Free chapter 路 Read without an account
Chapter 1
by Aysha 路 Tudu Biyu!
*Tudu Biyu!*馃挒
*Aysha Shafi'ee.*
*#WomenOfWords*
*****
*1*
~~
FANNE MUHAMMAD NASIR.
05:30pm
Kowa ya sani cewa babban burin Fanne shine ta koma gidan mijinta Hadi, amma duk da haka a cikin lissafin Aunty Halmu bata taba kawo cewar zata iya kallonta kai tsaye ta fadi wannan maganar ba, don haka bata san lokacin da ta juyo ta nemo salati a cikin bakinta ba.
鈥淚nalillahi wainna ilaihir raji'un... Fanne? Me kike nufi? Auren kisan wuta zaki yi?"
Matashiyar da ta kira da Fannen ta bata rai sannan ta girgiza kanta.
"Ni fa ba haka nake nufi ba, kawai cewa nayi da ace akwai wata hanyar da zan iya komawa gidan Hadi wallahi sai na bi ta."
Aunty Halmu ta girgiza kanta, ta ja tsaki sannan cikin yarensu na shuwa arab tace.
"_Ma'arfa shunu no'a al-junuun fihaa..._ Ban san wace irin mahaukaciyar yarinya ce ke ba wallahi Fanne, bana jin a rayuwata kaf na taba haduwa da mace irinki mai taurin kai da kuma banzan ra'ayi..."
Aunty Zainab dake can zaune gaban mudubi tana fente bakinta da wani jan jambaki ta juyo ta katse ta.
"Dan Allah Halmu ki ja bakinki kiyi shiru akan al'amarin yarinyar nan, wallahi don dai a musulunce auren ya kare tsakaninta da Hadin nan ne da wallahi ni kaina sai na san yadda zanyi na komar da ita gidan nasa taje can ta cigaba da cin uw*r da take ci."
Ta juya a fusace ta cigaba da dadira jambakinta kamar tana ganin har yanzu tasirinsa bai kamo kalar jan kayan da take sanye dasu ba.
Fanne ta sake bata rai tana taune gefen bakinta kamar tana son hana kanta fito da maganar da take son furtawa.
Aunty Halmu ta tabe baki ta dauki wani turare tana fesawa duk a cikin shirin fita bikin da suke yi sannan ta cigaba.
"To ba gashi nan ba, duka mata sa'anninta sun tafi wajen kwalliya amma ita an barta damu tsofaffi, muna gyara tsufan namu ma amma ita tana zaune ta kima daurin kai kamar Ladi Kwali."
Ba shiri Fanne ta saki lebben bakinta da ta cije don a yanzu maganar da take dannewa ta kai gejin da ba zata iya cigaba da dannewar ba.
"Ni fa ba son kwalliya nake ba kun sani, ko da bikina ma ai banyi ba, kuma ko ita Safar na gaya mata ba wata kwalliya da zanyi don za'ayi bikinta. Zancen da kuke yi kuma ai naga gwara ni, tunda daga ni har mijina muna son komawa auren namu, ku duk da aka sako ku ai ko biko mazajenku basu taba zuwa ba..."
Kwalbar turaren dake hannun Aunty Halmu ce ta fadi daga hannunta har kasa ta tarwatse yayin da Aunty Zainab ta debo salati tun daga farkonsa har karshe ta dire.
" Inalillahi wainna ilaihir rajiun.... Na shiga uku ni Zainab _shunu ana amla kida?_ mu kike gayawa haka Fanne?"
Fanne ta sake hade ranta.
"Kuyi hakuri idan ranku ya baci amma ai gaskiya na fada, kawai sai ku sani a gaba kuyi ta fada don nace ina san in koma gidan mijina? Bani da uwa bani da uba, da inyi ta rabe- rabe a gidan yanuwa ba gwara na koma inda nake da gata ba?"
Aunty Halmu ta gyada kanta sannan ta nuna mata hanyar fita.
"Tabbas, na ganewa idona fitsarar da ake fada kina yi akan yaron nan, to idan ba so kike yi mu hadu muyi miki dan banzan duka a dakin nan ba Fanne zo ki fita, mota ai tawa ce ko? ba zan dauke ki in kai ki gidan bikin ba, ki fita ki kira Hadin da kike ganin shine gatanki yazo ya kai ki."
Tana rufe bakinta kuwa Fanne ta suri jakarta a gefe ta mike.
" Allah ya baku hakuri, amma dan Allah to ku bani kudin mota sai in tafi da kaina wallahi bani da cash a jikina."
Da Aunty Halmun ta lailayo wani zagi bata san sanda ta tsinci kanta a wajen dakin ba tana rufo musu kofa.
A hanyar korido kafin ta karasa tangamemen falon gidan ta tsaya a bakin wani mudubi na ado da aka ajiye, ta kalli kanta da akace kamar na Ladi Kwali tana tunanin yaya zata yi dashi, don girma yayi girma amma ai gashinta ne ya jawo, bayan yawan da yake dashi bashi da laushi sosai irin na mafi yawancin dangin nata, wani irin fumm natavyake yi da idan ta dade bata je saloon ba kuma ta barshi a tsefe, to duk yadda ta kai ga danne shi da ribbon sai ya yi tashin nan... Sai taja tsaki kawai tana tunanin ai ba wanda yake binta bashin daurin mai kyau balle ace sai tayi.
Ita bikin ma fa gabadaya don kar ta kwana da yunwa ne zata je, tunda event din jiya da akayi da bata je ba da aka dawo dare yayi kin yin girki akayi gabadaya a gidan akace wai anci abinci a wajen bikin kowa ya koshi, 拼an aikin gidan kuma sunyi nasu sun cinye, haka ta kwanta tana juyi sai tsakar dare da taji zata mutu ta tashi ta yi Kitchen, a cikin katon store din Kitchen din ta dinga lalube kafin ta nemo inda indomie take ta samu ta dafa wajen karfe uku kamar mayyar aljana.
Duk girman gidan yanzu ma shiru yake banda yan aiki sai wasu tsilla-tsillan mutanen da basu gama tafiya wajen bikin ba, yawanci dangin kishiyar Aunty Halimatu ne uwar amaryar ne wadda ta kasance yayar babarta. Amaryar Safa cousin dinta ce kuma ba ita kadai ake bikin ba har da yayan kishiyoyin gidan guda biyu su ma duk mata, don haka duka bangare uku na matan gidan koina biki ake yi.
Ita duk zamanta a gidan ba shiga shirgin sauran matan da yayansu take yi ba balle har ta san yanuwansu, ko kafin tayi aure da take zaune a gidan idan ba makaranta zata je ba sai ta shafe kusan sati a cikin bangaren Aunty Halimatun batafito ba, tunda kowanne bangare kansa tamfatsetse ne da zaka manta ma wai ba gida ne guda ba idan kana ciki.
Don haka a duk tarin yayan gidan nan kaf banda yayan Aunty Halimatun mutum daya ce wata Sa'adatu yar gidan uwargidan sula 蓷an yi shiri da ita a baya, shima kasancewar ajinsu daya ne a islamiyya to bayan sun girna kowaccensu tayi aure, ita Sa'adatun ma an cilla ta can Lagos, sai zumuncin ya kare dama na karfin hali ake yi tundaba wani shiri akeda Aunty Halimatun da sauran kishiyoyin ta suke yi ba, kawai dai ba'a fada tunda akwai kudi, don haka kowa zaman cin gashin kansa yake yi shi da yayansa. Ta cigaba da tsaiwa kawai a bakin bangaren Aunty Halimatun tana tunanin ko dai ta hakura nekawai ta koma, don bata hango kanta tana jigilar neman mai POS da kuna neman Napep din da zai kaita.
Ta bude jakarta ta zaro katin gayyatar da dole sai dashi za'a shiga wajen bikin, ta sake karanta sunan wajen, da nisa gaskiya, cikin wadannan lungunan dake unguwar Nasarawa ne don haka ta san ba kowanne Napep zata tare kai tsaye ya kaita bam
Ta cije lebbenta ta mayar da katin ciki sannan ta zuge jakar tana yanke shawarar ta koma ciki kawai tayi kwanciyar ta, sai dai me? Tana dago da idonta tayi arba da wata farar mota tana karasowa inda take tsaye, motar ta tsaya a daidai gabanta sannan aka zuge gilashin kasa daga ciki.
Musa. Idonta ya gane mata zaune a ciki yana mata murmushi... Musa 茩anin babbar matar gidan ne wadda take uwargida, ma'ana 茩anin kishiyar Aunty Halimatun, ya so ta tun kafin ta auri Hadi, kuma kasancewar tana ganin kirkinsa a lokacin sai taji kamar zata iya aurensa amma dabi'arsa ta shaye- shaye ta dakatar da ita, ta gama lissafin cewa babu ta yadda za'ayi dan shaye-shaye ya bata irin kulawar da take fata da hange a gidan aure, kuma bayan haka ma kuma yayar tasa ba sonta take yi ba, itama kumaAunty Halimatun tun a lokacin ta nuna mata bata so, don haka ba awani dade batasokeshi aciki n lissafinta.
"Baby girl... Sai ina? Kike tsaye anan wajen ke kadai?"
Ya kira ta da sunan da yake kiranta tun a wancan lokacin kafin tayi aure.
Da yake bata iya karya ba kai tsaye ta matso gaban motar sannan tace.
" Wajen bikin zan tafi."
" Ke kadai?"
Ya tambaya watakila shima ya danyi mamakin duk bataliyar gidan ya akayi ta rasa wanda zata bi, sai kuma yace.
"Kuma baki kira ni inzo in kai ki ba kin san definitely I wil be around."
Ta dan yi murmushi kawai, don har cikin zuciyarta ba son bin nasa take yi ba amma kuma tana hango dama ce ta samu.
"Ni ai bana jin ina da numberka ma yanzu Musa."
Ta fada kai tsaye tsakaninta da Allah, sai ya yi dariya.
"Kece ai baki so samu ba, yanzu dai shigo mu tafi nima daga can nake, kaya suka hada ni dashi na dawo musu dashi gida."
Ta danyi jim kamar zata barar da tayin nasa, sai kuma ta daurewa zuciyarta ta karaso jikin motar ta bude kofar ta shigo, kamshin turarensa hade da wani abu kamar kauri- kauri ko hayakin taba ya shiga hancinta a lokaci guda, amma da yake da sanyin Ac sai baiyi tasiri sosai ba, hakan yasa ta daure.
" Nagode, dama ina ta tunanin ta yadda zan tafi don ban san wajen ba."
Yayi murmushi yana jan motar da wani irin gudu zuwa bakin gate.
"Kina nan dai yadda kike ashe Fanne, ba inda kike zuwa a garin nan, kowa ya waye banda ke..."
Kalaman suka dan dake ta amma da ya karasa fadin.
" Kina mana asarar kyan nan naki."
Sai kawai tayi murmushi tana kallon maigadin gidan dake daga masa hannu, bai ko kalle shi ba ya figi motar har titi kasancewar gidan akan titi gidan yake, suka hau wuce manya- manyan gidajen layin dake shaida duk mazauna wajen mutane ne dake jike sharjaf cikin daukar arziki.
Wayarta tayi kara a cikin jaka a lokacin, tayi sauri ta zaro ta... Khadi ce, dama ta san ita kadai zata neme ta a duk wajen nan idan bata ganta ba. Ta dauka ta kara a kunnenta.
" Wai Fanne baki taho ba har yanzu? Shi yasa nace ki biyo mu wajen makeup din ko baza kiyi ba sai mu tafi tare idan aka gama yi man...."
"Khadi gani nan a hanya, yanzu ma zan karaso insha Allah."
Ta katse ta, tana jin hayaniyar kidan bikin a kunnenta.
" Okay to,to."
Cewar Khadin kafin ta kashe wayar.
Musa ya kalli wayar tata bayan ta sauke daga kunnenta.
"Wai har yanzu irin wannan wayar kike amfani da ita?"
Ya jujjuya kansa.
"Dan Allah ki bari in 蓳ata ki mana Babygirl..."
A lokacin guda ta yi dariyar mamakin kwarin gwiwarsa yadda ya fadi kalaman kai tsaye sai ta yi murmushi ta mayar da abin wasa.
" Wallahi ba zan bari ka 蓳ata ni ba Musa, ka kyale ni a yadda ka ganni kawai."
Shi ma yayi dariya, ya miko hannu ta saman cinyarta kamar zai taba ta don har sai da ta dan matsa, sai kuma ya bude drawer dashboard din dake gabanta, a ciki ya zaro wata waya da taga kamar irin ta Kahdi ce da taji tana kiranta 14 promax ya ajiye akan cinyarta sannan ya naushi drawer ta koma ta rufe.
" Ki dauki wannan ki saka sim dinki, i think sau daya nayi amfani da ita tunda na siya, so babu komai a ciki."
Fanne ta kalli wayar, ta sa hannu ta dauka, tayi mata kyau sosai, wata suluf a hannunta, amma sai ta girgiza kanta, karbar kayan Musa a wajenta yanzu ai tashin hankali ne, ba'a wajensa kadai ba, har a wajen su Aunty Halimatun.
Sai kawai ta bude dashboard din inda ya dauko wayar ta mayar masa da abarsa.
"Nagode Musa, amma ka barshi kawai wannan ma da nake amfani da ita ba abinda tayi."
Yayi guntun tsaki.
" Ai matsalarki kenan Fanne, ba'a taba miki gwaninta, mata ana basu abu jikinsu na rawa ke ko a jikinki balle ma mutum ya san yadda zai shawo kanki."
Ta gyada kanta tana kallon titi.
"Kyauta ka min ai, nace maka nagode kuma na gaya maka dalilin da yasa ba zan karba ba."
Maimakon ya bata amsa, sai ya girgiza kansa kawai, kamar ba zaiyi maganar ba sai kuma yace.
"Kina da dukkan damar da zaki more rayuwar nan a hannunki Fanne amma ke ba kya gani, kina da kyau, kina da opportunity din cewa kin taba aure zaki iya yin duk abinda kike so idan ma auren zaki sake a gaba kije kiyi ba wanda zai tuhume ki amma..."
Ya sake girgiza kansa.
"Amma kamar ke ba kya ganewa."
Kamar mashi haka kalaman sa suka caki zuciyarta a lokaci guda, suka tabo wani abu da bayan takaici har daci- dacinsa ta shiga ji a cikin kirjinta yayin da bakinta ya shiga hado mata kalaman zagin da taji tana son dura masa, amma sai wani tunani ya gifta a cikin kanta, idan akace mutum yana shaye-shaye da sauran halayya irin ta Musa, to ba abin mamaki bane a same shi da dabi'ar da zai iya yi mata wani lahanin, don haka a maimakon kalaman da tayi niyyar furtawa, sai ta bawa kanta hakuri, ta juyo ta kalle shi, akan dan siririn lebbenta ta fito da kalmomi biyu kawai.
"Dan tsaya..."
"What... ?" Ya tambaya alamun bai gane abinda take nufi ba.
" Nace ka dan tsayar da motar dan Allah..."
Ga mamakinta bai mata musu ha sai kawai ya shiga rage gudun motar kafin ya koma gefen toti ya samu waje ya tsaya, daidai jikin wasu masu sayar da lemo da su apple dake kasan inuwar wata 茩atuwar bishiya.
Ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan tace.
"Maganganun da kake fada kaima ka san ba halayyata bace tunda balle yanzu, don haka ba zan iya cigaba da zama ina saurarar ka ba, nagode da rage min hanya da kayi."
Tana fadin haka ta bude kofar motar ta fita ta barshi da tsananin mamaki a fuskarsa yana kallonta. Ta koma daga bayan motar ta tsaya kamar tana jiran mai napep, kuma minti daya biyu yana tsaye kafin ya tada injin motar wani irin bada wuta da sai da kusan kowa ya juyo ya kalle shi, kuma da ta juya itama sai ta hango hannunsa a cikin motar rike da tabarsa tana hayaki, hakan ya tabbatar mata abinda ya tsaya kunnawa kenan dama ba wai mamakin saukarta ba.
Ta ja tsaki tana girgiza kanta.
"Allah ya tsare ni daga sharrin ka."
Ta fada a zuciyarta tana maida hankalinta wajen neman abin hawan a yanzu, ta tabbata duk tsiya dai daga daidai wajen da take yanzu kudin hakarta da basu da yawa zasu ishe ta ta karasa.
Tana kokarin tsayar da wani napep da ta hango ba kowa ne lokacin wata katuwar mota kirar range rover baka tazo daidai gabanta tayi parking ta hana mai napep din tsayawa a gabanta.
Ranta ya dan baci tana kallon motar amma da aka zuge glass din idanunta suka yi arba da wata kyakkyawar yarinya 拼ar kimanin shekara biyar a gaban motar sai taji ran nata ya washe a lokacin guda, kamar waya ce (tablet ) a hannun yarinyar tana danne-dannenta. Kuma bayan hakan kamar ance ta dago ta kalli mai tuka motar kawai sai suka hada ido dashi, wani mutum mai dauke da kalolin kamannin yarinyar, ya tsaya cak yana kallonta daga yadda yake zaune hannunsa rike da sitiyarin motar, idanunsa basa ko kiftawa kamar mai nazarin wani abu a tare da ita, wani irin kallo da taji ya wuce cikin idanunta yana tafiyar har zuwa inda ruhinta yake.
Sai abubuwa biyu suka faru a lokaci guda... Mai sayar da apple din nan na bayanta ya taso da sauri yasha gabanta zuwa jikin motar alamun dama wajensa aka tsaya, sai kuma horn din mai napep din da ta tare wanda ya tsaya daga can gaban motar.
Ba shiri ta motsa kafafunta ta bar wajen ta nufi mai napep din dake jiranta. Tana zuwa kuwa ta zaro katin bikin a cikin jakarta ta nuna masa sunan wajen.
" Dan Allah mai napep wajen wannan bikin zaka karasa dani."
Ya karbi katin ya karanta sai ya dago ya nuna mata kwanar dake gabansu kadan.
" Hajiya ai waccan kwanar ce, kina shiga zaki ga wajen."
Ta kalli kwanar sannan ta juyo da murnarta ta shoga gode masa.
"Nagode kuwa wallahi sosai."
Ta karbi katinta ta mayar jaka sannan ta nufi hanyar tana jin dadin yan kwabbanta ma basu tafi ba.
Tana yin kwanar kuwa taga sunan wajen, ta karasa ciki da murnarta ta wuce katon parking space din dake cike da motoci ta bada katinta ta shiga.
Duk girman hall din a cike yake dankam tunda bikin mata uku ake yi, bayan dangin iyayen kowacce da kawaye akwai dangin angwayensu ma don haka babu masaka tsinke, da kyar ta samu wani tebur acan baya ta zauna, tana neman su Khadi. Zuwa can ta hango su kuwa sunci makeup dinsu sai kai da kawowa suke acikin sauran yanmatan wajen.
Irin fabric dinsu itama shine a jikinta, amma yadda tasa mayafinta ma ta rufe ba wanda zai lura idan ba kalla kayi sosai ba tunda ita babu kwalliya ko digo a fuskarta.
Tsoron kar ta tashi ta rasa wajenta yasa tayi zamanta a wajen kawai tana fatan rabon abincin da taga an fara ya karaso teburinsu. Aikuwa cikin kankanin lokaci aka cika teburin nasu da kanyan abinci kala-kala sannan ta fara gane mutanen da take tare dasu ma, yanuwan daya amaryar ne yar uwargidan Auty Halimatun.
"Amma dai ke dangin su Safa fe ko?"
Wata mata a gefen ta ta tambaye ta.
Ta gyada kai tana tauna naman dake bakinta.
Matar tayi murmushi ita da ta gefenta.
" Masha Allah ai naga kama ne sosai."
Ta gefen ta girgiza kanta.
"Ah wannan ma ai tafi amaryar kyau, tubarkallah kina ganinta ita ko kwalliyar tasu bata yi ba."
Matar ta gyada kanta.
" Ai tun dazu nake ta kallonsu nace ikon Allah kinga su kuma duk danginsu kyawawa dasu masha Allah."
Sai wata ta leko tace.
"Ai larabawa ne fa su, ita Aunty Halimatun dama ai duk danginta larabawa ne."
Fanne ta dauki wani dan karamin kwali da aka zuba su samosa da fanke ta cigaba da ciye-ciyenta tana jinsu suna cigaba da hirarsu bata ce musu kanzil ba har daya matar tana cewa.
" Ni Halifa da zaiyi mana gata ai da yazo ya zabi daya a cikin yanmatan nan... Amma haka kurum ya daukomana wata yarinyar da bana kaunarta wallahi, ba茩a 茩irin da ita."
Sai da kalaman suka yiwa Fanne nauyi a kunnenta, ta jinjina kanta kawai tana kara tsinkewa da lamarin mutane. Haka kurum suna aibata yarinyar da idan za'a binciko asali ta tabbata ta fi su kyakkyawan asali mai kyau, amma tunda ita baka ce, su kuma farare, iyayenta basu da kudi su kuma nasu iyayen sun auri masu kudi shikenan sune mutane da har ido rufe za'a nemi a hada zuri'a dasu.
Idonta ya kai kan amarya Safa da Mc ke kiran su fito kan stage ita da angonta bayan duk sauran yanuwan nata suma sun tsaya tare da mazajensu. Ta tsayar da idon nata akan katon Alhajin da wai shi ne mijin Safa, Safa yarinya 蓷anya yar shekaru ashirin da biyu tare da Alhajin da tabbata ya doshi sittin, ba shiri wani tari ya kware ta da idonta ya hasko mata wani abu, ta dauki ruwa ta kora tare da yin ajiyar zuciya... Allah ya sani bata san me yasa aka taso da zuri'arsu kaf da tunanin cewa anyi su ne don su auri Alhazawa ko kuma maza kawai masu kudi ba.
Watakila abin ya samo asali ne daga kakaninsu wanda asali ba daga kabilar shuwa arab din da ake danganta su suka fito ba, irin yan gudun hijirar nan ne daga kasar lebanon da suka shigo Nigeria ta fuskar Borno a shekarun 1970's da ake yakin basasa a kasar tasu, kakannin nasu ne suka zauna a wajen da suka yi makotaka da wasu mutanen Shuwa arab, shikenan da yaransu mata biyu da suke kanana a lokacin suka taso sai suka tashi da yaren a bakinsu suka saki na iyayensu.
Wadannan yaran sune kakaninsu, ance tun asali lokacin aurensu duka su biyun wasu manyan alhazawa suka aura saboda tsanananin kyan da suke dashi wanda ya ceto su daga cikin talaucin da iyayensu ke fama dashi a lokacin.
Babbar yayanta biyu mace da namiji, karamar ce kakar Fanne wacce ta haifi yara uku duka mata. Halimatu, Falmata da kuma mahaifiyar Fanne Bintu, daga Aunty Halimatu har Aunty Falmatan kowacce da ta tashi aure mai kudi ta aura, haka yaransu ma da suke aurarwa yanzu ba wacce take auren wanda bai tada kai da dukiya ba wanda yawacinsu manyan mutane ne yan siyasa ko yan kasuwa... Wata 拼ar Aunty Falmata guda daya Aisha itace kawai ta auri wani saurayi daidai shekarunta amma shi ma dan gidan wani shahararren mai kudi ne da sunansa yayi shuhura.
Fanne bata ma damu da kudinsa ba haka ta dinga taya Aishan murna ganin ita bata kare akan wani tsoho irin sauran yayyenta ba... Amma da taje gidanta bayan kamar watanni biyu da auren, sai ta dawo gwiwa a sake da Aishan ke mata korafin tun bayan bikin da suka dawo daga kasar da suka tafi honeymoon, ganinta da mijin nata bashi da yawa, yana can yana al'amuran gabansa a wasu kasashen, ya barta sai sai da ta tashi ta kwanta kawai da sunan ya ajiye mata a gida.
Sai taga ai al'amarin nata bashi da banbanci da na sauran yanuwan nata da yawanci basa wani samun isashiyar kulawa daga Alhazawan nasu, al'amuran siyasa ko kasuwancinsu da ma na iyalansu ya cika kansu ta yadda sai lokaci-lokaci idan sun neme su kawai suke ganinsu, idan aka dankara miki katon gida aka ajiye ki a ciki, to a wajensu ai baki da wata matsala kuma. Mijin babbar 拼ar Aunty Halimatu mai suna Rabiya ma a yadda taji labari duk da ana boyewa shi 拼anmata yake diba kala-kala yana tafiyarsa kasa-kasa dasu, ita da sauran matansa suna zube a gida sai lokacin da ya ga damar waiwayarsu.
Don haka a cikin kan Fanne ko da da giftawar sakan guda irin wannan rayuwar ta ahalinta bata taba burgeta ba ko kadan, duk da cewar kowa yana cewa gadon ra'ayinta tayi daga wajen mahaifiyarta, tunda lokacin aurenta haka ta dage kai da fata taki auren wani kanin mijin Aunty Halimatu shima dan kasuwa da ya dage yana sonta, ta zabi wani Muhammad Nasir da idan za'a jera shi tare da mazajen yayyenta ko kurarsa baza'a gani ba balle shi, haka aka sha danbarwa kafin ba yadda zasu yi su yarda ta aure shi.
Da Allah yayi zaman nasu ba zai dore ba ma wata uku da auren yayi hatsari ya rasu, don haka lokacin da Fanne tazo duniya bata san mahaifinta ba, ita da mahaifiyarta suna zaune a gidan Aunty Halimatu da ta rike su, anan ta taso har kusan shekaru goma kafin mahaifiyar tata ta rasu itama.
Don haka ita da yayan Aunty Halimatu baka banbance su har suka girma, Bayan ta gama secondary ne ta hadu da Hadi, saurayin da da ta tsinci dukkan abubuwan da take fatan samu a namji tare dashi, dadin baki, iya nuna soyayya, da kuma karancin shekarunsa.
Sai ko kadan bai taka matakin dukiyar da danginta ke kallo wajen yin aure ba, don a farkon haduwarta dashi yace mata siyar da motoci yaje yi jafin daga baya ta fahimci kawai buge- bugensa yake yi don babu sana'ar da baya tsallakawa saboda tsananin burin son yin kudin da yake dashia zuciyarsa, kuma da wannan kwarin gwiwar ne kai tsaye ta wajen iyayenta Aunty Halimatu da Falmata, ina wuta su jefa Fanne a lokacin, musamman Aunty Halimatun da tafi daukan zafi tana fadin ba zata maimaita musu abinda mahaifiyarta tayi ba.
Ita kuma ta dage akan kudirinta musamman da Hadi ya cigaba da kunna mata wutar dadin bakinsa da lallami ganin yana shirin rasa ta, sai ta wanke kafarta ta tafi wajen dangin mahaifinta da kokon bararta, suka kuwa goya mata baya ta yadda ba yadda su Auty Halimatun suka iya dole aka daura mata aure da Hadi.
Sai dai me? Bayan wannan bakin fentin da ta shafawa kanta a wajen iyayen nata. Watanta takwas tare da Hadi sakin farko ya shiga tsakaninsu, ba wai ya daina sonta bane ko ya tsane ta, A'a wani irin mutum ne shi mai saurin fushi da kuma idan yayi fushin hankalinsa ke gushewa idanunsa su rufe, ita kuma ta san tata matsalar na bakinta da baya yin shiru a kodayaushe, karyane a fada ta rasa abinda zata mayar, saboda haka sakin da yayi mata na farko ba akan wani dalili mai karfi bane, kawai taje gida ne tayi dare bata dawo da wuri ba, ta barshi tsaye a kofar gida yana ta faman jiranta ba mukulli, don haka tana dawowar da ya fara banbami a wajen ita kuma ta shiga kare kanta, abinda ya harzuka shi kensn ya sake ta a kofar gidan yace ta koma gidan nasu ma kawai shi ya hakura da ita.
Ta koma tana kuka, amma ga mamakinta sai su Aunty Halimatun suka shiga yi mata murna tare da barkar wai wahalarta ta kare a gajeran lokaci tare dashi. Da ta tashi shayar dasu ruwan mamaki, sati daya da dukkaninsu suka huce kuma yazo ya kalallame ta da dadin bakinsa na tayi hakuri, a ranar ta bishi suka koma.
Don haka dukkan sauran saki biyun ma da suka biyo baya a cikin shekara biyu da wasu yan watanni na auren nasu, babu wani kwakwkwaran dalilin da yake haddasasu, sa'insar ce kawai da dukkaninsu basa kai zuciya nesa, amma bayan haka lafiya kalau suke zaune duk da matsalar rashin haihuwar da suke fama dashi, sai ranar da zuciyoyinsu suka birkice sai ya dankara mata sakin da zata taho gida, idan ya huce ya dawo ya lallame ta yanuwanta na kallo sai ta hada kayanta ta koma, a haka har aka kawo gejin da suka rasa mafita a yanzu.
Allah ya sani ita tana son komawa ne saboda zuciyarta tana mutukar son Hadin har a yanzu kuma duk inda taje ma ba dadi take ji ba saboda kusan duka yanuwan nata kowa haushinta yake ji musamman na yadda har yanzu take nuna son komawa gidan nasa.
A wannan ranar bayan gama dukkan hayaniyar bikin da kuma dawowarsu gida, Fanne ta jawo wayarta lokacin da take kwance akan gadon dakin da aka sauke su, ta bude ta ta shiga cikin whatapp kan hirarsu da Hadi, idonta ya karanta tattaunawarsu ta karshe... Alkawarin da yayi mata.
_Kin amince zaki yi duk abinda nace ko?_
_Na amince Hadi, zanyi koma meye in dai zamu kara kasancewa tare._
Ya karanta abinda tace, amma bai ce komai ba har yanzu. Sai ta dago yatsanta daya ta rubuta sunansa cikin sigar kira
_Hadi..._
Bayan ta aika, sai layi guda ya nuna a kasan sakon alamun bai karasa tafiya ba, amma duk da haka ta tsirawa koren rubutun ido zuciyarta cike da fata, kamar roko ma, rokon yazo ya kara bata tabbacin kalaman nasa.
***