Free chapter · Read without an account

THE LOCKED DOOR

by Nihaal Maalik · KIRAN KADDARA

SOKOTO

Mama na jin daadin zama da hauwa koulu diyar anty maimouna da kuma meramu Diyar kawu, se taji ta rage kewar maryam sosai, suna taya ta fira, kuma suna yimata aikin gida, se dan abinda baza’a rasa ba takeyi, ita meramu tana zuwa makaranta don tana jss2 ne, ita kuma hauwa koulu sun gama rubuta jarabawar kammala secondary suna hutu ne, har mama tache ma anty maimouna ta roqar mata mijinta ko ze bari ta zauna wurinta idan result dinsu ya fito se ta nema mata Jami’a nan sokoto

Mama Tana yawan shiga gidansu imran wurin inna saboda taga ya imran yake, Har inna ta lura da yawan zuwan da mama takeyi saboda imran ne, don tana yawan kawo abnci ko kayan marmari tache ta kawo ma dan ta, ranar suna fira inna ke chewa “wai nikam ko dai imrana ya koma chan wurinki kawai a bashi daki don In huta da kai da kawon ga da kikai tunda naga ba saboda ni kika zuwa ba, se hwamar kula kikai da shi se kache wani Qaramin yaro, ga autana nan shi ka buqatar kula ba imrana ba” 

mama tayi dariya “ai kina kula da autan ki da kanki shiyasa nima nike kula da yarona da kaina” 

Wani lokaci inna tana chema imran ya tashi ya shirya yaje wurin mama suyi hira, se ko shirya yaje wurinta su dan yi fira sannan ya dawo gida, ranar ya shiga gidan da sallama hauwa koulu tana shara ta dago ta ansa mishi se ya ganta kamar maryam, dama yana lura da ita kwana biyu da yake shigowa wurin mama, yanayin sanyin jikinta da natsuwar ta da siffar ta kamar maryam, a ranshi yake fadin kenan maryam da dangin mama na Niger take kama, tunawa da yayi chewa matar aure che yasa yayi istighfari ya shiga parlour ya zauna, hauwa ta kawo mishi ruwa sannan taje ta kira mishi mama


ABUJA 

Jiya da dare maryam ta dade sosai batayi baccee ba saboda tunanin qofar nan, “Anya idan na shiga bazan samu wani abu a ciki da zesa in gano wani abu gameda Aisha ba? Idan ma babu, me ke cikin dakin da ake ta yimin gargadi?” Batayi baccee ba se bayan 2am ta gota sannan baccin ya sache ta, da Asuba daqyar tayi sallah tanata gyangyadi ta koma kan gado ta kwanta

Da safe ta tashi da tunani daban daban a ranta, maganar Hajiya Raliya che ta dawo mata.

Ba duk ƙofar da kika gani ba ce dole ki buɗe.

Sai kuma muryar Zaid.

Kar kije chan don ba bangaren mu bane

Maryam ta buɗe idanunta.

Ta kalli saman ɗakinta.

“Me ke cikin dakin nan?” ta faɗa a hankali.

Ta juya ta kalli window.

A bayanta ne garden ɗin yake.

Ta tashi daga kwanche ta zauna kan gadon.

Tun da ta ga ƙofar jiya, zuciyarta ta ƙi samun nutsuwa.

Ba don ta ga wani abun a wurin ba.

Sai dai yadda mutane biyu daban daban suka gaya mata abu ɗaya.

Hajiya Raliya, Da Zaid.

Kuma babu wanda ya ba ta gamsassar Ansa ko dalili

Ta sauka daga kan gado, ta shiga bathroom.

Bayan ta gama wanka, ta dawo ta zauna a gaban mirror tana shafa moisturizer.

Ta buɗe wayarta se ga Saƙo daga Mama.

“Kin tashi? Ya kuke dake da mijin ki da mammi? Ina gaishe su duka, Allah ya yimiki albarka”

Maryam ta yi murmushi.

Ta rubuta:

“Na tashi Mama, Kowa lfya qalau kuma Zasuji in shaa Allah”

Sai ta ajiye wayar, Ta kalli kanta a madubi, Gashinta ya fito sosai bayan ta cire hulla

Ta tuna abin da Zaid ya faɗa jiya.

“Meyasa kikesa extension a gashin ki?”

Sai ta yi murmushi kaɗan.

“Extension kuma? Ni maryama?”

Ta girgiza kai.

“Wai ban san gashina bane?”

Ta tashi, tayi salatul duha se ta koma ta haye gado ta kwanta rigingine, baccee na fizgar ta a hnkali saboda dama baccin be isheta ba

A can ɗayan ɓangaren gidan, Zaid na parlour kwanche tun asuba da ya fito daga ɗakinsa yaje masallaci ya yi sallar Asuba be koma baccee ba, bayajin daadin jikin sa, kwankin nan dai gabadaya haka yake baccee cikin wani irin yanayi, Ya duba agogon parlorn da yake kwance 8am na safe

Ya hau upstairs da niyyar yaje dakin shi ya kwanta amma sai ya tuna bai ji motsin Maryam ba, lfya take? Ya tambayi kan shi, Ya yi tunani na ƴan seconds se ya miqe zuwa dakinta yana takawa a hankali har ya kai kofar dakin 

Knock. Knock.

Babu amsa.

Ya sake bugawa.

“Maryam?”

Shiru.

Ya ɗan daɗe a bakin ƙofar.

“Maryam?”

Har yanzu babu amsa.

Ya buɗe ƙofar a hankali.

“Assalamu alaikum.”

Shuru

Ya shiga kaɗan.

Sai ya gan ta tana kwance a kan gadon a rigingine baccee ya dauketa, Tiny figure ɗinta ta nutse cikin gadon, blanket ɗin ya rufe kafarta kadan, Gashinta ya bazu a kan pillow don batasa hulla ba. Zaid ya tsaya, Ya kalleta na ƴa seconds, Bai so ya tada ta, amma wani abu ya sa ya matso kaɗan, ya duqa Ya kalli gashinta dakyau, Sai ya gane, Ba extension ba ne, Natural hair ɗinta ne, Dogon curly gashin ya bazu a kan pillow wani har ya sauka kan fuskar ta, Zaid ya ɗan yi shiru se ya duqa ya kai hannu ya taba, Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana furta

“Fatabarakallah ahsanul khaliqeen.”

Ya ɗan yi murmushi ba tare da ya sani ba yana jin wani irin daadi na ratsa shi, Jiya ya yi tunanin extension ne, Ashe gashinta ne, Ya girgiza kai.

“Yarinya qarama haka se kyau, ni ban taba ganin gashi irin Haka da yawa ba se wurin turawa a wasu qasashe amma ba Nigeria ba…” Ya faɗi a hankali, yanata shafa gashin da hannu daya, hannu daya kuma yana riqe da hannun ta, hannun nan dai da yakeso, ganin ta dan motsa ya tashi da sauri ya juya zai fita, Amma kafin ya fita, ya lura da littafin da ke gefen gadon, Qur’ani ne, yana jin daadin yadda take da qoqarin ibadah, Ya gyara shi ya mayar da shi a kan ƙaramin table da ke prayer corner, Sai ya sake kallon Maryam na dan lokaci, Sai ya fita ya rufe ƙofar a hankali.

Bayan kusan awa ɗaya, Maryam ta farka.

Ta buɗe ido, Ta kalli ɗakin, tana jin qamshin wani turare wanda ba nata ba, amma tasan qamshin, qamshin zaid ne, wani irin feeling taji kamar ya shigo dakinta da take baccee

Ta tashi ta zauna ta kalli agogo 9:15am, Ta kalli ƙofar, A rufe take.

Ta ɗaga hannunta ta gyara gashinta ta daure shi in a messy bun, Sai ta ga Qur’an a prayer corner kan table, Ta tsaya, “Ni na mayar da shi nan?” Ta yi shiru.

Sai ta ɗauki wayarta tana dubawa, chan kuma Ta  tashi ta sauka downstairs.

Zaid yana parlour yana aiki a laptop.

Da ya ɗago kai ya gan ta, ya ɗan tsaya, Tana sanye da simple long English gown da veil.

Ta gaida shi “Ina kwana.”

Be ansa ba se chewa yayi “Kin tashi lfya?.”

Sai ya kalle ta dakyau

“Jiya bakiyi baccee da wuri ba ne?.”

“Eh.”

“Kin chi abnci?”

Ta girgiza kai.

Zaid ya rufe laptop ɗinsa.

“Muje.”

“Ina?”

“Mu chi abnci.”

“Bana jin yunwa.” Ta furta don ita dai tsakani da Allah ta fara gajiya da abncin cooks dinnan 

Ya kalleta, ya tako har gabanta, kirjin ta ya buga da qarfi, ya kamo hannunta ya riqe yana dan murzawa

“Mahreeyam”

“Naam?”

“Muje mu chi abnci.”

“Toh.” Kawai ta amsa, Suka nufi dining still yana riqe da hannunta yasa dayan hannun yaja mata kujera ta zauna, sannan ya saketa shima ya zauna se ji tayi yache 

“Ashe ehmm…”

Ya dago kai ta kalleshi 

“Gashin ki, Ba extension bane ashe.”

Ta ɗan yi murmushi Kadan 

Zaid ya ɗaga gira.

“Baki gayamin ba”

“Na gaya maka ba extension bane.”

“Aa baki gayamin ba.”

Maryam ta yi dariya kaɗan.

“Amma yadda ka yi min magana ne kamar na yi committing wani crime, shiyasa na kasa chewa komi”

Zaid ya yi shiru, Sai ya ce:

“Na dauka extension ne”

“Yanzu fa?”

“Ynzu na gane ai”

“Ya akayi ka gane?”

Yayi shuru

Itama bata sake chewa komai ba

Bayan sunyi breakfast din Zaid ya tashi.

“Znje office.”

Maryam ta gyada kai kamar zatayi kuka

“Okay”

Ya ɗauki mukullan sa

Sai ya tsaya.

“Kinaso ki fita?

Maryam ta ɗan yi tunani, tanaso ta fita amma kuma tanaso ta zagaya baya wurin qofar nan 

“Aa zan tsaya gida”

“Okay”

“Yaya” 

Ya juyo, shi dai kawai ya kusa gaya mata ta rinqa kiranshi zayd dinshi kawai 

“Naam?”

“Maganr jiya.”

“Wace magaana kenan?”

“Wannan qofar.”

Fuskarsa ta sauya

“Me ya faru da ita?”

“Meyasa kache kar inje Chan?”

Zaid ya yi shiru.

“Saboda nache kada kije don haka kada kije”

Maryam ta kalle shi jin yayi magana kamar yayi fushi 

Ya dan sauke ajiyar zuciya.

“Mahreeyam, miye damuwar ki da wannan kofar? 

Ta yi shiru.

Ya kalle ta.

“Ba wai takura ki nike, bnso ki shiga abunda be dame ki ba, ynzu me ya shafe ki da wannan qofar don Allah?”

“Ba komai”

“Good.”

Sai ya fita.

Maryam ta tsaya tana kallon ƙofar da ya fita.

“Bakason in shiga abnda be dame ni ba?…”

Ta maimaita.

Sai ta ɗauki wayarta.

Ta buɗe notes din wayarta Ta rubuta:

Back door — Zayd yaqi yayi min explaining 

Ta tsaya,Ta kalli rubutun.

A hankali ta rufe wayar ta aje

Da rana, Maryam tana zaune a garden, taje part din mammi bata nan, de ta dawo garden ta zauna, Ba ta je kusa da ƙofar ba.

Ta zauna ne a wasu kujeru da suke dan nesa da wajen, Ta buɗe wani littafi kamar tana karatu, 

Amma bayan ƴan mintuna, ta ɗaga kai, Ta kalli can, Ƙofar tana nan A rufe, CCTV ɗin ma tana nan, Ta fara tunani.

“Me suke boyewa?”

Sai wayarta ta yi ringing, Safiyya ce.

“Hello?”

“Amarya!”

Maryam ta yi dariya.

“Safiyya, kinsan fushi nike dake shiyasa naqi kiran ku duka daga ke har bahijja”

“Ba komi zaki sauko idan na gaya miki good news, Ya zaman Abuja?”

“Alhamdulillah, miye good news din?”

“Ya Zayd?”

Maryam ta yi shiru, dazu mama ta tayi mata text ta tambayeta ya Zayd, Toh meyasa ake tambayarta ya yake? Ta zumburo baki

“Me ya sa kika yi shiru?” Taji muryar Safiyya kafin ta dawo daga tunaninta da sauri

“Ba komi, gayamin good news”

Safiyya ta yi dariya.

“Maryam, na sanki fah.”

Maryam ta yi murmushi.

“Ke shin yana nan lfya toh”

Safiya tayi dariya

“Kin fara son mijin naki kuwa? Shi dai nasan zuwa ynzu kam ya fada soyayya in dai har yana ganinki kullun, fuskar nan taki, da shape dinki da gashi…”

Maryam ta yi saurin kallon surroundings din garden din kamar wani zai ji abnda Safiyya ke fadi

“Safiyya!”

Ta yi dariya.

“Me?”

“Kakki fara shirmen ki”

“Tayi dariya Okay, okay Toh ki kula da kanki da mijinki Mrs Zayd”

Maryam ta yi shiru.

“Me kika ce?”

“Na ce ki kula da kanki.”

“Safiyya…”

“Naam?”

“Kin san wani abu game da Balarabe family?”

Shiru ya biyo bayan tambayar.

“Wani abu kamar me kenan?”

Maryam ta gyara zama.

“Ba komai, bashshi kawai”

Safiyya ta yi shiru na ɗan lokaci.

“Maryam, Me ke faruwa?”

“Ba komi.”

“Kin tabbata?”

“Eh”

“Okay. Amma idan akwai wani abu, ki gaya min.”

“In Sha Allah, kema gaya min goods news din” 

“Inada ciki sati..”

Ai ihun da maryam tayi yasa safiya ta kashe wayar tana dariya kawai.

Maryam ko se daadi takeji tana tunanin inda tana sokoto da ita zaayi renon cikin safiya har a haife shi, a hnkali ta furta “Allah ya bamu rayayye/ya me albarka, Allah ya sauke ki lfya”

Ta kalli garden ɗin.

A wannan karon, ba ƙofar kaɗai take kallo ba.

Ta fara kallon CCTV ɗin.

Sai ta lura da wani abu, Camera ɗin ba kofar kawai take kallo ba, akwai wata tana kallon hanyar da take zuwa wajen, Kamar ana son ganin duk wanda ya kusanci wurin.

Maryam ta ɗan matsa qarshen bench ɗin.

“Duk wannan security me ake karewa?”

Sai ta ji motsin mota daga compound.

Ta ɗaga kai.

Fahad ne ya shigo, yana parking mota yaji ihu daga garden ya nufo wurin da murmushi don yasan itache 

Da ya gan ta a garden, ya daga mata hannu.

“Anty Maryam!”

Ta yi murmushi.

Ya ƙaraso.

“Ke kadai kike zaman ki?”

“Eh.”

Ya kalli garden.

Sai ya kalli Maryam.

“Komi lfya ko?”

Maryam ta yi murmushi.

“Alhamdulillah.”

“Good, saboda naji ihu ina fitowa daga mota”

Ya zauna opposite ɗinta.

“Waya che nikeyi da Safiyya”

“Ohh Allah sarki, Ina yayana?”

“Yana Office.”

Fahad ya gyada kai.

“Of course, dama nasani”

Ya kalli wayarta da ke ajiye a gefe

“Kina Busy ne?”

“Aa”

“Kina busy kinata tunani manah”

Maryam ta ɗan yi murmushi.

Fahad ya yi dariya.

“Kiyi hnkali, kibar tunani me zurfi.”

Maryam ta yi shiru.

Fahad ya yi murmushi kamar wasa yake.

“Okay wasa nike.”

Maryam ta yi murmushi.

“Okay.”

Amma a zuciyarta tunani take…

Me yasa kowa yake gaya min in kula?

Fahad ya tashi.

“Muje ciki, akwai zafi.”

Maryam ta gyada kai.

Ta tashi suka nufi part dinsu,

Lokacin da ta juya, idonta ya sake sauka kan ƙofar, Fahad ya lura, Amma bai ce komai ba.

Sai ya yi murmushi kawai, seda ya zauna a parlor suka dan yi fira sannan ya wuche part dinshi, maryam tashi tayi ta shiga kitchen don ita kam abncin gargajiya takeso, ta girka tuwon Shinkafa da miyar taushe ai ko se qamshi ke tashi a kitchen din, tache ma cooks din su zuba a food warmers su aje mata dining sannan su zuba a wasu warmers su kaima mammi. 

Se Da dare, Zayd ya dawo.

Maryam tana zaune a parlour tana kallon wani movie.

“Salamu alaikum”

“Wa alaikas salam”

“Sannu da zuwa” ta karbi jakar

Ya zauna opposite ɗinta, “yawwa sannu ya gida”

“Alhamdulillah”

“Fahad yazo?”

Maryam ta kalle shi.

“Eh, a waje ma muka hadu se muka shigo tare”

“Me yakeso?”

“Ba komai ya leqo ne kawai.”

Zaid ya gyada kai, “yache min ze leqo yayi miki fira, na dauka yazo neman rigima ne”

Maryam tayi murmushi

Sai ya juya ya kalli TV.

“Me kike kallo?”

“Nothing serious.”

Ya kalli screen yaga anta fadah da halbe halbe

“It Looks serious though”

Maryam ta yi dariya, ta tashi ta hau sama ta bude dakin shi, sanyi da kuma qamshin turaren nan nashi suka shiga hancin ta, ta qarasa ta aje jakar kan coffee table, se taga dan Qaramin frame, shine a cikin hoton Yana kan doki da Kayan polo, yayi dariya har haqoran Shi sun fito, Maryam ta dade Tana kallon hoton a ranta take tunanin ashe da gaskiyar Safiyya, yanada kyau, ta sha’afa da kallon hoton har batasan ya shigo dakin ba, se ji tayi ya riqe hannunta yana murzawa, ta zabura da qarfi tana ambaton sunan Allah, yayi sauri ya riqeta don yaga alamar ta tsorata, a kunne ya rada mata “shhhh nine fah” ta sauke ajiyar zuciya tana qoqarin dawowa dd, yana nan riqe da hannunta, se ji tayi yache “Kinta kallon hotona ba gani ba? Kiyita kallona live ba se a hoto ba” maryam taji wata irin kunya kamar zata nutse, ta sauke kanta qasa ta rasa me zatayi se ji Tayi yache “yunwa nikeji, I’m famished” da sauri ta fara magana “akwai..akwaii..abbb..bbinccciiii a dinnnii…ng” a dabirce, ya kalleta yayi guntun murmushi “muje ki zuba min” sa sauri Tayi qoqarin fizge hannunta ta juya amma be saketa ba, tare suka sauka seda suka kai dinning ya saketa, ta dauko plate ta fara zuba mishi tuwo, ta kawo gabanshi ta ajiye, ta dauki container din da ta juye man shanu “insa maka man shanu?”

“Eh”

Ta zuba mishi itama ta zuba a wanda ta diba sannan ta zauna suka fara chi

Lomar farko zayd yaji wani irin daadi ya ratsa kan shi har cikin kunnuwa “wa Yayi tuwo?” 

Ta ansa “ni nayi” be sake chewa Komi ba amma be yadda ba, sanda ya dawo seda ya shiga part din mammi kuma tuwon ya tarar tana chi, kenan daga part din mammi aka aiko musu dashi nan, abnda be sani ba, maryam ita che ta aika ma mammi da tuwon, yachi tuwon sosai saboda ya yimishi daadi sannan ya sha drink din da ta hada na lemon da zuma, shima yakai mishi ko’ina, duk lemonade din da yakesha ai da sugar ake hada su, amma wannan da zuma ta hada, gaskiya Yayi mishi daadi, seda suka qare ta tattare kwanukan da suka bata ta kai kitchen, shi kuma ya koma parlor ya zauna

Shiru ya ratsa parlour, kafin Maryam ta kalle shi.

“Yaya?”

A zuciyar shi yache inna lillahi wa inna ilaihir raji’un, bari inyi hakuri in karbi sunan nan kawai tunda dai ni naje na auro yarinyar da na girma har shekaru 19 dole ai ta rinqa kirana yaya

“Naam?”

“In tambayeka?”

Ya kalle ta.

“Eh”

“A gidan nan…Ka saba da kowa?”

Zaid ya ɗan yi tunani.

“Wasu”

“Fahad fah?”

“Na saba dashi sosai”

“Hajiya Raliya fah?”

Ya yi shiru.

“Meyasa kike wa’innan tambayoyin?”

“Ba komi.”

Zayd ya kalle ta.

“Mahreeyam”

“Naam?” Ta ansa sunan na qara yimata daadi

“Kar kiyi judging din Mutanen gidan nan kan yadda suke mu’amalantar ki”

Ta kalle shi.

“Me kake nufi?”

“Ba komi, kawai kisa a ranki, zan kula dake in shaa Allah.”

Ta yi shiru.

Zayd ya tashi.

“Na gaji dayawa inaso in kwanta.”

“Seda safe, Allah ya huta gajiya”

Ya fara tafiya, Sai ya tsaya.

“Mahreeyam” 

Itakam duk sanda ze kira ta da wannan sunan se zuciyar ta tayi tsallen jin daadi “Naam?”

“Wannan qofar ta bayan garden…kar kije wurin pleaseeee”

Wannan karon muryarsa ba ta da tsauri.

Maryam ta lura kamar magiya yake mata”

Ba umarni yake bata ba, Kamar yana roƙonta ne.

Ta gyada kai.

“Okay In shaa Allah”

Zaid ya kalleta na ƴa seconds.

“Seda safe”

“Allah ya tashe mu lfya”

Ya hau sama

Maryam tana zauna ita kaɗai.

A karo na farko, ta fara tunanin wata sabuwar tambaya.

Idan babu komai cikin dakin… me yasa Zayd yake tsoron ta je can?

Ta ɗauki wayarta, Ta buɗe notes.

Ta rubuta:

Zayd yana boye min wani abu

Ta tsaya, Sai ta goge.

Ta sake rubuta:

Zayd yasan wani abu

Ta kalli kalmomin, Ta ajiye wayar.

Tana nan zaune parlor, yayin da gidan ya yi shiru, Maryam ta ji wani ƙaramin sauti daga bayan garden..

Kamar ƙarar ƙarfen ƙofa da aka buɗe.

Ta ɗago  kai.

Zuciyarta ta buga.

Ta sauka daga kan sofa, Ta tsaya tana sauraro.

Shiru.

Sai kuma—

clink..clink

Wani ƙaramin sautin ƙarfe.

Maryam ta kalli hanyar garden din ta cikin window, Ta yi taku ɗaya, Sai ta tsaya.

Ta tuna da muryar Zaid.

“Pleaseeee”

Ta tuna hajiya Raliya.

“Kar ki shiga abnda be dame ki ba”

Ta yi shiru.

Amma kafin ta koma ta zauna..

ta ga wani shadow ya wuce a bayan windown ta ta cikin garden ɗin

Maryam ta daskare, Ta kasa motsi.

Ta matso kusa da window ɗin.

Amma lokacin da ta leƙa…babu kowa.

Ta kalli hanyar da ze sadaka da ƙofar da ke can nesa, Sai ta sauke ajiyar zuciya.

Amma a wannan daren…

Maryam ta san wani guda abu ɗaya.

Tabbas Wani yana zuwa wajen ƙofar.

Kuma ko waye…ba ya son a san yana zuwa

Bazata iya chigaba da zama a parlor din ba don taji tsoro, Ta tashi ta hau stairs a tsorache ta nufi hanyar dakinta se kofar zaid ta bude don kamar yaji tana magana a qasa tana tambayar waye shiyasa ya bude ya gani, ai tana jin qarar budewar qofa ta zura a guje tana qoqarin bude dakinta, jikinta se rawa yake, zayd ya nufeta yana fadin “Subhanallah, lafiya?” Amma ina bata ma jin abnda yake fadi, fitillun saman da qasa duk a kashe suke bata ganin fuskar shi, hankalinta a tashe don ganin take kamar wanda taji motsin shi a garden ne ya biyo ta, har ya iso tana qoqarin bude qofa, tsabar tsoro ta mance da murda hannun zatayi se tura qofar kawai take a razane iya qarfin ta, tanata karanto adduar duk da tazo bakinta, zaid ya dafa hannuwanta da ke kan qofa ai ko ta saki wata irin qara seda duk gidan ya amsa, ya jawo ta da qarfi ya rungumeta a jikinshi, ya fara shafa bayanta yana karanta addua yana tofa mata a kai, jin qamshin turaren shi yasa ta gane shine, ta rage kukan tanata sauke ajiyar zuciya a hnkali amma idonta yanata zubar da hawaye, seda yaga ta dan natsu se ya dan dago ta a hnkali ya kalli fuskar ta da duk ta bachi da hawaye, fuskarta tayi ja, dan Qaramin bakinta Yayi pink, a ranshi yake fadin ita dai ko kuka take kyau yake mata

A fili ya tambayeta “lfya?” Ta kasa magana se nuna mishi qasa tayi, ya fara tunanin ko wani ya shigo ne don yaji Tana chewa “waye” shine ma dalilin fitowar shi daga daki, ya dan saketa “Ina zuwa bari inje in duba” ina maryam bata yadda da wannan zanchen ba, ta sake qanqame shi Tana girgiza kai se ya tallabeta kawai ya shiga dakinta da ita, ya zaunar da ita kan gado ya dan duqa a gabanta ya kama hannuwanta ya riqe, ya sake tambayar ta “me ya faru?” 

“Ina zune parlour nijji motsi a waje kuma nigga inuwa ta window, ina tambaya waye amma baa Ansa ba shine ina haurowa sama nijji ana bude qohwa” yanayin hausarta da yadda take magana a shagwabe yasa zaid duk ya shagala da kallonta gabadaya ta tafi da hnkalin shi, dakyar ya bude baki ya fara magana “inaga securities din gida ne daya ya zagaya, kinsan suna patrolling gidan da dare, yi hakuri tashi kiyi shirin baccee ki kwanta, ta riqeshi ta qarfi tana girgiza kai don har ga Allah a tsorace take, “yau ban iya kwana nidai cikin dakin ga” ta fadi a shagwabe hawaye suna gangaro mata, yasa hannun shi yana goge mata zuciyar shi na matsewa a kirjin shi “toh kizo muje dakina” ta girgiza kai da sauri wasu hawayen da sake saukowa, seda ya chije lips dinshi na qasa sannan ya ta tambayeta toh mi take so “ni kawai ka kaini wurin mammi in kwana a chan” sora kadan dariya ta kucce mishi, ya zaayi ya dauketa da wannan Daren yaje da ita wurin mammi Tana kuka haka? Ai se ache wani Abu Yayi mata, se dubara ta fado mishi “kinche kinji motsi a waje, nima fah inajin tsoro bazan iya fita ba, amma idan ina nan hnkalina a kwanche nasan baza’a iya bude qofa a shigo ba, in wurin mammi kikeso zan kirata a waya in che mata Gaki nan zuwa don a bude miki qofar part din, ni Kuma ynzu zan sauka in bude miki wannan qofar ki fita da sauri se in rufe, in kin fita ki sheqa da gudu kada ki juyo se kin shige kofar part din mammi” ai tun kafin ya kai qarshen maganar take girgiza kai hawaye na zubowa, ya miqe ze tashi ta riqe rigar shi gam, yana dariya qasa qasa ya tambayeta “zakizo dakina ki kwanta?” Da sauri ta gyada mishi kai

Toh ki chnja kaya zan jira ki a nan  “aa muje kawai zan kwanta a haka”, Yayi dariya “ai ina nan dakin ba fita zanyi ba” ta sake shi, ta dauko kayan baccee riga da wando maroon color ta nufi bathroom, seda ta juyo ya kalleshi Idonta duk hawaye sannan ta shiga toilet, da sauri ta chnja Kayan tayi brush ta fito yana nan tsaye a inda ta bashshi, “muje?” Ta gyada kai sannan ya nufi qofa, ya kai hannu ze bude qofar yaji ta riqeshi ta baya, Yayi Dariya ya bude kofar yana takawa a hnkali saboda yadda take riqe dashi, har suka shiga dakin shi, Yayi mata nuni da gadon “Hau ki kwanta” ta hau ta kwanta a takure ta matse jikinta wuri daya, ya dauko duvet ya rufeta sannan ya shiga toilet Yayi wanka Yayi arwallah ya fito, da ze shiga closet yana kallon yadda ta matse idanu wai ita a dole baccee take, Yayi dariya ya shiga ya saka Kayan baccee ya fesa turarukan shi ya hau carpet ya tayar da sallah, tun maryam na kallon shi yana sallah har baccin gaske ya kwashe ta, ya dade yana salloli sannan Yayi addu’o’i ya tashi ya nufi gado, ya chire rigar kayan baccee, daga shi se wandon kayan don baya iya baccee da Riga ko singlet che, sedai ya rufe jikinshi da duvet idan akwai sanyi, kayan baccee yana sawa ne da dare Yayi yan abubuwan da zeyi amma idan ze kwanta baccee se ya chire rigar, a hnkali ya hau kan gadon ya kwanta yana jin qamshin turarukan maryam suna cika hancinta shi, ya qura mata ido, hullar kanta ta zame fiye da rabi, gashin kanta duk ya fito, yasa hannu yanata shafa shi a hnkali, wani irin qamshi ke fitowa daga gashin shima, ya kalli fuskarta, ga hawaye sun bushe alamar tayi kuka kafin Tayi baccee, qasa qasa ya furtabatada wuyar yin kuka, ya Kalli dan Qaramin lips dinta yaga duk sun bushe, se ya sauka ya dauko Vaseline ya shafa mata a hnkali kan lips din, motsa lips din tayi a hnkali don taji kamar an taba, ya tsaya yanata kallonta yadda take motsa bakin duk ta gama kashe mishi jiki, kafin ya miqe yaje ya maida Vaseline din yazo ya sake kwanciya, ya miqa hannu ya kashe lamp din da ke kunne, dakin Yayi duhu amma akwai dan haske na security lights da ke shigowa ta window, yayi adduoin baccee ya shafa mata a fuska da kai a hnkali, se kawai ta matso ta rungume shi, zayd seda ya dauke wuta ta yan sakanni sannan ya kalleta yaga tana magana qasa qasa, ya matso da kunnenshi saitin bakinta se yaji tana chewa “mama safiya zata haifa muna baby, mama nima inason baby” yayi murmushi sosai yana kallon hannuwanta da ta rungume shi, a take zazzabin da ke damun shi ya fara sauko mishi a hnkali, yanason ya gyara kwanciyar shi amma kuma yadda take riqe dashi bayason ya tada ta, haka dai har baccee ya dauke shi yana shafa gashin ta a hnkali da dayan hannun shi yana shaqar qamshin jikinta, dayan hannun shi kuma yana murza hannunta da ta rungume shi


Follow this link to join my WhatsApp group: ***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol