiya na gaji. Iyalina a kodayaushe hankalin ta a tashe yake”_ Maganar Nasir ta dinga yawo a cikin kaina. Na mance yaushe rabo da na zubar da hawaye da girma na ahaka se naji sanyi a fuska ta. Wani daga cikin soja ya riƙe min kafaɗa. “Mu tafi Ibrahim”
    “Nigeria ta gaza mana, Anas. Nigeria ta gaza mana”
Patting bayana yayi ya ja ni muka bar wurin. Gidana ma ba zan iya shiga ba. Ina jin kunyar haɗa idanu da Maryam. Ina yin dana sanin abinda nayi wanda yayi costing min abubuwa da dama a rayuwa ta. Nasan tana saƙawa a ranta ko sau nawa nayi irin wannan abun da na aikata. Fita daga barracks nayi na samu wuri ni ɗaya na keɓe ina tunanin rayuwa ta da abinda na jawowa kaina. Ba ni na koma gida ba se bayan Isha. Ina shiga da Maryam na fara haɗuwa tayi sauri ta shige cikin ɗaki. Ƙafa ta na ja na bi bayan ta bata rufe ɗaki ba. 
     “Maryam da...
 “Dan Allah a ƙyale ni”
Shiru nayi ina kallon ta ta kwanta a gado ta bani bayan ta. Na jima a tsaye ban tafi ba amma da naga da gaske take yasa na fito daga ɗakin na dawo parlour na zauna. 

A kwana a tashi aka tabbatar min da cikin da nake ɗauke dashi ya zube. Nayi baƙi duk na rame damuwa tana ci na kaɗan kaɗan na rasa yadda zanyi. A cikin barikin nan babu wanda nake iya zuwa nace mishi gashi. Yaya ta bana so na kira ta na tada mata hankali. Ban san yaya zanyi da Ibrahim ba. Aurenmu ban san ya zanyi dashi ba. Wani lokaci se nayi tunanin koda zasu duba na tafi abina amma ina duba ƴaƴana har dai Farida. Yanzu idan na tafi, ina zani? Ban yi tunanin Ibrahim ze taɓa rufe idanun shi ga abinda ke tsakanin mu ba yayi son zuciyar shi. Amma yayi kuma Allah ya tona mishi asiri. Ban san ko sau nawa yayi irin wannan abun ba lokacin da suka tafi Malawi suka yi shekaru biyu. Ban san ko Ibrahim yana da ƴaƴan da ba'a haifa da aure ba. Ibrahim yaci amanar auren dake tsakanina dashi be duba zaren da ya kulla rayuwar mu a wuri ɗaya ba yasa almakashi ya yanka ba tare da jin tsoron abinda ze biyo baya ba. 

Baffa ya taho gida ranakun hutu na karshen sati yace min ya gaji da zama hostel ɗinnan. Kallo na yake akai akai nasan yana so yayi magana akan yadda na zama. “Me yake faruwa kinyi baƙi haka duk kin rame Umma?”
        “Babu komai”
“Akwai wani abu Umma. Akwai wani abu da yake faruwa a gidannan ban taɓa jin gidannan irin yanzu yadda nake jin shi ba”
     “Kar ka damu kanka fa babu komai. Ayyuka kawai ne suke min yawa a gidan” 
    “Ki dinga hutawa Umma” Baffa yace yana nuna damuwar shi “Kar ki zo ki fara rashin lafiya”
Murmushi na mishi ban ce komai ba. Na tashi tsaye ina son ɗaga carpet na parlour inda yake zaune na ɗauko takardar asibiti. Nasan kuma halin Baffa da ɗaga carpet domin ɗaukar razor bana so ya ɗaga yaga abinda ya faru dani. Kafin na duƙa ɗaga carpet ɗin har ya ɗaga. Razor da yake so ya ɗauka ya gani ya ɗauka da takardar da na ajiye. Ban ce mishi komai ba na wuce ɗaki na na kwanta akan gado.

Takardar da Baffa ya ɗauka ya buɗe. Duk da ba Science class yayi a secondary ba ya gane abinda ke ɗauke a cikin bayanan. Tunani ya fara ko shine dalilin da yasa take cikin irin wannan halin. Amma kuma baya tunanin mahaifiyyar su zata so ta sake wata haihuwa har da ze sa ta shiga irin wannan damuwar saboda ta samu ɓari. Ya kuma lura da mahaifinsu ya rage zama gida kamar yadda yake yi idan yana gari. 
Fuskar Baffa ta zama gata nan baya jin daɗin gidan nasu ya ɗaga carpet ya maida takardar. 
Da dare mahaifin su ya dawo da siyayya sosai na kayan abinci da duk wani abu da suke buƙata na rayuwa da kuma jin daɗi. Su cornflakes ne macaroni, sphagetti, madarar gwangwo cartoon, bournvita ne, madarar gari babban gwangwo guda uku, Lipton ne su golden morn, custard duk ya siyo kuma isassu an basu kuɗi ne akan tafiyar da suka yi zuwa Maiduguri. Baffa ya taimaka aka shiga dasu gida cikin store kuma be faɗawa Maryam ba. Koda ma ya shiga ɗakin su ya same ta kwance akan gado ita ba kwana take ba duk ta rame fuskar ta tayi wani iri duk wanda ya ganta yasan tana cikin damuwa. Fitowa Ibrahim yayi daga ɗakin baya son zama a kusa da ita yana jin tsoron shirun ta da kuma abinda ke cikin ranta da duk wani abu da take tunani. 

Tsaye Baffa yayi a cikin parlour daidai wurin Tv yana son shiga ya duba mahaifiyyar shi kuma yana so ta faɗa mishi abinda ya dame ta. “Kasan abinda ke faruwa da Umma, Daddy?” Baffa yace 
Girgiza kai Ibrahim yayi be ce komai ba ya wuce ɗakin Farida. 

A chan wurin Maryam ji take kamar ta fito da zuciyar ta akan kasa shanye baƙin cikin da Ibrahim yasa mata. Gata nan tana fama da gidanshi da yaransu amma yana chan yana bin wasu matan banza. Hawaye ne masu zafi suka fito daga idanun ta zuwa kuncin fuskar ta. Bata share ba se tashi daga kwance da tayi ta jawo wayar ta idanun ta sun rufe tana son yin magana da ƴar uwarta. 
Tsayawa baƙin kofar dakin ta Baffa yayi yana tunanin shiga ko kuma ya juya ya wuce. Alamar kuka yaji baya son ya ganta tana kuka har ya juya ze tafi yaji tana waya. “Yaya. Yaya Ibrahim ya cuce ni ya cuce auren dake tsakanina dashi da duk wata alaƙa dake tsakaninmu akan aurenmu. Yaya ya yaran shi zasu kalle shi idan suka san abin kunyar da yake aikatawa idan ya tafi aiki?” Maryam ta faɗa cikin kuka me ban tausayi muryar ta na fitowa da kukan da take. 
Be san abinda aka ce on the other end ba amma mahaifiyar su tace “Muna waya dashi aikin nan da yaje a Maiduguri naji muryar mace a cikin waya tana cewa shi ba zaya zo suyi wanka ba, tana so su......” kuka ne yaci ƙarfin ta ta dena magana se kukan da take. Juyawa Baffa yayi ya wuce daga ɗakin ta ya koma ɗakin su. 

Zuciyar shi ce take bugawa da ƙarfi ya rasa natsuwar shi akan abinda yaji mahaifiyyar su na faɗa. Kasa zama yayi ya kasa tsayi jikin shi yayi sanyi muryar mahaifyyar shi kawai yake ji. 
Kasa haƙura yayi ya fito ya wuce ɗakin ta. Koda ya shiga ya samu mahaifin su a ciki tana magana ahankali cikin faɗa. “Ya kake so nayi akan irin wannan cin amanar Ibrahim? Me yasa da zaka aikata abinda kake son yi baka tuna da Ahmad da Baffa da Farida ba? Ka mance kana da yara ne? Da girman ka da duk tsawon shekarun da muka yi tare da juna cikin wuya da jin daɗi duk ka watsar dasu basu taɓa nufar wani abu a rayuwar ka ba”
“Dan Allah kiyi haƙuri Maryam. Dan Allah kiyi haƙuri. Dan Allah Maryam”
Tashi tsaye tayi cikin faɗa tace “Nayi haƙuri? Wane irin haƙuri kake so nayi? Zaka buɗe zuciya ta ne ka wanke duk abinda nake ji ko kuma zaka wanke kunnuwana daga ƙazantar abinda naji kana aikatawa?”
   “Maryam ba abinda kike tunani bane ba Maryam. Dan Allah kiyi haƙuri ki saurare ni”

Idanun Maryam suka cika da hawaye suna zubowa muryar ta ta disashe tace “Ka duba ka gani Ibrahim. Ina nan tare da kai cikin jin daɗi da wahala a cikin barracks ɗinnan. Baka San ina da cikin Farida ba se bayan na haihu kake sanin ciki ne dani. Na kare maka kaina da kana nan da baka nan. Na kula da yaran mu da akwai da babu. Wani lokaci baka san abinda yake faruwa damu ba na daga abinci a cikin barracks ɗinnan. Ban faɗa maka ba saboda bana so ka damu amma ka rasa sakayyar da zaka min se tafiya kana tarayya da matan da ba'a ɗaura maka aure dasu ba. Na yarda kar ka tuna dani ni ba taka bace ta ahalina ce amma yaran ka fa? Mutuncin su fa? Ashe duk soyayyar da kake faɗa karya ce Ibrahim? Akan ka, akan abinda naji a cikin waya cikina na watanni ya zube Ibrahim. Ka ci amana ta ka ci amanar aurenmu da ƴaƴanmu Ibrahim. Ban taɓa sanin zaka iya.........
Juyawa Baffa yayi ya bar wurin kamar ƙaramin yaro da yake cikin trauma wani balai da ya faru dashi. Zuciyar shi yaji tana yin tauri ga dukkan wani abu da ze iya faruwa dashi ko wani nashi. Ranar be samu yayi bacci ba. 

Dama yasan akwai abinda yake damunta kuma yasan idan shine mace a matsayin mahaifiyyar shi ba ze iya taɓa cigaba da zama da mahaifin su ba. Yana kuma jin tsoron karyewar da ƴan gidansu za'a yi da kuma shin, zasu iya taɓa dawowa kamar da ko kuma shikenan mahaifin su ya lalata musu farin ciki da zaman lafiyar da suke yi koda basu dashi dayawa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol