Free chapter · Read without an account

THE DOOR

by Nihaal Maalik · KIRAN KADDARA

SOKOTO

Salary din imran na farko ya ninka abnda akayi za’a biya shi so uku, ya dauka ma mistake ne seda yaje finance department yayi complain suka gaya mishi wai a kowane wata ana zabar staff din da yafi kowane staff qoqari a wannan watan (most hardworking staff of the month) se a ninka mishi salary dinshi so uku, wannan zanchen Yayi ma imran matuqar daadi, kuma daga nan yasa ma ranshi in shaa Allah ze qara jajircewa ya zamana shi ze rinqa karbar most hardworking na kowane wata, ya dawo gida da yamma bayan ya tashi daga aiki yana gayama inna da baba abun alheri, sunji daadi sosai sunyi addua sasai, daga nan inna tache mishi idan yayi sallar magrib ya kamata yaje ya gayama mama, da toh ya ansa sannan ya shiga daki. 

Da suka fito daga masallaci sallar magrib ya shiga wurin mama ya tarar da ita da maryam qarama duk hnkalinsu a tashe saboda hauwa koulou bata dawo daga lesson din da mama tasa take zuwa na Jamb ba, ya tambayi mama ko ta kirata 

“Na kirata wai bata samu abun hawa ba kowane ta tare se yache arkilla tayi nisa kuma yamma yayi idan ya shigo baze samu passengers din da ze fita ba” 

“Mama bani numberta se inje in dauko ta, dare na yi be kamata ache tana waje ba”

Mama taji daadi har ranta, ta karanto mishi number yasa sannan ya fita daga gidan, seda ya isa wurin da mama tache mishi suke yin lesson din sannan ya chiro wayar shi ya kira ta, se yaji ringing din waya ta gefen shi, koda ya duba se ya ganta a tsaye tana kallon wayar da ake kiranta da sabuwar number

“Numberta che, kiyi saving” taji an che, tana dago kai taga imran, ta sauke ajiyar zuciya taga Wanda ta sani, Tasan koda wani abu yazo yi a wurin toh baze wuche ya batta a wurin ba,

“Ina wuni” ta gaida shi

“Lfya qalau” ya ansa yana saukowa daga kan mashin dinshi, yayi parking ya shiga wani shago da ke kusa dasu, bottled water me sanyi da yoghurt ya sawo mata saboda yadda ya ganta da alamun ta wahala, ya dawo ya miqa mata ta karba tana godiya, ya hau mashin ya tsaya yana kallonta, kanta a qasa, tana yimishi yanayi da maryam sosai, seda ya hade wani abu da ya tsaya mishi a wuya sannan ya furta “hau muje”

Ta hau kan mashin din suka fara tafiya, tunda suka taso har suka iso qofar gidan ba wanda yayi magana cikinsu, seda ta sauka ta fara yimishi godiya, be amsa ba se tambayar da ya jeho mata “qarfe nawa kuke tashi daga lesson din?”

“Qarfe shidda” ta amsa 

“Idan an qare ki rinqa jirana zan rinqa dauko ki, kada ki fito ki tsaya a titi da yamma, ki bari se idan na iso se in rinqa kiran ki sannan ki fito”

Ta gyada kai “toh in shaa Allah Nagode sosai” sannan suka shiga gidan, se a lokacin imran ya gayama mama abnda ya shigo ya gaya mata dazu, mama Tayi murna sosai hadda yar qwallar ta, tayita yimishi addua, a nan yachi abnci seda aka fara kiran sallar isha sannan yayi arwalla ya fita. 

Tun daga ranar kullun idan imran ya fito daga wurin aiki se yaje ya dauko hauwa koulou sannan su dawo gida tare, mama da inna sosai suke jin daadi suna addua Allah yasa wani abu ya qullu tsakanin su.

Maryam che ke bude Idonta a hnkali daga kwancen da take, Ɗakin har yanzu duhu ne sosai saboda ba’ayi kiran sallar Asuba ba, curtains ɗin sun rufe windows ɗin dakin ruff

Ta juya kanta, taga Zaid yana kwance a gefenta ya matso kusa da ita sosai, hannun shi saqale da ita, Har yanzu yana bacci, Ta ɗan tsaya tana kallon shi, A kwanakin baya, wannan mutumin ya kasance kamar wani stranger a gare ta.

Mutumin da ta aura saboda wani dalili da bai san komai a kansa ba.

Amma yanzu…Ta saba da kasancewarsa kusa da ita, Ta saba da jin muryarsa da safe, Ta saba da yadda yake kula da ita da al’amurran ta, ta Saba da yadda yake rungumeta a jikinshi idan zasuyi baccee har takai ynzu idan be dawo ba bata iya baccee se ta jira shi, Kuma abin da ya fi bata mamaki…ta fara jin daɗin kasancewarsa kusa da ita, Ta yi ƙoƙarin tashi daga gadon a hankali, 

Amma kafin ta kai ƙafa ƙasa…ta ji hannunsa ya riƙe nata, Ta dan tsaya ta kalleshi, bai buɗe ido ba ya fara mata matana

“Ina zakije?”

Maryam ta kalle shi harynzu idon shi rufe yake kamar yana baccee 

“Lokacin fajr ya kusa.”

Ya buɗe ido a hankali.

“Oh!, je kiyi arwallah” 

Ta tashi taje tayi brush da arwallah ta fito shima ya shiga yayi

Bayan sun yi sallah…

Maryam ta zauna a kan prayer mat tana yin azkar.

Zaid ya gama nasa azkar ya kalleta, “hayatee karatun fah?”

Tayi murmushi Tayi bismillah ta fara karanto mishi suratul mu’minoon

Ya qura mata ido yaga yadda take karatun a natse, Zaid kam har ya fada tunanin ta haiho mishi yarinya me kama da ita, kamar yadda yake mafarkin zaune kullun idan tana mishi karatu, qwaqwalwarshi Tana hasko mishi su a zaune maryam tana koya ma diyar su karatun Qurani, a dd nan ta kai qarshen surar, ya kalli fuskar ta, Natural curls ɗinta sun fara leqoewa daga gefen hijab ɗinta.

Ya yi murmushi “hayatee”

Ta ɗago kai.

“Naam?”

“Kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

“Good.”

Ta kalle shi.

“Kai fah?”

“Ni me”

“Ka tashi lfya?”

Sai ya yi shiru yana kallonta 

Maryam ta lura da yadda yake kallonta.

“Me ya faru?”

“Ba komai.”

“Ka na ta kallona.” Ta fadi tana zumburo baki

“Can’t I? Ba na biya sadaki ba?

Ta yi murmushi.

“Yanzu ka fara irin haka ai ai da bakayi”

“Anya? Ynzu dai kika lura”

Tayi murmushi 

“Rouhi”

“Naam my haya”

“Ka canza akan yadda na fara sanin ka”

“Ta yaya?”

“Ban sani ba, Kawai dai nasan ka chnja”

Ya yi murmushi.

“Inaga kin fara ganina dayawa kwanan nan, zan rinqa dadewa a office se kinyi baccee sannan in dawo”

Ta turo baki “A’a ka rinqa dawowa da wuri please”

Ya kalleta ya chije lips dinshi na qasa

“Mu shirya mu fita, lokaci na qurewa kar kiyi missing lecture”

Ta miqe ta shiga bathroom, seda ta fito sannan ya shiga ita kuma ta fara shiryawa kafin ya fito ta sauka kitchen ta tarar da su Samantha a kitchen suna shirya musu breakfast, gaidata sukayi da fara’a itama ta ansa musu da fara’arta, ta fito kitchen da sandwiches da fresh juice ta koma daki ta tarar da zaid yana shiryawa, ta ajiye abncin a coffee table ta zaune tana jiran shi, seda ya qare shiri sannan suka chi abnci suka fita, suna zaune a mota shuru se ya fara magana 

“Kwana biyu bana ganin kina amfani da card din da na Baki, sedai few debits alerts nasan na sayen abnci ne a school, kin dena online shopping da abubuwa, why?”

“Karatu ne Ya fara yimuna yawa, mun dena fita da Susan ma, kullun daga library se lecture, amma yau zanje gidan su after lecture please, tunda gobe Saturday ba school 

“Idan kin qare ki kirani zan aiko driver ya kaiku, ze tsaya har ki qare, idan fita zakuyi daga Chan ya kaiku duk inda zakuje, kiyi amfani da card dinnan Idan zakuyi wani abu, kada ki bari ta biya, banason kiyi amfani da kuddin kowa”

“Okay sir” ta fadi tana dariya

“Im not joking haya, be spending the money, kar ki damu bazasu qare ba”

a dd nan sukayi parking a gaban hall din da zata sauka, yana riqe da hannunta be saketa ba seda yayi kissing hannun sannan ya saketa ta sauka ta shiga class, driver ya ja mota suka nufi office.

Bayan sun qare lecture seda suka jira driver ya iso sannan suka tafi gidansu Susan, mamar Susan taji daadin ganin maryam, sunchi abnci sunyi fira, a cikin firar take tambayar maryam a ina take zuwa gyaran jiki a Amsterdam tunda tanada miji, ta ansa mata da bata taba zuwa ko saloon ba tun da tazo, maman susan tache maza su tashi zata kaita wani wuri, maryam da Susan suka shiga motar da driver ke jiran maryam, maman susan kuma ta shiga tata Motar suna binta a baya har suka isa wani babban wuri da aka rubuta “PHENOMENA Maison of Beauty and Health” sukayi parking suka fito suka shiga ciki, maman susan keta yima Mutanen bayanin abubuwan da zasuyi da yaren Dutch, sannan dayar matar ta shiga da maryam zuwa wani daki, akasa ta cikin wani Abu me kamar rumfa amma a rufe yake se kanta kawai ke waje, wani irin hayaki ke fita daga ciki, ta kai kusan awa daya a ciki sannan ta fito da ita ta saka ta cikin wani babban baho me cike da ruwa kamar ruwan madara da kuma wasu irin flowers a ciki masu qamshi sosai, ta zauna ciki na kusan minti talatin sannan matar ta chiro hannunta tana murzawa da wata flower me kamar soso, se qamshi ke tashi, haka tayita murza jikinta seda ta murza koina sannan ta fara wanke mata kai, seda ta wanke mata gashinta sosai se qamshi yake sannan ta fito da ita daga cikin ruwan ta bata bathrobe ta saka sannan ta zaunar da ita akan wata kujera ta fara busar da gashin, ta gyara mata gashinta sosai tayi mata wani irin abu a kai, shi ba kitso ba kuma shi ba a kwanche ba, yayi kyau sosai, maryam ta kalli madubi taga kanta kamar Wata balaraba, se matar ta nuna mata bathroom ta shiga, an hada mata wasu ruwan wankan masu qamshi sosai da wasu irin shower gel masu qamshin flowers,

Maryam tayi wanka ta fito sannan matar tabi jikinta tana shafa mata wani irin mai me qamshi, har gashinta duk seda aka shafe shi da wani man gashi me qamshin flowers, se ta dauko mata wasu kaya ta bata ta saka, kafin ta qare saka kayan matar ta dawo wani abu a cup me kamar madara amma anyi blending din kankana da dabino da ridi an zuba a ciki, se Yayi kamar smoothie, maryam taji daadin shi sosai tanata sha a hnkali, seda ta kusa shanyewa matar ta miqo mata wata container tache ta dauki pills din da ke ciki ta sha guda biyu, maryam ta duba container din taga an rubuta “natures field eves desire” ita dai bata gane ko na miye ba amma ta karba ta sha, se matar ta saka mata container din a cikin jakar da akasa mata kayan da ta chire sannan suka fito reception, nan ta tarar da Susan da mamanta suna jiranta don su dama wanke kai da pedicure kawai sukayi, Susan ta saki baki tana kallon maryam “Wauw… kijk eens naar jou! Je straalt helemaal” maryam tayi murmushi don ta gane abnda Susan ke fadi tunda ta fara jin Dutch kadan kadan (wow look at you, you’re glowing from head to toe) 

maman Susan ma seda ta yaba kyaun da maryam tayi da irin kyaun gashinta, saboda su nasu gashin ba baqi bane, wata kala che da suke Chema blonde, kamar brown kamar maroon, sunje counter zasu biya maryam tayi sauri ta ciro black card din zaid da ke hannunta, maman Susan na hanata amma taqi tsayawa seda ta miqa musu, ai kuwa ta fara yimata fadah “ba ni na kawo ki ba? meyasa zaki biya? Ai se ki bari se next time idan kinzo ke kadai se ki biya, ko so kike ki nunamin bani na haifeki ba? Ai kamar Susan haka na dauke ki” 

maryam tayi murmushi ta fara bata hakuri “kiyi hankuri mummy, nima na daukeki matsayin mamata, inaso in yima mamata kirki shiyasa” haka dai maryam ta lallaba mummy sannan suka fito tana che mata “Idan Mijinki yaga gyaran da aka yimiki se ya rikice” saboda maman Susan irin Mutanen nan ne da babu ruwansu da kunya, Susan har laabrin samarinta take ba mamanta, maryam tayi dariya tana musu sallama ta shiga motar da driver ke jiranta, Susan kuma tabi motar mamanta suka wuche gida maryam ma suka kama hanyar gidan su. 

Koda maryam ta shigo gida ta tarar zaid zaune a parlour, Suit ɗinsa a jikinsa alamar be dade da dawowa ba, ya ɗan sassauta tie ɗinshi daga wuyan shi, Ya ɗago kai da yaji motsin ta

“Laa yau Ka dawo da sauri.” Ta fadi da alamar jin daadi a muryar ta

“I’m exhausted” kawai ya furta yana kallonta

Ta ajiye jakar ta, ta matso kusa dashi 

“Sorry, ka ci abinci?”

“Not yet.”

“Me yasa?”

“Na jiraki ne” duk maganar da yakeyi idonshi qur yana kanta, kallonta yake yaga Tayi wani irin kyau har sheqi takeyi

Maryam ta kalle shi.

“Jirana kuma?”

“Na jira ki muchi tare.”

Ta yi murmushi.

“Kawai inaso mu chi tare”

Sai ta zauna kusa da shi.

“Toh gani”

Ya kalleta, yasa hannu ya zame hullar da ke kanta tareda gyalen, yayi shuru yana kallon gashinta da ya watso a barbaje, seda ya kalleta na dan lokaci sannan ya miqa hannu yana tattare gashin kuma yana shafa fuskarta a hnkali, da mamakin wane irin kitso ne wannan, yayi mishi kyau sosai 

Samantha che ta zo ta kawo musu abnci a inda suke, maryam tana qoqarin chire hannunshi amma yaqi bari, Samantha se murmushi kawai take ta ajiye ta wuche, tare suka chi Maryam tana ba shi labarin wani lecturer ɗinsu yadda yake matsa mata da tambayoyi a class, 

Zaid ya dan daure fuska

“Meyasa to? Ai ba ke kadai che a class ba, ko in chanza miki school ne?”

Maryam ta bude baki tana kallon shi 

Shima ya kalle ta.

“Me kike kallona haka?”

“Ba komi.”

Haka suka qare chin abnci fuskar shi a daure,

Bayan dinner, Maryam ta shige bedroom dinsu da sauri ta wuche toilet, tanajin wani abu a jikinta ta dauka ma ko period ne har tana mamaki gabadaya Yaushe ta gama period dinta, se taga bashi bane, tayi tsarki da ruwan dumi ta fito, Ta buɗe wardrobe, Ta ɗauki wani simple satin nightwear na DKNY, Ta shiga closet ta chanja ta fito, ta dauko hijab dinta tasa, jikinta se wani iri yake mata kamar tanajin kasala da mutuwar jiki, a dd nan zaid ya shigo dakin, Ya tsaya na ɗan lokaci yana mamakin yadda kullun idan tasa kayan baccee se ta saka hijabi, kullun idan Tayi baccee se ya chire mata hijab amma kuma bata barin baccee dashi 

“Kin taba shiga cinema da ke underground?”

Maryam ta kalleshi underground na gidan nan cinema ne?” 

Ya gyada kai “eh private cinema dina”

“Ban taba shiga ba, inajin tsoron undergrounds, amma bari inje in gani, inason cinema, mun taba zuwa da Susan” ta fadi tana miqewa tsaye ta fita daga dakin, zaid kuma ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya yasa wandon kayan baccee kawai ya fita ya nufi underground din, kwanche kan qatuwar sofa din me kamar gado ya tarar da ita, ta daura pillows dayawa ta jingina dasu, ta chire hijab dinta ta ajiye a gefe ta dauko wani babban throw blanket cikin wa’inda ke ajiye a gefe ta lullube jikinta dashi, remote na riqe a hannunta ta kunna movie tana kallo, Yayi tsaye kawai yana kallonta, kamar inuwa ta gani ta jikin tv se ta juyo a tsorace ta ganshi a staye yana kallonta, sauri ta juyar da fuskar ta wurin tv don ta kasa sabawa da wannan rashin sa rigar tashi, zagayowa yayi ya hau kan kujerar ya zauna kusa da ita, yasa hannu yana shafa fuskar ta yana jaye gashin ta da ke kan fuskar ta, shidai wannan gyaran da aka mata yayi mishi kyau sosai, matsowa yayi ya kwanto da ita akan kafadar shi hannunshi daya yana shafa gashinta dayan kuma yana murza hannunta da ke cikin nashi, tanata kallon tv shi kuma idonshi yana kanta, ya kasa gane wani irin sheqi da yaga tanayi yau, ga hannunta da yake tabawa kamar ya qara laushi, ta dan dago kai ta kalleshi

“Menene?”

“Gashin ki…yayi kyau sosai, kuma naga se glowing kikeyi”

“Tayi murmushi kawai”

“Rouhi”

“Umm haya”

“Ka daina kallona haka ya isa manah”

Ya yi murmushi.

“Meyasa?”

“Saboda…”

Ta kasa ƙarasawa

“Saboda me?”

“Kanasa ina Jin kunya”

Zaid ya yi murmushi

“kunya ta?”

“Tayi shiru.”

Ya qara matsowa da ita sosai cikin jikinshi 

Maryam ta ɗago ido ta kalle shi, yasa hannu yana shafa fuskar ta a hankali, ya sauke hannunshi kan lips dinta yana shafa su a hankali 

Shiru…maryam ta kasa motsi saboda irin wannan shock din da take ji yau se ya hadu da wani irin mutuwar jiki, numfashinta ya fara barazanar daukewa..shuru Babu wanda ya yi magana na dan lokaci se yasa hannu ya dago da fuskarta ta kalleshi

Kallo ɗaya, Na dogon lokaci, ya kafeta da idanun shi kuma ya hana ta kawar da nata saboda yadda ya riqe fuskar ta, Sai ta sauke idonta qasa kamar zata rufe

Zaid ya kalleta sosai Yana tunani a ranshi, I love her so much amma she’s so small and young, Anya zan iya nuna mata soyayyata kuwa? Ni kaina abun ya fara fin qarfina ynzu qila bazan iya daurewa har zuwa sadda nike tunanin zata qara girma ba

“Haya”

“Naam?”

“Kalle ni”

Ta ɗago idonta

Ya yi murmushi kaɗan, Ta sauke idonta da sauri ganin wani irin yanayi a idonshi da ta kasa fassarawa, ga murmushin da Yayi se taji kamar cikin kanta murmushin ke shiga yana haifar mata da wani irin weakness a gabadaya jikinta

Zaid ya ɗaga hannunta ya daura a kan wuyan shi yanajin kamar kan shi na juyawa da qamshin jikinta da yake shaqa, Maryam bata janye hannunta ba saboda duk ya kashe mata jiki da idanun shi

“Haya…” ya kira sunanta da wata irin murya seda duk jikinta ya karba 

Dakyar ta iya chewa “umm”

“Kina Jin daadin zama nan?”

Kai kawai ta gyada don Jin take kamar muryarta ta dauke kwata kwata

“Kina Jin dadin zama dani?” Ta sake jin wata tambayar da wata irin murya kamar a tsakiyar kanta muryar ke shiga

Wannan karon daqyar ma ta iya gyada kanta

Zaid ya ɗan matse hannunta ya na jin wani abu na ratsa dukan jikin shi saboda yadda take abubuwa very slow gabadaya kunna shi takeyi, hannu yasa yana zare ribbon din da ta kama gashinta, ya fara daga wanda ya zubo akan fuskar ta, hannu yasa ya jaye throw towel din da take lullube dashi, da sauri tun kafin towel din ya zare ta rungume shi saboda yanayin rigar da ke jikinta batason ya gani, yaji wani irin shock har cikin qwaqalwar shi saboda yadda yanayin rigarta yake very light kuma satin material ne, dam dam haka qirjin maryam ke bugawa, shi kuma zaid se sauke numfashi yake da wani irin qarfi don ji yake kamar babu iskar da ze shaqa a dakin jin yadda maryam ta qanqame shi sosai a jikinta 

Jikin maryam na rawa ta furta mishi “Rouhi” a kunne, yadda Yaji saukar maganar ta a kunnen shi yasa Yaji kan shi na barazanar bugawa, ga wani irin qamshi na flowers da Gashin kanta ke fitarwa 

A hankali ya furta “things are about to get dangerous”

Maryam kamar zatayi kuka ta sake kiran shi “rouhi”

“Shhh” ya rada mata kunne, ita kuma yadda taji lips dinshi a kan kunnenta yasa ta qara qanqameshi sosai, zaid da keta qoqarin controlling din kanshi gabadaya ya fara loosing control jin yadda take qanqameshi, yayi kissing goshinta yanata kokuwar danne abnda yakeji a jikinshi amma ya kasa, a hnkali ya fara kissing dinta, yanajin wani abuna fizgar shi, maryam jikinta na rawa amma bata sakeshi ba

Miqewa tsaye yayi da ita a jikin shi ya fara tafiya har ya fito daga underground ya fara haurawa stairs, ya wuche dakinsu na sama ya hau kan gado, maryam bata yadda ta sakeshi ba saboda Batason yaga rigar jikinta, zaid kam chigaba yayi da abnda zuciyar shi ke ingiza shi yayi, saboda gabadaya tunanin shi ya gushe daga wannan duniyar, qoqarin chire rigar jikinta da yakeyi yasa maryam tayi yunqurin dakatar dashi amma hannayenshi yasa yana fizgar rigar ta balle bat, jin hannunshi na taba ainahin fatar jikinta yasa sauran notikan kanshi gabadaya suka ida kwanchewa, maryam se qara riqeshi takeyi a qoqarinta na kare jikinta don kada ya ganta, batasan wannan irin rungumar da take mishi tana manna ainahin jikinta da nashi shine yake ida hargitsa zayd gabadaya 

A wannan daren…kusancinsu ya kasance fiye da yadda ya taɓa kasancewa, tun maryam bata gane hanyar da zaid yake dauka ba har ta fara ganowa, tana qoqarin jayewa amma ina, ta makara, da lallashi da wata irin murya me kashe jiki wadda shi kanshi be taba sanin yanada irin wannan muryar ba har yakai inda yaqe buqatar kaiwa, wani irin abu yakeji yana yawo a jikinshi kamar bashi ba, wani irin yanayi ne da be taba kasancewa a cikin shi ba, ya rungumeta sosai a jikinshi yana jin wani irin yanayi da be taba sani ba, hawayenta da yaji suna sauka a jikinshi yasa ya kwantar da ita a hnkali, Ya tashi a daddafe ya shiga toilet yayi wanka sannan ya hada ruwan dumi a bathtub yazo ya dauketa ya shiga ciki yana rungume da ita a jikinshi, ruwan na ratsa jikinta ta saki wani kuka a wahale da sautin shi ke fita a hnkali, yana riqe da ita se shafa bayanta yake alamar rarrashi, seda ruwan suka huche ya sake hada wasu ya zauna da ita sannan yayi mata wanka, ya daukota ya dawo da ita yasa mata wata shirt dinshi da tayi mata yawa sosai ya kwantar da ita a hankali sannan ya kwanta ta bayanta ya qanqameta. 

Har baccee ya fara daukar zayd addua yake yima maryam a ranshi, cikin dare Zafin jikin maryam ya farkar da shi, ya tashi yaji sheshekar kukan maryam a hankli, ya qanqameta yanajin yadda Zafin jikinta ke ratsa nashi, ya dauko wayar shi ya kira assistant dinshi yache “i need a female dr at my house immediately” ya katse kiran ya tashi ya debo ruwa a container da towel yana jiqawa yana goge mata goshinta da wuyan ta a hankali, after 5 mins ya sake kiran assistant dinshi ze fara mishi ihu yache “sir she is at the gate but the security won’t let her in” zaid ya katse ya kira security “let her in” kawai ya furta ya katse call din, ya sauka downstairs ya hauro da ita sama har zuwa wurin da maryam take, tayi mata allura tana rungume a jikin zaid sannan tayi qoqarin daidaita temperature dinta, ta bashi sauran drugs sannan ta tafi.

Zaid ya zama overwhelmed da wani irin feeling, yanata tunanin yarinyar da yake ganin ta very small and fragile Itache tasa shi cikin wannan yanayin na farin ciki da annashuwar da be taba samun kansa ciki ba, yana cikin wannan tunanin yaji ta fara sauke numfashi a hnkali alamun baccee ya dauketa, ya gyara mata kwanciyar ta a jikin shi a haka ya kwana zaune riqe da ita har asuba, daqyar ya tada ta Tayi sallah, shi ya dauketa ya kaita toilet Tayi arwallah ya dawo yasa mata hijab sukayi sallah, da ya qare azkar ya chire mata hijab ya dauketa ya kaita kan gado ya bata magungunan da dr ta aje sannan ya kwantar da ita ya rungumeta suka koma baccee

Basu tashi ba se 11:15am

Maryam ta farka a hankali, Ta buɗe idanunta, Zaid yana kusa da ita yana baccee, abubuwan jiya da dare suka dawo mata a hankali

Taji qarfin jikinta ba kamar jiya da dare ba amma jikin ta da sauran zafi, Ta ja quilt ɗin ta rufe fuskarta kaɗan.

Zaid ya buɗe ido, Ya kalleta.

“Ina kwana, kin tashi lfya? Ya kikeji?”

Shuru bata ansa ba

“Haya kalleni manah”

Bata ko motsa ba

A hnkali ya jawota jikinshi yana chire quilt din da ta rufe fuska dashi, ya kalleta idonta ya ciko da hawaye har sun fara zubowa, ya jawota ya rungume yana patting bayanta a hankali, Ta jingina kanta a jikinshi ta chigaba da hawaye se taji muryar shi

“Good morning, Mrs. Zaid Rahman Balarabe.”

Bata ansa ba

“Haya, ke kika chemin kinason baby ynzu ai zaki samu in shaa Allah”

Batayi magana ba se qara sautin kukanta da tayi 

“Haya..” 

bata ansa mishi ba still

“I love you..I love having you here, right here in my arms”

Tayi shuru hawayen suka sake gangaro mata 

Sai ya kissing goshinta, “shhhh it’s okay”

Haka yayita lallashin ta har ya samu ta dena kukan, shi ya sauka ya dauko breakfast ya hawo sama dashi, pancakes ne da fruits, se kuma tea, ya bata tasha sannan ya sake kwantar da ita, yau baze fita aiki ba dama yau Saturday, ze tsaya gida ya kula da ita, seda ta koma baccee sannan ya fito ya sauka qasa study office dinshi, yana hawowa time to time yaje duba ta har rana tayi 

Wuraren 1:30pm ta tashi baccee, saukin ta daya yau Saturday da batasan yadda zaayi taje school ba saboda irin Zafin da take ji a qasan ta, duk da dai ynzu yayi saukee amma still tana dan ji

Ta dauko wayarta zata duba time se taga message daga unknown number, ta bude, hoto ne, wannnan qofar da ke garden din Abuja 

Maryam ta daskare.

Tun ranar farko da ta ga qofar nan, take tunanin akwai wani abu a ciki, me yasa aka aiko mata da hoton qofar? Ta yi zooming hoton Ƙofar sosai kamar me qoqarin gane wani abu

A ɗayan ɓangaren gidan…Zaid yana cikin study ɗinsa, Ya buɗe original records ɗin Northern Crest, Ya tsaya a kan wani document.

REFERENCE: FILE 17 — PRIVATE ARCHIVE

Sai daga qasa aka rubuta:

Balarabe Mansion — Abuja

Zaid ya ɗaga kai, Wannan ba zai yiwu ba, impossible, Ya ɗauki wayarsa, Kafin ya kira kowa…wani message ya shigo, wannan qofar da take ta Bayan garden dinku a Abuja, A nan ne shafin da ya ɓace ya fara”

Zaid ya daskare, A wannan lokacin…Maryam tana kallon tata wayar, Message ɗaya ne ya shigo, kada ki koma Abuja ke kadai, ki koma tareda zayd


Follow this link to join my WhatsApp group

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol