Free chapter · Read without an account
THE FAMILY DINNER
Sokoto
Imran ya saka ma kanshi dangana har ya fara chigaba da al’amurran shi na yau da kullun a hnkali a hnkali, ya kuma chigaba da rarraba cv dinshi wurare daban daban yana neman aiki saboda ya rufa ma kanshi da uwayen shi asiri, kuma yadda ya fara sakin jiki yasa inna da baba har ma da mamar maryam jin sanyi a ran su, haryanzu yana tunanin maryam lokaci zuwa lokaci, amma da ya dan fara idan ya tuna da matar wani che se yayi istighfari yayi qoqarin danne tunanin
Da yamma, Imran ya ɗauki makullin mashin ɗinsa ya fita kamar yadda ya saba.
Yana kan babur ɗinsa, bayan ya tsaya ya karɓi wani order, ya ɗauki wayarsa ya duba WhatsApp ya gani ko ze iya kiran wanda ze karbi saqon ta WhatsApp call saboda katin da ke wayar shi baze isa ya dade yana magana ba, number tana kan WhatsApp amma ya kira baa daga ba, se ya yanke shawarar ya dan jira, Ya shiga status ɗin mutane yanata kallo ba tare da wani tunani ba. Sai ya ga na Safiyya ya shigo, Hotunan bikin ne da me hoto ya turo bayan ya qare editing, Ya fara kallon su a hankali, Sai ya ga Maryam da Zaid Ranar daurin aure, Ta yi kyau sosai, Imran ya tsaya na ƴan sakanni yanata kallon ta, har ya wuche, ya dawo, Ya sake kallon hoton, Ya sauke ajiyar zuciya.
“Allah ya baku zaman lafiya…”
Ya matsa ya wuce hoton.
Sai ya rufe WhatsApp ɗin gaba ɗaya ya mayar da wayar aljihu, Ya kunna babur ɗinsa ya ci gaba da tafiya zuwa unguwar da akache ze kai saqon da tunanin idan ya isa me karbar saqon be kira ba se ya sake kira ta normal call
A hankali yake koya wa kansa cewa wasu mutane bazaka iya daina ƙaunarsu ba
Wani lokaci dai…ƙauna ita ce ka roƙi Allah ya sa wanda kake so ya samu farin ciki, ko da ba tare da kai ba.
Abuja
Maryam che zaune a gefen gadonta tana kallon envelope ɗin da ke hannunta.
Ta sake buɗe paper ɗin.
“Tabbas akwai wani abu da ba daidai ba dake faruwa a cikin iyalan Rahman Balarabe”
Har yanzu ba ta tantance ko Aisha ta gano wani abu mai girma ne ba tare da ta gaya ma kowa ba, Aisha irin mutanen nan ne da suke son ɓoye abu don kar susa wanda zasu gayama cikin matsala
Ta juya paper ɗin.
Northern Crest Holdings.
Old land records.
Rahman Balarabe.
Ta sauke ajiyar zuciya, Sai ta ji wayarta ta yi vibrating
Message ne daga Safiyya
“Amarya how far?”
Tayi smiling tana fadin “ai share ki zanyi tunda kuka wuche kuka banni babu ko sallama, ko reply bazan miki ba”
Kafin ta ajiye wayar, aka buga ƙofa.
Maryam tayi saurin mayar da envelope ɗin cikin drawer.
“Bismillah.”
Ƙofar ta buɗe.
Zayd ne.
Ya tsaya bakin ƙofa, “kin shirya?”
Maryam ta kalle shi, “zuwa ina?”
A hnkali ya furta “Mammi.”
Sai ta tuna,chan zasu chi abncin dare
“Oh,” Ta miqe da sauri “dan bani minti biyu”
Zayd ya kalli yanayinta.
“Kamar kin gaji, kiyi zaman ki kawai zanje ni kadai, kuma gobe ki bari a tayaki shirya sauran kayan nan”
“Ban gaji ba fah, bani minti biyu zan hito ynzu”
Ya gyada kai.
“Take your time.”
Ya juya ya fita.
Maryam ta tsaya tana kallon ƙofar, Sai ta kalli kanta a madubi
Ta gyara gashinta, Ta sa ƙananan yan kunne, ta yafa veil, Ta ɗauki wayarta ta fito
A hallway, Zaid na tsaye yana jiranta.
Da ya gan ta, ya ɗan tsaya.
Maryam tana sanye da simple long gown, babu makeup se lipgloss kawai, Ta yi kyau sosai.
Zaid bai ce komai a fili ba amma a zuciyar shi yake magama “yarinya yar qarama haka se kyau ma shaa Allah”
A fili Se yache mata
“Muje?”
Ta gyada kai.
“Eh”
Suka fara tafiya, yana tafe tana bayan shi har suka fito babban compound din gidan
Tsawon lokaci babu wanda ya yi magana, kafin ya fara magana
“Ki Kalli hanyar da zamu bi incase in zakije wurin mammi kar ki shiga wani part”, da toh ta ansa sannan suka ci gaba da tafiya.
Da suka shiga part ɗin Mammi, Maryam ta ji ɗan bambancin yanayin gidan, Wurin ya fi zama warm, se Taji kamar ana rage mata kewa, Akwai family pictures a bangon, Hotunan yara, Hotunan Zaid da Fahad tun suna ƙanana, Hoton Alh Rahman Balarabe da Mammi.
Maryam ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon ɗaya daga cikin frames din
A cikin hoton, Zaid ne yana kamar shekara 15, Fahad yana kusa da shi, Maryam ta kalli fuskarsu, Ta ɗan daɗe tana kallon fuskar zayd.
Sai da Taji Zaid na chewa
“Muje ko?”
Ta juyo, Se ga Mammi tana fitowa daga dining.
“Maryam!”
Ta sheqa ta rungume Mammi kamar ta dade da sabawa da ita
“Welcome, my daughter.”
Maryam ta yi murmushi.
“Ina wuni mammi?”
Mammi ta riƙe hannunta bata amsa ba se chewa tayi
“Kin yi kyau.” Ta sunkuyar da kai
“Nagode mammi”
Sai Mammi ta kalli Zayd
“Kana kula da Ita ko?”
Zayd ya ɗan yi murmushi.
“Kalleta ki gani she is fine.”
Mammi ta yi masa kallon da ya sa ya san ba ta yarda da amsar ba.
“Fine kawai?”
Zaid ya yi shiru.
Maryam ko kamar jira take ta fara hawaye, Zaid a hnkali ya furta “ya salam yarinyar nan so take ta hadani da mammi”
Mammi ta hau tambayar ta lfya, me ke faruwa? Zaid Ya yimata wani abu ne? Ta girgiza kai, da shesheka take fadin ”ni mammi inason in dawo wurinki in rinqa zama nan, banason chan part din”
Mammi ta sauke ajiyar zuciya don ta dauka ko wani Abu aka yimata “kar ki damu my daughter ai nan da kwana kadan mijinki ze koma Amsterdam idan ya tafi se ki dawo nan muyi zaman mu ko? Kafin ayi miki passport da visa ki bishi” da sauri tache “aa mammi ni ban binai nan zan tsayawa” yanayin hausar da yadda tayi maganar a shagwabe yasa zayd yayi dariya, mammi ma seda Tayi dariyar hausar “toh shikenan muyi zaman mu nan kawai, shikenan ko?” Maryam ta girgiza kai “toh mammi Yaushe ze tahi? Kuma inaso in tahi sokoto inga mama” Mammi ta riqe baki “toh in yasa rana ze gaya muna, mu bari se in ya tafi zan raka ki sokoton” ai ko maryam ta saki jiki da mammi sosai, zayd na zaune gefe yana kallon ikon Allah, shikam an hada shi da yarinya gashi se shagwaba take da wata hausar ta me ban dariya.
Mammi ta miqe tana chewa muje mu fara chin abnci kafin sauran su qaraso, nan wayar zayd ta fara ringing ya dauka ya fita, su kuma suka wuche dinning, suna zaunawa se ga Fahad ya shigo dining area din ya zauna, ya hango maryam kusa da mammi ta lafe a jikinta kamar mage, ya miqe tsaye yana dariya
“Anty Maryam.”😅
Tayi smiling
“Yaya Fahad ina wuni”
Ya yi mata murmushi.
Mammi na chewa kar ta sake che mishi yaya ai ita matar yayanshi che don haka Itache antyn shi
Yayi dariya yana fadin
“Ina yimiki welcome zuwa Abuja da kuma family dinmu.”
“Nagode”
Zayd ya shigo dining din shima yana kallon yadda take maqale da mammi, yaja kujera kusa da ita ya zauna yana ansa gaisuwar fahad
Maryam ta kalli dining table din da ke cike da abnci Kala kala, Kusan komi akwai wurin shinkafa kala kala, Grilled chicken, Beef, Salad, Soup, Bread, Desserts.
Mammi ta kalli Maryam, “me zaki chi?”
Maryam ta miqe tsaye ta dauko plate tana chewa mammi bari in hwara zuba miki abnda zaki ci
Fahad Yayi dariya “don Allah anty maryam ki bar hausar sakkwatawan nan a chan tunda kin baro sokoto”, zaid ya harare shi mammi kuma tana fadin “ka kyale min yarinya banason sa ido”
“Toh, na Kama bakina” Fahad ya fadi yana dariya
Seda tasa ma mammi abnci ta kawo mata
“Nagode sosai my daughter Allah ya yimiki albarka, kisa ma mijinki shima” da toh maryam ta amsa sannan ta fara tambayar shi abnda zata sa mishi “anything” kawai yache mata yana danna wayar shi, ta debo mishi komai da ke wurin seda Tayi plate hudu na abnci ta jera a gaban shi, yayi shuru yanata kallon abncin, mammi da Fahad se dariya suke qasa qasa, be che komai ba ya jawo wanda yake ganin ze chi ya fara chi a natse, dd nan itama maryam ta dauki spoon ta fara chin wanda ta debo ma kanta
Fahad ya fara magana.
“So, ya kike jin Abujan?”
Maryam ta kalle shi.
“Ba daadi, haryanzu baka shigo part dinmu ba, kuma ni ko’ina banje ba”
“Ashsha be kamata ache abj bata miki daadi ba keda kike da CEO na international company, kada ki damu zan shigo ayukka ne suka sha kaina”
Ta yi murmushi.
“Ni ai gani nazo wurin mammi”
Fahad ya yi dariya.
“Hakane, naga ma kina neman kwache min mammi na”
Zayd ya kalli Fahad.
“Kyaleta haka, ka batta ta chi abnci”
Fahad ya ɗaga hannayensa sama alamar surrender
“Okay, bro, naji warning dinnan”
Mammi ta yi dariya.
Yanzu kam ta yadda Zayd ze kula da matarsa tunda taga ya dauketa serious, dama shi idan dai ya dauki abu serious shikenan
Zayd ya yi shiru ya chigaba da chin abncin shi
Maryam ta sunkuyar da kai tachi gaba da chin abncin itama, Suna ta chin abncin su a natse, Mammi tana tambayar Maryam abubuwa sama sama
“Kinyi magana da mamanki kuwa?”
“Eh.”
“Tana lfya ko?”
Maryam ta yi murmushi hawaye na fara taruwa a idonta, cikin muryar kuka ta ansa
“Eh.”
Zaid a cikin ranshi yake fadin “ai shikenan mammi ta jangwalo muna aiki ynzu kuma”
Mammi ta riƙe hannunta
“Ki riƙa kiranta koda Yaushe, Kada ki bari ta ji kamar kin mata nisa saboda aure kinji? Kuma ai jiya da mukayi magana tache min an bata yan mata guda biyu da zasu tayata zaman gida tunda ynzu baki nan”
Ai nan maryam ta sauke ajiyar zuciya da dukansu seda sukaji, dama abnda ke karya mata zucciya tunanin wa ze taya mama aikin gida? Batason mamanta na wahala
Maryam ta gyada kai.
“In Sha Allah zanyita kiranta koda Yaushe, ina kewar ta sosai”
Fahad yana cin abinci yana sauraron su, so yake ya kawar da zanchen don ta dena kuka, abnda zayd be iya ba kenan
“Maryam, kin taɓa zuwa Abuja kafin yanzu?”
“So guda nittaba zuwa ni rakko mama biki”
Sora kadan ya fashe da dariyar hausar se yaga zayd ya harare shi shima yana qoqarin danne tashi dariyar, ya fuske ya chigaba da magana
“Ai kuwa akwai abubuwa dayawa da zan nuna miki”
Maryam ta yi murmushi.
“Da gaske? Yaushe?.”
“Fahad,” Zayd ya kirashi a kausashe
“Naam?” Ya ansa
“Ka bari se tayi settling tukunna.”
Fahad ya kalli ɗan zayd yayi dariya
“Kawai zan dan rinqa fita da ita don nasan kai bazakayi ba, zaka fara chewa aiki aiki”
Zayd bai ansa mishi ba.
Suna nan zaune a dining se ga aunties dinsu sun shigo. Sisters din Alhaji balarabe guda biyu (daya yayar shi hajiya raliya, daya kuma kanwar shi wadda suke kira anty fati) da sister din mammi daya anty hadiza. Maryam ta gaida su cikin girmamawa suka amsa mata anata tsokanar zayd, shi dai bayan gaisuwa be che komi ba. Maryam ta lura da qanwar mammi anty Hadiza da qanwar alh balarabe anty fati sunata janta da fira a qoqarin su na ganin ta saki jiki, amma dayar da aka ambata da hajiya raliya (yayar alh Rahman) sam bata saki jiki da maryam ba, se wani irin kallon warning take mata.
A cikin firar da suke da maryam suke gaya mata chewa su biyu gobe zasu wuce garuruwan da suke aure don tun da suka zo bikinta Harynzu basu koma ba, amma hajiya raliya balarabe nan zata zauna na dan lokaci akwai abnda takeyi a nan Abuja.
Bayan ɗan lokaci, Fahad ya fara magana da Zayd game da business.
“Bro, ka duba documents din da na turo maka?”
“Na fara dubawa amma ban qare ba”
“About Meridian Axis expansion dinnan ne, ya kamata ka dan dudduba abunda akeyi a nan kafin ka koma.”
“Zan duba yau da dare in shaa Allah.”
Fahad ya gyada kai.
“Okay.”
Maryam tana cin abinci amma kunnenta ya tsaya kansu
Documents?
Business?
Meridian Axis?
Ta kalli Zayd
“Meridian Axis kuna da branch office a Nigeria ne?”
Zayd ya kalle ta dan mamaki
“Eh”
“A Abuja nan?”
“Lagos ne head office na Nigeria amma akwai branch office a nan Abuja, kuma munada projects da mukeyi nan Abuja Yanzu haka”
Maryam ta gyada kai.
Fahad ya shiga maganar.
“Mijin ki bayason zama nan. Yafi son Amsterdam, ynzu haka yana planning ya koma ya bakki nan tare damu”
Zaid ya harare shi.
“Aiki nikeyi a chan ba zaune kawai nike ba”
Maryam itama ta karba
“Ai nafison ya tafi ya banni in dawo nan wurin mammi”
Zayd ya girigiza kai kawai
Fahad ya yi murmushi yana jin wani irin daadi
Sai Mammi ta katse su.
“Surutun ya isa haka, idan an qare chin abnci se a koma parlor ayi fira a chan”
Fahad ya yi dariya.
“Yes, ma”
Duk suka tashi suka nufi parlor bayan sun qare chin abnci, maryam ta bi mammi har parlor suka zauna tanata maqale mata
Zaid da Fahad suka rage a dining.
Mammi ta zauna a sofa, Maryam ta zauna kusa da ita. Su kuma anty fati da anty Hadiza suka zauna a kujerar opposite din su mammi
Hajiya raliya ta wuce dakinta tache zataje ta huta a chan
Su anty Hadiza ke gayawa Maryam idan ta koyi zama da Zayd zataji daadi saboda beda wuyar sha’ani
“Shi ba mutum ne mai yawan magana ba. Kada ki ɗauka shirun sa yana nufin be damu dake ba”
Maryam ta gyada kai.
“Na lura da haka”
“Mafi yawan lokaci, yafi yin abubuwa a aikache fiye da yayi magana.”
Maryam ta yi shiru.
Sai ta tuna da tissue ɗin da ya rinqa bata a jirgi.
Abincin da ya kawo mata.
Yadda ya ɗauke ta daga prayer corner ya kwantar ba tare da ya tada ita ba, don tanada tabbacin shine tunda su kadai ne a gida
Ta sunkuyar da kai.
“Hakane”
Mammi ta kalle ta.
“Ki ba shi lokaci kinji? Komi zeyi dd”
Maryam ta ɗago kai se kuma tayi sauri ta sunkuyar
“Mammi zan shiga toilet”
Kije upstairs dakin farko na hannun daman shine dakina, ki shiga kiyi amfani da toilet dina”
A can dining, Fahad yana zaune tare da Zaid haryanzu
Se Ya kalli ɗan uwansa..
“So…”
Zaid ya ɗago kai.
“So me?”
“Tambaya kawai zanyi ya rayuwar aure?”
Zayd ya kalle shi.
“Kwana nawa nayi da auren?”
Fahad ya yi dariya.
“Exactly, kwanakin da kayi yaya suke?”
Zayd ya ɗauki glass cup ɗin da ke gabanshi yasha ruwan da ke ciki ba tareda da ya sake chema Fahad komai ba
Fahad ya yi shiru.
Sai kuma ya chi gaba
“Naganta shuru shuru kamar bata sake ba”
“Gajiyar biki ne bata huta ba”
“Hmm.”
Zaid ya kalle shi.
“Menene?”
“Ba komi, ya akayi kasan bata huta ba? Ko kai ka tara mata wata gajiyar ne?.”
Zayd ya miqe ya nufi hanyar fita
Fahad nata murmushi, ya daga kai yana kallon upstairs, Amma bayan murmushin…idanunsa suna nan qyam na ɗan lokaci a kan stairs ɗin.
Fahad nata kallon stairs ɗin na ƴa seconds. Bai san me Maryam take tunani akai ba, amma tun da ya shigo gidan kafin su fara chin abnci, ya lura da wani abu a tare da ita. Ba ta yin magana da yawa, amma tana kallon abubuwa sosai. Kuma irin wannan kallon… shi ya sa ya fi son ta kasance kusa da su, inda zai iya sanin duk abin da takeyi, shiyasa yaji daadi da yaji zaid ze tafi ya batta.
Bayan kusan awa ɗaya da rabi, Maryam nata fira da su anty Hadiza da anty fati, mammi tache ya kamata ta koma part dinsu, ai ko kamar zatayi kuka, mammi ta kira zayd a waya tache yazo su tafi Batason Maryam ta fito ita kadai, seda ya dan shafa goshi yana tunanin Shiyasa fa dazu yache ya Kalli hanya, gashi ynzu anason a mayar dashi bodyguard, ya ansa da gashinan zuwa sannan mammi ta kashe wayar
Koda ya shigo parlorn da sallama maryam tana smiling alamar tanajin daadin firar da sukeyi, ya dan kalleta, Tayi kyau sosai, smiling yana mata kyau.
Mammi ta rungumeta tana mata seda safe, maryam kam fuskar ta har ta fara chanjawa kamar zatayi kuka
“Daughter kuje ki huta kinji”
“In Sha Allah Mammi, seda safe” ta fadi cikin muryar kuka
“Gobe za mu yi breakfast tare?”
Maryam ta yi murmushi.
“Eh mammi zanzo in shaa Allah”
Fahad yazo ze fita shima zuwa part dinshi
“Goodnight, anty Maryam.”
Ya kalli Zayd
“Goodnight, bro.”
“Goodnight.”
Suka fita.
A hankali suke tafiya yana gaba maryam tana bayanshi tana goge hawaye har suka isa part dinsu, shi dai zayd besan abnda ze che mata ba ganin yake kukan nan yayi yawa shi kuma be iya lallashi ba
Sun hau sama sun shiga corridor da dakunan su suke, Maryam tana tafiya kusa da Zaid.
Gidan ya yi shiru, Se kawai yaji tayi magana
“Yaya.”
Yayi mamaki wai shi take kira yaya? Jiya ma fah yaji ta kirashi da yaya, ya juyo ya ansa
“Naam?”
“Inaso in dan tambayeka ne?”
Ya kalle ta.
“Ina jin ki”
“Ehm..umm…dama…dama…gameda babanka ne…”
Zaid ya tsaya.
Maryam ma ta tsaya.
Ta lura da yanayin fuskarsa ya sauya.
Maryam ta yi saurin gyara maganar ta
“Naga hoton shi a parlorn mammi, kana kama dashi
Zayd ya dan kalli gefe
“Sunan shi Alh Rahman Balarabe”
Sai ya fara tafiya, Maryam ta bi Bayan shi.
Bayan ƴan few steps, Zayd ya chigaba
“Ya rasu shekarun baya.”
“Allah ubangiji ya jiqan shi Yayi mishi rahama”
“Ameen”
Maryam ta dan sachi kallon fuskarsa, Akwai wani abu a cikin muryarsa, Ba fushi ba, Ba damuwa kawai ba, Wani abu ne da ta kasa gane ko miye
Da suka isa kofar dakin shi, zaid ya bude qofa, se ya tsaya yana kallonta.
“Seda safe.”
“Seda safe”
Ya tsaya nan qofar yana jira idan ta shige nata ɗakin shima ya shige nashi ɗakin
Sai Maryam ta sake kiran shi.
“Yaya?”
Ya kalleta yana dan yamutsa fuska
“Naam?”
“Nagode”
“For?”
Ta ɗan yi murmushi.
“Komai da komai
Zaid ya kalle ta.
Sai ya gyada kai.
“You’re welcome.”
Ya shiga ɗakinsa, yana tunanin toh ita haka take? Ynzun nan tana kuka kuma ynzun nan tana dariya?
Maryam ta jingina da qofa bayan ta shiga dakinta, Sai ta ɗago wayarta.
Ta buɗe notes.
Ta ƙara rubutu:
Rahman Balarabe — ya rasu shekarun baya
Ta tsaya.
Sai ta ƙara:
Ya kamata in tambayi alaqar shi da northern crest
Ta kalli rubutun.
Amma kafin ta ajiye wayar, wani abu ya faɗo mata.
A lokacin dinner, lokacin da Fahad ya yi magana game da documents, Zaid ya ce bai duba su ba.
What documents?
Maryam ta ɗaga kai.
Wata sabuwar tambaya ta ƙara shiga zuciyarta.
Ta kashe wayar.
Amma a daren nan…
ba Aisha kaɗai ke cikin tunaninta ba.
Rahman Balarabe ma ya fara zama wani suna da ke buƙatar amsa akansa
Follow this link to join my WhatsApp group: ***