Free chapter · Read without an account

THE JOURNEY

by Nihaal Maalik · KIRAN KADDARA

Washe gari da imran ya fito daga sabon wurin aikin shi se yazo ya dauki hauwa koulou ya kaita cafe aka yimata registration na JAMB, an qare yimata komai ta bude jaka zata biya se imran ya chiro kuddin ya bada, “mama ta bani kuddi tache in biya idan an qare” imran seda yayi shuru na dan lokaci yana sauraren yanayin maganarta ma irin na maryam ne “kar ki damu bashshi kawai”

“Nagode Allah ya saka da alheri” 

Suka fita suka hau kan mashin dinshi ya mayar da ita gida, koda ya ajeta seda ta sake yimishi godiya sannan ta shige gida shima ya matsa gaba ya shige cikin nasu gidan, mama na ganin hauwa ta shigo ta tambyeta ko Anyi, ta amsa mata tare da sa hannu a Jakarta ta ciro kuddin da mama ta bata “mama ga kuddin da kika bani, shi ya biya yache in bashshi kawai” mama tayi murmushi “toh kin gode Allah ya saka da alheri” a ranta tana adduar Allah yasa abnda take hasashe ya tabbata. 

Imran ma koda ya shigo gida inna Tana tambayar shi “yau ka dade wurin aikin, hala akwai dayawa ne?” 

“Aa inna tun dazu niddawo na dauki hauwa koulu ta gidan maman na kaita Anyi mata registration na jamb”

“Ohh tohh Allah ya bada saa” mama ta fadi tareda addua a ranta Allah yasa wani abu ya Qullu tsakanin shi da hauwar, saboda tanason hada dangi da mama

Da ameen ya ansa sannan ya shiga dakin su


Yau Maryam na cikin wani irin excitement da ta kasa ɓoyewa.

Gobe zasuyi tafiya

Tomorrow… Amsterdam.

Zaune take a kan gadon tana kallon suitcase ɗin da ke bubbude gabanta.

A wannan karon ta fara packing da gaske.

Ta buɗe wardrobe, ta fara zaɓar kayan da za ta tafi da su.

Wasu gowns, wasu casual clothes, Jaket, shoes, Hijabs.

Sai ta tsaya tana kallon kayan na ƴa seconds.

“Amsterdam…”

Ta faɗa a hankali tana murmushi.

Se kuma tunanin zaid ya fado mata, yau koda ta tashi sallar Asuba bata ganshi a daki ba, haka tayi sallah tareda komawa baccinta da tunanin qila yana masallaci, seda ta tashi baccin safe wuraren 9am still taga baya nan, taje dakinta tayi wanka ta shirya se kuma ta sauka don tayi breakfast, a nan ne taji motsi a study office dinshi, ta leqa ta ganshi yana aiki kuma ga alama a nan ya kwana, yache mata so yake ya qarqare ayukkan nan kafin su wuche gobe, tafiya tayi ta hada breakfast ta kawo suka chi tare, a nan ne ya che mata taje ta hada kayanta shima sora kadan ya qarqare aiki, se ta duba lokaci, ynzu 2pm amma haryanzu bataji ya hauro sama ba, ta sauke ajiyar zuciya tana chewa “shi kam dai kullun aiki aiki aiki”

Ta ɗauki waya, zata kira Mama, Ta duba lokaci 

Ta yi tunani na ƴan seconds kafin ta danna number ɗin

Bayan ringing ɗin sau biyu, Mama ta ɗauka.

“Hello, Maryam?”

“Assalamu alaikum Mama.”

“Wa alaiki salam. Kina lfya?”

“Eh Mama. Lfya qalau Alhamdulillah”

Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jin kewar yar ta

“Alhamdulillah.”

Maryam ta zauna dakyau a kan gadon.

“Mama…”

“Na’am?”

“Kin san gobe zamu tafi ko?”

Mama ta yi shiru na ɗan lokaci.

“Eh, kin gaya min.”

“Amma Mama, tun lokacin da na gaya miki tafiyar, nake jin kamar baki ji daɗin maganar ba”

Mama ta yi shiru.

Maryam ta ci gaba.

“Yanzu gobe zamu tafi, amma ko jiya lokacin da muka yi magana na ji kamar kina cikin damuwa.”

“Maryam…”

“Na’am Mama?”

“Kada ki damu.” 

“Amma Mama…”

“Ki saurare ni.”

Maryam ta yi shiru.

“Ba wai bana son ki tafi bane.”

“Toh me yasa ko muna fira se kiyi shiru idan na ambaci tafiyar?”

Mama ta sauke ajiyar zuciya.

“Saboda ke kadai che ɗiyata a yanzu kuma zaki qara yin nisa Dani”

Maryam ta yi shiru.

“Na saba da ganin ki a kusa da ni. Na san inda kike, na san wa kike tare da shi, idan wani abu ya same ki ina iya zuwa wajenki.”

Ta ɗan tsaya.

“Yanzu za ki je ƙasar da baki taɓa zama ba, nesa da ni”

Maryam ta ji zuciyarta ta yi nauyi.

“Mama…”

“Amma wannan ba yana nufin bana son ki je ba.”

“Na fahimta.”

“Maryam, kin yi aure. Hakkin ki ya tashi daga kaina, Kuma kina da karatu da kike son ci gaba da shi.”

“Idan Allah Ya buɗe miki wata ƙofa, ba zan zama wadda da zata rufe miki ita saboda tsoro ba.”

Maryam ta yi shiru.

Hawaye suka cika mata ido.

“Mama…”

“Na’am?”

“Ki yi min addu’a.”

Mama ta yi murmushi cikin wayar 

“Addu’a ita ce kawai nake yi miki tun ranar da kika tafi.”

Maryam ta goge hawayen da suka gangaro mata.

“Ni ma ina jin tsoron tafiyar mama.”

“Kada ki ji tsoro.”

“Inajin tsoro inda zanje ban san kowa ba”

“Kin san mijinki ai”

Maryam ta yi shiru.

Mama ta ƙara da

“Ki kasance me yimishi biyayya, Ki saurare shi, Kuma ki gaya masa duk abin da yake damunki.”

Maryam ta tuna da maganar Hajiya Raliya.

Ta yi shiru.

“In Sha Allah mama”

“Maryam.”

“Na’am?”

“Ki kula da kanki.”

“Zan kula.”

“Ki yi karatunki sosai.”

“In Sha Allah.”

“Kuma kada ki manta da addua, kar kuma kiyi abukkan banza”

Maryam ta yi dariya cikin hawaye.

“Allah Ya tsare ki.”

“Ameen mamata”

“Allah Ya sa Zaid ya zama kariya gare ki.”

Maryam ta yi shiru.

“Ameen.”

Mama ta ɗan yi shiru.

Sai ta chigaba 

“Ki daina kuka.”

Maryam ta yi dariya.

“Ba  kuka nike ba.”

“Na san muryar kukan ki ai”

Maryam ta yi dariya sosai.

“Okay Mama.”

“Ki je ki natsu kiyi packing dakyau, ki dauki kayan abncin da kinka lura mijinki naso wa’inda baza’a samu a chan ba”

“In shaa Allah”

“Allah Ya kai ku lafiya.”

“Ameen.”

Suka yi sallama.

Maryam ta ajiye wayar.

Ta zauna shiru na ƴa seconds.

Sai ta kalli suitcase ɗin gabanta, se kawai ta daukesu hoto ta tura a group din da suka bude na WhatsApp su uku kawai, ita da safiya da bahijja saboda sharing din abubuwan karatu tun lokacin da suna ug1, tareda rubuta caption “Amsterdam loading”

Kafin ta aje wayar safiya ta kirata, cikin murya me sanyi ta fara magana “Qawata tafiyar tazo ko, ynzu wucewa zakiyi ki banni, ji nike kamar in biki”

Maryam tayi dariya a ranta tana chewa “lallai da gaske rashin lfyar nan na wahalar da Safiyya, inda Safiyya da ta sani che da ynzu tana nan tana ihu tana gayamin abubuwan da zanyi in naje” 

maryam tayi murmushi “Safiyya Allah ya baki lfya ya kawo muna babyn mu lfya” 

“Ameen kedai qawata, Allah ya kaiku lfya ya tsare hanya, don Allah ki samo muna dan Amsterdam ko yar Amsterdam”

“Wai ina zan Samo su? Fahad ma haka yache min” 

“Ban gane ina zaki samo su ba, mijinki ze baki manah, kar dai kiche min tun da muka kaiki bakuyi komai ba kallonki kawai yake”

“Banason walakanci Safiyya, idan be kalleni ba mi ze yimin?” 

“Lallai yarinyar nan na tabbatar baa miki komai ba tunda kiketa zuba haka, ai inda an miki wani abu da ko ynzu da na tado miki da zanchen se gabanki ya fadi, kai!  Gaskiya yayana nada hakuri sosai”

“Ke kije kiji da jikinki kinzo kinata yima mutane surutun banza a nan, inda lfyar ki qalau da se bakin naki yafi haka”

Safiya tayi dariya kawai “yarinyar duk ranar da za’a tabo ki zakiche na gaya miki”

“Ni ba Wanda ze tabo ni”

Sukayi dariya sannan suka fara firar su, sun jima suna waya kafin sukayi sallama


A downstairs, Zaid yana cikin office dinshi na gida, Laptop ɗinsa a gabansa.

A kan screen ɗinshi na laptop file ɗin da ya samu daren jiya ne, ga kuma carpet din sallah shimfide a qasa gefe daya wanda ke nuna a nan ya kwana

CONFIDENTIAL — NORTHERN CREST HOLDINGS

Ya sake buɗe attachment ɗin, Ya karanta records ɗin a hankali, Akwai wasu dates, Wasu land references, Wasu signatures.

Amma wani ɓangare na document ɗin ya ɓace.

Page 17 — Missing.

Zaid ya ɗan yi nazari

“Meyasa babu 17?”

Ya danna wani folder.

Babu komi 

Ya sake bincika email ɗin.

Sai ya ga wani rubutu a ƙasan message ɗin yayi popping

Zaka samu Original records idan kayi requesting

Zaid ya dan tsaya, se Ya rubuta reply:

Waye kai?

Ya aika.

Bayan seconds kaɗan…

notification ya shigo.

In ka shirya sani zaka sani

Zaid ya kalli screen din

“Mstw ka ma rena mutane”

Ya rufe email din

Dd nan wayarsa ta yi ringing.

Fahad.

Zaid ya ɗaga.

“Hello.”

“Bro.”

“Naam?”

“Tafiyar na nan gobe komi ya zama ready ko?

“Yes in shaa Allah”

“Anty Maryam fa?”

“Itama ta shirya”

Fahad ya yi shiru.

Sai ya ce:

“Da gaske dai da ita zaka wuche Amsterdam ku bammu a nan”

“Yes, ko in barmaka ita ne?”

Yayi dariya “ni bance ba”

Zaid ya lura da yanayin muryarsa

“Me ya faru?”

“Be komai.”

“Fahad.”

“Bro, Inajin daadi ne kawai, Kayi settling finally”

Daga nan Sunyi maganar what time ze kaisu airport suka yi sallama.

Zaid ya ajiye waya.

Maryam ta sauko downstairs da dayan suitcase ɗinta da ta gama hadawa, dd lokacin Zaid yana fitowa daga study office yana duba wani abu a waya

Da ya ɗago kai ya gan ta.

Ya kalli suitcase ɗin.

“Mijn kleintje kin qare shirin?”

“Na kusa”

“Wannan qaton luggage sannan kiche baki qare ba?”

Maryam ta yi mamaki.

“Wannan kaɗan ne fah”

Zaid ya kalli suitcase ɗin.

“Okay, idan kin hada wani kada ki dauko, ki kirani in sauko dashi”

Maryam ta yi murmushi.

“Ai hajiya Raliya ma ta ce kada in kwashi unnecessary kaya, wannan ne kawai se hand luggage qarami”

“Yayi murmushi”

Maryam ta zauna.

“Kaima ka shirya?”

“Yes, hand luggage kawai nike tafiya dashi da few things a ciki”

“Flight dinmu fah? Qarfe nawa ne?”

“Private charter.”

Maryam ta kalle shi.

“Again?”

Zaid ya gyada kai.

“Yafi sauki”

Ta ɗan yi shuru, se kuma tayi tambaya

“Gidan ka fa?”

“Wane gida?”

“Na Amsterdam.”

“Komi kache an shirya?

“Yes.”

“Hadda kayan sawa?”

“Eh, Na kira wasu designers nache suyi arranging komi, na tura musu details dinki da haj ruqaiya taje ta dauka ta aiko ma mammi lokacin da zasu hada lefe.”

Maryam ta yi murmushi

“Kada ki damu idan akwai wani abu da basu siya ba ko abnda be yimiki ba se muje a saye idan mun isa”

Ta ji wani irin warmth a zuciyarta.

“Thank you.”

“No need.”

Da rana, Mammi ta zo sashensu.

Maryam tana kitchen tana girki

Mammi ta rungumeta ta baya

“My daughter har na fara kewar ki da kewar girkin ki me daadi”

Maryam ta yi murmushi.

“Mammi ina wuni”

“Lfya qalau kin shirya kuwa?”

“Eh”

Mammi ta kalli Zaid da ya biyosu ya tsaya kofar kitchen

“Ka tabbata komai ya zama ready?”

“Yes.”

“Makarantar ta fah?”

“Nayi magana da wani already, idan munje zata zaba”

Mammi ta yi murmushi.

“Good.”

Ta kalli Maryam.

“Ki yi karatunki sosai my daughter”

“In Sha Allah mammi”

Mammi ta kama hannayenta ta riƙe

“Kuma kada ki ji kamar kina wani foreign country ke kaɗai, duk abnda kika gani da be miki ba ki kirani ki gaya min”

Maryam ta kalli Zaid.

Mammi ta lura, Ta yi murmushi kawai

“Ka kula da ita, Ba aiki kawai zaka yita yi ba”

Zaid ya yi murmushi kaɗan.

Mammi ta rungume Maryam.

“Allah Ya kai ku lafiya, se mun hadu goben kafin ku wuche

“Ameen.”

Da dare, Maryam ta gama packing hand luggage dinta, Ta rufe suitcase ɗin.

Ta zauna a kan gadon tana kallon ɗakin.

Akwai wani irin feeling na barin wani abu a baya, gida! Zataji kewar gidansu don ynzu zata qara nisa

Da kuma wannan gidan…da ta shigo a matsayin amarya ba tare da ta san yadda komai zai kasance ba, A Yanzu…ta kusa barin Nigeria tare da mijinta, Ta ɗauki wayarta, Ta buɗe notes, Ta rubuta:

Tomorrow — Amsterdam.

Ta tsaya.

Sai ta ƙara:

Aisha.

Sai:

Northern Crest.

Ta kalli rubutun.

Amma kafin ta ajiye wayar…ta ji Anyi knocking.

“Come in.”

Zaid ya buɗe ƙofar.

Ya tsaya bakin ƙofa.

“Kin qare?”

“Eh.”

Ya kalli suitcase.

“Good.”

Maryam ta kalle shi, yaga kamar tsoro a Idonta 

Se ya shigo ya zauna kusa da ita, ya riqe hannunta cikin nashi ya kalleta

“Tsoro kike?”

“Aa.”

“Kin tabbata?”

Maryam ta gyada kai tareda dago idanunta ta kalle shi.

“Ka tamayeni shekaranjiya, ko ina tsoro”

“I know.”

“Amma me yasa kaketa tambayata?”

Zaid ya yi shiru  kafin ya ansa 

“Because I want you to feel safe.”

Maryam ta kalle shi.

Wannan karon ba ta yi murmushi ba.

Ta dai kalle shi kawai.

Zaid ma ya tsaya yana kallonta.

“Ki shirya muje mu kwanta”

Ta tashi ta shiga bathroom shima ya wuce dakinshi yayi wanka yasa jallabiya ya dauki laptop dinshi ya zauna kan coffee table ze duba ayukkan shi da schedules dinshi na Amsterdam idan sun sauka, se ya sake samun irin Email ɗin da ya samu jiya ya sake fitowa a screen.

CONFIDENTIAL — NORTHERN CREST HOLDINGS

Ya buɗe.

Wannan karon akwai wani sabon message.

Kada ka yarda da duk wani record da ka samu, An canza wasu daga cikinsu.

Zaid ya tsaya.

Ya karanta shi sau biyu.

Sai ya rubuta:

Wa ya chanja su?

Amsar ta zo bayan ƴa seconds.

Ba abnda zaka tambaya kenan ba, ka tambayi abnda ya faru shekaru uku zuwa biyar da suka wuche

Zaid ya jingina da kujerarsa

Shekaru uku zuwa biyar? Me ya faru?

Ko ya tambayi maryam? Kamar Tasan wani abu,

Sai zuciyarsa ta darsa mishi wani Abu 

Maryam ta san wani abu tabbas 

Amma me ta sani?

Miqewa Yayi ya rufe laptop dinshi ya nufi dakin ta kai tsaye saboda ya tambayeta me ta sani, be tsaya knocking ba, ya shiga da sallama kawai, zaune take kan gado ta qare shirin baccinta, ta dago ta kalleshi a tsawwale, yau batayi niyyar baccee dakin shi ba, saboda rigar baccin da ke jikinta se a hnkali, duk masu rufe jikin suna laundry kuma baa dawo dasu ba, ya kalleta yana ganin yadda siffar jikinta ke bayyane a cikin rigar, rigar baka che, shiyasa hasken fatar maryam ya fito tar a cikin rigar, gabadaya se zayd ya manta abnda ya shigo yi a dakin, ya matso ya zauna kusa da ita ya kama hanneynta yana riqe su cikin nashi, “ya akayi ne, ba Kya jin baccee?” Ya tambayeta yana jin qamshin turarukanta suna shiga jikin shi yadda ya kamata, a bangaren maryam ma qamshin turarukan shi sun cika mata hanci se ta ma kasa ansa mishi, tashi tayi ya dauki hijab dinta da ke ajiye a prayer corner da niyyar sakawa, ai yadda take tafiya cikin rigar baccin ya fara kwanche notikan kan zaid, saboda yadda silk guntuwar rigar baccin ta Victoria’s Secret take lafe a jikinta, tashi kawai yayi ya dauketa cak ya fita ya nufi dakinshi da ita, maryam kam ta fara sabawa da wannan daukar da zaid yake mata amma rigar da ke jikinta yasa gabadaya take jin kanta a tsawwale, seda ya kai dakin shi sannan ya saukar da ita a kan carpet din sallah “kinada arwalla?” 

“Eh inada” 

“toh zamuyi sallah muyi addua Allah ya kaimu lfya gobe, kuma ya tsare mu” ya fadi yana qoqarin saka mata hijab dinta, ta gyada kai 

Ya shiga gaba ya kabbarta sallah, sukayi raka’a biyu, zaid ya dade yana addua sanna ya Kalli maryam yaga tana gyangyadi, tashi yayi ya chire jallabiyar shi sannan ya dauketa, yana daukarta ta tashi dama gyangyadi ne takeyi, tana bude ido ta ganshi ba riga tayi sauri ta rufe idonta, yana kallonta Yayi murmushi kawai ya kwantar da ita kan gado yana qoqarin chire mata hijabi, tayi sauri ta jawo duvet ta rufe jikinta sannan ta chiro hijabin ta miqa mishi, don tasan in yache ze chire hijabin ze iya hadawa da rigarta tunda guntuwa che sosai kuma silk, karbar hijabin yayi yana murmushin yadda ta rufe jikinta, ya nade ya ajiye sannan ya hauro yana rungumo ta sosai jikin shi, maryam ta matse Idonta sosai tanajin yadda ya shigar da ita jikin shi ya nannadeta da hannayen shi, wani irin vibration maryam keji jin yadda jikinsu ya hadu da na juna sosai saboda yanayin rigar jikinta, shi kuma beda ma rigar a jikin shi, hannun shi daya yasa ya zare mata hulla ya saka hannun cikin gashin ta yana murzawa, maryam ta fara shiga irin shock dinnan da take ji amma ta daure saboda tanaso tayi pretending kamar tana baccee, matsowa yayi da fuskar shi kusa da tata sosai har tanajin saukar numfashun shi a fuskar ta, murya chan qasan maqoshin shi ya kirata “Mijn kleintje” gabadaya ta fara rasa natsuwar ta, shi kuma ganin yadda ta qara rintse ido sosai yasa ya qura mata ido yana kallonta, yanajin yadda zuciyarta ke bugawa da qarfi a jikin shi, ji yayi jikinshi na shiga cikin wani irin yanayi saboda yadda ya manna ta da jikinshi, rigar jikinta da babu basuda wani banbanci, yana jin saukar numfashinta da takeyi da sauri a fuskar shi, bata Ankara ba se jin tayi ya fara kissing dinta a hnkali, kamar wancan lokacin maryam ta dauka ko suma tayi, gabadaya jikinta rawa kawai yake, zaid kam hnkalinshi ya fara nisa, kawai abnda zuciyar shi ke raya mishi yakeyi, seda yaji sanyin hawayenta a fuskar shi sannan ya janye a hnkali yana kallon yadda fuskarta ta wanke da hawaye, yasa hannu yana goge mata hawayen a hnkali ya rungumeta yana shafa bayanta, daurewa kawai yakeyi kada ya biye ma zuciyar shi amma ji yake kamar baze iya ba, maryam ta kasa baccee saboda tsoro, seda ta kusan raba dare a jikinshi tanata hawaye daqyar ya samu baccee ya dauketa, yaji ta fara sauke ajiyar zuciya cikin baccin sannan ya gyara musu kwanciya shima Yayi baccin a wahale

Washegari da safe tunda sukayi sallar Asuba basu koma baccee ba, yasa maryam tayi mishi karatu yana kwanche a kan qafarta, seda rana ta fito sosai sannan yache taje ta fara shiri 

Balarabe Mansion yau an tashi da motsin shirin tafiya, mammi tasa cooks daga part dinta sukayi breakfast aka kawo ma su maryam, zaid sama sama yachi abncin don ya fara sabawa da girkin maryam, baya wani jin daadin na cooks

Suitcases din maryam da hand luggage dinta na LV, Drivers suka saka a mota tareda hand luggage din zaid guda daya

Suka fito daga part dinsu suka shiga part din mammi, sun zauna na kusan 30 minutes suna bankwana da Mammi, Mammi ta rungume maryam 

“Ki kula da kanki.”

“In Sha Allah.”

“Ki kula da Zaid ma.”

Maryam ta yi dariya.

“Zan kula dashi mammi”

Mammi ta kalli Zaid.

“Ka kula da ita.”

“I will.”

Fahad ya ƙaraso.

Ya rungume Zaid.

“Bro muje?0

“Yes muje”

Fahad ya kalli Maryam.

“Anty Maryam.”

“Naam yaya Fahad.”

“Amsterdam ta kwace min yaya amarya dai kenan.”

Maryam ta yi dariya.

“Ba kwacewa bane, zamu dawo ai”

“In zaku dawo ku kawo muna wani abu.”

“Me kakeso?”

“Anything, maybe a babygirl or baby boy”

Zaid ya kalle shi.

“Kai Fahad”

Fahad ya yi dariya.

“Okay nayi shuru”

Sai ya kalli Maryam.

“Muje in kai ku”

“Thank you.”

Hajiya Raliya tana tsaye tareda mammi, Ta kalli Maryam, ta ɗaga mata kai a hankali alamar sallama, Maryam ta amsa da Kai tana daga musu hannu alamar bye, Suka fita inda zasu shiga mota

Ta shiga mota tare da Zaid.

A airport…private jet ɗin yana qasa already yana jiransu.

Sukayi sallama da fahad suka shiga, Basu bi wani dogon procedure ba suka wuche

Maryam ta tsaya tana kallon jirgin da tunanin yau zata qara nisa da mama

Zaid ya kalle ta

“First time? Private jet?”

“Ka manta dashi muka dawo daga sokoto”

“Eh haka”

“Zaki saba da shiga ciki”

Ta kalle shi.

“An ya kuwa?”

Zaid ya yi murmushi.

“Too late, Zo muje”

Suka shiga

Maryam ta zauna kusa da window.

Zaid ya zauna kusa da ita, ta fito da wayarta ta kira mama sukayi sallama tana hawaye zaid yana goge mata da handkerchief dinshi har suka qare waya, a lokacin ne bahijja taga message din da maryam ta tura a group jiya, se ga kiranta ya shigo, maganar da sukayi da bahijja yasa ta dan washe daga kukan da tayi lokacin da take waya da mama, seda suka qare magana suna sallama bahijja tache a samo musu baby a Amsterdam, maryam tayi sauri ta kashe wayar don kar zaid yaji, amma ya riga yaji sedai be che mata komi ba se murmushi da yayi, ita kuma ta turo baki

Bayan an gama preparations, jirgin ya fara motsawa yana taxiing, a tare suka karanta “subhanallahdhi sakhkhara lanaa hadhaa wama kunnaa lahu muqrineen, wa Innaa ilaa rabbinaa lamunqaliboon”

Maryam ta kalli Abuja daga window, zuciyarta ta yi wani irin nauyi.

Nigeria.

Mama.

Sai ta ji hannun Zaid ya Kama hannunta ya riqe yana murzawa

Ta dan kalle shi.

“Ready?”

Ta yi murmushi.

“In shaa Allah”

Zaid ya gyara seat belt ɗinsa, sannan ya janyo nata zesa mata, dd nan jirgin ya fara dagawa sama, a hnkali zaid ya furta “bismillah, Allahu Akbar”

Itama ta maimaita 

Jirgin ya fara tashi.

Maryam ta kalli window.

Abuja ta fara yin nisa.

Zaid ya kalle ta.

Ta yi shiru tana kallon sama.

A hnkali ya rada mata

“Welcome to the next chapter”

Maryam ta juyo,  idonta fal hawaye

Zaid ya yi murmushi ya rungumeta yana shafa bayanta

“Shhh, ina tare dake”

Amma a cikin zuciyarsa…

yana tunanin hawayen da ke cikin idonta, yana tunanin email ɗinnnan da aka turo mishi, Northern Crest Three to five years ago, Rahman Balarabe, Bashir me Salati, abubuwan sun yimishi yawa a kai, Kuma yanzu gashi ya wuche Amsterdam.

A inda yake da gidansa.

A inda yake da company.

A inda yake da sirrinsa.


Follow this link to join my WhatsApp group

***

9A764983-0DFC-4DFE-AEF3-454EDF405535.png

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol