Free chapter · Read without an account
GARGADI 👌
INUWAR ƘADDARA 🖤
Book 1
Page 9 ✍️
Daga gidan kansila asibiti suka nufa, inda yarinyar take, kuma sun samu jikinta ya yi sauƙi sosai.
Ko magana bai yi wa yarinyar ba, tun da ya ga jikinta ya yi sauƙi, likitan kuma ya ce zai sallami yarinyar yau. Kawai ya ce wa su Duna:
“Ku kwaso kayan ku aje musu!”
“Ba yawa, Madugu, muma ma samu mun ɗan fila ko ba komai mun ƙara jini, mu ba su uku-uku, mu kuma mu yi eh-yane da biyun.”
Wata harara ya aika wa Jagwa da yake magana, kafin ya ce:
“Yau a kaiku ƙiyama, ƙarshen rashin jini.”
Yana faɗin haka ya fita. Kwason kayan suka yi duka suka aje wa matar, domin sun san abin da yake nufi, dai ba za su sha wannan abu ba.
Maman ta ta nanata godiya ga Madugu, wanda ko kallonta bai yi ba, duk da a da tana ganinsa a matsayin mutumin banza kuma azzalumi, saboda ya taɓa bin yaron ta har gida ya sassare shi a ƙafa, wanda hakan ya zama sanadiyyar ƙafarsa har yanzu ba ta koma daidai ba, domin dingishi yake yi.
Amma kuma yanzu, abin da ya yi mata na taimakon yarinyarta daga lalata mata rayuwa da ɗan gidan kansilan zai yi, sai ta ji yana ƙoƙarin goge wancan laifin, duk da ta san yaron nata ne yake da laifi. Saboda a lokacin dawowarsa kenan daga Legos, yana ji da ɗanyen kai, irin shi ga shegen nan.
Bai san waye Madugu ba, amma yana dawowa, ya ci gaba da harkar daba kamar yadda ya fara kafin tafiyarsa.
Ga kuma kwacen waya, wanda aka fara bayan dawowarsa. Kuma a ƙaf yankin Madugu ya haramta hakan. Komai za a yi sai da izinin sa. Idan waya ce, akwai ta waɗanda yake ba da dama da kansa a bi su a ƙwato ta, amma idan har ba da amincewarsa ba ne, a ƙaf yankin babu wani ɗan daba da ya isa.
Yaron, wanda ake kira da Lagwani, bai ji ba. Ya ce babu uban da ya isa ya hana shi abin da ya ga dama. Aikuwa, ranar ya bi wani zai ƙwace masa mashin. Mutumin ya dinga gudu, ga shi da dare ne, garin yana cikin duhu. Ganin ba shi da wata mafita ya sa ya yi gudu har ya shiga unguwar su Madugu, domin ya san ya riga ya tsira, saboda babu wani ɗan daba da ya isa ya shiga wannan unguwa ba tare da umarnin Madugu ba.
Sai dai kuma, Lagwani bai daina binsa ba har sai da ya sare shi a hannu sannan ya ɗauke mashin ɗin.
Duk abin da aka yi, Madugu baya garin, ma ya tafi wani aiki, kuma tare da Duna da Jagwa suka tafi. Sai dai rashin sa’ar da aka yi a daren ranar, ya dawo.
Aikuwa, duk abin da ya faru ya samu labarinsa. Lallai ya yi mamakin wani mai tsaurin ido ne ya iya tsallakowa har ƙasarsa, sannan kuma har ya yanki wani. Lallai zai gane ba a tsallake umarninsa.
Washegari da safe, ƙarfe takwas, Madugu da Reza suka nufi gidan su yaron. Da farko, da ya ga Madugu, ya firgita, domin yanayinsa kaɗai ya kalla ya san wannan babban sa ne a rashin ji da tantiranci. Sai dai saboda kada ya ba da kansa, musamman yadda kowa yake gaya masa yana cikin matsala tun da har ya shiga ƙasar Madugu kuma ya yi ƙwace, to tabbas ba zai ƙyale shi ba. Duk da ya fara tsorata da lamarin Madugu, abin da yake gaya wa kansa shi ne:
“Shi da ya dawo daga Lagos, ina ne bai sa ƙafarsa ba? Ya je Oshodi, ya je Mushin, ya je Agege, ya je Ikorodu, ya je Alaba Rago, to har a gaya masa iskanci?”
Hakan ya sa ya fuske yana wani buɗawa.
Reza ne ya zuci ya kai masa sara da addarsa, ganin wani ƙaramin kwaro ya nemi cizawa a gaban Madugu.
Dakatar da shi ya yi, yana kallon yaron. Mari ɗaya ya zafga masa, ya yi tangal-tangal zai faɗi, sannan ya koma ya tsaya da ƙafafunsa. Wuƙarsa ya zaro daga rigarsa zai kai wa Madugu sara.
Ko gezau bai yi ba, sai ma wani marin da ya sake ba shi kafin ya fito da wuƙar da ke jikinsa.
Sarar da Madugu ya kai wa ƙafarsa ce ta sa ya yi saurin kaucewa. Da yake kuma a ƙofar gidansu yake, sai ya shiga gidan su da gudu yana neman taimako.
Haka Madugu bai yi wata-wata ba, ya bi shi a baya da gudu har cikin gidan. Mahaifiyar yaron tana ihu da neman taimako, amma bai saurara ba, sai da ya shiga har cikin ɗaki ya janyo yaron. Sara uku ya yi masa,sannan ya amsa duk wani abu da ya ƙwace. yaron nan kamar ba zai rayu ba. Tun daga ranar bai sake harkar daba ba, ƙarshe ma sana’ar cajin waya ya fara a shagon da yake ƙofar gidansu.
Bayan sun bar asibitin, inda suka aje yaron kansila suka nufa. Ko kaya babu a jikinsa, yau kwana uku kenan daga shi sai gajeren wando.
Gaba ɗaya Reza ya sauya masa kamanni, domin shi aka bar wa tsaron yaron. Shi kuwa dama Reza akwai mugunta, domin anba kura ajiyar nama ne. Duk takaicin da ya shaƙa a gurin kansila sai ya rama a kan yaron. Don kullum idan dai ya je duba shi, sai ya ba shi wahala. Yanzu ma ya gama masa abin da ya saba ne, sai ga Madugu.
Yaron yana ganinsa ya fara kuka da magiyar ya yi haƙuri, ba zai ƙara ba. Wallahi, in dai ya ƙara, ya kashe shi kawai.
Kujera ya janyo ya zauna a gaban yaron, zama na izza da takama. Kallon yaron ya yi kafin ya buɗe baki da muryarsa wadda take matuƙar tsorata su, ya ce:
“Tashi ka cire wandon ka! Maza cire shi, bari na ga abin da yake saka iskancin, ya kai girman da har kake kasa riƙe ta ba?”
Kallon sa yaron ya yi jikin sa yana rawa da faɗin:
“Don Allah ka yi haƙuri, ka rabu da ni, ba zan ƙara ba. Ka tuna yadda babana ya ɗauke ka, ka tuna fa ni ne Ammar, yaron kansila na...”
“Shiru!”
Ya faɗa da tsawar da ta sa yaron ya faɗi ƙasa ba tare da ya sani ba.
“Ka sa ƙasa da murya! Ba magana nake ba? Maza cire wandon dan ubanka!”
Da sauri kuwa ya miƙe ya sauke wandon, sai dai ko kallonsa Madugu bai yi ba. Ya kai minti biyar a haka, jikinsa sai rawa yake yi. Su kuwa Duna dariya suke sosai da sosai, yayin da yaron ya muzanta sosai. Jagwa ya kalli yaron ya ƙara tuntsirewa da dariya, yana nuna shi da faɗin:
“Wannan ai kai ne Lagwani, bala’i...”
Dagowa ya yi ya musu wani kalan kallo, take suka yi shiru gaba ɗayansu kamar an ɗauke ruwa. Maida kallonsa ya yi kan yaron yana jan tsaki. Kwata-kwata shekarar yaron ba ta wuce ashirin da uku ba, amma jin kansa yake kamar wani ɗan taure saboda bin mata.
“Muddin na sake ganin ka aikata abin da kake aikatawa, to ka tabbatar daga ranar ka rasa jelarka, domin kuwa sai na yi gutsi-gutsi da ita na ba wa karnuka kayan banza.”
Kallon Reza ya yi ya ce:
“Ɗauko masa duk wani abu nasa, kai kuma ka biyo ni.”
Maida wandon sa yaron ya yi, yana bin bayan Madugu. Haka sauran ma, bakin motar suka same shi yana tsaye yana amsa waya. Kallon Reza ya yi ya ce musu su tafi a waccan motar kawai, shi zai koma gidan kansilan ne.
Motar ya shiga, gefen mai zaman banza ya zauna. Yaron da bai fahimci abin da Madugu yake nufi ba ya nufi baya zai shiga.
“Ɗan baban ka, Madugu ne zai tuƙa ka?”
Duna ne ke magana, yana kai wa yaron tokari da ƙafa. Da sauri ya shiga gefen driver ya tada motar. Su ma ɗayan suka shiga suka bar gurin. Ko a motar bai kalle shi ba. Abin da kawai ya gaya masa shi ne:
“Gidan babanka.”
Daga nan yaron ya ci gaba da jan motar zuwa unguwarsu, domin ya fahimci abin da Madugu yake nufi.