Free chapter 路 Read without an account
Chapter 9
*Mai arziiki fa ko a garin kwara sai ya saida ruwa ya, haka Idan Ubangiji ya nufi bawa da rahama sai ya haska masa tunanin da da hasken imani ya hau kan turbar gaskiya, mai karatu wane guzuri kayiwa tafiyar da take gaban ka?*
*Akwai documents na littafin nan GARWASHI akan 1k ga mai bukata sai yayi magana akan wannan layin ****
_TUSHEN LABARIN_
............Kamar yadda Ammi ta sanar dani labarin ta shine nima Zarah zan sanar daku a yanzu kuji yadda kaddara tayi aikin ta akan Ammi da mahaifina, dama mu kanmu, kamar yadda ta ta sanar dani Justina shine asalin sunana ta, Yar gidan wani mashahurin me kudi mai suna ma'azi Nkem . Ma azi Nkem hamshakin Mai kudi ne Wanda ya amsa sunan sa duk fadin nigeria sunan sa ya tumbatsa ya kuma zagaye sako da linguna har masu kudi sun jera shi layin masu kudin da suka shahara, ma'azi nkem ya Tara dukiya Mai dumbun yawa saboda shaharar shi ta fuskar kasuwanci, komai saidawa yake kuwa, in nace komai to Ina nufin komai Domin ko Maazi Nkem har gidan giya gareshi bama guda Daya ba don Haka komai da Ruwan ka ne don mu a Al adar mu Dole ne ma mutum yayi kudi na kecw Raini don Babu abin kunya agaremu irin mutum ya Rayu cikin talauci Kuma ya mutu cikin talauci har Diyan jikoki sai an gorantawa ace Basu da k'ashin arziki don haka NE maza ke zagewa su nemi kudi ba sai lallai ta hanyar Sana a ba ta kowace fuska dai kayi kudi don ka kaucewa talauci Akasin wasu dake fita bakin Rai bakin fama su sata ko suyi kisa su kwashe koma su bi Dare su fasa gidaje ko shaguna Akasin Maazi Nkem Wanda shi Sana a ce ta Tara mishi kudin shi kowace iri ce kuwa zaiyi ya samu kudi inda ya Auro mamata madam Amaka ita Kuma ma aikaciyar Yar Boko ce don har Aiki ta Fara Amma ganin Maazi Nkem da kudin shi shi ya hanata Aikin Kuma ta yarda ta hanu.
Rayuwar gidan mu abin burgewa ce don mu uku iyayen mu suka haifa maza biyu mace Daya Kuma dukkan mazan biyu yayu nane nice karama Kuma mace Daya don Haka fasalta yadda Zan kasance a tsakanin iyayena
Idan nace sunaji da Ni naso Bata yawun bakina ne kawai ba garesu iyayena ba Baga Yan Uwa na ba guda biyu Sony da Emmanuel wadan da suke tsare da wasu bangarori na dukiyar Maazi Nkem
Wani Abu Kuma da ke burge mutane akaina shine Ni din tamkar ba jikin Amaka da Maazi Nkem na fito ba don ko kusa banyo kalar kowa ba tamkar ma ba Yar Nigeria ba nafi Kama da black American sai dai Ni farace tas irin farin Maazi Nkem Amma bayan wannan komai nawa daban ne kuma na musamman ba irin na Yan Matan garin mu ba. Manyan idanu da dogon hanci me idanu irin na yankan kifi lumsassu masu gashin girar ido gazar-gazar, gashin kaina kuwa har kafada ta, don duk asavar ni da amaka muke zuwa saloon shagon kawar ta cinyare, bakina Dan karami Wanda a gefe Kuma Ramin kyau ne (dumple ) da nayi murmushi sai ya loba
Kirjina daidai Ni da shafaffen ciki da budadden kuturi daga kasa ta ko Ina nayi daban da Matan yankin mu don za a Tara dari sai sa a mukai uku hatta d yatsun hannuna daban suke Kuma abin kallo ne wurin mutane mussamman maza sai Kuma akayi sa a bana son kallo da na kula ana kallo na yanzu ne zan fashe da kuka Kar ma ace tare nake da Amaka ko Maazi Nkem Wanda Yake alfaharin sakani gaba nayi mishi Rakiya duk inda zaije kuwa Akasin yasa ka babban Dan shi gaba suje wato Sony sai nice yake sakawa gaba muje
Duk wani Abu da Zan nema a gidan mu Zan sameshi wurin Maazi Nkem ko Amaka ko su Sony da Emmanuel kowa Yana min abinda nake so saboda gata, hatta makaranta ta kudi aka sakamu a komai sai an kure adaka ake Mana, sutura da abinci duk na gaske ake mana, Sony da Emanuel kuwa zo kaga motocin da suke murzawa irin na kece raini...
Sai dai Kuma a gefe guda iyayena sun tsani nayi mu Amala da bahaushen musulmi, don sun kula ina son hausawa, suna tsanar hausawa fiye da yadda suke tsanar mutywar su, Kai ba Ni kadai ba ko su Sony da Emanuel basu isa suyi aboki Bahaushe ba, Idan aka gan su da aboki bahaushe yanzu zakaji bakin Amaka wurin masifa tamkar zata fasa dodon kunne ,don tafi Ma'azi Nkem kin hausawa da ma addinin da sukeyi wato musulunci don Amaka ko siyayya batayi wurin musulmi bisa Dole su Sony suka hakura da abokai musulmi sukeyi da Yan jinsin su Wanda yaren da addinin Yake Daya
Sai dai kuma ni a wurina abin ba Haka yake ba don na Fi son nayi kawance da hausawa Kuma Ina masifar son mu zauna fira da su muna Labari don nagane su din suna da wayewa sosai kuma basa nuna min kyama Akasin wasun mu dake nuna kyama ga hausawa irin dai Amaka
Ni Kuma sai ya zamo kawaye na kaf musulmin hausawa ne irin Wanda amaka bata kaunar gani na dasu wai kar su yaudare ni su tallata min addinin su, kawaye na musulmai ina son su Ina Kuma Jin dadin taraiyar mu da su don na kula suna da mu'amula ta gaskiya, babu kyashi bare mugunta a tare dasu sai nake Jin dadin kasancewa dasu har bana son ayi hutu don kar mu Rabu harma nakan ziyarci wasun su a gidajen su Amma fa Ni ban taba gayyatar wata zuwa gidan mu ba don nasan yadda nake zuwa gidajen su iyayen su na faram faram Dani su idan sukazo gidan mu kunya kawai zasu Sha don nasan ba karamin aikin Amaka bane ta Rako su da bulala
Na kasance me lalurar aljanu Wanda ban mance mafarin cutar tawa ba wata kirsimeti ce munje gida can jihar imo kasancewar su Amaka duk Yan jihar imo ne ana ta bukukuwan crismeti muma muka shiga yawon bikin kirismetin har muka nutsa cikin jeji Ni da kawaye na su cika da Rebecca, kasance wa ta me son korayen tsiro da furannci na shiga keta daji da ganyaye ina Ciro duk kalar da ta burge ni ta bani sha'awa, Ina ta tsinko duk kalar koren tsiron da yayi min sai Kuma na hango wani wuri fetal babu komai a wurin tamkar an share ko haki guda Daya Babu abin ya bani mamaki ganin daji ne babu kowa Amma Wai wurin kamar an share tas tas sai kawai naje na zauna a wurin yayin da su coma suke can saman bishiyar kwakwa zasu Ciro Mana Ni Kuma Ina Zama a wurin Nan sai naji wani Abu Yana hau min Kai tamkar Yana tilasta Ni Rufe idanu inda Kuma naji coma na kwala min Kira Wai na tashi daga inda na zauna baban ta yace Kar su sake su taka ko da kafa ne bare su zauna .
Sama sama najiyo ta ban Kara sanin abinda ke faruwa Dani ba sai dai farkowa nayi na ganni Akanyar Amaka suna ta Rusa ihu Nima sai na Soma Rusa ihu inda aka kwasheni zuwa gidan Mai magani akayi ta banka min sauyoyi magani da hayaki
Haka muka dawo gida ba tare da tunanin cewa akwai wats sauran matsala Akan wannan ciwon ba don magani daban akayi ciwo daban. Sai ya zamo ba a Rufe kwanan wata ba tare da ciwon Nan ya tashi ba Kuma Haka akayi tayin magani daban ciwo daban har waje dai an kaini Amma babu wani sauyi sai bankar maganin bature nakeyi da neman sauki Akan ciwon tashin aljanu
Wata Rana a makaranta kawata sumayya Ahmed yabo ke fada min da ciwon nawa ya tashi a makaranta cewa ciwona fa ba na Asibiti bane warakar shi tana cikin Alkur ani don dai bamu sani bane
Sai naji kwarai na gamsu da maganar sumayya Ahmed don inda ciwon na Asibiti ne ai har waje an fidda Ni Amma dai ana Nan jiya iyau
Da na komo gida nake fadawa Amaka yadda mukayi da sumayya yabo cewa ciwona fa ba na Asibiti bane ...sai tayi maza ta tareni a fusace musamman da taji na baci sumayya yabo, a shake takea fadin....
"To na Ina ne in ba hospital ba? Na fada Mata yadda sumayya Ahmed ta fada min wai warkewar tana cikin littafin su mai tsarki wanda suke cewa Alkur ani, ai kuwa ban Rufe bakina ba Amaka ta gaura min wani matsiyacin Mari gigitarwa tana Sababi, don Idan akwai abinda Amaka ta tsana a duniya to musulmai ne, yadda ta tsani musulmi bata tsani mutywar ta haka ba, Allah yayi mata tsanar musulmi dama addinin su a cewar ta mayaudara ne da suke tallata maka addinin su don ka shigo su yaudare ka.........
_YANZU NE ZAMU FARA LABARIN GADAN GADAN_
_Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan labarin na GARWASHI daban ne da sauran rubutun gidan iko_
*Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunan ke cewa saduwar ALHERI*馃拑馃徔
_Masu Neman labarin daga farko su duba cikin channel din mu zasu samu farkon labarin_