Free chapter · Read without an account
MATAR GIDA PAGE 78
by Maimuna Bala · MATAR GIDA
*MATAR GIDA BOOK* 2
*SHUUKRAN*
*YOTA ASSOCAITION*
P78
Karfe goma na daren ranar Alhamis jirgin su Ɗalha ya diro garin legos filin jirgin Murtala Muhammad international airport,basu wani gaji sosai ba kasancewar tafiyar awanni biyu ce bayan fitarsu daga airport suka tsare taxi da zai su hotel,Ɗalha ya faɗawa driver taxi sunan hotel da za su sauka,har cikin harabar hotel driver ya sauke su,Muhsin ne ya biya driver kuɗinsa daga haka suka nufi entrance bayan shigowar su entrance Ɗalha ya kama masu ɗaki tare da biyan kuɗin ɗakin a tare suka jera Ɗalha da Muhsin har suka shiga ɗaki,bayan shigowar su ne Muhsin ya cewa Ɗalha gaskiya yunwa yake ji zai fita ya siya masu abinci a takaice Ɗalha ya basa amsa ya ce ''to'' daga haka ya yi shigewarsa bathroom,washe gari juma'a a ɗaki Ɗalha ya uni yana shirya speech ɗinda zai yi a gobe asabar,tun safe yake abu guda ya gyara nan ya canza can bayan dawowarsu daga sallar juma'a Muhsin ya ce su ɗan fita zaga gari amma fir Ɗalha ya ƙi,ba shi ya gama rubuta speech ba sai misalin uku na rana,sai a sannan ya samu ya fita daga ɗaki nan ma ba nisa ya yi ba iya harabar hotel ya zaga daga haka da koma ɗaki,Muhsin dai sosai ya yi yawace yawace a garin Legos,washe gari asabar misalin ƙarfe tara na safe Ɗalha na kwance idanunsa lumshi saƙon email ya shiga wayarsa Muhsin dake zaune kan kujerar dake ɗakin shima wayarsa ta yi ƙara alamar shigar saƙo Ɗalha ne ya fara duba wayarsa ya ga saƙon da sauri ya tashi daga kwanciyar da yake ya zauna yana ƙara karanta saƙon da kyau can ya mayar da dubansa ga Muhsin suka haɗa ido Muhsin ya buɗe hannayensa alamar tambaya fuskarsa cike da mamaki ya ce ''me mutanen nan suke nufi da wannan sakon?" Ɗalha dafe goshinsa kawai ya yi,ya yi shiru na wasu ƴan mintina can ya ɗago ya kalle Muhsin kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ransa ya ɓaci a hankali ya buɗe baki ya ce ''yau zan bar garin nan wallahi aiy wannan iskanci ne'' ya kare magana tare da miƙewa tsaye ya nufi hanyar bathroom Muhsin ya bisa da ido kafin ya ce ''lallai mutanen sun san kan tsiya just two hours to program su ce sun yi cancel program'' shi dai Ɗalha ya yi shiru bai ce komai ba ya yi shigewarsa bathroom bayan mintina ashirin ya fito sanye da bathrope yana kallon Muhsin ya ce ''mallam tashi ka shirya mu tafi bazan ƙara kwana garin nan ba'' wani kallo Muhsin ya jefo masa kafin ya ce ''me ka ke nufi baza ka kwana garin nan ba mota za ka bi ko kana da kuɗin jirgi ne?mallam ko mota za ka bi sai gobe za ka samu mota shima kuma sai ka yi booking nan da fa Kano bace ko Kaduna da za ka tashi tsakar rana ka je tasha ka shiga mota'' Ɗalha bai kula sa ba ya wuce wajen saif inda suka sa jakukkunan su, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce ''flight ticket zan siya mana yau zan koma gida na dai faɗa maka so If you like sit there and be making noise'' ganin da gaske Ɗalha ke yi yasa Muhsin tashi ya shiga shiri,cikin abinda bai fi mintina talatin ba Ɗalha ya yi masu booking flight daga legos zuwa Kano,wani fancy restaurant suka tsaya suka yi breakfast daga haka suka wuce airport jirgin karfe sha ɗaya Ɗalha ya masu booking kadan ya rage su yi missing Flight ɗin su,karfe sha ɗaya dai dai jirgin su ya tashi,misalin sha karfe ɗaya na rana jirgin ya yi landing Aminu Kano international airport,sai da suka yi sallah suka ci abinci garin Kano misalin karfe biyu da wasu ƴan mintina suka kama hanyar Kaduna wani irin mahaukaci gudu Ɗalha ke yi a mota sosai cancel program ya bata masa rai,gani yake an ɓata masa lokaci a banza baban abinda yafi ƙona masa rai shine zaman rubuta speech da ya yi gwara ma Muhsin ya yi yawon sa iya son ransa,hakan yasa tafiyar awanni huɗu ya yi cikin awanni uku da ƴan mintina,suna daf da fita Zarai ya yi parking mota gefe hanya wajen masu siyar da kayan miya da kayan lambu nan ya jido masu da yawa,inda ya siyawa kowacce aka cika masa ledoji uku ɗaya Unaisa ɗaya Amirah ɗaya kuma zai ba Muhsin shima ya kai tsaraba,Muhsin na zaune cikin Ɗalha ya buɗe driver sit ya shiga ya zauna bayan ya zuba ledojin boot,a daidai wannan lokaci gidan Ɗalha na cike da matan gida sai harkokinsu suke hankali kwance Amirah da Aina'u na ɓangaren Amirah sai mamakin Unaisa suke musamman Amirah ita ko Unaisa hankali ta kwance tana zaune a parlour tare da matan gida ana hira da dariya tare da ɗaukan hutuna duk sun haɗa mata kuɗin taro kamar yadda suka saba kaɗan daga cikin su ne sun tafi gida amma da yawa suna nan baje parlourn Unaisa,ko kaɗan Unaisa bata yi tunanin Ɗalha zai dawo yau ba,dalili kuwa karfe takwas na safe ta kirasa sun gaisa bayan sun gama gaisawa ta ƙara tambayar yaushe zai dawo ya ce mata sai gobe Lahadi tun daga wannan lokacin basu sake yin waya ba,haka zalika Amirah tun safe da suka yi waya bai sake kiranta ba ita ma kuma bata kira sa ba,duk san da ya yi tafiya sau biyu suke waya safe da dare hakan yasa babu wacce ta sake kiransa karfe biyar da mintina arba'in Ɗalha ya shiga da motarsa harabar gidansa,tun karfe biyar da mintina ashirin suka shigo garin Kaduna sai da ya biya gidan Muhsin ya ajiye shi kafin ya nufo gida,tun kafin ya fita daga mota ba yake bin compound da ido ganin wasu motoci da bai san masu shi ba,nan ya fara tunanin ko wani abu ya same ɗaya daga cikin matansa ne ba a faɗa masa ba,saninsa kansa ne babu wacce ta sanar masa zata baƙi ko wani abu makamancin haka,fita ya yi daga mota yana ƙara bin motocin dake compound,kafin ya je ya buɗe boot ya fidda ledojin kayan miya da kayan lambu,su Sudais na wasa playing ground inda aka ƙiɓe masu ɗan wasa a compound sosai wasan da suke ya dauke masu hankali,Ɗalha ya mayar da dubansa gare su cikin ɗan ɗaga murya ya kira Sudais jin muryar Ɗalha ya sa duka yaran waigowa tare da kallon inda suka jiyu sautin muryar mahaifinsu,lokaci guda suka ruga juje suna faɗin ''Dady oyoyo Dady oyoyo'' Ɗalha ya buɗe hannayensa duka biyu tare da rungumar yaran cak ya dauki Fauziyya da ta fara kukar rigima su Afef sun riga ta rungumar Dady Ɗalha ya shiga yi mata wasa yana rarrashinta hannun ya kai ya goge hawaye dake fuskarta daga haka ya mayar da dubansa ga Sudais ya ce ''su wayi suka zo da motoci nan?"
Kallon motocin Sudais ya yi kafin ya dauki ledah ɗaya na kayan miya daga haka ya mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''Anty ce ta yi baƙi'' daga haka ya nufi hanyar main parlour cikin ɗan ɗaga murya Ɗalha ya ce ''ka kaiwa Mumyn ku ledar'' Sudais ya amsa da to Ɗalha na riƙe da Fauziyya ya dauki ɗaya ledar ya shiga main parlour tun daga main parlour yake jiyu muryuyin mata suna magana cikin ɗan daga murya da hayaniya daga site ɗin Unaisa muryuyin ke fitowa kai tsaye Ɗalha ya nufi ɓangaren Unaisa,zuciyarsa ce ta yi wani bugu ganin Hajiya Bilƙisu zaune tare da wasu matan sun yi rashe rashe hankalin su kwance sai hira suke suna ciye ciye abubuwa biyu suka haɗima Ɗalha ɓacin rai haɗe da tsantsan mamakin Unaisa,me haka ke nufi har yanzu Unaisa na tare da mutanen nan duk wani jan kunnen da ya mata shi da Mama ya tashi banza anya kuwa Unaisa mutum ce? ƙilah aljanah ya aura a sufar mutum,tsabar yadda ransa ya ɓaci har wani rawa jikinsa ke yi nan take idanunsa suka riƙida suka yi ja wasu jijiyuyi sun fitso a goshinsa tun aure sa da Unaisa bata taɓa ɓata masa rai irin yau ba a hankali ya sukuyu tare da dire Fauziyya da ledar kayan miya, yana bin su Hajiya Bilƙisu da ido da suke gaishi sa,ko kadan bai bi ta kan gaisuwar da suke masa ba ya shiga raba ido yana niman Unaisa,Unaisa na ɗaki tare da wata ƴar kungiyar tana ɗibar mata humrah cikin wata kulba ko kaɗan bata san abinda ke faruwa ba,bayan ta gama ɗibarwa matar turare suka fito daga ɗaki matar na gaba Unaisa na biye da ita,bayan fitowarsu Ɗalha ya sauke idanunsa fuskar Unaisa da take ta sakin murmushi,tana hira ƙasa ƙasa da matar da ta dibarwa turare muryar Hajiya Bilƙisu ce ya katse masu hira inda ta ce ''wai ina ki ka shiga ne tun ɗazu mijinki ya shigo yana niman ki?'' da fari Unaisa bata yarda da zance Hajiya Bilƙisu ba ita a tunanin ta Hajiya Bilƙisu ta faɗa hakan ne kawai dan zolaya hakan yasa Unaisa sakin murmushi tare da faɗin ''ba dai mijina ba mutumin da yake legos me zai kau sa Kaduna da yammar nan'' ta kare magana tare da zama saman kujera bayan ta zauna ne Zainab yayar Fadeelah ta ce ''ke da gaske fa mijin ki ya dawo ba kya gani ne?" wani irin yanayi Unaisa ta shiga da za a kira denial ma'ana ka san gaskiya abu amma zuciyarka ta karyata maka wanann abun ta nuna maka ba haka yake ba alhali haka abin yake tun kafin Unaisa ta kalle Ɗalha ta shiga wannan yanayi tabbas ta ji abinda Hajiya Bilƙisu da Zainab suka faɗa amma zuciyarta ta riƙa ƙaryata zance su,ji da ganinta da numfashinta ne suka tsaya cak na wasu ƴan sakanni daidai lokacin da ta sauke idanunta fuskar Ɗalha tabbas shi ɗin ne ba gizo idanunta ke mata ba,lokaci guda fetuses (jarirai) dake cikinta suka yi wani juyi da tun sanda ta dauki cikinsu bata taɓa ji sun yi irin wannan juyin ba,cike da kiɗima ta miƙe tsaye tana kallon fuskar Ɗalha wasu hawaye da bata shirya zuwan su ba ta ji saukar su fuskarta, da wani irin sauri ta shiga jijjiga masa kai cikin rawar murya tana faɗin ''no Please..no dan Allah ka yi hakuri ba yin kaina bane'' Unaisa bata taɓa tsintar kanta cikin yanayi da dake ciki a yanzu ba,wani abu ta ji me kama da ruwa ko fitsari ya jangaro mata ji ta yi jarirai dake cikin sun tukareta da wani irin sauri ta kai hannu ta riƙe mararta,a hankali Ɗalha ya tako daga inda yake tsaye yazo daidai inda take fuskarsa cike da tsantsan ɓacin rai iya zaman ta da shi bata taɓa ganinsa cikin wannan yanayi ba hakan yasa ta ƙara shiga ɗimuwa,ɗaya bayan ɗaya wasu daga cikin matan kungiyar matan gida suka fara fita daga parlourn Unaisa cike da hikima da dabara suke daukar jakukkuna da takalmarasu suna fita daga parlour cikin sanɗa,yayinda wasu daga sun gyara zama tare da baza idanuwansu da kunnuwa dan ji da kuma ganin yadda zata kaya tsakanin Unaisa da Ɗalha cikin wa'inda suka zauna harda Hajiya Bilƙisu da Hajiya Zulfa'u sai Zainab Hajiya Bilƙisu sai sakin murmushi take yayinda Hajiya Zulfa'u da Zainab tare da wasu matan tausayin Unaisa ya cika masu zuciya, Hajiya Zulfa'u ta buɗe baki da niyar bawa Ɗalha hakuri ta ji wata mammunar furuci ta fita daga bakin Ɗalha kalma ce da duk yadda mace ta kai ga karfin zuciya da karfin wanna kalmar tana gigita ta,kai ba iya mata ba har maza wannan furucin babu wani ɗan adam dake son jinta, in har ke musulma ce ko makiyarki aka furta wa wannan furucin sai kin kaɗu furuci be dake tayar da hankulan al'umma musamman ma'aurata,sai dai wani sa'ilin tana iya zama maslaha ga wasu ma'aurata ta kuma zame masu alkairi, parlourn ya dauki shiru baka jin motsin komai sai numfashin Unaisa da take sauke da ƙyar furucin da Ɗalha ya furta ne yasa Hajiya Zulfa'u tsayawa cak gaba ɗaya ta ƙasa ko da motsi ba iya Hajiya Zulfa'u har sauran mutanen parlour harda wa'inda ba wani son Unaisa suke ba duk saida sun girgiza jin furucin Ɗalha, amma banda Hajiya Bilƙisu wacce ta sake wata iriyar murmushi marar sauti daidai sanda Ɗalha ya ce ''Unaisa na sake ki'' ya furta hakan yana kallon fuskar Unaisa yana aika mata da wata iriyar kallo dake nuna tsantsan tsana
*SHUUKRAN*