Free chapter · Read without an account

Chapter 31

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 31

Bayan sun yi tafiya na ɗan tsawo, garin Kano ya fara bayyana a gabansu. Jabir ya ƙara sauri, duk da cewa hankalinsa yana kan Irfan da ke kwance a gefensa cikin rashin kuzari.
"sannu, jabir ya riƙa jerawa Irfan a hankali.
Irfan yana kwance a gefe, ba shi da bakin amsawa. Shi kaɗai ya san irin azabar da ciwon yake jefa shi ciki.
Ba su ƙara yin tafiyar mintuna talatin ba, suka shiga wani private hospital da ke Nasarawa GRA mai suna Anwar Hospital.
Tun suna kan hanya Jabir ya kira Dr. Anwar, ya sanar da shi halin da Irfan yake ciki. Don haka da suka shiga harabar asibitin, Dr. Anwar da kansa ya fito tare da wasu ma'aikatan asibitin. Nan take suka taimaka aka fitar da Irfan daga motar, aka shiga da shi cikin asibitin.
Jabir ya nemi wuri a reception ya zauna, yana jiran fitowar likitan. Duk da ƙoƙarin da yake yi na nuna nutsuwa, zuciyarsa cike take da fargaba.
Bayan kusan mintuna talatin, sai Dr. Anwar ya fito ya kalli Jabir.
"Jabir, ka biyo ni."
Ya miƙe suka shiga office ɗin. Kowannensu ya nemi kujera ya zauna.
Dr. Anwar ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sannan ya gyara gilashin da ke fuskarsa.
"Ba wani abu mai girma ba ne. Irin matsalar da yake fama da ita ce kawai ta sake tasowa, kuma muna ganin kamar bai samu cikakkiyar kulawa a kanta ba. Hala baya mayar da hankali wajen shan magungunansa?"
Ya ƙarasa maganar yana kallon Jabir.
Jabir ya sauke ajiyar zuciya. Tunda dai ba wata gagarumar matsala ba ce, ai da sauƙi.
"Yana ƙoƙarin shan maganin, gaskiya ban san inda matsalar take ba. Maybe maganin ne ya daina masa aiki."
Likitan ya gyara zamansa.
"Yanzu dai babu wata matsala. Mu jira farkawarsa, daga nan za mu sake dubasa."
Jabir ya miƙe ya yi wa Dr. Anwar sallama.
"Zan je gida ne, in dawo kafin ya farka."
Daga asibitin ya fice ya nufi gidansu da ke cikin GRA, tunda ba wani tazara mai yawa ne tsakaninsu da asibitin ba.
Motar Jabir ta shigo cikin babban gate ɗin gidan a hankali. Mai gadi da ke bakin gate ya gane motar tun daga nesa, nan take ya buɗe masa hanya.
Gidan kuwa babban gida ne na alfarma, mai hawa biyu, yana ɗaya daga cikin manyan gidaje masu kyau da ke cikin unguwar.
Harabar gidan tana da faɗi sosai, an shimfiɗa ta da interlock mai kyau, yayin da gefen gidan yake cike da lawn da furanni da aka tsara cikin tsari mai kyau.
A gefe guda na harabar kuwa akwai manyan motoci masu kyau. Wasu suna cikin carport ɗin da aka yi musu rumfa, wasu kuma a jere cikin harabar gidan. Kusa da babban gate akwai ɗakin masu gadi, inda ma'aikatan tsaro ke kula da shigowa da fita.
Jabir ya faka motar a gaban babban ƙofar gidan, sannan ya fito. Ya ɗan tsaya yana gaisawa da masu kula da gidan. Bayan sun gama gaisawa, ya nufi babbar ƙofar da za ta sada shi da falon gidan.
Da ya shiga, babban falo ya bayyana a gabansa.
Falon yana da faɗi sosai, an kawata shi da manyan kujeru masu kyau, babban carpet da ke shimfiɗe a tsakiyar falon, da kuma teburin gilashi a gabansu.
A saman falon kuwa akwai babban chandelier da ke ƙara wa wajen kyau, yayin da manyan tagogin gilashi da labule masu kyau suka ƙawata bangon.
A gefe kuma akwai wasu kayan ado masu kyau da aka tsara cikin nutsuwa, waɗanda suka ƙara nuna irin darajar gidan.
Komai yana cikin tsari da tsafta. Ko'ina sai ƙamshi yake, wanda ya nuna cewa akwai masu kula da tsaftar gidan a kai a kai.
Jabir ya nufi matattakalar bene da ke cikin falon, ya fara takawa domin hawa sama.
Gidan ya kasance kamar wata aljannar duniya. An zuba dukiya da kulawa a cikin komai, tun daga harabarsa har zuwa cikin ɗakuna. Kyawunsa da tsaruwarsa sun sa duk wanda ya shigo zai iya gane cewa masu gidan ba mutane ne da suke wasa da jin daɗin rayuwa ba.
Daya daga cikin bedrooms ɗin ya nufa. Da ya shiga, ya fara rage kayan da ke jikinsa. Ya zauna a gefen gado na ɗan lokaci, kafin ya hau ya kwanta, yana ƙoƙarin huce gajiyar da ya kwaso.
Umsar ✍️ 


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol