Free chapter · Read without an account
THE QUESTIONS
Yau zaid be tashi ba seda aka fara kiran sallah, ya bude ido yana kallon maryam, itama ta bude idonta a hnkali se suka hada ido, tayi sauri ta rufe, murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga bathroom Yayi arwallah ya fito, itama ta shiga ta fito, suka yi raka’atanul fajr sannan sukayi sallar Asuba, kamar kullun seda suka qare adhkar dinsu na safe zaid ya kama hannunta yana tasbihi dasu, seda ya qare sannan ya kalleta
“kiyi min karatu da muryar ki me daadi Mijn kleintje”
ta dan kalleshi “wace surah zan karanta?”
Ya lumshe ido yana fadin “kowace”
bismillah maryam tayi ta fara karanta suratul kahf a natse, tun yana saurarenta daga zaune har ya kwantar da kanshi a kan kafar ta da ta miqe kan daddumar, yana jin sautin karatun na ratsa duk wani sashe na jikin shi, yana murza yatsun hannunta a hnkali, seda ta kai qarshen surar ta kalli fuskar shi da ke kan kafarta, kamar ma yayi baccee, se ya bude ido suka kalli juna, yayi mata murmushi
“inajin daadin karatun ki sosai Mijn kleintje, idan kinayi kamar kada ki tsaya”
tayi murmushi
ya miqe tsaya yana qoqarin chire jallabiyar shi, maryam ta kawar da fuska da sauri ta miqe tana qoqarin fita “Ina zakije? Zo mu kwanta”
“Ehn..dama..dama..umm..inaso..zan sha ruwa ne”
“Zo akwai fridge a nan”
Tayi tsaye a inda take ya tako yazo ya dauketa ya zaunar da ita kan gado ya dauko ruwa ya miqo mata, ta karba ta bude tanasha, sam taqi yadda ta hada ido dashi, ta miqa mishi gorar, ya karba ya rufe ya aje sannan ya hauro gadon bayan ya rufe labulayen dakin da hasken rana ya fara shigowa, ya janyota zuwa jikinshi, se yaji jikinta yana rawa “shhhh, muyi baccee” ta dan saki jikinta amma bata yadda baccinta yayi nauyi ba, seda ta lura jikin zaid ya saki yana sauke numfashi da dan nauyi ta tabbata yayi baccee se ta sauka a hankali ta fiche daga dakin ta wuche dakin ta, bathroom shiga tayi wanka ta fito ta shirya ta sauka qasa, se kawai tayi tunanin bari tayi masa, ta gyara shinkafar tayi blending ta hada se ta kunna oven seda yayi zafi se ta kashe ta bashshi ya dan rage zafi se ta zuba hadin masar a wani container me girma ta rufe ta saka cikin oven din da keda dumi ta kulle, ta bude freezer ta dauko naman rago tayi pepper soup da yaji spices se qamshi ke tashi, ta zuba na mammi a warmer ta ajiye a kitchen island sannan ta juye saura a wata warmer ta ajiye a dinning sannan ta fito da hadin masar ta, ya tashi sosai kamar ma ze fara zuba, taji daadin yadda taga ya tashi, ta gyara pan dinta tasa mai sannan ta fara zubawa tana soyawa a hnkali har ta qare, ta zuba ma mammi nata ta ajiye kusa da peppersoup dinta, sannan ta juye nasu ta kai dining ta ajiye ta dauko turaren wuta tasa a burner sannan ta zauna a parlor, seda taji cooks sun bude kofar kitchen sun shigo sannan tache su dauki na mammi su kai mata.
Tana nan zaune tanata tunanin yadda zaayi tasan abunda ke cikin dakin nan na bayan garden kafin su wuche Amsterdam, Tana tunanin iya binciken da take tunanin yayarta Aisha tayi kafin ta bache, tayi zurfi sosai a tunani se kawai ji tayi an shafa mata fuska, firgigit ta dawo cikin hnkalinta taga zaid a gabanta yana kallonta, sanye yake da wando me duhu da riga fara, ita kam batasan ma sanda yazo gabanta ba, batasan ma saukowar shi ba
“Wane irin tunani kike haka da zurfi? Ki dena it’s dangerous”
Tayi murmushi kawai, “ina kwana?”
“Bayan kin gudu kin banni?”
Tayi murmushi kawai
“Breakfast yana dining” ta miqe yabi bayanta, ya zauna ta zuba mishi masa da peppersoup da hada mishi tea sannan itama ta zuba ta zauna, tun da zaid ya fara chin masar yake jin wani irin daadi ba iya bakin shi ba har cikin ran shi se addua yake mata daban daban
Seda suka qare ya kalleta “nagode sosai, Allah ya yimiki albarka”
Tayi murmushi “Ameen”
Suka dawo parlor tana tambayar shi ko zeje aiki yau “bn sani ba, maybe zuwa anjima in dan leqa, kin hada documents dinki na school?”
Ta gyada kai a sanyaye “eh”
Ya lura da yanayin ta “Zakiji daadin garin idan mukaje in shaa Allah”
Maryam ta ɗago kai.
“Anya kuwa?”
“Eh in shaa Allah Because zaki chi gaba da karatu, zaki samu sababbin abokai”
Ta yi murmushi.
Zaid ya kalle ta a zuciyar shi yache “da kadan fah ta wuche 20yrs, dole zataji kewar gida”
Sai ya ƙara chewa
“Kuma zakiga sabon wurin da ba Nigeria ba.”
“Amma ba ka san ko zan so garin ba ai”
“Zaki so shi”
“Ta ya ka sani?”
“Saboda kina tare dani”
Maryam ta sunkuyar da kanta qasa
Be sake chewa komi ba na dan lokaci.
Se ya tashi ya shiga office dinshi na cikin gida
Maryam kuma ta hau sama bedroom dinta ta dauko laptop dinta
Ta zauna kan dressing chair.
Ta buɗe, Ta fara searching Northern Crest Holdings.
Akwai information kaɗan
Company profile.
Construction.
Land development.
Agriculture.
Sai wani tsohon article.
Maryam ta karanta heading din
Northern Crest Holdings expands international partnerships.
Ta danna shi
Amma page ɗin bai buɗe ba, taja tsaki
“Seriously?”
Ta sake gwadawa amma ba komi, article din ya ma bache
Ta koma Google.
Ta rubuta:
Northern Crest Holdings Amsterdam
Akwai wasu results, Amma yawancinsu ba su da cikakken bayani. Ta ga sunan wani tsohon project.
NCH — European Trade Partnership.
Ta ɗan matsa kusa da screen din
“European…”
Ta yi screenshot.
Ta aika ma kanta a WhatsApp.
Sai ta ji knocking a ƙofa
Ta rufe laptop da sauri
“Bismillah”
Zayd ne ya bude
Ya tsaya bakin ƙofa.
“Aiki kike?”
“A’a.”
Ya shigo
“Zanje part din Mammi.”
“Okay.”
Ya kalli laptop.
“Me kikeyi?”
“Ba Komi.”
Ya kalle ta.
“Kawai ina dan duba universities in Amsterdam”
Ya gyada kai.
“Good.”
Sai ya bata wani envelope da ke hannunsa.
“passport documents, da visa Dinki da komai”
Ta karɓa.
“Nagode”
“Ki kula dasu.”
“Okay.”
Ya juya ze fita, Sai Maryam ta kira shi.
“Yaya”
Ya tsaya
Ya juyo yana kallonta yana dan yamutsa fuska
“Me kikache?”
Ehm..ummm..Dama inaso in tambayeka ne
“Wane suna kika kiranni?”
Ta sunkuyar da kai “My G”
“Toh tambaya ina jin ki”
“Akan Northern Crest holdings”.
“Northern Crest?”
“Eh.”
“Me kikeson sani akan northern crest?”
Ta yi shiru na ɗan lokaci.
“Na ji sunan ne.”
Zayd ya kalle ta.
“A ina?”
“Just…emm..fahad ya taba chemin yana aiki a Chan”
Ya yi shiru.
Sai ya ce:
“Kampanin babanmu ne, fahad ke kula da komi tun bayan rasywar Shi haryanzu”
“Ka san abubuwan company ɗin sosai?”
“Aa”
“Sunada branch an Amsterdam ne?”
Zayd ya kalleta.
Wannan karon ya yi shiru na ƴa seconds.
“Babu shi, sedai maybe partnership da projects”
Maryam ta gyada kai.
“Okay.”
Zayd ya kalleta.
“Meyasa kike tambaya?”
“Ba komi”
Ya kalle ta sosai.
“Mahreeyam.”
“Naam?”
“Akwai wani abu da kike boye min ne?”
Zuciyarta ta buga.
Ta yi murmushi kaɗan.
“Aa”
Zaid ya ci gaba da kallonta.
Kamar yana son ya gano abin da take ɓoyewa.
Amma se kawai yache
“Okay.”
Ya juya ze fita se taga itama tanason zuwa wurin mammi “ina zuwa bari insa hijab zan bika muje wurin mammi tare”
ya ansa mata “zan jira ki a qasa”
Ya fita, maryam kalli ƙofar bayan ya rufe.
Sai ta sauke ajiyar zuciya.
Suna hanyar tafiya part din mammi suka hadu da Fahad
“Anty maryam kinsa yayana ya natsu fah, naga kwanan nan baya ma fita ya duba projects din da kampanin shi sukeyi”
Tayi dariya kawai, suka gaggaisa sannan ta wuche ta bassu, nan fahad ya yima zaid bayani wai Ashe imran ma ya taba zuwa ya kawo cv dinshi a nan sokoto branch na northern crest, ynzu dai sunyi contacting dinshi sunche yazo interview, zaid yaji dadi, daga nan kuma ya tuna alqawarin da yayima maryam “Fahad akwai wata Islamiyyah a nan unguwar su maryam, ta Gayamin sunan amma na manta, ka bincika dai tache kusa da gidan su ne sosai, akwai wani malami a nan Islamiyyar tache sunan shi mlm muhammad, inaso a biya mishi umrah da hajj tareda matar shi in yanada aure, se kuma islamiyyar inaso a gyara ta sosai, a tura engineers da architect suga wurin ayi sabon building kuma duka malaman makarantar inaso a rinqa biyan su albashi me kyau, a qirga ko su nawa ne zansa a rinqa turo salary dinsu tareda na imran, kayi calculating komi cikin satin nan kayi min sending ya email”
Kafin zaid ya gama bayani Fahad kam har ya riqe baki “se da kai yayana, lallai na yadda kayi aure😂 ai mukam anty maryam ta zamar muna alheri wannan irin sadaka haka”
Zaid murmushi kawai yayi ya nufi part din mammi
Ya tarar da maryam da hajiya raliya a parlor, ya gaida hajiya a natse, ita ke gaya mishi wai mammin bata nan ta fita, shima se ya fice ya koma part dinsu, Maryam na nan zaune a parlour ita da hajiya se taga ai ga dama ta samu tayi tambaya, Ta yi tunani na ɗan lokaci.
“Hajiya…”
“Na’am?”
“Zan iya tambayar ki abu?”
Hajiya Raliya ta kalleta.
“Tambaya muji”
“Kin san Northern Crest Holdings?”
Fuskar Hajiya Raliya ta sauya a take
“Me yasa kika tambaya?”
“Na ji sunan ne kawai”
Hajiya Raliya ta yi shiru na dan lokaci
“Maryam.”
“Na’am?”
“Ki daina tono abubuwan da ba ki san iya inda suka kai ba.”
Maryam ta kalleta.
“Amma Hajiya, me yasa kowa yake gaya min in yi hankali?”
Hajiya Raliya ta sauke ajiyar zuciya.
“Saboda ba ki san abin da kike kokarin shiga ba.”
“Amma idan akwai wani abu da ya shafi yayata fa?”
Raliya ta daskare a take
Maryam ta lura.
“Hajiya…”
Hajiya Raliya ta kalleta sosai.
“Me kika ce?”
“Na ce idan akwai wani abu da ya shafi sister ɗina fa?”
Raliya ta ɗan sauke idonta.
“Kin dena neman Aisha, ai naji anche ta rasu”
Maryam ta ji zuciyarta ta buga.
“Hajiya Me kika sani game da Aisha?”
Hajiya Raliya ta kalleta.
“Ba komai.”
“Amma gashi kin san sunan ta ai.”
“Kin taɓa ambatarta ne har naji”
“Ni? Yaushe?”
Hajiya Raliya ta yi shiru.
Sai ta tashi tsaye, inaga sadda mukaje sokoto bikin ki ne naji anche kinada yar uwa Aisha wadda ta rasu
“Hajiya..”
“Maryam ki kama kan ki”
Ta fara tafiya.
“Hajiya!”
Hajiya Raliya ta tsaya.
“Don Allah hajiya”
Raliya ta juya ta kalle ta.
“Idan har bazaki hankura ba kina son sanin gaskiya…”
Ta yi shiru.
“Ki fara da abin da kika sani.”
Maryam ta kalle ta.
“Toh ni me na sani?”
Hajiya Raliya ta ce:
“Kin san sunan Northern Crest.”
Ta ɗan tsaya.
“Kin san sunan Rahman Balarabe.”
“Kin san kuma yayar ki Aisha tana bincike.”
Hajiya Raliya ta kalleta sosai.
“Wadannan sun isa ki fara ai, Nidai nayi warning dinki”
Sai ta juya ta tafi.
Maryam ta zauna a wurin kamar an zuba mata ruwan sanyi
Tabbas Ta san Aisha tana bincike.
Hajiya Raliya ma ta sani kenan?
Amma ya akayi ta sani? daga ina?
Da wannan tunanin ta koma part dinsu se ta tarar zaid baya nan, ta zauna a parlor tanata tunani, se bayan zuhr ta tashi ta shiga kitchen, zucciyar ta ba daadi yau, stir fry pasta tayi, tayi marinating kaza tasa a fridge, tangerines din da ke cikin fridge kawai ta dauko tayi juicing dinsu, yau batada energy din hada wani drink, sannan ta dauko kazar ta gasa.
Da yamma, Zaid ya dawo daga fitar da yayi
Maryam tana nan parlor zaune
Ya shigo.
“Mahreeyam.”
Ta dago
“Sannu da zuwa.”
“Yawwa.”
Ya lura da yanayinta
“Lfya?”
“Lfya qalau”
“Zo ki rakani wani wuri”
“Yanzu?”
“Eh.”
“Ina?”
“A Walk.”
Ta tashi tsaye
Suka fita garden.
Ba ta hanyar da ƙofar take suka bi ba, wani side na garden din ne
Iskan yamma na kadawa a hankali.
Maryam shiru.
Zaid ma shiru.
Sai chan ya kalleta
“Harynzu kina tunanin bi na Amsterdam ne?”
“Eh.”
“Tsoro kike?”
“Kadan.”
“Meyasa? Bazan chanye ki ba ai ko?”
Maryam ta kalli ƙasa
“Saboda komai sabo ne a wurina”
Zaid ya gyada kai.
“That’s normal ai”
“Ni ban taɓa barin Sokoto ma na dade haka ba”
Zaid ya kalle ta.
“Ina tare dake, bazakiji wahalar komai ba”
Ta kalle shi.
“Ta Yaya tunda kullun kana aiki?”
“Kar ki damu, bazan bakki ke kadai ba se kin Saba da garin sosai.”
Maryam ta yi shiru.
Sai Zaid ya chigaba
“Zan rinqa zuwa school din tare dake, I’ll help you har kiyi settling, And immediately kikaga abnda be miki ba ki gayamin”
Ta yi murmushi.
“kana bani confidence ne?”
“Yawwa kin gane kenan”
Ta yi dariya kaɗan
Suka ci gaba da tafiya, seda suka zagayo suka dawo qofar part dinsu suka shiga, dama zaid so yake kawai ta dan sake kuma ta sake din
Maryam na kan carpet bayan ta idar da sallar magrib tanata tunanin abnda hajiya raliya tache mata, se zaid ya shigo ya zauna kusa da ita
“Inajin yunwa Mijn kleintje”
Ta miqe tsaye “abnci yana dining”
ya riqe hannunta suka wuche dining, ta dauko plate da niyyar dibar mishi abnci se tallabo warmers din yayi ya kai parlor yana yimata nuni da ta biyo shi, a chan parlor suka chi abncin a plate daya, suna nan zaune aka kira isha ya fita masallaci, ta tattare kwanonin ta kai kitchen ta hau sama zuwa dakinta, ta gama sallah da adhkar ta dauko wayarta, Ta buɗe notes din wayar, Ta rubuta:
Hajiya Raliya tasan wani abu gameda Aisha.
Sai ta ƙara:
Tasan wani abu gameda Northern Crest.
Ta tsaya, se Ta buɗe gallery ɗinta.
Ta nemo hoton Aisha, Ta dubi fuskar yayar tata, Ta yi murmushi mai rauni.
“Aisha…”
Ta faɗa a hankali.
“Me kika gano ne wai?”
Sai wayarta ta yi vibration.
Maryam ta kalli screen
Zaid ne
Message ɗaya:
“Zaki sauko ko in inzo sama?”
Maryam ta kalli message ɗin.
Sai ta yi murmushi ta rubuta
Zan sauko
Bayan Dan lokaci tana ta karanta abubuwan da ta rubuta a notes din wayarta se message ya sake popping
“Na siyo miki chocolates, ko in chanye abuna?”
“Aa gani nan zuwa”
Tayi wanka da brush tareda arwalla sannan ta fito ta shafa mai da turarukanta ta shirya cikin kayan baccinta se tasa hijab ta sauka qasa
Yana kwance kan kujera idonshi a lumshe amma yana jin tafiyarta har ta iso ta tsaya kusa dashi, yana shaqar qamshin humra da sauran turarukanta a hancin shi ya bude ido a hnkali ya ganta a tsaye,
“chocolates din fah?”
“Bakizo cikin lokaci ba har na chinye”
Ta zumburo baki zata juya ya fizgota, kamar zata fadi qasa ya jawota ta fadi a kan shi
“Na chanye chocolate din keche bakizo da wuri ba, idan kinaso in baki wannan..” ya bude baki yana nuna mata sweet din da ke cikin bakin shi
“Toh ka bani”
“Zo gashi” Yana turo mata bakin shi
“Aa ni wani zaka bani”
“Ai ba wani wannan ne kawai”
Ta Zumburo baki “toh ka bashshi kawai”
“Ai shikenan tunda kin hakura”
Ya zaunar da ita dakyau “zo muyi kallo”
Ya kunna tv da remote din da ke hannunshi yasa channel din aljazeera, maryam kam ita dama news ai sedai ta gani a social media don bata kallon news channel, zaune kawai tayi ta qura ma tv ido har baccee ya fara fizgar ta, daga nan zaune tayi baccin zaid na kallonta, seda yaga baccin nata yayi nisa sannan ya kashe tv ya dauketa ya hairs sama ya wuche dakin shi, seda ya kwantar da ita kan gado ya chire mata hijab din jikinta, wata rigar baccee che pink color a jikinta, tayi mata kyau sosai, ya qura mata ido yana kallonta, komai na jikinta ds da ita, kamar ya kai hannu ya taba ta amma yayi qoqari ya danne, se kawai ya gyara mata duvet shima ya kwanta yayi hugging dinta ta baya, ajiyar zuciya ta sauke ta shige cikin jikinshi kamar Wata mage, Dariya yayi yana fadin ga tsoro ga son jiki
Follow this link to join my WhatsApp group