Free chapter · Read without an account
Chapter 2
*_The Amazing Pen_ ✍️....*
*Bani da Madogara*
(Sai Allah...)
002
Daram!!! Dam! Dadammmmmm! Haka ƙirjin Hujayrah ya buga,fashewa tayi da matsanancin kuka mai ratsa k'ashi da b'argon duk wani mai sauraronta, cikin kuka ta fara magana
"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Na shiga uku na lalace ni Hujayrah yanzu a rasa wanda za a had'ani dashi sai da wanda ya haife ni kuma mugu"
Daka mata wata uwar tsawa Alhaji Zakari yayi domin yaga alama tana da niyyar b'ata masa plans,cikin kakkausar muryar ya fara magana
"Me kike nufi da tsoho ne, waya ce miki tsoho bai auran galleliyar budurwa sabuwa fil a kwali,mun ce ki kawo wanda kike so ki aura kin ce mana babu, to ya kike so mu yi, zuba miki idanu kike so mu yi har ki tsufan mana a gida tunda baki da niyyar fid da miji kiyi aure ko kuwa, duk sa'anninki sunyi aure har da yaransu, k'annanki ma haka yanzu suna d'akin mazajensu, a garin nan ban tunanin akwai wacca take da shekaru irin naki bata yi aure ba"
"Babu gaskiya" cewar Baba Zubairu wanda sai yanzu ya tofa albarkacin bakinsa
Kakulle ta ce
"D'an Inna tunda Hujayrah ta nuna b'ata son auran nan, a k'yaleta kawai,shi aure lokaci ne inda rai da rabo ita ma za ta yi auran kamar sauran y'an uwanta"
"Haba Inna so kike ta dawwama a gida duk sauran 'yan'uwanta sun yi aure sannan mutanan gari suyi ta gulmarmu , a gaskiya Ina bayan Zakari d'ari bisa d'ari,sai naga a zamanin da can aure ake ma mace ba tare da tasan mijinta ba,kuma ta zauna dashi lafiya har Allah ya basu haihuwa" cewar Attine k'anwansu wacca take bi ma Baba Musa
Abbu dai shiru yayi domin an zo gab'ar da bai san abin da zai iya furtawa ba saboda ba gani yake ba balle ya tantance mai kyau ko marar kyau, ganin Alhaji Zakari shi ne babba a d'akinsu sannan shi ya kawo shawarar, hakan yasa bazai yi jayayya dashi a wannan al'amarin ba,don kuwa ya yarda dashi a matsayinsa na d'an uwansa na jini uwa d'aya uba d'aya yasan bazai tab'a zab'ar wa y'arsa mutumin banza ba ko kuma tumin dare .Mammi abin duniya ya gama dame mata, ta ma rasa abin cewa sai dai kallon yadda Hujayrah take ta faman dirzar kuka mai sauti, gwanin ban tausayi.
Gudidi ce ta k'ara goyan bayan kawai a yi ma Hujayrah aure a huta,nan kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa har da matansu Zubairu da Alhaji Zakari wanda kusan kowa ya aminta da shawarar Alhaji Zakari,Fatsima matar Musa da Kakulle ne suka ga rashin dacewar hakan, hak'ik'a an kai ruwa rana tsakanin Kakulle da yaranta wanda a k'arshe suka yi galaba a kanta, ranta bai so ba amma haka nan ta hak'ura.Duk wannan kai ruwa ranar da aka yi Hujayrah na duk'e tana kuka, a zuciyarta tana cewa 'Saboda kunga Abbuna baya gani, bai iya tantance aya da tsakuwa,bazai iya gane mai kyau ko kuma akasinsa ba shi ne kuke son saka rayuwata a halaka,babu wanda a cikinsu zai yarda y'arshi ta auri Alhaji Sambo Dala,mutumin da duk lokacin da na had'u dashi ya zo wurin Baba Zakari sai k'irjina yayi mugun bugawa,wallahi komai za a min bazan tab'a zaman aure da Alhaji Sambo Dala ba'
haka tayi ta sak'e-sak'e a zuciyarta, su kuma sunata shawarar yadda auran zai kasance, Mammi dai mik'ewa tayi tabar d'akin ba tare da ta kalli kowa ba,Hannatu da Murja matar Zubairu suka had'a ido sai suka sakar ma junansu wani shegen murmushi, Fatsima ta kula da abinda suke, murmushi kawai tayi a zuciyarta tana cewa "A juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, Allah baya bacci'
Haka aka tashi taro tare da tsayar da magana akan anba Alhaji Sambo Dala auran Hujayrah,haka kowa ya watse, Hujayrah ta mik'e tare da taya Abbunta mik'ewa, sandar da take taimaka masa wurin tafiya Hujayrah ta rik'e ita tana gaba shi kuma yana biye da ita hannunsa rik'e sandar har suka bar sashen Alhaji Zakari.
Bayan kowa ya watse Hannatu ta rangad'a gud'a har da mik'ewa tana taka rawa saboda farin ciki,cike da murna Hannatu ta dubi mijinta da ta ce
"Aaayyyiriri nanaye! Wayyo dad'i kasheni! A gaskiya mijina wallahi yau ka bala'in birgeni da ka kafe ka tirje ka murd'e sannan ka dage akan sai ta auri Alhaji Sambo Dala,wuhuhu dad'i ni Hannatu kamar an biyamin aikin Hajji haka nake ji, shegiya kya k'arata can da bak'in halinki a gidan Alhaji Sambo Dala"
Dariya Alhaji Zakari yayi har randameman tumbinsa na sama da k'asa saboda tsabar girmansa, shima farin cikin yake sosai da plans d'inshi suka tafi sumul k'alau ba tare da an samu wata tangard'a ba,gyara babbar rigarsa yayi sannan ya ce
"Bar tsinanna hmmm za ta gane kuranta,na ji dad'i da Musa baya garin nan aka yi taron,da yana garin nan shegen zai iya kafewa akan bazata auri Alhaji Sambo Dala ba kinsa Hujayrah shi da gado a matsifa da tirjiya y'ar k'wal-uba kawai, shikenan da ya rusamin plans d'ina wanda nayi shekaru Ina wahalar tsarawa, gashi idan Hujayrah bata auri Alhaji Sambo Dala ba kashina ya gama bushewa a wannan k'auyan"
"Ai gwanda da baya nan a kayi taron,yanzu dai kar ku b'ata lokaci wurin saka rana mai tsayi har Musa ya dawo domin nasan munafukar matarsa mai nanannan hanci za ta iya gutsura masa zancen,don haka kawai idan da hali cikin sati biyu a yi auran ya d'auki shegiya su bar mana gariiii hohoho! !!"
"Shawara mai kyau haka za a yi kuwa, kiransa yau d'in nan zanyi na labarta masa komai,kinga tun yau sai mu fara shiri"
"Da kyau angon Hannatu ita kad'ai tilo har a aljanna, Ina tare da kai ruwan zumana,Sadauki mai mulkin zuciyar Hannatu,gaba dai gaba dai jarumina" (ki ce dai kuna tare har a jahannama tsundum dum, ko ba haka bane my Esteem fans😂😂😂)
Chakwaikwai kenan in ji Alhaji Zakari ,domin yana Jin dad'in yadda take wasashi a duk lokacin da yayi abinda ya faranta mata rai,shiyasa yake ji bazai iya k'aro mata kishiya ba sai dai kishiyar waje domin Alhaji Zakari shahararran mai neman mata ne ciki da wajan k'auyan wanda babu wanda yasan da wannan d'abi'ar tasa,a matuk'ar b'oye yake yin ta sannan da taka-tsantsan .Haka suka ci gaba da hirarsu suna raha da farin ciki hankalinsu kawance.
*Wace ce Hujayrah da danginta*
Hujayrah y'a ce ta biyu ga Abdullahi Kamalu wanda ake kiransa da Audu ,Babban d'an Audu mai suna Mansur ya rasu a sanadiyar tafiya dashi almajiranci a birni,su uku ne aka ba wani malami a nan k'auyansu wanda yake zuwa ci-rani birni da almajiransa har da matansa sai lokacin damina yake dawowa. koda suka dawo sai malamin yaba Audu da matarsa hak'uri akan Allah yayi ma Mansur cikawa wata uku da suka wuce bayan yayi rashin lafiya na kwana biyu, Zaytuna matar Abdullahi tayi kuka sosai kamar ranta zai fita saboda tun farko bata amince da tafiyar Mansur almajiranci ba,haka Audu yayi ta lallashinta har ta hak'uri, su Hannatu da Murja sai habaici suke sakar ma Zaytuna suna Jin dad'i d'an da aka k'wallafa ma rai ya mutu.Sannan tun daga kan Mansur aka daina kai yaran gidan almajiranci.
Sai da Zaytuna tayi shekara takwas sannan ta haifi d'iyarta mai suna Hujayrah, haihuwar Hujayrah ta karad'e ko'ina na k'auyen saboda ba a tab'a haihuwar d'a mai koren idanu sai akan Hujayrah, tun kafuwar k'auyen da tarihi ba a tab'a samun wani da kalar k'wayar ido mai launi daban sai akan Hujayrah,haka Hujayrah ta taso da shegen rashin ji, surutu, neman fad'a, tun tana k'arama y'an gidan suka tsani Hujayrah musamman Hannatu da Murja, ita Fatsima matar Musa ba ruwanta da shiga sabgar su Hannatu, hasalima jawo Hujayrah take a jiki shiyasa koda Hujayrah ta girma tana k'aunarta da yaranta.
*Su waye ahalin Hujayrah*
Malam Kamalu Adamu Giwa shi ne cikakkyan sunan kakansu Hujayrah,d'an Zaria ne amma ya dawo da matansa kwanar faru k'wai da zama kasancewarsa manomi ne sosai shiyasa da dawo k'auyan da matansa saboda Allah ya albarkacin k'auyen da k'asa mai kyau kuma ta noma ga yalwataccen wuraran noma a garin sosai,matan Kamalu biyu ne ;Hindatu kakarsu Hujayrah sai Tsahara wacca Allah yayi mata rasuwa a wurin haihuwa shi ma yaron ya bita kasancewar tana amarya suka dawo k'auyan da zama . Hindatu ta haifi yara bakwai,Babban d'anta Zakariyya wanda take kiransa da D'an inna kasancewarsa d'an farko, sai Zubairu,sa'annan Abdullahi mahaifin Hujayrah wanda suke kiransa da Audu, sai Musa, sai da Kakulle ta jera maza hud'u sannan ta haifi yara mata,Hasiya wacca ake kiranta da Attine ita ce d'iyarta mace ta farko, sai Saratu wacca suke kiranta da Gudidi, Samira wacca suke kiranta da Larai ta rasu tun tana y'ar shekara goma a duniya.
Alhaji Zakari yaransa biyar ne rayayyu;Jamilu,Baraka,Harira, Maryam,sai autansa Faisal ban cin wa'inda suka rasu tun suna tsumman goyo,ya aurar da yaransa mata duka sai dai Jamilu wanda yake wurin mahaifiyar Hannatu sannan autansa Faisal.Zubairu yana da yara hud'u ;Hadiza wacca ta kasance y'arsa ta farko sai Jibrilu,Balki da autarsa Aliya,shima kamar Alhaji Zakari duk ya aurar da yaransa har da namijin.Na ukunsu Abdullahi wanda suke kiransa da Audu mahaifin Hujayrah yana da yara uku;Hujayrah mai bi mata Salim sai autansa Haroon, d'ansa d'aya ne ya rasu mai suna Mansur, Audu bai tab'a aurarwa ba.Na hud'unsu Musa yana da yara biyar;Hajara, Nazira, Maimuna, Halima sai autansa Kamalu wanda ya gaji sunan mahaifinsu, shima kamar su Zubairu ya aurar da yaransa mata, Kamalu kad'ai ne ya rage.Mai bi ma Musa Attine wacca take auran Tukur wanda aka fi saninsa da D'an Lami, sun haifi yara shida dashi sannan dukkaninsu sunyi aure har da mazan kasancewar Attine ta riga mazan gidan aure, sai autarsa baki d'aya Gudidi wacca ta auri Shamsuddini amma an fi kiransa da D'an Innayi sun haifi yara biyar dashi matan ne suka yi aure banda mazan.
Su Alhaji Zakari da y'an uwansa maza suna zaune dukkaninsu a gida d'aya kuma koda Alhaji Zakari yayi kud'i lokaci guda bai bar gidan ba sai dai ya gyara gidan kamar a birni, ko'ina ya gyara banda sashen mahaifan Hujayrah da sashen Baba Musa, da yake shima Baba Musa babu laifi yana samu daidai gwargwado, shima sai ya gyara sashensa. B'angaren mahaifan Hujayrah kad'ai ne babu gyara a duk fad'in gidan. Kasancewar Abbun Hujayrah ya makance sai ya zamana baya iya fita neman na abinci, Baba Musa ne yake taimaka musu da na abinci da y'an wasu abubuwan da ba a rasa ba.
*Cikin Labari*
Tunda Hujayrah ta taimaka ma Abbu zuwa sashensa ta dawo d'akin Kakulle, saman gado mai rumfa da haye tana rusa uban kuka babu k'akk'autawa , tabbas yau ta tabbatar da y'an uwan mahaifinta basa k'aunarsu idan aka cire Baba Musa wanda tasan da yana nan idan tayi rantsuwa ko kaffara baza tayi ba, zai hana faruwan auran nan domin shi mai k'aunar farin cikinsu ne sannan mai hana zubar hawayensu ne,amma kashhh!!! Baya kusa sannan ba lokacin nan yake dawowa k'auyen ba duk da lokacin damina ne,da yake hayar mutane yake suna noma masa gonakinsa.Tana a wannan yanayin Kakulle ta shiga d'akin bayan ta kewaya bayi, ajiye butar tayi a inda suke ajiye butocinsu sannan ta k'araso wurin gado mai rumfa, cike da damuwa Kakulle ta kira sunanta amma shiru babu amsa sai dai kuka, sake kiran sunanta tayi sannan ta ci gaba da magana ba tare da jira amsar Hujayrah ba,cike da dumbin damuwa wanda ya nuna a fuskarta k'arara ta ce
"Hujayrah nasan basu miki adalci ba a matsayinsu na y'an uwan mahaifinki uwa d'aya uba d'aya, tabbas da Musa na garin nan da zai yi k'ok'arin hana auran nan sai dai nesa bata maganin kusa, babu yadda muka iya Hujayrah kinga yadda nayi iya k'ok'arina ni da Fatsima amma haka suka rinjayemu kasancewar sun fi mu yawa da hujjoji masu k'arfi, ki dogara ga Allah domin babu wata madogara sai tashi, ki yarda da k'addara la'alla ita ce kawai hanyar da zata sada ki da farin cikinki"
Duka nasihar da Kakulle take mata suna shiga cikin kunnanta sai dai bakinta a yanzu yayi nauyin da bazai iya furta koda harafin A ne balle magana mai tsawo.Kakulle na cikin mata nasiha sai Fatsima tayi sallama tare da shigowa har inda Kakulle take da y'ar Airtel d'inta k'arama a hannu cike da damuwa take cewa
"Inna hankalina yayi mugun tashi gashi Ina son kiran Babansu Nazira amma tak'i shiga dana danna kira sai shegiya matar nan tashe min *Siwici of* tunda muka fito nake ta faman kiransa"
"To Allah yasa dai lafiya,nima gani nan Ina ta faman lallashinta "
"Allah sarki Hujayrah kiyi hak'uri dukkan tsanani yana tare da sauk'i,ki sani mai hak'uri kad'ai ne a duniya yake iya dafa dutse har yasha romansa, tabbas ba a miki adalci ba amma Allah na tare dake Hujayrah in shaa Allah hanyar daukakarki ci ta zo,ki d'auka wannan ita ce k'addarki wanda Allah ya rubuta miki a cikin littafinki na rayuwa wanda babu makawa sai ta sameki,kodan cin amanar zumincin da suka yi Allah ba zai tab'a barinki ki tab'e ba"
Kamar ana k'arama Hujayrah kukan , sosai take kuka har da shasshek'a, duka jijiyoyin goshinta sun yi rad'a-rad'a, idanunta sun k'ara girma saboda kukan da take. Kuka mai sauti take sosai hannayanta na k'ara jaye zanin gadon.Fatsima ce ta dubi Kakulle sannan ta ce
"Kinsan Allah Inna ban yarda da auran nan ba, anya babu wata a k'asa kuwa"
Juyowa Kakulle tayi sannan ta ce
"Me kike fahimta a wannan zaman ta aka yi Fatsima "
Samun wuri tayi a bakin d'an k'aramin gadon ta zauna sannan ta ce
"Inna Idan na fahimta akwai wata a k'asa domin yadda naga su Murja da Hannatu sun kalli junansu tare da sakin murmushi jinin jikina ya tsinke da wannan auran, Kinsan tun fil-azal ba k'aunar Hujayrah suke da Zaytuna ba,kansu suka sani ya yaransu"
Sauke nauyayyar ajiyar zuciya Kakulle tayi sannan ta ce
"Suyi yadda suke so lokacinsu ne,wataran su zasu koma abin tausayi, su bar ganin sun aurar da yaransu a tunaninsu basu da wata matsala, Ubangiji yakan iya jarabtar bayinsa a yanayin da ya so kuma a lokacin da ya so,hmmm muje dai zuwa kowa zai kwashi kashinsa a hannu"
"Allah dai ya kyauta, wai nikam tunda muka baro sashensu Hannatu banga Zaytuna ba"
Sai yanzu Kakulle ta Samu wuri kusa da Fatsima ta zauna tare da cewa
"Kinsanta da kawaici k'ila taje gidansu kakar Hujayrah ne"
"Eh nima haka nake tunani, Allah sarki Baban Salim ya ban tausayi, kasancewar baya iya tantance mai kyau da marar kyau shiyasa yaba Zakari wuk'a da nama ganin d'an uwansa ne bazai yi sanadiyar cutar da jininsa ba"
Tab'e baki Kakulle tayi tana cewa
"Ai k'yale munafiki ni ban yarda da D'an Inna ba, nasansa da shegen don abin duniya da son kansa tun yana k'arami,Allah yasa babu wata muna-muna a zancensa "
"Ameen dai"
Haka suka ci gaba da jajanta alamarin ita kuma Hujayrah tana kuka.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎
Mammi tunda tabar d'akin ta wuce sashensu ta d'auko jakarta ta fita zuwa gidan mahaifiyarta, a hanya sai sak'a da warwara take,tana ayyana abubuwa a cikin zuciyarta, har ta iso gidan wanda babu wani nisa tsakanin gidanta da na mahaifiyarta,da sallama ta shiga gidan kasancewar mahaifiyarta kad'ai ce a gidan sai jikarta ta wurin k'anwar Mammin Hujayrah suke zaune gidan, su biyu ne a wurin mahaifiyarsu daga Mammin Hujayrah sai k'anwarta wacca take aure a marabba, yaranta bakwai ne biyar mata biyu maza,ta aurar da matanta biyu saura uku da mazan,ganin mahaifiyarsu bata da wanda zai d'aibe mata kewa yasa aka bata rik'on Zainab wacca suke kiranta da Abu.
Har cikin d'akin ta shiga da sallama ganin ba kowa waje, mahaifiyarta ta zauna tana sak'a tabarmar kaba wacca ita ce sana'arta tun yarinta har tsufanta.Amsa mata sallamar tayi tana dubanta, zama Mammi tayi kusa da mahaifiyarta tana gaisheta, cike da kulawa mahaifiyar take amsa mata tana k'ara dubanta dakyau ganin damuwa kwance a fuskarta, mahaifiyarta tasan rayuwar da take a gidan da wahalhalun da take sha daban-daban,shiru d'akin yayi ganin idan ba tambaryata meke damunta tayi ba, to ko za su shekara suna a haka baza ta ce da ita komai ba saboda miskila ce ta k'arshe, magana bata dameta ba sai an takura mata, gata da hak'uri da juriya samun mai hak'urinta sai an tona, amma idan tura takai bango to bata da mafad'i,tafi matsifaffe iya bala'i.
Mahaifiyarta ce ta ce
"Y'ar Gwaggo lafiya naga kin shigo da damuwa shimfid'e a fuskarki "
Sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta ce
"Umma matanan nan sun kusa kaini bango "
Ajiye sak'ar tayi a gefe sannan ta mai do hankalinta kacokar! Ga d'iyarta tana cewa
"Mai ya faru ne"
Bata b'oye mata komai ba har da munafikin murmishin da Alhaji Zakari yayi duk sai da ta sanar mata, sosai hankalin Umma yayi k'ololuwan tashi, cike da damuwa ta ce
"Lallai mutanan nan ashe kuwa suna da aiki ja sarar dawa da hak'ori, idan sun san wata to basu San wata ba, abinda nake so dake y'ar Gwaggo kiyi hak'uri duk da nasan hak'urin kike a kai, Ina so ki k'ara wani hak'urin ki bari a yi auran nan, Ina ji a jikina auran nan zai zamantowa Hujayrah hanyar da za ta sadar da ita da farin cikinta ,tabbas basu muku adalci ba amma hausawa sun ce ramin k'arya k'urarre ne, muna nan dake Allah zai saka muku zalincin da suke muku, ba dai sun yi hakan don su wulak'antaku ba, ganin mijinki Allah ya jarabcesa da cutar makanta shi ne hakan ya basu damar tozarta shi da y'arsa, ki barsu da Allah shi zai yi maganinsu muna nan dake, Ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai dai in shi ne ya zalunci kansa da kansa "
Shiru Mammi tayi tana sauraron mahaifiyarta, bayan ta kammala nasihar sai ta ce
"To Umma zan k'ara hak'uri, sannan auran zan bari a yi, Allah na tare da masu hak'uri "
"Yawwa y'ar Gwaggo ki nuna musu auran Hujayrah bai dameki ba, don nasan da gangan suka yi hakan don kiji haushi"
"In shaa Allah Umma "
"Maa shaa Allah, idan kin koma gida ki turomin Hujayrah "
"To Umma bara na koma nasan sun kammala tsinanna taron nasu"
Sallama tama Umma sannan ta wuto gida a zuciyarta tana amanna da shawarar mahaifiyarta, domin ita kad'ai ce za ta kai su ga gaci, a haka har ta iso gidan sashensu da wuce direct wanda a lokacin Abbu na zaune kamar kullum bisa tabarmar kaba, hannunsa d'auke da carbi yana lazumi.Da sallama ta shigo d'akin sai ta cire hijabinta ta linke, yana a zaunan ya amsa mata sai ya ci gaba da lazuminsa, samun wurin tayi kusa dashi ta zauna. Motsin zamanta ya ji kusa dashi sai ya d'ago idanunsa kamar mai gani ya ce
"Har kin dawo Zaytuna "
Eh kawai ta iya ce masa, sai ya ci gaba da cewa
"Nasan ba a mana adalci ba musamman ke a matsayinki na wacca da d'auki cin Hujayrah har na tsawa wata tara, kika haifeta, kika raine ta har girmanta tare da bata ingantacciyar tarbiyya,tabbas ba a miki adalci ba amma babu yadda za muyi Zaytuna k'addara ta riga fata, da a ce idanuna suna gani, Ina iya gane mai kyau da akasinsa babu mahalukin da ya isa ya bada auran Hujayrah saini mahaifinta sai dai kashhh! Zaytuna banda k'arfi a yanzu,Ina da rauni babba, ban tab'a damuwa da rashin ganina ba sai a yau d'in nan,Jin sautin kukan d'iyata wacca tayi soyuwa a gareni, bani da maganin da zai iya warkar da rad'ad'in da zuciyarta take ciki, babu babu!!!.... "
Kawai sai ya fashe da kuka wanda rabonsa da kuka tun lokacin da mahaifinsa ya rasu, ita ma Mammi hawayan suke zuba a bisa kuncinta, babu mai lallashin d'an uwansa, kowa a cikinsu yana bama hawayensa damar zuba don taimaka masa wurin rage rad'ad'i tare da zugin ta zuciyoyinsu suke yi .Suna a haka sai ga sallamar Salim da Haroon cikin d'akin, turus! Suka yi a tsaye ganin mahaifansu suna zubda k'walla wanda hakan bak'o ne a cikin rayuwarsu wanda basu saba gani ba,da sauri kamar suna rige-rige suka je wurin da mahaifansu suke, ba tare da sanin dalilin kukan nasu ba, suma suka fashe da kukan gwanin ban tausayi, Haroon har da shasshek'a,suna a wannan yanayin Fatsima da Kakulle suka shigo d'akin da sallama a bisa labb'ansu sun baro Hujayrah a d'akin Kakulle tana ta dirzar kuka, sun yi lallashinta har sun gaji sun k'yaleta sai suka bar d'akin zuwa sashensu Mammi.Kamar su Salim tsayawa suka yi cak! suna kallon ikon Allah uwa, uba da y'ay'a suna kuka kamar wa'inda aka turo musu da sak'on wani shak'ikinsu ya rasu . Kakulle ce ta k'araso cikin d'akin cike da damuwa tana cewa
"Ya Subhanallahi ni Hindatu mai zan gani haka, Audu! Zaytuna! Lafiya kuke kuka haka"
Basu iya amsa mata ba sai ma auta Haroon da yaka k'ara sautin kukan nasa (kai kai kai su Haroon iyayen rigima da kuka,yooo an yi kuka a banza balle da dalili😄😄😄)
Sun kasa ce mata komai, shi Abbu yana k'ara tausayawa d'iyarsa tare da damuwa da cutar makantarsa wanda a da hakan bai damesa sai yanzu, da a ce yana gani shin akwai wanda ya isa yayi masa shisshigi a auran y'arsa ce,babu shi wallahi duk a cikinsu.Ita Mammi abubuwa ne da yawa suka sha kanta, matsalar gidan da mutanan gidan wa'inda basu k'aunarsu mazan da matansu kai har ma da yaransu idan ka cira Kakulle da Baba Musa da ahalinsa sauran kamar jira suke wani abun bak'in ciki ya samesu su musu dariya da habaici, ko yaran Kakulle mata su Attine da Gudidi *Samma-kal ne* domin sun d'inke da Hannatu da Murja suna musu wulak'anci son ransu, gashi wacca take taimaka musu wurin k'wato musu y'ancinsu Hujayrah duk da wani lokacin tana mata fad'a akan tsiwarta amma tana musu rana yanzu suna da niyyar yi mata auran dole, wannan wace iriyar musiba ce haka, Allah Allah mun tuba ka yafe mana, idan ma wani laifi ne muka maka a b'oye ka yafe mana tare da kawo mana d'auki,ka sanyaya zukatanmu,kai kad'ai ne me yaye mana k'uncin da muke ciki, mun dogara gareka don a duk fad'in duniyar Bamu da madogara sai taka, Allah! Allah! Allah! Mun tuba, sosai yanzu Mammi take kuka a da hawaye kad'ai take zubarwa amma yanzu kuwa kuka take sosai tana tonu wahalalliyar rayuwar da suke ciki ita da mijinta da yaranta dan ma Baba Musa yana taimaka musu da na abinci da abubuwan da ba a rasa ba na yau da kullum. Katse mata tunani da zantuttukan zuci Kakulle tayi da cewa
"Zaytuna ba kuka ba ne mafitarku a yanzu addu'a da neman Allah ya kawo muku sassauci ya dace kuyi "
Cikin kukan Mammi ta fara magana wanda muryarta bata fita sosai saboda kuka ta ce
"Bbbakomai Allah na nan..... "
Sai kuma ta ci gaba da kukan, Fatsima sai da ta zubda k'walla saboda tausayin da ya kamata a game da wa'nnan bayin Allah a gaskiya suna cikin jarabtar Ubangiji,Allah ya kawo musu d'auki a al'amuransu, yayi musu katanga daga sharrin mak'iyansu.Haka su Fatsima da Kakulle suka ci gaba da lallashinsu da ban baki har suka yi shiru, sai a sannan Salim yasan abinda ke faruwa ashe Hujayrah ce za a auran dole kuma ga tsoho wanda shima kasan mutumin bai masa ba.
A B'angaren Hujayrah tunda su Kakulle suka fita daga d'akin ta sauko k'asa idanunta a d'an rufe saboda matsanancin ciwon kai da yake damunta, duk'awa tayi k'ask'ashin gado ta ciro kwallar da take d'auke da magunguna, a hankali take duba magungunan har ta d'auko maganin ciwon kai, d'an d'ina tayi da yatsunta biyu Babban yatsa da na kusa da manuniya, gogawa tayi a k'asan hancinta bata yi second biyar da shak'ar maganin sai ta fara jero atishawa babu k'akk'autawa kake Aaaatttijjinn! Aaaatttijjinn! Da kyar ta iya mik'ewa ta hau saman gadon mai rumfa da kwanta zuwa wani d'an lokaci bacci yayi awan gaba da ita.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎
K'asurgumin daji ne mai cike da miyagun halittu a cikinsa, kowanne ka kalla baza kayi marmarin sake had'a ido dashi ma,bak'akyen tufafi ne a jukkunansu gasu gajeru masu zara-zaran farata duk bak'in gashi ya dabaibai ko'ina na jikinsu har da fuskokinsu, suna da manya-manyan idanu amma farare tar! Babu alamun k'wayar bak'i a cikinsa, tabbas! Duk wanda yayi arba da wa'innan halittu sulalewa zai saboda tsabar firgici.Miyagun halittun sun karad'e kusan ko'ina a daji, babu abinda dajin yake d'auke dashi sai bishiyun kuka dana tsamiya,ga dajin da duhu sosai.Wata budurwar yarinya ce take ta faman gudu a dajin,ga miyagun halittun nan suna biye da ita har da wani kabjejen mutum wanda yafi kowannansu muni shi ne a gaba su kuma sauran suna biye dashi,su ba a k'asa ba su ba a sama ba suna bin yarinyar, sosai take gudu tana ambaton sunan Allah akan ya kawo mata d'auki kamar wasa sai taga ta fara yi ma wa'innan miyagun halittun nisa sosai, abin farin ciki sai taga tana kusanto wani lambu mai cike da kayan marmari da yalwataccen haske ba mai cutarwa ba, k'ara k'arfin gudu nata tayi nan da nan ta iso lambun kuma koda ta juya don ganin ko miyagun halittun suna nan biye da ita sai taga Wayammm!!! Babu su babu alamunsu, juyowan da za tayi sai idanunta su ka yi tozali da bayan wani kyakkyawan namiji mai yalwataccen su man kai, dogo ne k'akk'arfa mai faffad'an k'irji,nan take sai yarinyar ta kwad'aitu da son gani wannan saurayin, da bud'e bak'in za ta kira sa sai ta ji ana cewa
"Hujayrah! Hujayrah! Ki tashi kiyi sallar magrib da sallolin da baki samu kinyi ba saboda bacci,wannan wani irin bacci ne haka, kin fa dad'i kina yinsa"
Firgigit Hujayrah ta tashi daga kwance tana waige-waige so take taga fuskar wannan bawan Allah wanda ya juya mata baya.Duk ilahirin cikinta ya jik'e sharkaf! Da gumi, ga k'afafuwan sun fara mata ciwo kamar da gaske daman gudun tayi .Ganin bata da niyyar sauka yasa Kakulle ta zo idan take tana cewa
"Hujayrah lafiya kuwa? "
Fuskar nan a kumbure ga idanun sun k'ara manya saboda kukan da tasha ta amsa mata da cewa
"Kakulle nayi mummunan mafarki "
Dafe k'irji Kakulle tayi tana cewa
"Ya Subhanallahi mummunan mafarki kuma "
"Eh Kakulle "
Hujayrah bata b'oye mata komai a yadda tayi mafarkin ba,har da siffofin wa'innan miyagun halittun sai da ta kwatanta mata da kuma saurayin da ya juya mata baya a cikin lambu,shiru Kakulle tayi tana sauraronta har takai aya, Sauke wani goron ajiyar zuciya Kakulle tayi sannan ta ce
"Hujayrah idan na fahimci wannan mafarkin naki, yana nuni da abu biyu, da farko za ki had'u da k'alubale da dama a hanyarki sannan daga k'arshe za ki had'u da farin cikinki kuma mahad'in rayuwarki,Hujayrah shawarata a gareki ki yarda da auran nan saboda ita ce za ta sada ki da farin cikinki a yadda na fahimci mafarkin da kikayi, ki yarda wannan ce k'addararki wacca babu makawa sai ta sameki "
Hujayrah na zaune kamar gunki tana sauraron Kakulle, maganganunta ne take d'auka d'aya bayan d'aya tana aunawa sannan tana analyzing d'insu a cikin k'wak'walwarta. Bayan Kakulle ta gama mata nasiha sai Hujayrah ta ce
"Kakulle na aminta da auran zan d'auki auran a matsayin k'addarata in shaa Allah sannan zan ba marad'a kunya"
"Yawwa Hujayrah ta Ina so kamar yadda mutanan gidan nan suka ji dad'i za a d'aura miki aure da tsoho, to kina nuna musu kinyi farin ciki da hakan sannan zuwa gobe da sassafe zan je dauji da kaina na samo miki magungunan kambun baka,daga can kuma zan wuce gidan Malam Tani na amso miki maganin karya sihiri har da na aljanu duka zan amso kiyi ta sha, sannan idan anyi auran za kiyi guzirinsu, bayan haka akwai wani b'oyayyen sirri na wannan bada maganin wanda ban fad'a ma mahifinki ba balle ke,anjima da daddare zan sanar miki dashi in shaa Allah, nima sai sanda babana yake kan gab'ar mutuwa sannan ya fad'amin"
"Allah ya kaimu anjima Kakulle, ke ta daban ce a rayuwarta "
Murmushi Kakulle tayi sannan ta d'auki buta ta fita, itama Hujayrah saukowa tayi da k'yar da d'auki buto zuwa makewayi.
Bayan ta rama sallolin da ake binta sai tayi sallar magrib, koda Fatsima ta kawo musu abincin dare kasa ci tayi saboda bakinta bai mata dad'i,daman a gidan daga Fatsima sai Mammi suke kawo ma Kakulle abinci sauran matan basu bata, abin takaicin mazajensu suna sane amma sun k'i musu magana a kai.Bayan sallar Isha'i Hujayrah ta nufi sashensu mahaifanta wanda ba ita ta dawo d'akin Kakulle ba sai 10:30pm na dare kasancewar a d'akin Kakulle take kwana tunda ta girma. A can ta kwantar ma iyayenta hankali akan zata aureshi sannan za ta d'auki auran a matsayin k'addarata,jin maganar Hujayrah sai iyayen nata da k'annanenta suka kwantar da hankalinsu, har ta cema Mamminta manna ma y'an gidan hauka za tayi ta nuna farin cikin auran.
Bayan dawowarta d'akin sai Kakulle ta sanar mata b'oyayyen sirrin da mahaifinta ya sanar mata, nayi iya yi na don ganin na jiyo muku tattaunarwarsu amma Ina abun ya faskara sai hak'uri .
Washe gari da sassafe Kakulle tayi sammakon barin gidan zuwa dauji, ita kuma Hujayrah ta nufi gidan kakarta ta wurin uwa, da yake a jiyan da Hujayrah ta je sashensu Abbu sai Mammi take sanar mata da sak'on Umma. Sun tattauna sosai da Umma sannan Umma tayi farin cikin rashin damuwar Hujayrah a kan auran, bata wani dad'e ba ta dawo gidan.Sai yamma Kakulle ta dawo gidan d'auke da buhu bisa kanta da wata leda babba a hannunta. Sai bayan Isha'i ta kwance komai tare da fad'a ma Hujayrah yadda za ta yi amfani da maganin . shiri na musamman Kakulle take ma Hujayrah har da k'ara mata maganin maciji da kunama da duk wani k'waro ko abin cutarwa,sosai Kakulle take tsima jikarta da magungun daban-daban.(O'o'o wannan soyayya haka Kakulle😂 anya ba shiyasa y'an gidan suka tsani Hujayrah ba😄)
🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A b'angaren sauran matan gidan habaici kala-kala suke sakar ma Hujayrah da Mammi, su kuma sai manna musu hauka suke musamman uwar gayya Hujayrah, har ma su Hannatu da Murja suke tunanin anya ba wani shiri suke akan wannan auran ba.
Alhaji Zakari a ranar ya sanar ma Alhaji Sambo Dala an bashi Hujayrah kuma a ranar ya turo da kud'in komai kama daga kud'in na gani ina so, kud'in saka rana da sadaki, mak'udan kud'i ya turo ma Alhaji Zakari amma sai ya bada kud'in auran kamar yadda al'adar garin take tare da rik'e sauran kud'in . Kamar yadda Hannatu taba Alhaji Zakari shawarar kar a saka ranar auran mai tsayi haka kuwa a kayi don sati biyu Alhaji Zakari ya saka. Su Hannatu su ne gaba a gayyar matan garin daman tun a ranar da a kayi taron suka tsaigunta ma yaran *wai mai idon mujiya za ta auri tsoho*
Kwanci-tashi ba wuya wurin Allah, a yau aka d'aura auran Alhaji Sambo Dala da Hujayrah Abdullahi Kamalu,wani abun ban mamaki da takaici shi ne Alhaji Sambo Dala shi kad'ai ya zo d'aurin auransa babu aboki balle d'an uwa, Alhaji Zakari ne ya neman masa wanda zai wakilcesa a d'aurin auran.Kun san y'an k'auye da ririta abu koda k'arami ne kuwa, haka maganar auran Hujayrah ya yad'u a k'auyan dama mak'otansu wai za ta auri tsofo wanda ya haifeta sannan bashi da y'an uwa . Duk wannan dambarwar da ake Baba Musa bai san da komai ba domin Fatsima tayi kiransa a waya har ta gaji sai dai a ce mata switch off haka nan ta hak'ura tana addu'ar Allah yasa lafiya.
Kuka sosai Hujayrah tasha ita da mahaifanta har da k'annanenta gwanin ban tausayi, a ranar Alhaji Sambo Dala zai wuce da ita ba tare da kariyar y'an uwanta ba wanda hakan ya sab'ama al'adar garin amma kamar an furewa kowa baki haka akayi shiru da baki,haka ya d'auketa bayan an saka mata y'ar jakarta a booth wanda Kakulle ta shirya mata kayan tafiya tare da magungunanta har da na kwalla wasu ta had'a mata a sabuwar jakarta y'ar madaidaiciya. A kujerar gaba Hujayrah ta zauna sai kuka take tayi, haka Alhaji Sambo Dala ya tada motar suka bar layin su Hannatu da Murja sai cewa suke Allah ya rake taki gona.
Shiru motar tayi suna tafiya har suka bar k'auyan sai ya hau babban titi,gudu yake sosai a titin kamar ubansa ya gina titin, Hujayrah kowa abinka da ba a saba hawa mota ba hasalima bata tab'a barin garin zuwa birni ba sai yau shiyasa take ta jin tsoron yadda yake gudu a titin.Sun share kusan awa biyar suna tafiya, ita Hujayrah ma har tayi bacci,jin tsayawar mota yasata bud'e idanunta wa'inda suka d'an sirka saboda bacci, bud'e mata murfin mota yayi yana cewa
"Mai idon duniya mun iso fadarki"
Magana yake yana kashe mata ido irin na tsofaffin rik'akk'un y'an duniya, idanuna nakai duba gareshi tabbas tsoho ne sosai har ta girarsa akwai sirkin gashin furfura,bak'i ne mai tsayi da rangwajejan tumbinsa a gaba har ma yafi na Alhaji Zakari.
Ba tare da ta ce mai komai ba ta sauka daga motar, wani basamudan mutum ne ya ciro mata jakarta daga booth, bayan ta fito daga motar ta kalli gidan da suke ciki, gida ne babba wanda tunda uwarta ta haifeta bata tab'a ganin gida mai kyau da tsari irinsa ba,a zuciyarta tana cewa 'Nan kuma Ina ne? Aljannar duniya' Katse mata tunani yayi da cewa
"Mai idon duniya mu shiga ciki mana, ai gidanki ne"
Jefo masa tambaya tayi fa cewa
"Gidan babu mata ne sai maza"
Ras! Haka k'irjin Alhaji Sambo Dala ya bada,don bai yi zaton irin wannan tambayar za ta fito daga bakinta ba, cike da barikanci ya ce
"Mu shiga mana ki huta, sai na kaiki b'angaren su ku gaisa "
Binsa kawai tayi ba tare da ta ce komai har suka shiga cikin gidan direct ya wuce da ita bedroom, basamuden Katon yana biye dasu da jakarta, ce mata yayi ta zauna za a kawo mata abinci shi zai fita zuwa anjima zai dawo, bata ce masa komai ba ya fita shima Katon ya fice bayan ya ajiye mata jakarta, bayan y'an wasu mintuna sai k'aton nan ya dawo da tray shak'e da abinci, ajiye mata yayi ya fita, zaunawa k'asa tayi tare da bud'e kulan abincin,Dummmm! Haka k'irjinta ya bada kenan abinci babu alkhairi a cikinsa haka ta fad'a, sai wani tunani ya zo mata,bud'e jakarta tayi ta ciro soyayyar gujjiya da nama wanda Kakulle ta saka mata ciki,gyara zama tayi taci sosai sannan ta mai da sauran cikin jakarta , tana zaune sai wata dubara ta zo mata, abincin ta d'iba a plate sai ta zuba a k'ark'ashin gadon, ruwan kuma da wuce toilet dashi, juyeshi tas! Tayi a k'asa sannan ta dawo cikin bedroom d'in ta ajiye gorar a saman tray sai tayi kamar ta ci abincin, kwanciya tayi wanda bata fi mintuna biyar ba sai ta ji motsin bud'e k'ofa,shigowa wannan k'aton yayi da Alhaji Sambo Dala,ji tayi Alhaji Sambo Dala ya tambayi ko ta ci abinci, amsa masa yayi da Eh,sai kawai Hujayrah ta ji ya tsintsire da dariya yana cewa
"Maganin ya fara aiki tunda har tayi bacci yanzu mu wuce kawai anjima abokina zai zo mu tattauna"
Suna maganar suna barin d'akin,gaban Hujayrah ne yayi mugun fad'uws kenan akwai wata manufa a tattare dasu a kanta.Hujayrah dai tana a kwance batayi bacci ba tana sak'a da warwarar yadda za ta b'ullowa wannan bala'in da yake shirin tunkarota.Sama-sama take d'an jin kamar ana maganganu,sai a hankula ta mik'e zuwa k'ofar bedroom d'in Allah yasa a lokacin da za su fita basu kulle k'ofar ba sai ta fito zuwa inda take jin kamar ana magana, wani bedroom ne wanda yake kallon nata bedroom sai ta je kusa dashi tare da kai kunnanta daidai inda za ta ji maganar da kyau,ai kuwa rad'au take jin maganar, natsuwa tayi da kyau don sauraron mai suke tattaunawa a kai, ai da wani irin k'arfi k'irjinta ya bada Ras! Ras! Rarassssss! ,lokaci guda k'wak'walwarta ta tafi wuce gadi na d'an wasu sakanni, komai na duniyar ya koma mata bibbiyu, waro dara-daran idanunta tayi waje tare da rufe bakinta kar tayi ihu su jiyota, a zuciyarta tana cewa' Ni Hujayrah na shiga uku na lalace daman...................'
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***