Free chapter · Read without an account
MATAR GIDA PAGE 80
by Maimuna Bala · MATAR GIDA
*MATAR GIDA BOOK* 2
*SHUUKRAN*/022
*YOTA ASSOCAITION*
P80
Misalin ƙarfe takwas na dare Hajiya Zulfa'u ce zaune tare Zainab kofar thearter room,kallo ɗaya zaka masu ka fahimci lallai suna cikin tashin hankali Hajiya Zulfa'u ce ta mayar da dubanta ga Zainab ta ce ''ya kamata a sanar da ƴan gidan su ko kina da lambar su?" shiru Zainab ta yi na ƴan sakanni tana nazari can ta ce ''gaskiya bani da lambar ko daya sai dai nasan gidan nasu'' Hajiya Zulfa'u ta gyara zama tana ƙara kallon Zainab ta ce ''in babu damuwa ko za ki iya zuwa gidan nasu ki faɗa masu halin da ake ciki'' ɗan jimm Zainab ta yi kafin ta ce ''babu matsalah'' daga haka ta tashi ta fita daga asibitin,tafiyar mintina arba'in ce tsakanin asibiti da gidan Mama daidai kofar gidan Mama Zainab ta yi pakin motarta lokacin karfe tara saura na dare har sannan yara na wasa layin unguwar,sallama dauke bakinta ta tura kofar gidan Mama na zaune farfajiyar gida saman tafurma a hankali ta waigo tare da mayar da dubanta ga Zainab kasancewar dare ne babu haske sosai,sai hasken ƴar tocilar Mama da ta gama shan wahalar duniya ko rabin farfajiyar gidan tocilah bata haska ba,Mama ta kurawa Zainaba ido tare da amsa sallamar cike da girmamawa Zainab ta samu waje ta zauna gefen Mama sai a sannan Mama ta gane Zainab Mama ta faɗaɗa fara'arta ta shiga tambayar Zainab lafiyar gidan da yara Zainab ta ce kowa yana lafiy,Anty Aisha ce ta fito daga bayi hannuta riƙe da buta idanunta kan Zainab tana faɗin mararaba Zainab ta faɗa tare da ɗaukar sabulu a magudana tana wanke hannu bayan ta gama wanke hannu ne ta dawo inda Mama da Zainab ke zaune ta samu waje ta zauna sai a sannan suka gaisa da Zainab bayan sun gama gaisawa ne Zainab ta sauke doguwar ajiyar zuciya kafin ta gyara zama cikin nitsuwa ta kalle Mama da Anty Aisha ta shiga basu labarin abinda ya faru gidan Unaisa,wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa Mama da Anty aisha suka tsinci kansu ciki musamman Mama da ta yi mutuwar zaune bayan Zainab ta kai karshen zancen ta ne Anty Aisha ta ce ''ki ka ce ya sake ta?" Anty Aisha ta yi magana cikin tsantsan tashin hankali tana kallon Zainab shiru Zainab ta yi ta ƙasa cewa komai,Mama dai na nan zaune kamar wacce aka dasa shiru ne ya biyu baya na wasu ƴan sakanni kowacce da tunanin da take da kyar Mama ta buɗe baki da ya mata nauyi sosai ta ce ''in take? tana gidan nasa ne har yanzu?" cikin kwantar da murya Zainab ta yiwa Mama da Anty Aisha bayanin halin da Unaisa ke ciki wani irin kuka ne ya kufcewa Anty Aisha cikin kuka ta ce ''amma Unaisa bata da hankali so take ta kashe kanta?wata iriyar yarinya ce wannan sau nawa za a mata magana kan kungiyar nan shikenan aiy ta samu abinda take so ta kashe aurenta ta sa cikin da take kulaface a haɗari Allah dai ya rabata da cikin lafiya'' Anty Aisha ta kare magana tana fice majina,can ta mayar da dubanta ga Zainab ta ce ''yanzu tsakani da Allah abinda ku ke daidai ne Zainab baza ku tuba ku daina ba kun bar sheɗan da zuciya na rudan ku baza ku tuba ku daina ba,Zainab a dalilin ki Unaisa da Fadeelah suka faɗa wannan masifar ke kina zama da mijinki lafiya saboda ya yarje make zama ƴar kungiya ita kuma Unaisa mijinta ya ce baya so amma saboda rashin hankali irin na Unaisa ta ƙi fita cikin ku,shikenan aiy ta samu abinda take so'' ta kare magana tana jan hanci Mama dai ƙasa magana ta yi ta kurawa waje ɗaya ido Anty Aisha na kuka ta mike ta shiga ɗaki, bayan shigarta ɗaki hijab ɗin da ta yi sallah ta dauko ta zura ta dauki kuɗi dubu biyu daga jakarta,wani Black simple shoe ta zura daga haka ta fita daga ɗakin har sannan Zainab na zaune Anty Aisha ta kalle Mama ta ce ''Mama taso muje'' sai a sannan Mama ta kalle Anty Aisha muryarta can ƙasa ta ce ''ki je Aisha Allah ya sauke ta lafiya'' daga yadda Mama ta yi magana Zainab da Anty Aisha sun fahimci ran Mama ya ɓaci shiru Anty Aisha ta yi na wasu ƴan sakanni can ta mayar da dubanta ga Zainab ta ce ''wani asibiti ne?" Zainab ta mike tsaye tana faɗin ''muje'' bayan fitar Anty Aisha tare da Zainab Mama na nan zaune inda suka baro ta wani abu ke mata yawo a zuciya,mamaki tare da nadamar sakaci da tarbiyyar Unaisa,bata taɓa sanin rashin jin maganar Unaisa ya kai haka ba sai yau duk yadda ta yi dan ganin Unaisa ta zauna lafiya gidan miji amma Unaisa sai da ta watsa mata ƙasa a ido ta ƙi fita kungiya gashi kungiyar ta yi sanadiyar mutuwar aurenta wata doguwar ajiyar zuciya Mama ta sauke tana jin yadda kanta ke juya mata harda yanayin gari babu zafi amma zufa Mama ke yi babu kakkautawa sosai hankalinta ya tashi ga wani irin ciwo da kanta ke mata cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa kar cutar hawan jinin ta ya tashi,da kyar take sauke numfashi tabbas zata yi maganin Unaisa,Unaisa zata hadu da fushinta babu kalar shawara da tausasawa da Mama bata wa Unaisa ba amma sai da Unaisa ta yi abinda Ɗalha ya saketa,wani irin jiri ke ɗibar Mama harda a zaune take amma tana jin yadda gari ke juya mata,a hankali ta kwanta saman tafurma da take zaune kai,murya can ƙasa take maimaita kalmar ''innalillahi wa inna ilaihi raji'un'' a asibiti kowa cikin abinda bai awa ɗaya ba likitoci suka yi nasara ciro tagwayen yara mata biyu kyawawa da su babu inda suka baro Unaisa harda jarirai ne amma kamininsu da mahaifiyarsu bai ɓoya ba,cikin taimakon Ubangiji duka yara lafiyarsu ƙalau,bayan gwaje gwaje da likitoci suka masu dukkaninsu suna cikin ƙoshin lafiya babu laifi sun yi girma abinsu sai dai ɗaya ta fi ɗaya nauyi ba tare da ɓata lokaci ba ɗaya daga cikin likitocin da suka ma Unaisa aiki ya dauko babies ɗin duka biyu ya nufi Neonatal inteneive Care Unit (NICU) bai tsaya ɓata lokaci ba ya sa su cikin incubator,kamar yadda muka sani jarirai da aka haifa watanni bakwai da wasu satika ko ƙasa da haka suna a bukatar agajin gaggawa kasancewar huhunsu da kuma hanjinsu bai yi karfi ba, iskar da muke shaƙa ya kan fi karfinsu wannan dalilin yasa ake kai su NICU a saka su cikin incubator wanda ake kira da kwalba a hausance,bayan fitar da jarirai ne likitoci suka mayar da hankali kan Unaisa yadda aka ɗinke ta staf,bayan komai ya kammala aka fitar da ita daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin hutu daidai lokacin Anty Aisha da Zainab suka shigo asibitin
Washe gari misalin ƙarfe shidda na safe Amirah na zaune ɗaki bata dade da idar da sallar asubah ba,bayan ta idar da azkar Kur'ani gabanta saida ta ƙasa karatun tunanin take kan maganganun da Ɗalha ya faɗa mata daren jiya tabbas ta san ta yi kuskuri duk abinda ya faɗa gaskiya ne sai dai abinda yake kara ba ta mamaki shine rashin faɗa mata kuskurenta da Ɗalha bai yi ba tun a baya,shiru ta yi tana ƙara nazari bayan wasu ƴan sakanni ta yi magana ita kaɗai murya can ƙasa ta ce ''kenan da ya samu yadda yake su wajen Unaisa Allah kadai ya san halin da zan shiga Allah kadai ya san irin wulaƙanci da zai yi min'' wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin a hankali ta furta ''alhamdulillah Allah nagode maka,tabbasa na yi kuskure na yi sake'' shiru ta yi tana tuna rayuwarta ta baya da ta tashi da safe zata ma yara shirin makaranta ta gyara gida ta shirya ta fita aiki da ta dawo zata dafa abinci ta kuma gyara gida ta yiwa yara homework da ƙyar take iya zama jiran Ɗalha wasu lokutan da ya gama abinda zai yi zata kwanta ta yi ta bacci sai daf da sallar asubah zata tashi ta yi wanka ta yi sallah ko sallar dare bata iya yi dah haka ma karatun Alkur'ani,daga ranar da Ɗalha ya mata saki ɗaya ya ce mata aure zai yi daga ranar ta farka ta cigaba da ibadah yadda take tun kafin ta haifi Sudais,sai bayan nan ta fahimci ba ta tsarawa kanta aiyukan gida yadda ya kamata ba wanda hakan ya sa ba ta samun lokacin hutawa da rana,da kyar Amirah ta samu ta yaƙaci tunani ta yi tilawar Alkur'ani,karfe bakwai daidai ta yi addu'a ta shafa daga haka ta fita daga ɗakin zuwa kitchen, bayan ta sauya kayan jikinta,kasancewar ranar Lahadi ce babu makaranta karfe takwas da wasu ƴan mintina Amirah ta gama haɗa abin kari daga haka ta tayar da tara ta yi masu wanka ita ma ta yi nata ta shirya kanta cikin wata atamfa ɗinkin riga da siket tana zaune daining tare da yara sun ƙari Ɗalha ya fito daga ɗakinsa kai tsaye ya nufi daining area kujerar da ya saba zama ya ja ya zauna,kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ya yi wanka sanye yake cikin wata maron jallabiya ga wani sihirtatcen ƙhamshi dake fita daga jikinsa,ƙhamshin turarensa ya haɗe da ƙhamshin turaren Amirah da su Sudais nan take parlourn ta dauke wani ƙhamshi mai kwantar da hankali da sanya nitsuwa,cike da girmama Amirah da yara suka gaishi sa fuskarsa dauke da murmushi ya amsa gaisuwar yana yiwa Fauziyya wasa,Amirah ta mayar da dubanta ga Ɗalha da Fauziyya dake ta faman dariya a hankali ta ajiye spone ɗin hannuta ta mike tsaye tare da sarving Ɗalha abinci,bayan sun gama cin abinci ne Sudais ya kwashe kwanuka da aka yi amfani da su ya kai kitchen Amirah ce ta wanke kwanuka daga haka ta dawo parlour ta zauna gefen Ɗalha Fauziyya na makale jikinsa yayinda sauran yara suna kallon carton,wayar Ɗalha ce ta yi ƙara alamar shigar kira,hannu Ɗalha ya kai ya ciro wayar daga aljihun rigar jallabiya da yake sanye da shi sunan Anty Aisha ne ya fita screen ɗin wayar Ɗalha ya ƙurawa wayar ido ganin bai amsa kiran ba yasa Amirah kallon screen ɗin wayar ganin sunan Anty yasa Amirah bude baki da niyar magana amma kiran ya katse hakan yasa ta yi shiru,bayan wasu ƴan sakanni wayar ta sake fara ƙara alamar shigar kira lokacin wayar na daure kan center table da ido kawai Ɗalha ya kalle wayar Anty Aisha ce ke sake kira ganin bai da niyyar amsa wayar yasa Amirah daukar wayar tare da miƙo masa ta ce ''ka amsa ka ji dalilin kiran ƙilah abu mai muhimmaci ne'' shiru Ɗalha ya yi bai ce komai ba yana kallon Amirah wayar tana daf da katsewa ya sa hannu ya karbi wayar daga hannunta daga haka ya amsa yasa wayar a speaker,bayan ya amsa kiran ne suka gaisa da Anty Aisha kamar yadda suka saba nan dai Anty Aisha ta yi masa bayanin abinda ya sami Unaisa shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni tun sanda Anty Aisha ta magana jikin Ɗalha ya yi sanyi zuciyarsa na bugawa da sauri,wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke sanda Anty Aisha ta ce ''tun jiya ta farka yara duk suna lafiya ita ma jikin nata da sauki sosai'' a dakile ya ce ''wani asibiti?" Anty Aisha ta basa amsa a takaice ta faɗa masa sunan asibitin,daga haka suka yi sallama fuskar Amirah cike da mamaki da rashin fahimta take kallon Ɗalha kamar jira take yana ajiye waya ta ce ''me ya sami Unaisar haihuwa ta yi ne? daman bata kwana gidan nan ba?" ta ƙare magana with so much confusion a natse Ɗalha ya mayar da dubansa ga Amirah kallon ta ya yi na wasu ƴan sakanni can ya shiga bata labarin abinda ya faru tsakaninsa da Unaisa jiya ''sosai jikin Amirah ya yi sanyi ita kanta ta ga wauta da rashin wayo irin na Unaisa amma sai ta kwantar da murya ta cewa Ɗalha ''amma da ba ka sake ta ba wallahi kuruciya da rashin wayu ke damun yarinyar da kora ta gida ka yi ka bta hutu ya fi ka sake ta'' murmushi kawai Ɗalha ya yi yana kallon Amirah can ya ce ''wani irin zuciya gareki ne me yasa ki ke son yarinyar nan kishiyarki ce fa'' wani irin kallo Amirah ta masa ta taɓe baki ta ce ''kai ka sani'' har cikin zuciyarta da gaske bata ji dadin sakin Unaisa da Ɗalha ya yi ba gaba ɗaya ta rikice hankalinta ya tashi amma sai ta yi ta danna kar Ɗalha ya fahimci hakan abu ɗaya ta sama zuciyarta duk yadda zata yi sai ta sa Ɗalha ya dawo da Unaisa,Unaisa yarinyar kirki ce matsalarta ɗaya wauta da rashin wayu,ba za ta yi sanyi a gwiwa ba insha Allah zata yi iya yinta sai Ɗalha ya dawo da Unaisa kar ya je ya kwaso mata wacce bata san halin ta ba,ta zo ta sata a damuwa,sanin kanta ne tunda Ɗalha ya san ɗaɗin zama da mata biyu zai yi wuya ya iya rayuwa da ita kadai, ''zan turawa yayarta Anty Aisha 300k ya isa ko?" ya ƙare magana da sigar tambaya Amirah ta kallesa ta ce ''uhm Abban Sudais kenan ka dai kara masu kamar 700k haka ban sani ba ko ta siya kayan baby ka ga dai suna asibiti yanzu haka kuma jiya aka yi aikin ƙilah su yi sati kafin a sallamesu saboda yaran'' a takaice ya ce ''shikenan tun da haka ki ka ce'' nan take ya turawa Anty Aisha 700k kamar yadda Amirah ta faɗa masa dama yana da account number Anty Aisha,tun kafin bikinsa da Unaisa a account ɗin Anty Aisha ya tura kuɗin lefen Unaisa
*SHUUKRAN*