Free chapter · Read without an account
Page 3
...FARAR TUMFAFIYA.
©UMMU AFFAN
Page *3*
Tana layi da jin ƙugi a cikin ta, ta miƙe tamkar za ta faɗi, da ƙyar ta iya ɗaga ƙaton zanin gadon, don har saman kafaɗarta sai da ta ɗaura shi, taje katangarsu da ƙyar ta iya ɗaurawa saman katangar bayan ta taka ƙaton turmin Iyah da take dakan magani na gargajiya da take sayarwa. Tun da ta ɗaura shi saman katangar ta sakko ta zauna gefe tana sauke numfarfashi tamkar wacce taci tseren gudu, da dafa bangon ma ta iya hawa don jirin ji take tamkar zai kayar da ita ƙasa, bayan ta sakko kuwa taji idanuwanta sun mata nauyi, ga wani duhu dumm! Da ya mamaye su, ta dafe kanta da ya fara mata ciwo lokaci guda.
Yaya Usman ne ya shugo, ganin halin da take ciki ya ƙarasa jikin katangar ya baza zanin gadon a jiki yadda zai samu iska da rana da kyau, bayan ya sakko daga turmin ya dube ta a karo na biyu.
"Tun da kin gama zaman me ki ke yi a nan?"
Ta ji shugowar mutum, har lokacin da taji an raɓa gefenta an gyara shanyar, sai dai ba tasan shi ba ne saai da taji muryarsa. Tayi ƙoƙarin buɗe idanuwan duk da nauyin da suka mata ta ce,
"Kai na ke ciwo, idanuwana ma duhu nake gani, ga yunwa ina ji, bazan iya tafiya ba."
Bai ce mata komi ba, ta ga ya yi gaba, tayi mamakin abinci ta ga ya kawo mata, sanin kanta ne da Andi tana kusa ba zata bari ba, duk da ba yawa sosai lokacin da ta kai hannu taji, amma hakan bai hana farin cikinta ɓoyuwa ba, nan ta fara ci hannu baka hannu kwarya. Shi kuma ɗaki ya wuce sai ga shi da magani da ruwa, yana dawowa har ta cinye tana suɗe hannu, lokacin da ta ɗago fuska sai ta ga idanuwan nata sun rage duhu da nauyi, ta amshi maganin da ya miƙa mata da ruwan tana sha, a hankali kuma ta furta.
"Na gode Yaya Usman!"
"Usman me ka ke yi a nan?"
Muryar Andi da yaji ne ya saka shi miƙewa da sauri, ita ma ta ƙaraso wurin tana ƙare musu kallo.
Da sauri Yaya Usman ya yi niyyar miƙewa domin ya bar gurin, sai yaji ƙafarsa ta riƙe masa ya kasa ko da motsawa, nan take kuma jikinsa ya fara rawa, "Usman lafiya? Mene ne kuma haka?" Kafin Andi ta ƙaraso gabansa jikinsa ya fara wata irin jijjiga kamar wanda ya taɓa soket ɗin wutar nepa bakinsa na zubda miyau.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Usmanu!"
Andi ta faɗa a gigice tana taɓa shi, nan take kuwa idanuwansa suka fara kakkafewa, ihu ta saka wanda ya sa Iyah da ke ciki ta fito haka Saudatu da ƙaninta Faruk, duka tsoro mai tsanani ya shiga jikinsu har ɓari yake ganin irin halin da Usman yake ciki.
Barirah tafi kowa shiga tashin hankali ganin a inda take wannan abin ya sami Usman, tuni ta fara kuka tana kama jikinta da ƙanƙame shi guri guda. Iyah na zuwa ta kama Usman suka mayar da shi ƙofar ɗakin Andi da ƙyar don Usman ya girma saurayi ne mai ji da ƙarfi don haka har da jan sa suka yi suka samu aka koma inuwa da shi, nan Iyah ta fara ba shi taimakon gaggawa. Andi kuwa cikin kukan kura ta shaƙe wuyan Barirah ta fara bugu, ji ka ke gum ta haɗata da bango, nan take kuwa gafen goshinta ya fashe ya fara jini, ta fashe da kuka tana kama wurin tana girgiza kai.
"Shegiya algumguma, baƙar kumurci mai saran na dawa da na gari. Allah wadaran halinki Barirah, baƙar fura kowa ya shaki sai ya yi amai. Usman duk tausaya mikin da yake sai da ki ka cutar da shi makira mai baƙin hali,, to wallahi ki sani idan ki ka kashe mini Usmanu ke ma sai kin baƙunci lahira wallahi Allah ba zai tafi shi kaɗai ba!"
Duk cikin maganarsu ta Sokkwatawa take maganar cikin tashin hankali da kiɗima, don tana da yaƙinin Barirah ce tayi wa Usman wani mugun abin, zuwa can kuma kamar mai tsuma ganin yadda jikin Usman ɗin yaƙi daina jijjiga duk da maganin da Iyah ke ba shi da sauri ta kuma wawuro Barirah taci gaba da bugu, wacce ke kuka da neman ɗauki amma cikin Iyah ko Saudatu babu ma wanda ya kalli inda suke, ballantana ta sakaran za a kwace ta, daman Iyah ce ta saba katsalandar har ta ceto ta idan Andi tana bugunta, da alama ita ma yau an kaita munzalin da za tayi watsi da ita, don ko juyowa ba tayi ba balle har ta sakaran za ta taimaka mata, hakan ya sa ta ƙara duƙewa tana sakin ɗan marayan kuka lokacin da Andi ta kai mata wani bugu a ciki, ta saki wata furgitacciyar ƙara, daidai da Usman ya yi wata ƙara da ta saka Andi komawa inda suke da sauri. Da ace ta lura da kyau da zata ga yadda wani hayaƙi ke fitowa daga idanuwansa da suka fara kakkafewa, amma tsabar tsoron da take ciki ba ta ankara ba sai ta shige ɗaki ta ɗauko wayarta tare da kiran Kawu Balarabe cikin kuka take sanar da shi ya dawo gida Barirah za ta kashe Usman, ga shi nan a kwance idanuwansa suna kakkafewa.
Kawu Balarabe da ke Office, ma'aikacin gwamnati ne a kamfanin inshura, da sauri ya miƙe cikin tashin hankali yake tambayarta me ke faruwa, amma jin Usman ya kuma wata ƙara ta saki wayar ta fito cikin tsananin tashin hankali.
"Na shiga uku!"
Andi ta furta tana ƙara sakin ɗan marayan kuka tare da zubewa kusa da Usman tana kama shi tana kuka, shi kuwa sai wata irin miƙa yake idanuwansa suna kakkafewa har wasu tururi ne ke fita ta cikinsu ga jikinsa yana wata irin zabura.
Barirah tsaye gefe da fasasshen goshi jingine take jikin bango, don muddin ta ce za ta tsaya tasan faɗuwa za tayi cikinta idan ban da ciwo babu abin da yake mata sakamakon naushin da tasha, sosai take kuka, ba kukan ciwon jikinta ba sai kukan halin da Yaya Usman ya tsinci kansa a lokaci guda haka, ta sani duk cikinsu shi ne yafi kowa tausaya mata duk da idan tayi masa zai dake ta amma yafi kowa ƙaunarta da tausayinta, tana ƙaunarsa ko ba komi yana kula ta da aikenta duk da yasan asara aiken ke kawo masa, amma yana gwadawa ne a cewarsa idan ana gwada aikenta ƙilan akwai ranar da za tazo da daina jawo wa kowa asara, tana girgiza kai tana kuka da addu'ar Allah ya ba shi lafiya a zuciyarta.
Kusan mintuna ashirin kenan da kiran da Andi tayiwa Kawu Balarabe sai ga shi ya shugo gidan a matuƙar furgice, Yaya Aliyu na bin bayan shi don kusan tare suka yi kiciɓis a ƙofar gate ɗin shugowa, don Andi na ajiye wayar ya kira shi cewa su haɗu gida ance babu lafiya.
Dukansu sunji tsoron halin da suka iske Yaya Usman a ciki, Aliyu cikin tashin hankali ya ce, "To zaman me ma ake yi a gida ne da ba za a kai shi asibiti ba?" Da sauri ya ƙarasa ya saɓa Usman a bayan shi, Kawu ya taimaka masa wajen riƙe masa ƙafafuwa suka yi wajen gidan inda Kawu ya bar motarsa suka shiga da shi ciki. Andi tayi saurin ɗauko mayafinta za tabi bayansu Iyah ta ce,
"Da kin zauna gida ni sai na bi su!"
"A'a, ko na zauna hankalina ba zai kwanta ba gara naje kawai."
Ta ƙarashe maganar tana bin bayansu, Saudatu da Faruk kuka kawai suke, haka Barirah da ke gefe gabaɗaya a tsorace take ga wani irin kukan da take yi na tsananin damuwa da rashin sanin makomarta a gidan.
Kawu Balarabe bai tsaya a ko ina ba sai Asibitin Murtala da ke kusa da unguwar tasu, an tarbe su cikin gaggawa ganin halin da Usman yake ciki, sai dai abin mamaki duk binciken da likitocin suka yi babu abin da suka gani da ke damun Usman, hakan ya sa suka jona masa ƙarin ruwa suka fito daga ɗakin, likitan ya ce Kawu Balarabe ya same shi a ofishi, nan yake ma sa bayanin babu abin da na'ura ta nuna musu akan ciwon, sun yi iya yinsu idan jikin babu sauƙi sai dai ko za a canza mishi asibiti ne a gani ko za a dace.
Hankali tashe Kawun yake yiwa su Andi bayani, wacce tun kafin ya sauke aya ta fashe da kuka tana faɗin.
"Na shiga uku, Barirah da abin da zaki sakawa Usman kenan? Wallahi mayya ce ita ce ta lashe masa kurwa kuma bazan bari ba, gara ma mu koma gida ta tsallaka shi sau uku shine zai sami lafiya."
Yaya Aliyu ya girgiza kai yana cewa Andi tayi shuru amma sai kururuwa take a asibitin, mutane har sun fara kallonta, yayin da wasu suka ɗauka ko mutu aka yi mata ne da take kuka haka, wasu har haƙuri suka fara ba ta da faɗin.
,"Ko wanne mai rai mamaci ne ayi haƙuri ba kuka yake buƙata ba sai addu'a."
Wannan maganar da taji ne ya sakata yin shuru don dole, don ta fara rayawa kar a amshi addu'ar mutanen yaronta ya mutu, duka suka shige ɗakin da aka kwantar da Usman, wanda har lokacin bai bar girgiza ba, a cewar nurse ɗin da ke wurin da abin ya yi sauƙi, amma shugowarmu ɗakin ya ƙara assassa jijjigar ta shi har yana gotar da ƙarin ruwan da ake masa, nan take kuwa hannun ya fara jini, da sauri nurse ɗin ta cire allurar kawai tare da fita kiran likitan.
Andi ta ƙarasa gaban gadon tana kuka sosai, ta dubi Kawu Balarabe ta ce,
"Kana gani fa, kana ganin halin da Usmanu na yake ciki, shin taya Barirah za ta zamo alkhairi a gare mu kamar yadda mutanen ƙauye suka faɗa? Wallahi sharri ce kuma ni bazan cigaba da riƙon mayya ba, ko ta sakar mini kurwar ɗa ko ayi kan mai uwa dawabi, wallahi sai dai ita da shi su mutu!"
Ta ƙarashe da sakin gunjin kuka na tsantsar baƙin ciki.
Kawu Balarabe ya kasa magana, shi kansa yana cikin tsantsar damuwa, girgiza kansa kawai yake kana kallonsa kasan baya cikin natsuwarsa, Iyah wacce ke tsaye gefe tun shugowarsu tana kallon Usman cike da damuwa, shi ɗin yaron ɗakinta ne tafi shaƙuwa da shi fiye da kowa a gidan, daga shi sai Barirah. Ta rausayar da kai cike da tausayi ta furta.
"Sannu Usman, yanayin abin a tausaya gaskiya wannan kam da wata a ƙasa."
"Da wata a ƙasa mana, ai Sabuwa kina ganin abin nan kasan shafar mayu ne, ido ba mudu ba ai yasan kima."
Cewar Andi tana kallon Iyah wacce sunanta na asali Sabuwa ne.
Kusan awarsu huɗe a asibitin tun ɗaya har biyar na yamma abin na Usman maimakon sauƙi sai gaba yake yi, Yaya Aliyu ya fara masifa akan likitoci basu san aikinsu ba, taya majinyaci kamar Usman amma sun kasa yi mishi magani da ko sassauci zai kasa samu, su kam sun yi bakin ƙoƙarinsu ganin abin na shi ba na wasa ba ne dole ƙanwar naƙi suka rubuta takarda cewa a kai shi wani asibitin. Hankalin Andi fa ya ƙara tashi gani take shikenan Usman kuma mutuwa zai yi, ba shiri ta wanke ido tar ta ce ita atafau fa su koma gida, babu wacce za ta iya maganin matsalar Usman sai Barirah, tun da ita ce ummul aba'isin duk wani abu da yake yi, Kawu Balarabe bai musa ba ya karya mota zuwa gida duk da Aliyu ba haka yaso ba, don yana ta faɗin Barirah ba ta isa tayi komi ga Usman ba sai abin da Allah ya rubuto, to akan me ma za ta aikatawa Usman hakan? Bayan su kansu shaida ne tafi shaƙuwa da Usman ɗin a cikinsu.
"Aliyu kayi shuru kawai, ni nasan abin da kai baka sani ba, komi kuma aka ce Barirah ta aikata bazan iya musawa ba, domin ɗan gado ai yafi taka haye!"
Jin abin da Kawu Balarabe ya ce dole Aliyu ya yi shuru, amma zuciyarsa zafi take masa, duk da ya tsani Barirah ko son ganinta ba ya yi saboda mugun halinta na asara komi ta taɓa ya zama asararre hakan ne ya ƙara sakawa yaji ya tsane ta, amma kuma tsanar da yake ba ta baya nufin ya zalumce ta, shi dai baya tunanin ita ce za ta aikata hakan akan Usman shi shaida ne akan yadda shaƙuwarsu take ita da shi.
Yana wannan tunanin har suka iso gida saboda a unguwarsu Nakasari asibitin Murtalan yake, hakan ya sa mintoci kaɗan suka iso ƙofar gate ɗin gidan. Aliyu ne ya fita ya buɗe gate ɗin Kawu ya shugo da motar ciki. Tun kafin ya gama parking Andi ta fice har tana kusan faɗuwa ta shige ciki.
Barirah.
Tun da su Kawu suka fice da Usman ranga-ranga su Iyah suka ta ke musu baya take kuka, ta koma gurin da ta gama wanki ta rakume jikin katangar tun tana kuka da hawaye har ya zamana hawayen ya daina zuba, ko motsi kaɗan taji sai ta furgita ta miƙe zumbur, ko ta kama duk abin da ke gefenta, gabaɗaya ta fita a hayyacinta, ga ciwon kanta ya ƙara tsananta sosai, Saudatu kuwa zaginta kawai take tare da aibata ta.
"Muguwa in sha Allahu ke ce zaki mutu ba Yaya Usman ba, me ake da azzaluma kamar ke? Gara ma ki mutu mu huta da zamanki cikinmu."
Ba ta iya magana sai dai ta ɗago ta kalli Saudatun ta mayar da kai ƙasa, sai taji kan nata tamkar zai sakko tsabar ciwo, dole tayi sama da kan don ta samu sassauci, haka Saudatu ta dunga guma mata baƙaƙen maganganu. Tayi kuka tayi takaici ita ma ba son ranta ba ne da tazo a hakan! Shin mutum ya isa ya sauya ƙaddararsa ne? Da a ce ana sauyawa da tuni ta sauya ko don 'yan'uwanta su kalleta tamkar su, Kawu Balarabe ya riƙeta kamar yadda Saudatu take a gurinsa, haka Andi ta ƙaunace ta tamkar yadda take ƙaunar Saudatu, sai dai ba ta isa ta sauya hakan ba, ba ta isa ta gyara kuskuren da ba nata ba.
Tun kafin mu fahimci kanmu, muna rayuwa ne ƙarƙashin inuwar wasu mutane masu daraja a garemu. Iyayenmu sukan zama hasken farko da ke nuna mana hanyar rayuwa, su kan share mana hawaye kafin ma mu koyi dalilin kukan, yayin da soyayyarsu a gare mu ba ta da misali su dai suna ƙaunarmu a duk yadda muka zo ba tare da nuna wariya ba. Ko bayan mun girma, akwai wasu lokutan da zuciyarmu kan koma kamar ta ƙaramin yaro idan muka tuna da irin kulawar da suka mana, sai dai shekaru ba sa tsayawa, lokaci yana tafiya da komai nasa, yayin da mutum ke ƙara girma, haka rayuwa ke ƙara nuna masa fuska daban-daban. Akwai ranar farin ciki da zata saka ka manta duk wata damuwa, akwai kuma ranar baƙin ciki da zata koya maka darasin da babu makarantar da zata iya koya maka shi, daga nan ne mutum ke gane cewa rayuwa ba wai kawai numfashi ba ce jarabawa ce mai cike da zaɓi tsakanin daidai da kuskure.
Da aka kira sallar azahar ta tashi za ta ɗauki buta Saudatu ta dire gabanta cikin tsantsar rashin mutumci.
"Wallahi ba zaki yi amfani da butar nan ba, tun da ba ta ubanki ba ce azzaluma mai rama sharri da alherin da aka miki."
Babu ja Barirah ta sakar mata butar, harabar gidan ta koma inda Kawu ke ajiye motarsa akwai fanfo ta wajen, ko da tayi wanki anan take zuwa ta zuba ruwa, ganin ba kowa ta duƙa a wurin tayi fitsari tare da tsarki sannan a wurin dai tayi alwalarta ta jikin fanfon, ta koma ciki sai ta shiga ɗakin Iyah, tasan dai nan ne kawai Saudatu ba za ta iya hanata shiga ba, ta zura hijabi tayi sallah, a wurin ta ɓungure wani wahalallan barci ya yi awon gaba da ita.
Misalin uku ta tashi, sai taji cowon kan naya ya yi sauki sosai, daman kuma haka take idan kanta na ciwo muddin ta samu barci to zai sauka ko ba duka ba idan tayi barci tana samun sauƙi, ta dunga hamma don ba ƙarya yunwa take ji, abincin da Yaya Usman ya kawo mata ɗazun duka bai fi loma biyar ba, sai dai tunowa da halin da Yaya Usman ɗin yake ne ya saka ta sakin kuka, lokaci guda kuma ta fito daga ɗakin cike da tunanin ko sun dawo yanzu, amma ba kowa sai Saudatu da Faruk zaune tsakar gidan suna cin Indomie, da alama ita ta dafa musu a kwano ɗaya suke ci har da dafaffen kwai, Barirah ta haɗiye wani miyau lokaci guda taji yunwarta ta dawo musamman da ta ga sunaci ga shi har da kayan miya da albasa a ciki, da alama tayi haɗi mai kyau da za ta dafa ta.
Miyun da Barirah ta haɗiye a idanuwan Sauudatu, tayi wani murmushi na takaici ta ƙeta ta ce,
"Mayya kawai, wallahi ni da Faruk mun fi ƙarfinki, sannan ki sani ko zaki mutu kin bar cin abincin nan, mayya kawai."
Barirah ta sauke kai ƙasa tana jin wani ƙunci na sake jiyartarta, ta tsani wannan kalmar ta maita da suke alaƙantata da ita, shin me zai sa suna kiranta da mayya? Ba ta da amsa duk da ita a gurinta tasan ba mayyar ba ce amma ba zata ce ga dalilin da ya sa su suke ganin kamar tana cin mutane ba.
Gefe ta samu ta zauna tana ta haɗiyar yawu, har Saudatu ta miƙe ta shige ciki, sai Faruk da ta barwa sauran shima ya tashi yana harararta ya fice daga gidan, da sauri ta ƙarasa wurin tunkiyar da ta dafa ba komi ciki sai ƙanzo, ragowar da suka bari ta ɗauka tana sauri ta cinye sannan ta kankare ƙanzon tukunyar ta cinye, da gudu ta ƙarasa wajen fanfo ta tulawa cikinta ruwa sai taji ta samu dama har da sakin gyaza, ta kuma yin alwala ganin an kusa kiran sallah ta koma ɗakin Iyah.
Motsin da taji a bedroom ɗin Iyah ne ya saka ta ɗanyin shuru, sai ta kuma jin motsin na ƙaruwa da sauri ta miƙe ta shiga ɗakin, saitin durowarta motsin ke fitowa, don da farko tayi tunanin ko ɓera ne duk da kuma gidan ba su cika samun ɓera ba don Kawu Balarabe na sayo magani suna sakawa don baya son ɓera ko kaɗan, ta ƙarasa har ta taɓa durowar sai taji muryar Saudatu a kanta.
"Sata zaki yi mata ne? Ki bar parlour ki shugo mata har Bedroom?"
Da sauri ta sauke hannunta ƙasa duk da har lokacin tana jin wannan sautin haka ta koma parlour ganin Saudatun ta juya tana jan tsaki, tana fitowa ta tada sallar da aka tayar yanzu a masallacin unguwarsu.
Bayan ta idar ta fito waje, wankin da tayi ne ta fara kwashe duk waɗanda suka bushe, wandunan Yaya Aliyu ne tasan wuni suke a igiya da katanga saboda nauyinsu, ta koma parlourn Andi ta nunke su tsaf, ta ɗauki tsintsiya ta fara sharar gidan, duk wasu abin kaye-kaye ta kauda, bayan ta gama ta zauna tana hutawa, jin ƙarar an buɗe ƙofar gate mota ta shugo gabanta ya faɗi, addu'a take Allah ya sa Yaya Usman ya sami lafiya ya faɗa musu ba ita ce tayi masa wani abu ba ko sa daina kallonta a muguwa kuma mayya, sai dai kafin ta yunƙura sai taji saukar dukan Andi jikinta ta ko ina, daman a furgice take kuma babu zato taji dukan lokaci guda ta miƙe tsaye tana ihu taci karo da bango don ko gani ba ta yi sosai, ai kuwa ta cake da wata ƙusa take goshinta ya fashe ta saki wani kukan azaba....
***
Tallah.
Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.
Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.