Free chapter 路 Read without an account

Chapter 8

by Gidan Iko 路 GARWASHI

*Idan rayuwa tayi zafi sai bawa yaji tamkar ba zai kai labari ba, Idan al'amura suka yamutse sai bawa yaji tamkar shi kadai yake a damuwa, amma kuma lokaci yana zama alkalin yanke hukunci, wata rana kukan mai godiya ga Allah ya kan zama murmushi*

 
_*Akwai complete din littafin nan ga mai bukata akan 1k kacal,*_
Mai bukatar complete din littafin yayi magana akan wannan layin, ***


............Muryar Ammi najiyo akaina cikin wata murya da na Gama fahimtar cikin yanayi da alhini  tayi maganar

"Kiyi hakuri Zahra komai Kika ga ya faru ga bawa Rubutacce ne bawa Kuma Bai Isa ya sauya shi ba. In ba Allah ba wa ya Isa yayi hakan? Nasan kinajin zafina Akan wannan hanyar da na dauko wadda nake ganin itace mafita Domin ko ya zame min Dole na tashi na Kare mutuncin ku tunda Dani a cikin Wanda sukayi sanadin zuwan ku Duniya Ashe ko ya Zama Dole na SHIGA na fita don ganin ba kuyi kukan Rasa wani Abu ba . Ba Zan sake Barin Abdullahi ya komawa aikin Nan Mai wahala ba nice ya kamata nayi tukin mota Amma ba fita garuruwa ba iyakata Nan cikin gari kawai na Kuma yi Miki alkawarin Kare mutunci na da naku in Sha Allah duk Runtsi duk wuya inaji ajikina Zahra akwai lokacin da komai zai zamo tarihi kamar ba ayi ba don Haka Daina kuka kinji ? ADDU A nake Rokon kiyi min Allah ya tsare Ni sharrin karfe da Kuma sharrin mutum da aljan

"Ammi ba haushin ki nakeji ba illa tausayin ki Ammi ban taba ganin mace na tukin taxi ba shiyasa nake tausaya Miki Kar kema wahala tayi Miki yawa irin wadda ta riski Yaya Abdullahi..... 


"Babu komai Zahra Allah ya Rufa min Asiri don na lura Ubangiji ya saka min nasibi don kusan Dubu biyar na samu bayan na fidda Dubu biyun Mai da na siya kinga sai mu biya haj ladi kudin ta abinda na samo gobe Kuma sai mu siyo abinci mu aje in Sha Allah wahalar mu ma tazo karshe

Haka kuwa Ammi ta zage fita Aikin tuki Kuma tana samo kudi sosai inda na Gane shi Ubangiji da ka tashi da nufin kana son ya taimake ka to zai kuwa taimake ka sai dai Kuma Yaya Abdullahi dake kwance Bai San hakan ba Kuma ammi tace Kar mu sanar dashi don da yaji ba zai yarda ba Kuma gashi ba lafiya gareshi ba


Tuni aka biya haj ladi kudin hayarta muka zauna lafiya har ma Ammi ta samu kudin da ta siyawa Yaya Abdullahi magani ta Kuma siya Mana kayan abinci Wanda Rayuwa ta koya Mana cin dangogin su Wanda bamu waye su ba amma dole muka Saba tun muna ci cikin mu na baci muyi ta zawayi har muka Saba daga wannan sabon sauyin zuwa Wanda Muka sani muka Kuma Saba

Jikin Yaya Abdullahi yayi sauki har ya Soma tambayar kanshi yawan fitar da ammi takeyi Amma dai Bai tambaye ta ba Bai Kuma tambayi kowa ba inda a yau ya fito waje Yana zaune Yana kallon yadda mutane ke ta Kai kawon su kawai sai yaga Ammi ta shawo kwana cikin motar da aka mayar taxi Kuma ga Alama kamar garin take zaga wa

Ya taso ya karaso daidai da tafito Rike da ledar da ta siyo Dan Raba Mana dangin makulashe ya karbi ledar suka shigo ciki Yana mata sannu da Zuwa ita Kuma tana murnar ganin ya Soma fitowa waje Alamar sauki ya samu 

"Iska kake Sha ne Abdullahi? Masha Allah Allah ya Kara lafiya kaji ? Ya amsa da Ameen Ammi Amma ya Naga motar Nan anyi Mata fentin taxi? Ya fada Yana kallon Ammi wadda ta shiryawa tambayar tashi 
"Sai dai kuyi hakuri Abdullahi Amma ai ya Zama Dole na Mike tsaye don na ga Baku yi kukan Rashi ba in kun Rasa Uba jajirtacce to tabbas Baku Rasa jajirtacciyar mahaifiya ba don Haka Kai ma inaga makaranta ya kamata ka koma don yadda na samu sa ar Nan abubuwa suna tafiyar min yadda ya Dace kaima na yanke shawarar ka koma karatu kawai.......


Ya Soma kada kanshi Alamar A a ba zai iya Barin ta da wannan dawainiyar ba. ......

"Ammi nine fa Ubangiji ya baku don kuyi alfahari da haihuwa ta . Nine Wanda Ubangiji ya kawo muku don na dauki takalifin ku keda Daddyn mu da Kuma kanne na to tunda Ubangiji Bai yarda Daddyn yaga Haka ba sai ke don me Zan Bari kiyi ta wahala Haka ? Don Haka don Allah don Annabi kiyi hakuri da fitar Nan nine Zan fita na Nemo muku duk abinda kuke so tunda na samu lafiya dama sai da wani ya fada min ulcer ce ke neman kamani da na fada mishi abinda nakeji shi Kuma yace akwai maganin Hausa da zai bani Zan Rabu da ita Yana a funtua ne in naje Zan neme shi ya bani shikenan Ammi don Allah don Annabi kar kice A a idan Kika ce a a kamar Baki yarda Zan zamo Miko abin alfahari ba.... 


Ammi bata yarda ba daga farko don cewa tayi bashi da lafiya ya Bari ya Kara samun sauki tukuna shi Kuma ya CE baya son yaga tana fitan ne don Haka ta hakura da fita shi Kuma ya zauna zaman shanye maganin shi kafin ya koma bakin aiki

Sati guda Daya Tak ya koma aiki inda Ni da kaina naji gaskiya bana son aikin Nan na Yaya Abdullahi hankali na ya Fi kwanciya Akan na ammi ban San Dalili ba ko da Yake dalilin ba zai wuce na kaddara ba wadda Ubangiji ke darsawa wasu Jin wani Abu da zasu yarda dashi ko Akasin hakan Wanda matukar suka bibiyi abin Nan da Basu yarda dashi ba sannu a hankali sai su Tara's da kaddara acikin shi kaddara kuma me ciwo a zuciya

Aikin Yaya Abdullahi ya Dore don yanzu har wata Yar kiba ya somayi bayan ya karbo maganin ulcer ya Kuma yi amfani dashi har ya warke daga cutar ulcer harkokin shi suka tafi daidai komai namu ya tafi daidai kamar dai irin rayuwar da ta samemu a tsakar Rana guda daya tak

A dangin mahaifina kuwa shiru babu Wanda ya neme mu bare yaji ya muke Rayuwa ya muka Fadi ya muka tashi ko da Yake naso na yaudari kaina idan nace so nake Wai wani yazo da sunan duba mu ai ko a mafarki naga hakan Zan karyata suna wurin su muna namu sai ma Nana ce ke fada min wai Yan uwan Daddy sunzo Kan maganar gidan mu har ma sun saida shi Wanda ya siye shi ma yace Rushe shi zaiyi ya sake sabon Gini, naji wani irin tashin hankali ya ziyarce ni jin wai su kawu Gide sun siyar da gidan mu, lallai kaddara guda ce amma ta kasu fiye da milyon. Sai kawai naji haka Allah ya kaddara mana, mutuwar Daddy ce tonon asirin mu. Mutywar Daddy ce zata rushe mana komai har mu kasance cikin garwashi

Kasancewar makarantar mu daya da nana ta gidan mama kusan ma itace kawata ta kusa kusa don a tare ake kaimu makaranta a wani lokaci can da ya Jima da shafewar tarihin shi 
Wannan magana ta Nana ta kadani ba kadan ba don da nadawo gida ma sai da na sanarwa ammi abinda nanar ta fada min

"To ya za ayi Zahra in ma Basu saida shi yanzu ba zasu saida shi Nan gaba  Allah ya Baku mafiyin abinda kuka Rasa Ina Rokon Allah yayi muku gata fiye da Wanda mahaifin ku yayi nufin yi muku na amsa da Ameen ya Rabbil Alamin

Da na kebe ma sai naji Ina son yin dogon nazari Akan shin Wai mu kadai ne muka kuskuro shigowa Duniya da Rashin Dacewa Akan Yan uwan Daddy ko ko Ammi da Ubangiji yayiwa nasibin shigowa hasken musulunci? Yan uwa da dangi dai ta bangare biyu ake alfaharin samun su wato Uwa da Uba shi Daddy nashi Basu da kirki suna kin Ammi ne don kawai ta kasance ahalul kitabi suke kinta to su Kuma dangin Ammi fa? Su Kuma meye matsalar su damu da suka yada mu basa  son mu Basu rabar mu ? Da na nutsa sai Nagano yadda Ammi ta sanar Dani shigarta cikin musulunci ya bar baya da kura Wanda har nemanta suka Rakayi don su kasheta Allah ya kareta Daddy ya dauke ta suka bar kasar Baki Daya shine fa ta tsira daga harin da ake kawo Mata Amma Kuma sai Naga indai Haka akayi Rabuwar to Babu dalilin da zasu neme mu don a fahimta ta ma yadda su kawu gide suka tsani Ammi saboda ta fito daga wata kabila da yare akasin nasu suke kinta to su Yan uwan Ammi na tabbatar da sunfi su kawu gide kinmu tunda su neman Ammi suke ma su kasheta Akasin su kawu gide da basu nemi kisan ba don Haka kuwa Ashe yaudarar Kaine ince zasu tallafe mu don Haka sai Naga Bari na koma baya na hasko muku madubin kaddarar da ta haske Akan Ammi da Daddyn mu Wanda haduwar su CE sanadin kaddarar mu har Kuma zuwa yau din Nan da muke tsaka da garari a cikin Duniya don Haka ku biyo Ni kuji haduwar mahaifina da mahaifiya ta da irin kaddarar da ta taka Rawar da har suka Zo Kan gabar Aure da haihuwar mu muka Kuma shigo Duniya cikin wani mashahurin gata Amma dare Daya Ubangiji ya sauya komai duk dai acikin waccan kaddarar da take Rubutacciya.

Kamar yadda Ammi ta sanar Dani sunanta Justina............


Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin daban yake da sauran 


Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI馃拑馃徔


_Masu Neman labarin daga farko su duba cikin channel din mu zasu samu farkon labarin_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol