Free chapter · Read without an account
A LOVE UNFOLDING
Maryam tunani take me ake nufi da kada ta koma Abuja ita kadai? Ta dade zaune tana wannan tunanin kafin daga qarshe ta tashi ta shiga bathroom, seda ta sake gasa jikinta dan taji daadin yadda taji ruwan Zafin jiya, Ta cika bathtub ta zauna ciki tana jin yadda ruwa ke shiga jikin ta
Zaid yayita karanta message din “wannan qofar dake Bayan garden dinku cen Abuja, A nan ne shafin da ya ɓace ya fara” me ake nufi da haka? Shine abnda yakasa ganewa, a sanin shi wannan qofar tun Bayan rasuwar baban su babu me shiga ciki, dama babansu da yanada rai shi ke ajiye abubuwan office a ciki, toh ko dai ya tambayi maryam ne? Yanada tabbacin tasan wani abu tunda tayita tambayar shi gameda kofar, kai baze iya tambayar ta ba cikin wannan yanayin da take ynzu, a zabure ya miqe da sauri don yaje ya dubata saboda lokacin sallar zuhr ma yayi
Bude qofar dakin yayi a hnkali ganin bata kan gadon, yasan bazata wuche bathroom ba, kai tsaye ya nufi kofar bathroom din ya bude, zaune ya ganta cikin bathtub Idonta a lumshe kuma duk sun kumbura, fuskar ta tayi pink alamar kukan da tasha, takowa yayi a hnkali yazo gaban tub din ya tsugunna yana kallonta, maryam batasan ma ya shigo ba saboda kofar bata kowane irin sound don haka bataji qarar budewa da shigowar shi ba, nauyin idanu taji kamar ana kallonta, a hankali ta bude idonta ta ganshi tsugunne gabanta fuskar shi dab da ita
“Ya jikin ki?”
Gabadaya kunya ta rufeta ta rasa me zatayi kawai se ta maida Idonta ta rufe
Ya lura da yadda kunya ta rufeta se kawai yakai bakinshi a kan dan Qaramin lips dinta da sukayi pink saboda yadda ya wahalar dasu jiya, ya fara kissing dinta a natse, bude idonta tayi da dan sauri saboda abun yazo mata unexpected , tayi sauri ta rufe idon, ganin yadda yake kallonta, bata jaye ba kuma bata hanashi ba seda ya janye don kanshi.
Batajin zata iya bude idon ta dan kunya, ta fara tunanin ko dai ta daure tace ya bata space ta qarasa wankan, se taji yana mata magana a hnkali yana shafa gashinta
“In taya ki wanka” ya fadi yana saka hannun shi cikin ruwan tareda shafa chinyar ta
Da sauri ta girgiza mishi kai haryanzu bata bude ido ba
Murmushi yayi, ya chire hannunshi yayi kissing dinta a goshi ya fita ya rufe mata kofa
Da sauri tayi wanka ta fito don gudun kar ya dawo, tana takawa a hnkali daure da bathrobe a jikinta, yana zune kan gadon yana kallon yadda take tafiya a hnkali, tausayinta ya Kama shi, tasowa yayi ya riqo ta ya zaunar da ita kan gado ya kawo mata abubuwan da yasan zata buqata na shiryawa sannan ya dauko mata chiffon gown ash color ya ajiye mata kusa da ita sannan ya shiga bathroom shima
Kafin ya qare wanka ya fito maryam har ta qare shiryawa, tare sukayi sallar zuhr, bayan sun qare shi ya sauka dining ya debo musu abnci ya dawo, suka fara chi a hnkali
“Haya, banason shurun nan, punishment din ya isa haka ki yafe min manah”
Zumburo bakinta kawai tayi bata chemishi komai ba
“Pleaseee hayatee..” ya sake fadi
Ta dago kai ta kalleshi sannan ta mayar da Idonta kan abncin
“Kin yafe min?”
Ta gyada kai sannan tache “amma se idan bazaka qara ba”
Zayd ya zaro ido qasa qasa yana chewa “tabb ai ynzu ma na fara”
“Me kache?”
“Chewa nayi ya zaayi in yadda in sake saka haya dina kuka” ya fadi yana jan kumatun ta
Batache komai ba suka chi gaba da cin abncin har suka qare ya bata ruwa tasha sannan ya sauka da plates din.
Haka suka wuni a daki yanata biye ma duk shagwabar maryam har dare sukayi shirin baccee suka kwanta, yana rungume da ita yayi musu adduar baccee tanata qanqame jikinta saboda tsoro, suna nan kwance shiru har zaid ya fara bacci.
Dare ya yi nisa amma bacci bai ɗauki Maryam ba, Tana kwance jikin Zaid, tana kallon fuskarsa cikin duhun ɗakin, yayin da kalaman da ta karanta a saƙon da ba ta san wanda ya aiko mata ba suke ta maimaituwa a cikin tunaninta. “Mijinki yana kusa da gaskiyar fiye da yadda kike zato.” Ta daga kanta a hankali ta kalli mijinta. Shin da gaske Zaid ya san wani abu game da mahaifinta ko yayarta da bai gaya mata ba? Ko kuwa shi ma yana neman amsoshin tambayoyin da suka daɗe suna damunta ne? Ta yi tunanin ta tambaye shi gobe da safe, amma a ƙarshe ta yanke shawarar tayi shuru kawai, Ba ta son ta fara sabuwar rana da tambayoyin da ba ta san inda za su kai ta ba.
Da asuba ita ta fara tashi ta qura ma zaid ido tana kallonshi tanata tunanin abubuwa da suka faru tun haduwar ta dashi da yadda take tunanin bazata iya zaman aure dashi a da ba, amma ynzu bata iya bacci se tare dashi, ta tuna abubuwan da suka faru shekaranjiya da dare, bata taba tunanin irin wannan rayuwar da zaid ba, amma ynzu bata jin zata iya rayuwa ba tare dashi ba saboda ta tabbatar da ynzu ita cikakkar matar shi Che, bude ido ya fara yi a hankali lokacin ta tashi ta zauna a gefen gadon. Ya miƙa hannu ya kama nata, ya jawota jikin shi, yana kallonta da murmushin da ya saba yimata ynzu wanda kesa ta manta da duk abin da yake damunta.
“Me ke yawo a wannan ƙaramin kan naki tun da sassafe?” ya tambaya cikin muryar barci. Maryam ta yi murmushi ta girgiza kai “Ba komai.” Ya ɗaga gira “na san fuskarki idan kina ɓoye wani abu.”
Ta ture hannunsa a hankali tana murmushi
“Ka tashi muyi sallah”
Shima murmushin yayi, sai dai cen qasan murmushinta, akwai tambayoyi da take tsoron amsoshinsu. a lokacin da suke shirin fuskantar sabuwar rana, rayuwarsu tana dab da sauyawa ta hanyar da babu wanda ya yi tsammani.
Tare sukayi sallah kuma yasa maryam tayi mishi karatu kamar kullun, yau kam seda ya gayama maryam abnda yake mafarki daga zaune kullun idan tana mishi karatu da Asuba.
Hannuwanta cikin nashi yana murzawa har ta qare karatun suratul Luqman, ya kalleta
“Haya Allah ya bani baby girl da zata rinqa yimin karatu kamar irin naki, kullun se in yita tunanin Gaki nan zaune kina koyama babyn mu karatu”
Maryam murmushi kawai tayi batache komai ba
Tashi tsaye yayi ya chire jallabiyar jikinshi ya dauki maryam har kan gado sannan ya fara qoqarin chire mata hijab, seda ta jawo duvet ta rufe jikinta sannan ta sakar mishi hijab din ya ajiye shi tareda jallabiyar shi sannan suka kwanta suka koma bacci
A hankali maryam ta fara bude idonta lokancin 10am daidae, abu na farko da ta fara gani shi ne fuskar mijinta, wanda yake kwance a gefenta cikin kwanciyar hankali. Hannunsa yana zagaye da kugunta, yayin da fuskarsa take nuna alamar natsuwa da kuma dadin da baccin yake mishi, ta danyi murmushi,
Tun lokacin da suka dawo Amsterdam, ta fara fahimtar wani sabon hali na Zaid da ba ta saba gani ba. A wajen mutane, shi ne mutumin da ba kasafai yake murmushi ba, wanda kallonsa kaɗai zai iya sa mutum ya nutsu, Amma tsakaninta da shi, akwai wani Zaid daban, mai yawan son ya kyautata mata yasa ta farin ciki, mai son ya ji muryarta, kuma wanda yake neman kulawarta fiye da yadda take zato duk da be furta hakan ba.
A hankali tayi ƙoƙarin cire hannunsa jikinta ta tashi amma sai ya ƙara matse ta jikinsa.
“ina zaki da sassafen nan?” ya tambaya cikin muryar bacci.
Maryam ta juyo ta kalle shi.
“Da sassafe? Karfe goma fah”
Ya bude ido yana kallon direction din da agogon dakin yake, sannan ya juyo ya kalleta, baccin ya mishi dadi sosae dan besan har lokaci ya wuce haka ba
“Idan munyi breakfast zamu fita”
“Ohk Ina zamu?” Ta tambaya tana kallonshi
“Me yasa kike tambaya? Kina tsoron zan sace ki ne, ko kuwa kina fargabar abin da mijinki zai yi da ke idan mun je wurin?”
Ta yi dariya a hankali kafin ta ture hannunsa ta sauka daga gadon.
“Ina zakije?” Tsaya ki amsa min manah”
Ta shige toilet tana murmushi
Bayan tayi wanka ta fito tana shiryawa a natse tana rera waqar shatbiyya wadda Imam Abu al-Qasim al-Shatibi ya rubuta, cikin irin muryar da Shaykh Mishary Rashid Alafasy ya rera ta
Duk inda tayi zayd na binta da idanun shi
Seda ta qare tayi kyau sosae cikin riga cream mai laushi ta balmein, da dogon wando camel brown, sannan ta saka doguwar jacket itama me launin camel brown, ta dauko yar qaramar handbag dinta da veil na Prada
Sai ta juya ta ga Zayd kwanche yanata kallonta daga kan gado.
Seda tayi murmushin ta me kyau sannan ta juya hannu alamar ‘menene’
Ya girgiza kae shima alamar ‘bakomai
Ta qara fadada murmushin ta “Ba kache zamu fita ba? Ko ba wani abu da zakayi yau?”
“Inada su dayawa ma, Amma kallon ki ya fi mini daɗi.”
Maryam ta yi ƙoƙarin ɓoye murmushinta.
“Allah na gode da ka bani mata me kyaun hali da kyaun zuciya, idan na ɓata, ke ce za ki nuna min hanya naga alamar ke malama che a boye”
Ta girgiza kai tana murmushi
“Kae da kake babba ae sedae ka nuna mini” ta fadi tana zumburo baki
“Babban ma ai ana nuna mishi tunda mutum baya wuce kuskure uhm.”
Shuru tayi don ta rasa abnda zatache mishi
Dariya ya yi, sannan ya miƙe ya tako zuwa inda take yayi kissing goshinta sannan ya shige bathroom, Wucewa tayi wurin da jerin takalminta suke ta dauko brown color heels na Prada Sannan ta zauna kan gado tana jiran shi
Ya fito ya shiga closet ya shirya cikin riga me dan kauri cream color me turtle neck, yasa wando black da jacket doguwa chocolate brown, ya dauko black leather Chelsea boots na kampanin Christian Louboutin
Seda yazo kusa da ita “shall we?” ya fada yana miqa mata hannun shi ta riqe ta miqe tsaye
Tare suka sauka qasa suka wuche dining sukayi breakfast sannan suka fita, shi ke driving da kanshi hannunshi daya cikin nata har suka isa wani wuri da taga an rubuta “Rijschool Amsterdam”
Parking Yayi suka fito suka shiga wurin a tare,
Direct wurin counter din suka wuche zaid na magana da mutumin da ke wurin da yaren Dutch, maryam ta dan fahimci abnda suke cewa sabida tanajin yaren ynzu ba laifi, ta fahimci driving school ne ya kawota yake qoqarin yimata registration
Seda suka qare sannan yache mata ze tafi ya batta a nan se after 3 hrs ze dawo ya dauketa
Wata mata tazo tana gaisawa da maryam sannan tache tazo suje, tayi sallama da zaid tabi matar, wani daki suka shiga wanda aka rubuta VIP a sama, akwai wasu dakuna a gefe da students ke ciki teachers suna yimusu bayani akan driving amma ita wanda take ciki ita kadai che, matar tache mata ta zauna tana mata nuni da kujera, seda ta zauna sannan matar ta bata wani littafi ta fara yimata bayani da turanci akan driving da abubuwan mota gabadaya, a natse take yima maryam bayani cikin qwarewa wanda maryam ta fahimta sosai har tana ganin kamar idan aka bata Motar a ynzu ma zata iya tuqawa. Seda suka qare matar ke chemata monday zasu fara field class, mijinta yache tana zuwa school don haka class din yamma za’a yimata na 1 week
Daga nan suka fito, ta tarar da zaid a waje yana jiranta
Takowa takeyi zuwa wurin shi Tana murmushi har ta iso ya miqa mata hannunshi yana murmushi ta riqe suka fito tare
Shopping mall suka wuche daga nan zaid na complain chewa bata amfani da card din da ya bata har suka isa
Shagon perfumes suka fara tsayawa, shi da kanshi ya zabi turarukan da yakeso ta rinqa amfani dasu, tanata mamakin duk turarukan da ke gida amma ya kwaso mata wa’innan kamar za’a bude shago
Nan suka bar turarukan suka bada address na gidan su sannan suka fita suka chigaba da tafiya cikin mall din, tun daga nesa Wata small Hermés handbag ta dauki hnkalin maryam sedae ganin price tag dinta yasa tayi kamar bata gani ba ta ci gaba da kallon wani wurin, zayd ya Lura da ita se kawai yaja hannunta suka shiga shop din har wurin handbag din, ya dauki jakar sannan yache ta qaro wasu da suka yimata kyau, seda ta zaro ido waje tana kallon shi, tana girgiza kae “sunyi tsada sosae fah”
Seda ya kamo hannunta yayi kissing
“Just spend your time with me, and I will spend the money”
Kasa chewa komi maryam tayi se kallon zaid take, ganin ba dauka zatayi ba yasa ya dauko mata wata qaramar zara bag dan ya lura tanason qanan bags ya hada da ta farkon suka biya suka fita daga shagon bayan sun bar musu address, wani restaurant da ke cikin mall din suka shiga suka chi abnci sannan suka wuche gida, basu wani dade da zuwa gidan ba kayan su suka iso bakin maryam har kunne dan taji dadin kayan sosae se godia take ma zaid tana murmushi,
Da dare bayan sunyi shirin bacce sun kwanta zayd ya jawo maryam jikinshi se ta riqe hanayen shi a nata, murmushi yayi saboda yasan abnda take tsoro, qyaleta yayi ta riqe hannun hr ta fara baccee sannan shima yayi
Da Asuba bayan sunyi sallah basu koma bacci ba, saboda yau Monday, shirin fita kowanensu keyi, suka shirya tsab, Seda zaid ya kae maryam school ya gaya mata idan ta qare lecture driver zezo ya dauketa ya kaita driving school ta gyada kae tareda cewa
“Please kaci abincinka, kakka zauna da yunwa”
Ya yi murmushi yana kallonta
“Ya kike yimin magana kamar mammi”
Itama murmushin tayi
“saboda kai ba ka iya kula da kanka se an kula da kai, dama mammi tache in kula da kai”
Ya yi murmushi yana kissing hannunta
“Ki shiga class, take care”
“You too, bye”
Zaunawa tayi class Tana jiran susan ta shigo, se ta fara tunanin yadda rayuwarta ta canza cikin ɗan lokaci. A baya, ba ta taɓa tunanin za ta taɓa zama a wata ƙasa mai nisa tayi rayuwa ba, hr tayi jami’a a can, ga kuma auren mutumin da a da take jin tsoronsa.
Amma yanzu, abubuwan da suka taɓa zama kamar mafarki sune suka zama rayuwarta ta yau da kullum.
Sai dai har yanzu tana kewarsu mama, safiyya da bahijjja da kuma Aisha, wadda har yanzu rashin sanin inda take yake mata zafi a zuciya.
Ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe wayarta domin duba WhatsApp messages dinta saboda rage wannan tunanin, tana tsakiyar chatting dinta taji Susan na kiranta
“Maryam!”
Susan ta ɗaga hannu tana yi mata waving
Maryam ta yi murmushi Tana kallonta har ta qaraso wurinta
“Good morning sweetheart”
“Good morning! You’re late today”
Susan ta kalli agogonta.
“I’m not late, there’s still 10mins left before the lecture starts.”
Sukayi Dariya a tare, Susan bata dade da zaunawa kusa da maryam ba Lecturer ya shigo ya fara bayani, Maryam ta fitar da littattafanta, yana bayani ita kuma tana rubuta muhimman abubuwan da yake faɗa.
Karantu takeyi da gaske, Ta yi niyyar yin amfani da damar da ta samu a wannan jami’a domin ta inganta kanta, da rayuwar ta ma gaba daya.
Sun tsaya break bayan sun qare wannan lecture din kafin Su shiga wata, Susan ke tambayar maryam
“Maryam, kin gama assignment din da aka bamu ranar Friday?”
“Na kusa gamawa. Ina so in sake duba wasu reports kafin inyi submitting”
“Kinyi ƙoƙari gaskia Ni har yanzu ina fama da shi ban wani yi nisa ba”
Maryam ta yi dariya kawai
“Maryam kina son karatu kamar yadda nike son bacci”
“Ke dai kawai teasing dina kikeyi”
“Gaskiya nake faɗa!”
Suka yi dariya tare.
Daga baya, suka zauna suna tattauna aikin da aka ba su. Maryam ta taimaka wa Susan da wasu bayanai
A hankali a hankali, Maryam ta fara sabo da rayuwar jami’ar. Tana da mutanen da za ta yi hira da su, tana koyon abubuwa, kuma tana samun ƙwarin gwiwar cewa za ta iya cimma burinta daga yanayin mu’amalarta da students da lecturers duka
Amma da ta samu ɗan lokaci ita kaɗai, zata buɗe wayarta ta shiga duba hotunan Mama da na ƙawayenta, tana kewarsu sosae, ynzu ma hakane, suna zaune kafin lecturer ya shigo ta bude gallery din wayarta tana kallon pictures
Ta ga wani hotonta tareda da Safiyya da Bahijja.
Murmushi ya bayyana a fuskarta, amma bayan ɗan lokaci sai ta ji wani irin kewar gida ya mamaye zuciyarta.
Muryar Susan taji tana tambayar ta “are you okay?”
Maryam ta kulle wayarta tana qaqaro murmushi
“I’m okay, just missing home”
Susan ta gyada kai cikin fahimta
“Sorry dear, you’re even doing great so far, and don’t worry you have me” ta qarashe zanchen tana hugging din maryam
Maryam ta yi murmushi.
“Thank you Susan”
Ta san tana samun sabuwar rayuwa me inganci amma hakan ba ya nufin ta manta da tata tsohuwar rayuwar ba, gidan su iyyenta,kawayen ta harma da garinsu.
Zaid yana cikin makeken office dinshi da baa jin komi se qarar Ac da flipping pages da yake yi, yana duba report papers na wani babban aikin da company dinshi ke shirin kammalawa.
A gabansa akwai babbar apple desktop, wasu files, da kuma schedules dinshi na ranar.
“Sir, the Amsterdam partnership documents are ready for your review,” assistant dinshi ya faɗa bayan ya shigo.
Zaid ya ɗaga kai.
“Leave them on my desk,
I’ll review them before the meeting.”
“Yes, sir.”
Assistant din ya fita yana rufo qofa
Zaid ya koma ga computer din da ke gabansa, amma se wayarsa ta yi vibrating
Saƙo ne daga Maryam.
Maryam: “by 3 zan qare lecture please ka aiko da driver da ze kaini driving school, I hope kachi lunch? It’s already past 1”
ya yi murmushi sosae tareda daukar wayar ya jingina jikin kujera sannan ya mata reply
Zaid: okay Good girl. Kin shiga lecture kuwa, ko kina nan kina hira da Susan ne?
Maryam ta amsa da sauri.
Maryam: nashiga lecture sir, kasan ina maida hankali sosae, I’m a serious student” tasa emoji din smiling daga qarshe
Zaid: Toh, ki mayar da hankali sosai, Kada ki yi ta tunanin mijinki.
Maryam ta turo masa emoji na dariya.
Zaid ya duba yayi dariya a hankali.
Assistant dinshi ne ya dawo yake tsaye a ƙofar office din yana kallonsa. Bai saba ganin ogan nashi yana murmushi shi kaɗai haka ba.
Zaid ya ɗaga kai ya gan shi a tsaye yana kallon shi
“Yes? How may I help you?”
Ya gyara tsayuwarsa.
“Sir, the meeting is about to begin.”
Zaid ya ajiye wayarsa, ya koma yanayin aikinsa na yau da kullum.
“Okay Let’s go.”
Kafin ya shiga conference room din seda ya daedaeta nutsuwar shi tareda mayar da fuskar da ya saba mu’amalantar ma’aikantan shi da ita mai natsuwa, mai tsauri, kuma mai sa mutane su mai da hankali ga abin da yake faɗa.
Babu wanda zai yi tunanin cewa mintuna kaɗan da suka wuce yana murmushi saboda yana karanta saƙon matarsa.
Ynzu ya gane dalilin da yasa mammi ke matsa mishi yayi aure, ynzu ya samu wata rayuwa da yafi ba muhimmanci fiye da aikin shi, rayuwar da ke sashi nishadi da kwanciyar hnkali, yar qaramar yarinyar da ta gama zuzutashi har yake jin baya iya rayuwa ba da ita ba
Kuma wannan jin daɗin yana sa mishi dokin komawa gida da wuri ba kamar da dayake raba dare a office ba
Har Qarfe uku suna meeting amma hakan be hana ya tuna da saqon maryam ba, 2:30 na bugawa yayi ma driver text yache yaje ya dauketa ya kaita driving school kuma ya jirata har ta qare
Wuraren 7pm Maryam ta dawo gida, ta tarar da Zaid bai dawo daga aiki ba.
Daki ta wuche tayi wanka ta saka wata simple English gown yellow mara hannu, Tayi sallah sannan ta sauko qasa, Tana saukowa taga an bude qofar parlour, da sauri ta qarasa taga ko zaid ne, aiko shi dinne, ya tsaya yana kallonta sannan ya bude hannun shi alamar tazo, ta taka taje yayi hugging dinta
“Haya I’m exhausted”
Ta dago ta kalleshi
“Sorry, muje kayi wanka se mu chi abnci”
Tare suka hau sama har cikin daki se ya miqo mata hannu a dunqule, ta gane abnda yake nufi se ta Kama hannun ta chire mishi ogogon shi, ya daga mata wuya, seda ta daga ta tsaya kan yatsunta sannan ta zare mishi necktie dinshi, nuni yayi mata da button din shirt dinshi tayi murmushi ta girgiza kai, kama hannunta yayi ya dora akan button din saman yana chewa “ki karasa ladar ki manah”, tayi dariya ta fara chire mishi daya bayan daya har ta chire duka
“Zaki tayani wan..?”
Kafin ya qarasa zanchen ta sheqa da gudu tana fita daga dakin, dama a shirye take dan ta gane take taken shi, Murmushi yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya nufi closet, chan ya shirya cikin simple casual polo outfits ya fito yaga maryam ta hauro da abnci sama tana jiran shi a kan coffee table
Seda ya shirya yazo ya zauna suka fara chi a natse Bayan sun qare chin abincin suka zauna suna fira. Maryam ta ba shi labarin abubuwan da suka faru a university da driving school
Zaid ma ya ba ta labarin abubuwan da yayi office, sunyi fira sosae, maryam na mamakin yadda zaid ke zaunawa yana bata lokacin shi da attention dinshi, bata taba tunanin mutum irin zayd zeyi irin wannan rayuwar auren da ita ba
Ta fara zurfi a tunani taji ya kama kumatun ta ya ja
“Ouch” ta fadi tana dafa kumatun
“Tunanin me kikeyi gani nan a gabanki kiyi yadda kikeso dani”
Murmushi maryam tayi tana sosa wurin da yaja
“Mu gani, kinji zafi ne?”
Ta gyada kai tana nuna mishi
Seda ya matso dd saitin wurin yayi kissing dinta, ta dan matsa zata jaye fuskar ta amma yasa hannu ya jawota ya sake yimata wani kiss a wuya, qoqarin tashi maryam tayi amma zaid ya jawota ta fado jikin shi gabadaya, kallonta yakeyi yaga yadda numfashinta ke hawa da sauka ta cikin rigar ta da batada hannu,sake matsowa da ita yayi sannan ya fara kissing dinta a hnkali, maryam kam batasan ya akayi ba ji kawai tayi ta fara maida masa da martani, mamaki ya kusan saka zaid ya daskare jin yadda maryam ta fara maida martanin abnda yake mata, wannan wani abu ne da bata taba yi ba, zaid ji yayi wani irin abu yana ratsa ilahirin jikinshi tun daga kwakwalwarshi har tafin kafa, chigaba yayi da abunda yakeyi, hannu ya kai ta bayanta ya zare zip din rigar jikinta ta sauka a hnkali, be taba kallon ainahin halittar jikin maryam ba se yau, white laced Underwears din da ke jikinta sun karbi jikinta sun zauna dass, a hnkali ya kai hannunshi ya zare ribbon din kanta, gashinta ya zubo yasa hannu ciki yana wasa dashi tare da kissing dinta, Kama hannunta Yayi ya daura Akan wuyan shi, ya dauketa sama ya ajiyeta kan madubi yana chigaba da abnda yakeyi, hannu yasa ya zubar da dun abunda ke kan madubin sannan ya sake zaunar da ita dakyau, saqon zaid na shiga ko’ina a jikinta se jin tayi ta kai hannu cikin gashin kanshi wanda yasha gyara sosae, ta fara wargaza shi tsab ba tareda ma ta sani ba, shi kuma jin hannunta a gashin shi wata irin ajiyar zuciya ya sauke da seda taji sautinta har cikin kan ta, daukar ta yayi ya kwantar ita kan gado yana jin wani abu na fizgar shi, maryam bata tashi dakatar dashi ba seda taji abnda yake qoqarin yi,
“Please haya, I promise bazeyi ciwo kamar last time ba”
Runtse ido maryam tayi gabadaya jikinta na qara mutuwa jin yanayin muryar da yake yimata magana, a wannan Daren, zaid ya sake tabbatar ma kanshi maryam matar shi che, shi kadai, matar da yakeda cikakken iko akanta, ynxu kam besan Wace irin soyayyar ze nuna ma maryam ba saboda irin wannan yanayin farin cikin da take saka shi, rungume yake da ita jikin yana jin hawayenta suna sauka a wuyan shi
“Haya ai beyi zafi kamar last time ba ko”
Bata amsa shi ba se qara riqeshi da tayi
“Subhanallah” kawai zaid ke furtawa a ranshi saboda maryam batasan irin yadda take riqeshi yana qara sashi cikin wani yanayiba.
“Shhhh, I’m sorry” yake rada mata a kunne
Shi ya kaita toilet yayi mata wanka sannan ya dawo da ita sannan shima yaje yayi, maryam kam Tasan yau bataji wani zafi ba se dan abnda baza’a rasa ba, amma a haka take ta lafewa kafin ya fito toilet har tayi baccee
Wandon Kayan baccee yasa sannan shima kwanta kusa da ita, yana kwanciya ta matso kamar zata shige jikinshi ta qanqame shi, Murmushi kawai yayi ya riqeta dakyau sukayi baccee
Bayan sunyi sallar Asuba ma da zaid yaga maryam ta tashi lfya qalau seda ya sake nema ma kanshi natsuwa kafin suka shirya suka fita, maryam kam taqi yadda ta hada ido dashi har sukayi dropping dinta school duk kunya da wani nauyin shi sun kama ta, amma ga alama taga shi zaid kam bema san wani abu wai shi kunya ba
SOKOTO
Rayuwa tana tafiya a nata tsarin.
Imran ya ci gaba da aiki tuƙuru a wurin aikinsa. Tun bayan da aka ba shi ƙarin albashi saboda ƙoƙarinsa, ya ƙara dagewa, yana son ya inganta rayuwarsa da kuma taimaka wa iyalinsa.
Amma akwai wani abu da ya fara ɗaukar hankalinsa fiye da yadda yake zato.
Hauwa Koulou.
Tun da ya fara ɗaukar ta daga karatun JAMB, sun saba yin hira a hanya. Da farko, maganganunsu basu wuce gaisuwa
“Ina wuni”
“Lfya qalau”
“Ya karatun yau?”
“Alhamdulillah”
Haka Haka har aka kai yana iya tambayarta
“Ya karatun yau?”
“Alhamdulillah. Amma wasu tambayoyin suna da wahala.”
“Ki ci gaba da ƙoƙari. In sha Allah za ki yi nasara.”
A hankali, hirarsu ta fara tsawaita.
Wani lokaci Hauwa za ta ba shi labarin abin da ta koya a aji. Wani lokaci kuma Imran zai ba ta labarin aikinsa, yadda yake son ya samu ci gaba, da irin burin da yake da shi na gaba.
A haka har akasa ranar da zaayi jamb
Shi ya dauketa ya kaita har centre din da zatayi kuma ya jirata seda ta fito suka dauki hanyar zuwa gida yana tambyarta “ya paper” ta bashi amsa da “alhamdulillah, batayi wahala sosai ba”
“Allah yasa an rubuta a sa’a”
“Ameen ameen Nagode sosai”
Ya tsaya a hanya ya saya mata ruwan sha da yoghurt.
Hauwa ta karɓa tana mishi godiya, ta qara da
“Me ya sa ka saye? ai gida zamuje”
“Kin sha wahalar exam. Na ga alamar kina jin ƙishirwa.”
Ta yi murmushi
“Na gode yaya”
Imran ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “Babu komai.”
Amma a cikin zuciyarsa, ya san cewa ba wai kawai taimaka mata yake yi ba, kamar ya fara jin daɗin kasancewarta tare da shi.
Da suka isa unguwarsu, ya tsaya inda ya saba sauke ta bakin qofar gidan, Sukayi sallama Tana qara mishi godiya
Imran ya jira har sai da ta shiga gida kafin ya wuche, lokacin da ya koma gida, Inna ta lura da murmushin da yake yi.
“Imran, me ke faruwa? Tun da ka shigo kake murmushi.”
Ya zauna yana bude food warmer din da aka aje mishi abnci
“Babu komai, Inna.”
Baba ya ɗago kai daga wata jarida da yake karantawa.
“Idan babu komai, me ya sa kake murmushi kamar wanda aka yi wa albishir da hajj ko umrah”
Imran ya yi dariya.
“Innna bincike fah ba kyau”
Inna ta kalli Baba, sannan suka yi murmushi
A zuciyarsu, sun fara zargin cewa akwai wata yarinya da ta fara samun wuri a zuciyar ɗansu.
Kuma ba su ƙi hakan ba, Sai dai suna adduar Allah yasa hauwa koulou che
A haka Kwanaki suka ci gaba da wucewa.
A Amsterdam Maryam ta ci gaba da zuwa school, tana ƙoƙarin haɗa karatu da sabuwar rayuwarta ta aure, driving school sati daya tayi tana zuwa ta qare kuma an bata certificate da driving license
Ta fara karanta rayuwar mijinta kuma ta kula zaid yana cikin irin mazan nan masu yawan buqatar matan su, shiyasa ta dage da tafiya saloon din da maman susan ta kaita tana gyara jiki kuma tana shan wannan hadin smoothie din da suke bata saboda ta gane amfanin shi, a gefe daya kuma tana shan wannan supplement na natures field me suna eves desire kullun guda biyu
Zaid ya ci gaba da aikinsa dakyau dama baya wasa da aiki, kuma a haka yana ƙara koyon yadda zai ware lokacin matarsa, duk abnda yakeyi baya kai dare office, duk abnda yakeyi ajiyewa yakeyi ya ya dawo wurin matar shi, ya saba da zama kusa da ita sosai, komi na maryam burge shi yakeyi, Haddai yanayin maganarta da shagwabarta.
SOKOTO
Tun ranar da akayi jamb bayan 12hrs result ya fito kuma hauwa ta samu makarantar da ta nema sokoto state university, mama taji daadi sosai ta Kira anty maimouna ta gaya mata.
Imran ya fara jin kewar hauwa koulu saboda ynzu basu haduwa sosai tunda bata zuwa lesson, sedai idan ya dawo aiki wasu lokutan ya shigo gidan mama, ya matsu hauwa ta fara zuwa maakranta saboda ya rinqa kaita kuma ya daukota tunda dama office din northern crest bado yake, babu nisa da state university
A haka Rayuwa ta ci gaba har imran ya saye mota 406, kuma ya fara neman gidan da ke kusa dasu yanaso ya saye su tashi daga gidan da suke gadi saboda inna da baba su more rayuwar su kafin shi ya nemi wani Qaramin gidan ya sema kan shi.
Hauwa koulu ta fara zuwa makaranta da taimakon imran da yake kaita kuma su dawo tare kullun, a hnkali dai wani abu ke shiga tsakanin su, wata irin kula da tsabtatacciyar soyayya da su kansu basu riga sun ankara ba
Follow this link to join my WhatsApp group