Free chapter · Read without an account
Page 4
...FARAR TUMFAFIYA.
©UMMU AFFAN
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement? Ta na sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci, sannan tana garin Kaduna haka tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar WhatsApp kamar haka *** kar ku man ce sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kun zo.
Page *4*
DK.
Ya zauna daɓaras a gefen katifarsa yana tamke da kumatu, wannan tafiyar fa dole ya yi ta, bai taɓa saka rai da samun abu ba kuma ya gagara neman duk hanyar da zai bi ba, ya sauke numfashi lokacin da ya tuno wani abokinsu Faisal da suka yi karatu tare, kwanaki Mansoor ke faɗa masa sun haɗu da Faisal lokacin da yaje amsar bizar Daddynsu da zai je US inda ake duba lafiyarsa, idan bai mance ba ya faɗa masa a wurin yake aiki har ma ya ba shi lambarsa ya ce ya kira shi su gaisa don ya faɗa masa zai ba shi tashi shi ma ya ba shi ta Sadaukin, ai kuwa bai kira sa ba bayan kwana biyu da maganarsu da Mansoor sai ga Faisal ya kira shi a waya, nan suka gaisa sosai har ya yi saving lambar. Tuna hakan da sauri ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga neman lambar Faisal, cikin sa a kuwa ya ganta nan take ya danna mata kira.
Ringing huɗu Faisal ya ɗauka, tun kafin ma Sadauki ya yi magana ya rigashi.
"Abokina DK kana nan ba ka zuminci ko?"
Sadauki ya sauke numfashi tare da yi ma shi sallama, bayan sun gaisa ne ya fara maganar dalilin kiran nasa.
"Faisal biza nake nema ta China! Naji labarin da 5m za a iya zuwa can ɗin ba tare da wata wahala ba, yanzun bayan kuɗin me ya kamata na nema kasan ba taɓa zuwa nayi ba."
Faisal ya yi dariya yana jiyo sautinta ta cikin wayar kafin ya ce,
"DK kana wuta fa, ba dai aiki ka samu a can ba? Ko kuwa da amaryarmu za a je cin amarci ne don na sani dai baka kwanka sai da zakara?"
Sadauki ya ɗan shaƙa jin kuma jihar da ya koma a zancen.
"A'a ko ɗaya, aikin dai muke so ya samu, kana ganin me zan kawo kafin tabbatuwar biza ta?"
Ya ƙarashe da sake jefa masa tambayar da ya yi masa tun farko bai amsa mashi ba.
"Da farko dai za ka sanar da manufarka ta tafiyar wato, ziyara ne (yawon buɗe ido ko ziyartar dangi/abokai) kasuwanci ne, karatu ko aiki ne, Sai ka tanaji fasfo, hotunan fasfo, fom ɗin neman biza. Sai ka nemi biza ta hanyar ofishin jakadancin China ko cibiyar karɓar buƙatun biza da aka amince da ita, za ka gabatar da takardunka, biyan kuɗin biza, sannan ka jira sakamako."
Sadauki ya cika baki da iska ya fesar kafin ya furta, "Na gode Faisal, idan ina son wani ƙarin bayanin daga baya zaka ji ni."
Haka suka yi sallama ya ajiye wayar jiki a saɓule, tabbas da aiki gabansa, amma abiun da yafi ci masa tuwo a ƙwarya bai wuce kuɗin tafiyar nan ba, idan ya sami kuɗin sauran duk masu sauƙi ne a gurinsa.
Yaji kamar ya kira Mansoor don ya sani duk faɗin Sokoto da kewaye ba shi da gatan da ya wuce shi ɗin, shi ne dai zai iya taimakonsa a ko wanne irin hali yake ciki, amma kuma ɗazun ba su ƙareta ta daɗi ba, amma yasan laifinsa ne na rashin haƙuri. Ya kwanta rigingine a Katifar idanuwansa a sama yana kalllon kwanon ɗakinsa da ko arziƙin silif babu, kafin ya lumshe su a hankali wasu siraran hawaye suka biyo gefen idanuwansa, haka ya dinga sauke numfashi tun yanayi da sauri har ya dawo sauka a hankali, a hakan barci ne ya kwashe shi na kusan mintuna arba'in kafin ya farka, tashi ya yi yana miƙa yaje ya buɗe ƙofarshi, ko gidan bai shiga ba ya fice masallaci, har lokacin Sadiya na suyar dankalinta don wuni take a wurin tun safe sai gab da magriba take tashi babu arabi babu boko, ganin yadda ta zuba mashi ido tun fitowarsa ya kau da fuska tare da ƙarashan kunu kamar kullum dai yadda fuskarsa take.
Sadiya.
Tunda ya fito take kallonsa ga uban layi don ba ƙaramin ciniki take ba, amma hakan bai hana ta zuba masa ido har ya wuce ba, jin hayaniya a kanta ta dawo hayyacinta da sauri.
Wani murmushi ta saki har ga Allah tana ƙaunar Sadauki za ta so tayi rayuwar aure da shi amma ta sani abu ne mai wahalar gaske duba da yadda shi Sadaukin ke shaɓuratun ɓangaro da ita, ita dai a duk yadda yake ƙaunarsa kawai take ita dai.
Sai gab da magriba ta kammala komi, almajiranta suka kai mata komi gida kamar kullum, ita kuma a lokacin ne Alhaji Bashar ya iso inda take suyar, hakan ya sa a motarsa ya ƙarasa da ita gida, kallonta yake cikin kalamai irin na mayaudara.
"Sadiya ban san me ya sa har yanzu ki ka kasa bani dama ba, da gaske ina jinki sosai a cikin jini na, kusan wata biyu kenan da haɗuwata da yake ya kamata ki bani dama."
Ya faɗa yana kamo hannuwanta cikin nasa yana wani latsawa cikin wani murnushi na tsantsar yaudara, a hankali cikin dubara ta zame hannun nasa daga nata ta ce,
"Alhaji ba haka ba ne!"
"Haka ne mana Sadiya, ina so ki sani dama kaɗan zaki bani ki ga yadda zan mayar da rayuwarki abar kwatance a cikin ƙawayenki, ke hatta 'yan unguwarku sai sun shaida ke ta musammance a cikinsu."
Ta lumshe ido a hankali ta buɗe su a fuskar Alhaji Bashar da ya sakar mata wani murmushi irin nasu na cikakkun 'yan duniya, mutumin nan tasan zai yi sa'an mahaifinta idan ma bai girme shi ba, amma yazo yana kashe 'yar cikin sa da kalaman yaudara, ita dai tun haɗuwarsu yake kashe mata manyan kuɗaɗen da har mamakinsa take don ba ta taɓa amsa masa cewa tana son shi ba, haka mahaifiyarta tana matuƙar ƙaunar Alhaji Bashar don ya gama saye su daga ita har Babanta mai matacciyar zuciya, don ba shi da aikin fari balle na baƙi sai zaman majalisa da gulmar matan mutane, sana'ar dankalin da Sadiya ke suya da shi suke ci suke sha a gidansu, ita ce babba a 'ya'yan Babanta da Mahaifiyarsu kuma a haka ƙannanta tara a gidan, yanzu haka Mamarsu na da cikin na goman kuma duka mamar tasu ta haife su su goma da cikin na sha ɗaya. Haihuwar ake kawai kara zube babu abin ɗaukar nauyinsu don dukansu babu arabi ba boko sai yawon talla lungu da saƙo, haka a gidan haya ma suke zaune, don kusan mutane goma ne a gidan ko wacce mata da nata tulin 'ya'yan.
"Kin yi shuru Sadiyata!"
Maganar da Alhaji Bashar ya mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, ta sake lumshe ido jin yadda Alhaji Bashar ya jawota jikinsa, ko ƙaurin suyar dankali da take bai dame shi ba duk da shi nashi jikin ƙamshin turare kawai ke tashi, a hankali ta zame jikinta daga nashi ta ce,
"Alhaji ni zan shiga gida."
"Haba Sadiyata ki bari na ɗan samu natsu a jikinki ko kaɗan ne mana! Na sha faɗa miki kizo gidan hutuna amma ki ka ƙi zuwa kullum cikin nacin hakan nake miki amma kin ƙi, kin san kuwa yarda nake jinki? Wallahi Sadiya komi zan iya miki idan ki ka ba ni haɗin kai, hatta gida zan sayawa iyayenki ku bar unguwar yaku bayin nan."
Ruwan hawaye ne suka taru a idanuwanta ba ta ce komi ba, buɗe wani marfi ya yi a gaban motar ya ciro kuɗi dami ɗaya 'yan dubu-dubu, ya jawo hannunta ya danƙa mata kuɗin.
"Amshi wannan, yanzun ki shiga ciki ki sake tunani akan maganata, ke har ƙasar nan zan iya fita dake idan kin amince, duniyarki zata dawo sabuwa."
Hawayen da suka taru mata suna suɗaɗo a hankali daidai lokacin da ya buɗe mata murfin motar ta fice, yabi bayanta da kallo yana murmushi, tabbas zai iya komi domin ya samu yarinyar nan, ya lumshe ido lokacin da ya tuna yadda bokan tsafinsa ya nuna masa hoton Sadiya a kwaryarsa da tabbatar masa ya yi duk mai yuwuwa domin ya mallaki Sadiya ba tare da aure ba, yin hakan ne kawai zai saka kasuwancinsa da danne abokan hamayyarsa yaci gaba da tarisantuwa, haka dukiyarsa taci gaba da samuwa ba kakkautawa, ya girgiza kai da duban layin, idan ba don wannan ba me zai kawo shi unguwar talakawa haka? Shi da ko a ƙasar nan bai cika rayuwa ba idan baya Abuja to yana London ko Dubai. Da wannan tunanin yaja motarsa ya bar shiyar.
Sadiya kuwa bayan ta tsallaka kwatar ƙofar gidansu da ta fito tun daga cikin gidan, ga shi gurin ba wai damina ba ko Rani da kaka ake gurin baya rabi da ruwa da chaɓali, ta shiga ƙofarsu do ko arziƙin ƙofa babu, kana shiga ɗakunan gidan zasu yo maka sallama a jajjere yaran da ke gidan kuwa sun fi ɗari yara da manya samari da 'yan mata, ga iyayensu gidan gamin gambiza kenan don gabaɗaya shiyar ba gida mai yawan wannan, shi ya sa suke cewa gidan gamin gambiza da ance to nan za a kawo ka. Ɗakinsu shi ne ɗaki na uku a gidan falle ɗaya ne amma yana da faɗi haka ko wanne ɗaki yake a gidan kuma ko wacce da yaranta haka suke gwamitsa masu yara maza ne manya suka haɗa kuɗi suka kama musu ɗaki ɗaya to sai a haɗa kuɗi a biya duk shekara. Itakam ɗakinsu ita ce babba ƙannanta masu bi mata uku maza ne, su ma tuni aka haɗa da su a ɗakin samarin gidan. Gado ne ɗaya mai faɗi a ɗakin nasu sai ƙatuwar katifarsu da ta gama lalacewa a ƙasa daga lungu inda ita da ƙannanta sauran suke kwanciya Hauwa mahaifiyarsu da Babawo mahaifinsu kuma a saman gadon, tun usuli Babawo ba shi da wata kwakkwarar sana'a sai buga-buga da bin benci yana shan sigari, a haka ake har yanzu sai zaman ɗimama benci mace ke ciyar da gida tunda ita ke ɗaurawa yaranta Sana'a, Ko ace 'yarta, don duka maza take haihuwa, Sadiya ce mace sai ƙannanta biyu mata kuma ƙananu ne maza bakwai Allah ya ba ta mata uku sai cikin jikinta kuma ba a san mace ko namijin za a samu ba tukun.
Sai da ta share fuskarta don kar Hauwa ta ga hawayenta ta shiga cikin ɗakin, tun kafin ta zauna Hauwa ta buga shewa,
" 'Yar gudaliyata mai abin ban sha'awa, da ka haifi gwamna gara matar gwamnan!"
Kirarin da Hauwa ke mata kenan, duk ranar da take cikin farin ciki ko idan Sadiya ta dawo suya, don gaba ɗaya gidan babu mai kan sa'a kamar Sadiyan shi ya sa take alfahari da 'yar ta tare da cusawa matan gidan baƙar magana akan farin jini da kuma sa'ar Sadiyalle ko 'Yar gudaliyar tata. Murmushin yaƙe Sadiya tayi tana kallon mahaifiyar tata da indai fagen son abin duniya ne ba ta da tsara.
"Ai Hafizu da gudu yazo yake sanar mini Alhaji Bashar ne ya kawo ki gida!"
Jin Hauwa ta ce hakan ne ya sa ta gano inda farin cikin da take ciki ya samo asali, don tasan irin alkhairin da yake yiwa Sadiya, ai kuwa kuɗin da ya ba ta ta fara danƙawa Hauwa nan take ta ɗaga hannu ta rangaɗa buɗa.
"Ayiriyiri!!"
Tana juya kuɗin da a ƙalla na dubu ɗari ne tana sake sakin sabon murmushi mai tafe da farin ciki da annashuwa.
"Oh ni Hauwa, Allah ya kashe ya ba mu, shekarar fitarmu daga talauci ta kama Sadiya, gara in fara tari mu samu ki samu a bin arziƙi kema don na lura Alhajin nan da gaske yake."
Ita dai ba ta ce komi ba ta kwanto kwagirin kuɗin cinikin Dankali ta ajiye mata daidai shugowar Babawo, da sauri kuwa ya ƙaraso har yana ɓari da kwanukan tsakar ɗakin wanda da alama su Hafizu ne suka ci abinci suka bar su gurin, baƙar ƙazanta irin ta Hauwa kuwa ba zai bari ta ɗauke ba, sai yanzu da Sadiyan ta shugo zata tattare su.
"Hauwa, fitowarmu masallaci aka ce mini yanzu motar Alhajin nan ta fice a ƙofar gidan nan, nasan Sadiya ya kawo ban mukashe, kai haihuwar 'ya mace mai rana."
Cewar Babawo cikin ɓarin jiki kamar zai faɗawa Hauwa da ke zaune da tsohon cikinta. Hauwa kam daman da sauri ta cusa kuɗin cikin zaninta tun lokacin da Babawo ya ɗaga labulen ƙofar ɗakin.
"Gaskiya sai dai idan idon magulmata ne suka gano maka ƙarya, Sadiya dai gata nan yanzun ta shugo gidan daga suya."
"Ke Hauwa ni zaki yiwa ƙarya? Wallahi naso mu gaisa nima na kwashi rabona amma fa yanzun ma ba ta ɓaci ba sai kin ba ni wani abu."
"In ba ka me?"
"Arziƙin da aka samu na jikin 'yata, in ce ba ke ɗaya ki ka haife ta ba?"
"Mu biyu ne da kai, amma me ka sani akanta cinta shanta karatu ko suturarta?"
"Ko me zaki ce yasin sai kin ba ni rabona, yo tsuntsu daga sama gasasshe."
Hauwa na ƙunƙunai ta zaro dubu biyu a kuɗin suyar dankali ta miƙa masa, ya dubi kuɗin a raine sai kuma ya saka aljihu yana faɗin.
"Raba mugu da makami ibada ko sigari nasha yafi na bar miki su."
Hauwa taja tsuka tana kauda fuska gefe, Sadiya ta miƙe tsam ta fice daga ɗakin don tasan ba abin kunyarsu ba ne su fara faɗan nasu da suka saba a gabanta ba, don Babawo ya kaiwa Hauwa bugu da cikin nan ba abin kunyarsa ba ne, ita kuma ko zai kashe ta bakinta ba zai mutu ba..
Barirah.
Iyah da ta biyo bayan Andi da gudu ce tayi saurin shiga tsakaninsu tana kama hannun Barirah don daman ta sani komi zai iya faruwa idan ta shugo, shi ya sa ma tayi azamar biyo bayan nata.
"Haba Rakiya, idan tunani ya gushe ai hankali ke nemo shi, shin baki da tawakkali ne? Ko kuwa ke kin yarda Barirah za ta iya aikata miki komi bayan kin san babu wani mutum da zai iya aikata maka wani abu wanda daman can Allah bai ƙadarto maka shi ba."
Iyah ta dire jawabanta daidai shugowarsu Yaya Aliyu da Kawu Balarabe rungume da Yaya Usman yana ci gaba da jijjiga tamkar dai yadda suka fita da shi ɗazun, ganin hakan kuwa hankalin Barirah ya ƙara tashi ta kuma sakin kuka mai ban tausayi, Saudatu tuni ta fito tun jin kukan Barirah da hargagin maganar Andi, ai ganin yadda aka shugo da Usman zuciyar Andi ta ƙara tsinkewa ta rarumo wani katako da Barirah ta ajiye shi gefen gurin da tayi kaye-kaye, ai kuwa babu wata-wata tana ɗauka ta jefawa Barirah, a gurin ta duƙe saboda sosai taji saukar katakon a jikinta. Cikin kuka na tsantsar tsana Andi ke faɗin.
"Wallahi na gama zama da ke a gidan ko ni ko ke, bazan yarda ba akan abin da ki ka yiwa Usmanu, azzaluma algumguma baƙar kadara baƙar fura mai wuyar ban damu."
Haka suka shige ciki suka bar Barirah tsakar gidan ɗaya kwal kamar mayyar da suke faɗar.
Kakarta Kulu ce ta faɗo mata, ranar wata Talata shidda ga watan Ramadana na shekarar da ta gabata, duk wannan abin da ake yi idan na ce muku Barirah ba tayi shekara ɗaya a gidan Kawu Balarabe ba zaku sha mamaki,, azumin shekarar da ta gabata ne da yammaci wajen bakwai na dare sun idar da sallah suna shan koko da ƙosai, a lokacin ta dubi Kaka Kulu ta ce,
"Kaka me ya sa naji Innarsu Alawiyya na faɗin kar na sake zuwa gidansu, wai ke ɗin mayya ce haka iyayena wai mayu ne shan jini ya sa suka bar garin nan da faɗin ba ma a san inda suke ba sun sayar da jininsu?"
A lokacin Kaka murmushi tayi tare da tafa kaina ta ce,
"Barirah ba gaskiya ba ne, ko ma akwai gaskiyar to akwai sirri sosai da ba na so a yanzu ki sani, amma a gaba zaki san komi Andinki da Kawunki Balarabe nasan ba zasu ɓoye miki komi ba, sai dai ina so ki zamo bai haƙuri da tawakkali." Ta numfasa da kurɓan kokon ta idanuwanta suka sauya kala alamar damuwa kuma ta bayyana ƙarara a fuskarta ta ce.
"Haƙuri shi ne mabuɗin kwanciyar hankali, kuma tawakkali ga Allah shi ne ginshiƙin zuciyar mumini. Duk abin da ya same ka, ka sani yana cikin ƙaddarar Allah, mutane na iya ƙoƙarin cutar da kai ko hana ka wani alkhairi, amma idan Allah ya ƙaddara alkhairi gare ka, babu wanda zai iya hana shi, haka kuma idan Allah bai ƙaddara maka wani abu ba, babu wani mutum da zai iya tilasta wa ya same ka. Akwai hadisin da yake cewa, 'Ka sani cewa da al'umma gaba ɗaya za su taru domin su amfane ka da wani abu, ba za su amfane ka ba sai da abin da Allah Ya rubuta maka. Kuma da za su taru domin su cutar da kai, ba za su cutar da kai ba sai da abin da Allah Ya rubuta a kanka.' Saboda haka, ka yi haƙuri idan ka fuskanci ƙalubale, ka mai da komai ga Allah, ka guji ɗaukar fansa da gaggawa kuma, wanda ya dogara ga Allah ba ya taɓa faɗuwa ƙasa banza, kawai ka ci gaba da addu'a, ka yi aiki na gari, ka bar sakamako a hannun Mahalicci. Domin babu mai iya hana abin da Allah ya bayar, kuma babu mai iya bayar da abin da Allah Ya hana."
Sosai ta gamsu da maganganun Kaka a lokacin, don haka haka suka gama shan kokon a natse, har za ta miƙe sai ta kuma zaunawa ta ce ma ta, "Amma Kaka iyayen nawa fa? Shin da gaske sun bayar da jininsu?"
"A'a."
Ta amsa mata a takaice.
"To amma..."
Da sauri ta katse ta, ta hanyar ɗaga mata hannu, "Takwarata, maza ki amso mana abincinmu gurin matar Kawunki."
Jiki a sanyaye ta miƙe a lokacin. Abin da ta sani sunan ƙauyen da suke Kalambaina cikin Wamakko local government Sokoto, anan ta buɗe idanuwanta ta ganta hannun Kakar ta Kulu, sai Kawun nan ta biyu da matansu, Kaka ta taɓa faɗa mata yaranta huɗu ne maza uku mace ɗaya, Bature ne babba sai Habule, Balarabe da ƙaramarsu Tsaiba, sai 'yar ƙanwarta da ta mutu ruƙonta ya dawo hannunta wato Rakiya. Sana'ar mutanen ƙauyen Gumi-gumi ne sana'ar da kowa yasan mutanen garin Kalambaina da shi, haka su Kawu Bature sana'ar su kenan da ma sauran ƙannansa, kuma sun shahara sosai musamman Kawu Balarabe da ya kuɗance.
Sana'ar ce ma har ta komar da Kawu Balarabe cikin birnin Sokoto a yadda ta sani, kuma Kaka ta faɗa mata Rakiya ɗiyar ƙanwarta ita Kawu Balaraben yake aure don ta girmi Tsaiba mahaifiyar Barirah nesa ba kusa ba, za ta iya cewa abin da ta sani kenan daga tarihinsu kafin mutuwar Kaka su Kawu Bature suka ce ba zasu iya riƙonta ba don a cewarsu baƙar ƙaddarar Barirah mai muni ce, shine fa suka ce dole Kawu Balarabe ya riƙeta tunda shi yake auren Rakiya don idan ba Tsaiba Rakiya ce ta dace da ruƙon Barirah, ga shi ba tasan kowa na dangin mahaifinta ba, ko labarinsu ba ta taɓa ji a wurin Kaka ba ballantana Kawu Balarabe ko Andi, hakan ya sa taji cewa akwai wani sirri mai girma da ba a son ta sani ne, haka tazo Sokoto tana da shekaru 15 zamanta a gidan Kawu Balarabe bai ƙare ta da komi ba, abu ɗaya ta sani kowa da ke gidan ya tsane ta sai Sabuwa wato Iyah wacce ita ce amaryar Kawu Balarabe anan Sokoto ya aure ta ba ta taɓa haihuwa ba kuma yadda taji Andi na faɗi tun tana goyan Usman aka aurota don shi ne ɗanta na biyu Aliyu babba, Saudatu ce ta uku sai Faruk. Ta sani Usman na tausayinta lokaci zuwa lokaci ko da ita mayya ce ba zata taɓa cin namansa ba ya haramta a gare ta....
***
Tallah.
Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.
Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.