Free chapter · Read without an account
Chapter 3
by Aysha · Tudu Biyu!
*Tudu Biyu!*đź’ž
*Aysha Shafi'ee.*
*#WomenOfWords*
*****
*3*
~~
KHALID.
11:15am
Daga inda Khalid yake zaune a cikin dakin, yana jin nauyin idanun mahaifinsa dake kallonsa daga can kan kujerar da yake zaune.
Watakila idan zai iya kirgawa sun yi kusan minti biyu zaune a haka tun bayan dake kallonsa daga ya gama zayyana masa bayaninsa na barin kamfanin.
Kallonsa kawai yake daga inda yake zaune, ba tare da yace komai ba.
Kuma hakan yafi komai kara rikita zuciyarsa.
Ya sake dunkule hannayensa idanunsa na cigaba da kallon carpet din da yake zaune.
Shirun da ke tsakaninsu ya kara kauri, irin shirun dake faruwa a tsakanin mutane biyun dake kaunar junansu amma fahimta tayi karanci a tsakaninsu. Khalid ya sake gyara zamansa. Kuma kafin ya gama yanke hukuncin abinda zaiyi sai muryar Proffesor Sulaiman din ta fito.
“Cewa kayi ka bar aiki Khalid.”
Khalid ya sake sunkuyar da kansa kasa, kafin ya amsa.
“Eh Abba.”
Sai Proffesor Sulaiman ya cire gilashin fuskarsa ya ajiye a gefe.
“Wani abu ya faru tsakaninka da Sadiq kenan.”
Khalid ya runtse idanunsa, tabbas ba’a banza iyaye ke amsa sunansu na iyaye ba, suna da ilhamar da ko baka furta abu ba kallonka kawai zasu yi su fahimta. Don abinda Professor Sulaiman din ya fada ba tambaya bace, kamar wani abu ne da ya tabbatar dashi kawai kuma yake gaya masa.
Baice komai ba yayi shiru kawai don ya tabbata idan ya bude bakinsa a wannan lokacin, to dukkan abubuwan da baya son ya furta ne zasu fito.
Don haka baice komai ba har lokacin da mahaifin nasa ya sake cewa.
“Saboda wata matsala da ta faru tsakaninka da danuwanka zaka dakushe rayuwarka Khalid.”
Ya girgiza kansa.
“Ba matsala bace ta tsakanina da shi ba Abba.”
Sai Proffesor yayi ajiyar zuciya.
“To ina jinka, matsalar daga ina take?”
Khalid ya cije lebbensa, wannan dama ce a wajensa, damar da idan yana so zai zayyanewa mahaifin nasa dukkan abinda yake faruwa, abubuwa da Sadiq ke yi da ma wanda ya dade yana yi.
To amma ya riga ya san me zai biyo baya bayan hakan, ko da mahaifinsa zai yarda dashi to na kankanin lokaci ne Amma zata san yadda zata rushe hakan. Ta sake bata shi a idanun kowa, a ga cewar shine mai laifin mai kokarin jawo rigima.
Don haka ko meye a cikin kansa, ya san ba zai taba yin kuskuren fadar laifin Sadiq a gaban mahaifinsu ba.
Don haka sai kawai ya girgiza kansa a hankali yace.
“Kawai ina son barin aikin ne Abba.”
Proffesor Sulaiman ya girgiza kansa.
“Ba kai ka kai kanka kamfanin ba Khalid don haka ba kaine zaka ce ga lokacin da zaka tafi ba.”
“Na riga na bar kamfanin nan Abba.”
Ya fada kai tsaye cike da son mahaifin nasa ya fahimce shi ya kuma yarda da shi. Amma maimakon hakan sai yace.
“ A matsayina na mahaifinka ni kuma ban yarda da hakan ba.”
Kalaman suka daki kansa da karfin da baiyi zaton zai ji shi a zuciyarsa ba. Amma duk da haka ya hadiye su. Sannan yayi karfin halin dagowa ya kalle shi.
“Abba…. Dan Allah.”
Kuma a yadda ya gani har mahaifin nasa ya bude bakinsa zaiyi wata maganar sai kuma ya fasa. L watakila magiyar da yayi ce ta bashi mamaki.
Don ya dade da sanin cewa magiya ba dabi’arsa bace, tun yana yaro zai nemi hanyar da duk zai iya warware matsalarsa ne ba tare da ya kaskantar da kansa a gaban ko waye ba.
Amma a yadda muryarsa ta fito yanzu a yadda Professor Sulaiman yaji ta a cikin kunnensa kamar wani abu a tattare dashi yana daf da karyewa ne.
Amma duk da haka sai ya kara matsawa don ya tabbatar da abinda yaji din daga gare shi.
“ Dan Allah me?”
Khalid ya juyar da kansa gefe. Yana kallon hasken fitulun harabar gidan dake shigowa ta tagar falon.
“Dan Allah ka karbi uzurina, wallahi na gaji, ba zan iya sake zama a wannan wajen ba.”
“ Ka gaji da yin aiki?”
“A’a” Ya girgiza kansa.
“ Na gaji da responsibility din kamfanin ne.”
“Khalid namiji baya gujewa responsibility a rayuwarsa.”
Ya gyada kansa.
“ Na sani Abba.”
“To me yasa zaka gudu daga abinda ka san watarana dole naka zai zama?”
“Abba ko a nan gaba kamfanin ban ba irin na mutane irina bane, akwai irin mutanen da zasu iya da wajen.”
Ya fada yana cije bakinsa, yana jin kamar sauran maganganun dake bakinsa na shirin fitowa, don haka ba shiri yayi ajiyar zuciya, a hankali yana jin zafin da kirjinsa ke yi masa.
Sannan ya juyo ya sake kallon mahaifin nasa, kuma da idanunsu suka hadu ya tabbata ya fahimta, ya fahimci cewa a karo na farko a rayuwarsa ya gaji, ya gaji kuma ya kai karshe.
Don haka ya sake girgiza kansa sannan yace.
“Abba…” ya sake fadi a hankali. “Dan Allah ka bar ni na tafi.”
Kuma ga mamakinsa kawai sai yace.
“Me zaka yi idan ka tafi?”
Khalid ya hadiye yawu a makogwaronsa… yana jin kamar da iya wadannan kalaman kadai nauyin da yake ji a cikin kansa ya ragu.
Nauyin da ya dade yana dauka.
Nauyin shekaru.
Nauyin yin rayuwar da baya jinta a matsayin tasa.
“So nake in gina rayuwarta akan abinda nake so daga yanzu, lokacin da zan tafi karatu University na zabi course din Real Estate Management ne saboda shine abinda zuciyata take so, I studied it for a reason Abba, shine passion dina shine abinda nake hangowa zan zo inyi a gaba a wancan lokacin.”
Muryarsa na fitowa ne a hankali, cikin fatan mahainfin nasa ya fahimci wannan bangaren nasa da ya dade yana rufewa tsawon shekaru.”
“Ina so in gina wani abu da zan kira nawa ne Abba, wani abu da zan tashi a kullum ina jin dokin yinsa ba don ya zama dole inyi ba.”
Kuma ga mamakinsa sai kawai Proffesor Sulaiman din ya gyada kansa sannanya fadi kalaman da bai taba lissafinsu ba.
“Zan amince da barinka kamfanin nan ne akan sharadi guda daya Khalid, shine ka sake yin aure, nayi maka alkawari duk ranar da kawo mata aka daura muku aure to na lamince maka kaje kayi dukkan abinda kake so!”
A yanzu haka a wannan matakin rayuwar Khalid take, Professor Sulaiman tabbatar masa da cewar a duk ranar da ya kawo wadda ya daura masa aure da ita, to a wannan ranar ne zai karbi uzurinsa na ajiye aiki a kamfaninsa tare kuma da bashi yancin yin dukkan abinda yake do a rayuwarsa. kudin da ya bukata.
Kuma Khalid ya tabbata a yadda ya zura masa ido yana kallonsa yanzu, yana so ne ya ga idan har zai bi umarnin nasa na son yayi aure wannan karon ko kuma uzururrukan da ya saba bashi zasu sa ya hakura da abinda yake so.
Abinda bai sani ba shine duk irin yadda ya kange zuciyarsa daga sha’awar sake yin auren da a baya to wannan katangar daga ya gina ta rushe ne har garinta daga sanda mahaifinsa ya furta hakan. Sai yake ganin auren ba wani abu ba, ba wani abu mai wahala ba idan har zai sami yancin da yake so, don haka ya shiga tunani da neman mafita kala-kala a cikin kansa... Tunda bai san ina zai tunkara da neman a bashi aure ba. Ko ma irin macen da zai zaba a yanzu wadda zai rayuwa tare da ita.
Don haka ganin bashi da wani zabi yasa ya yanke shawarar ya nemo kowacce irin mace kawai zai biyata ta aure shin bisa sharadin cewar bayan auren idan ya sami abinda yake so daga mahaifin nasa bayan wani lokaci gajere sai su nemi dalilin da zasu rabu cikin ruwan sanyi.
Kuma bayan dogon nazari da lissafe- lissafe, ya tabbatar da wannan shawarar har ma ya nemi wani amintacce a cikin mutanen da ya mu’amalanta na ma'aikatan kamfanin, mai suna Sameer wanda ya saba tattauna wasu al'amuransa dashi ya baje masa kolin dukkan manufarsa, kuma baiyi mamaki ba da a lokaci guda Sameer din ya taya shi amincewa da shawarar tare da sake kwadaita masa amfanin samun wannan damar a wajen mahaifin nasa.
Kuma bayan haka ya tabbatar masa da cewar samun wadda zata amince da wannan bukatar ba abu ne mai wuya ba muddin zai bada kudi sosai.
Sai ya bar komai a hannunsa da cewar ya taya shi nemo wadda zata amince da hakan tare kuma da cewar baya so a dauki wani lokaci mai yawa a tsakanin samun matar dama auren gabadaya.
Wanda a yanzu haka akan matakin da yake kenan, matakin da mahaifinsa ke kallonsa ta cikin gilashin idanunsa a kullum yana jiran ji daga gare shi yayin da shi kuma yake jiran ji daga wajen mutumin da yake ganin kamar yana rike da wani bangare na ragamar rayuwarsa ne a yanzu.
**
FANNE
11:30am
"Hadi..."
Muryar Fanne ta fada a hankali cikin wayar dake kare a kunnenta jin yada yake zaro wasu manyan kalamai yana hada Aunty Halimatu dasu.
"Kar ka manta fa ko ba komai yayar mahaifiyata ce."
Ta fada tana jin dacin maganganun nasa a wani bangare na zuciyarta.
Sai ya ja guntun tsaki, sannan yace.
"Yi hakuri, matar ce kin san ba sona take yi ba, shi yasa nima na tsani wani abu da duk ya dangance ta. Kina gani fa yadda tun kafin ki gama idda tasa aka zo aka kwashe duk kayan gidan nan duk don ta tozarta ni."
Ta cije gefen lebbenta.
"To ni dai yanzu na gaya maka ba'a gidanta nake ba ma,ina gidan Aunty Falmata tun da aka gama bikin ban koma ba."
Ta san ya gyada kansa kafin yace.
" Shikenan, kinga nan zan iya zuwa in dauke ki na san ba matsala."
Ta girgiza kanta.
"Nan din ma baka san me zai iya faruwa ba, kawai ka bani kudin mota zan zo in same ka a duk in kake."
Sai ya ja wani tsakin.
"Idan muka sake yin aure Fanne, inaga garin nan zamu bari gabadaya kawai, don bana jin yanuwanki zasu taba barinmu tare.
A karo na farko sai taji ya fadi wani abu da zuciyarta bata kwanta dashi ba, ta san yanuwanta basa sonsa ko kadan, to amma ai basu suke kashe musu aure ba, hasalima idan ba wani abu na dole ba babu wanda take gani a gidanta, matsalar rabuwar aurensu daga shi ne, shi ne yake lalata komai da kansa, to don me kuma zai ce zai dauke ta daga cikin yanuwan nata bakidaya?
Kamar tayi magana sai tayi shiru kawai, sanin ba hakan ne abu mai muhimmanci a yanzu ba.
" Zan turo miki da kudin motar ta access dinki, dan Allah Fanne zuwa nan da sha biyu kizo ki same ni a wajen nan saboda watakila akwai inda zamu je daga nan."
"Wani waje? Ina kenan?"
"Zancen shine dalilin haduwar da zamu yi Fanne, so idan kinzo zakiji komai."
Bata fahimta ba amma sai ta gyada kanta kawai ta amince, don ita kawai tana son ganin nasa ne ma.
"Shikenan Allah ya kaimu."
Ya amsa da Amin sannan ya fadi kalmar da ta saba jinta a bakinsa.
"Nagode."
Kafin ya kashe wayar.
Kuma watakila minti biyu bayan hakan tana cigaba da kwanciya tana sake-sake a ranta sai wayarta ta yi wannan yar guntuwar karar ta alamun shigowar sako.
Ta dauka ta kunna ta a lokaci guda da sakon da yayi baje- baje akan screen din wayar ya shiga idanunta. Alert ne na shogowar kudi har naira dubu hamsin.
Ba shiri ta mike zaune tana sake karanta sunan wanda ya turo kudin. AbdulHadi Muhammad... Shi dinne dai ba idonta ne ke mata gizo ba... Hadi ne ya turo mata kudi har dubu hamsin a matsayin kudin motar zuwa ta sameshi kawai?
Hadin da idan zata lissafa a zamanta dashi kaf kyautar dubu ashirin a dunkule bata jin yafi sau biyar da ta shiga tsakaninsu, dubu goma ce tsakaninta dashi a kodayaushe, sai dai kawai yana bata hakan akai-akai tun kafin aurensu da ma har bayan auren, zai bata dubu goman da cewar tayi hakuri ta san yanayin samunsa, don haka duk sanda ya bata ashirin to ta san akwai wani abu da yake so daga wajen nata ko kuma dai yana son nuna mata bajintarsa ne.
To dadinta shine ita bata taba saka sha'anin kudi a zuciyarta tunda yana iya kokarinsa wajen bata ci da sha mai kyau wanda take bukata, sutura kuwa a wajen yanuwanta ne bata da matsalarsu wannan, su dai da wuya suyi kyautar kudi haka kurum ba tare da mutum ya tambaya ba amma idan akwai abinda zata kira zumunci mai karfi a tsakaninsu to bangaren sutura ne don ko da biki ko babu, kawai sai asamu wani mutum guda da zai ware kudadensa ya siya kayayyaki ya rarraba musu. Su Aunty Halimatun da suke iyayensu ne suka fara yin hakan tun suna yara, duk wacce ta tashi yiwa yaranta kaya sai ta siyo na kowa da kowa a rarraba tunda kudi ba matsalar su bace.
To yanzu da suma yaran suka tashi kuma kowacce tana takama da nauyin aljihun mijinta sai suka dauki wannan dabi'ar ta iyayen nasu, sai dai kawai tana zaune a gida a aiko mata da tsadadadun kaya wani lokacin ma a dinke, tun Hadi na jin haushi har ya hakura ya daina tunda ya san shi ba kayan yake yi mata ba daga sallah sai sallah sai kuma idan za'ayi wani biki a danginsa.
Don haka ita bata taba dorawa kanta kalatar son kudinsa ba, tunda ko kafin ta aure shi ma bata tambayar kowa kudi, sai idan Aunty Halimatu ko Aunty Falmatan sun bushi iska sun tuna da ita ne sai su dunƙulo su bata, kuma abinda aka batan shi zata yi ta cancanawa har asake bata, ba ruwanta da facakar da yayansu keyi da kudi, a cikinsu ta taso amma ko sau daya bai taba manta matsayinta m ba sanin cewa su kudin iyayensu ne suke ci, ita kuma nata iyayen har suka gama rayuwarsu suka koma ga Allah basu da komai.
Ta sake rike wayar a hannunta tana kallon dubu hamsin din da ta doru akan sauran kudinta na cikin bankin, me ya sami Hadi? Ya san nawa kuwa ya turo mata? To ai ko farkon dawowarta gida da ya turo nata kudi sau biyu duka dai dubu goman nan tasa ce, to ko dai yana da wani abun ne daban sabanin kokarin nenan mafitar da suke yi?
***
HADI.
11:50am
Bayan da Hadi ya gama tura mata kudin da yake fatan su kara mata kwarin gwiwar fahimtarsa, sai ya lalubo lambar abokinsa a cikin wayarsa, zuciyarsa cike da hankoro da kuma fatan rashin samun wata tangarda a cikin al'amarin da yake hangowa a idanunsa.
Al'amarin da Sameer din ya kwadaita masa, shi kuma ya zauna ya kawata shi a cikin tunaninsa dama zahirin da yake hangowa a yanzu.
Bugu daya biyu na kiran Sameer din ya dauka.
" Ya dai Hadi kun taho ne?"
Babu wata gaisuwa ko kwana-kwana Sameer din ya tafi kai tsaye ga maganar, sai ya girgiza kansa.
" Nace mata dai wajen sha biyu to na tabbata kafin karfe goma sha biyun zata isa wajen, kuma duk maganar da zamu yi ba zata wuce minti talatin ba."
"To shikenan" Sameer din ya amsa kafin ya cigaba. "Zan karaso kafin É—aya nima insha Allah."
Hadi ya gyada kansa.
" Ba matsala, nagode sosai Sameer, nagode!"
Da haka suka kashe wayar. Hadi yayi ajiyar zuciya sannan ya sauke wayar daga kunnensa, a hannunsa ya cigaba da riketa yayin da kwakwalwarsa ke tsara masa dukkan abinda zai faru a yau din idanunsa kuma yana hangowa.
Komai zai tafi daidai. Komai! Haka ya gayawa kansa saboda ya san wacece Fanne, ya san irin matakin son da take masa, yasan yadda take bin dukkan maganganunsa, ko bata son abu idan yace tayi zata yi, sai dai kawai ya fahimci cewar bata so din ya kyale ta.
Sai dai a yanzu ya tabbata ko da ya fahimci wani abu na rashin amincewa daga gare ta, ba zai taba daga mata kafa ba, dole ne ta bashi hadin kai ya taka wannan TUDU BIYUN da yake hangowa, na sake samunta a cikin rayuwarsa da kuma dafe kuÉ—aÉ—en da yake wa kallon dami a kala.
Allah ya sani yana son Fanne, duk da cewar so ba shine abinda ya fara kwadaitar dashi ita ba, dukiyar ahalinta ce da kuma irin girman da suke dashi a cikin mutane saboda tarayya da irin manyan mutane masu mukamin da suke aure.
To amma bayan ya matso kusa da ita sai ya fahimci gibin dake tare da Fannen daya zaba a cikin sauran Ć´anuwa nata... Ya fahimci ita bata da komai kuma bata da wata madogara mai karfi tunda dangin nata mahaifin ba masu kudi bane, kawai tana zaune ne a cikin daular yanuwan mahaifiyarta.
Gaskiya daya ce, bayan ya fahimci hakan yaso ya janye jikinsa ya fasa auren nata, to amma Fannen ta riga ta kamu da soyayyarsa da yayi nasarar sanyawa a zuciyarta, sannan ko ba komai tana da irin kyawun da yake fata a matarsa, don haka ya cigaba da kasancewa tare da ita har zuwa aurensu, inda kafin nan ya gama fahimtar cewa dangin nata da kwadayin dukiyarsu ta kawoshi basa sonsa ko kadan, don wulakanci ba irin wanda bai gani ba duk don ya rabu da Fannen, shi kuma wannan abin sai ya kara sakawa ya dada dagewa har sai da ya aure ta shima duk don ya baƙanta musu.
Bayan aurensa, abinda yayi tunanin ne dai ya faru na cewar babu wani abu da zai samu daga danginta, don ko kayan daki basu yi mata irin wanda yake tunani ba suka fake da cewar karamin gida ya basu. Don haka a zaman shekaru biyun da suka yi tare duk lokacin da ta bata masa rai, sai ya ajiye duk wani abu da yake ji a kanta ya tattaro tsana da haushin danginta duk da yake ji ya yaɓa mata, idan hakan ya hadu da fushinsa da kuma bakin Fanne da baya mutuwa wajen kokarin kare kanta sai tsautsayin sakin dake faruwa a tsakaninsu ya kasance.
Kuma sai bayan hakan ta faru sannan sai duka su kasance cikin nadama, shi duniyarsa ma gabadaya tsayawa take wajen gane irin rawar da Fannen ke takawa a rayuwarsa, ya fahimci son da yake mata da kuma yadda ta saita abubuwa da yawa a rayuwarsa tun bayan kasancewarsu tare, kwana daya ne kawai zai ji ba zai iya ba, nadamar yin sakin ta kama shi ta kowanne fanni, tun da dama shi ba wani tallafi yake dashi a rayuwarsa ba.
Iyayensa sun rabu tun yana yaro, ance zaman nasu baiyi dadi ba sam don mahaifinsa mutum ne mai baudadden hali da matsawa, don haka tunda mahaifiyar tasa ta samu ta fita sai ta tattara daga shi har mahaifin nasa duk ta tsane su, musamman da ta sake aure ta fara hayayyafa tare da sabon mijin shikenan ta manta da sha'aninsa bakidaya, don ko da ya fara wayo ya fara nemanta a inda take sai ta nuna masa bata so, don haka daga ita har yayanta da yanuwanta ba wani saninsu yayi sosai ba sai lokaci-lokaci kawai yake ganinsu.
Bayan mahaifinsu ya rasu kuma sai gidan nasu gabadaya ya koma kusan kowa zaman kansa yake yi, don yawansu ya fi karfin ace an samu mai daukar dawaininyarsu gabadaya ko da akwai hadin kai a tsakaninsu ma balle babu, wannan shine asalin fara sana'ar buge-bugensa, don ko sakandire bai karasa ba ya fada neman kudi, ba irin sana'ar da kuma kokarin da baiyi ba don ya tara irin kudin da yake mafarki, ciki har da kokarin auren Fanne da ya yi amma har yanzun dai bai karasa inda yake so ba.
Shi yasa bayan wannan sakin na karshe da ya shiga tsakaninsu sai hankalinsa ya tashi mutuka na ganin yana shirin yi biyu babu a rayuwar tasa bakidaya, na rasa Fannen da kuma yadda harkar samunsa ma bakiÉ—aya ke shirin tsayawa. Don haka Allah ya sani ya shiga cikin damuwa fiye da ita Fannen da a kullum ke nuna masa nata tashin hankalin musamman da yaji irin murnar da tace yanuwanta suna yi tare da aibata shi, sai zuciyarsa ta dada dugunzuma ya shiga neman duk hanyar da zaiyi don ya mayar da ita.
A haka kwatsam, wani abokinsa Sameer yazo masa da wani tagomashin labarin da ya kira TUDU BIYU...!
Tiryan- tiryan kuma daki- daki Sameer ya shaida masa yadda wani abokin aikinsa a kamfanin da yake aiki yake neman macen da zai aura na wani dan gajeran lokaci kawai don ya sami wasu kudade daga mahaifinsa da ya kafa masa dokar yin auren tukunna, kuma watakila babu inda Sameer din ya bata wajen shaida masa dukkan labarin mutumin da kuma dalilansa duk don ya kara fahimtar manufar tasa.
" Wannan duk labarin a boye yake Hadi, zan iya rantse maka idan ba ni kadai ya shaidawa wannan manufar tasa ba to ba zamu wuce mu biyu ba, don ko yanuwansa baya so su san komai, yafi son dukkan wannan abinda ya tsara ya tafi daidai ba tare da wata matsala ba, ya zabi nima ya gayamin ne saboda in taya shi neman macen da zata amince da wannan yarjejeniyar don shi ba mai shiga jama'a bane,
Ya tabbatar min idan na samo wadda ta amince, zai bata kudade masu nauyi Hadi, sannan dan gajeran lokaci ne kawai auren zai kasance, da ya sami abinda yake bukata zai san hanyar da zai nemi dalili mai karfi wanda zai rabu da ita ba tare da wata tashin- tashina ba.
Kuma bayan ya gama shaida min ka san dai ina da kanne mata amma wallahi babu wanda ya fado a raina sai kai da matarka, nace ga hanyar da zaku sake kasancewa tare cikin sauki sannan har ma ku dafe wasu kudade hankalinku a kwance. Don wannan matar taka tsaf zata saje a irin matan da zai aura ba tare da ayar tambaya ba."
A cikin kan Hadi gani yake ai iya wadannan kalaman ma sun isa su saka ya fahimci labarin gabadaya, amma bayan ya yi masa tambayar dake cikin bakinsa ta cewar nawa yake ganin zai bayar kuma Sameer din ya gyara zama yace.
" Bamu gama tattauna wannan ba amma na tabbata ba zai bada wani abu da zaiyi kasa da miliyan biyar ba, don kudin da zai karba a wajen mahaifinsa da yawa kuma auren ne zai sa ya same su."
Sai yaji baya bukatar duk wani sauran bayani kuma, sai yaji ya gane komai. To me yake nema dama? Hanyar da zai sake samun Fanne a matsayin matarsa, to ga ta tazo kuma har ma da tagomashin kudin daya tabbata kusan duka hannunsa zasu zo don ya kwana da sanin halin Fannen, bayan sha'anin kudi da bai dame ta ba, tsaf zata iya daukan kudin gabadaya ta bashi saboda son da take masa… kudin da zai maida su jarin wani abin su zame masa tagomashin arziki.
Don haka babu wani bata lokaci balle har ya bawa Sameer din damar da zaiyi tunanin tuntubar wani bayan shi da zancen, ya tabbatar masa da amincewarsa dama yakinin cewa babu wata matsala da za'a samu daga Fannen, da ya gaya mata shikenan ya tabbatar zata amince don itama neman hanyar da aurensu zai sake dawowa take ido rufe.
Don haka a yau din da ya shirya gaya mata, ya bawa Sameer din dake jiransa tabbacin zuwa ya same su don ya kai Fannen wajen shugaban nasa a sami amincewar sa game da ita.
Ya san tabbas son da take masa ba zai sa taki amincewa dashi ba, kawai abu daya yake tsoro wajen samun matsala da ita, wannan ra'ayin nata, don ko yaya ta kawo wani cikas, ba lallai ne su cigaba da samun wannan damar a wajen Sameer din ba, zai iya mantawa dasu ya nemo wanda baza su bashi matsala ba.
Ya kalli agogon dake saman dakin da yake zaune, karfe goma sha daya saura, sai ya mike da niyyar tashi ya shirya don tabbas a halayyar cika lokaci irin na Fanne, ya tabatta sha biyun da ya fada mata baza ta cika ba zata karasa wajen.
***
12:13pm.
Wani irin tari ne ya taho a lokaci guda ya turnike makogwaron Fanne, ta shiga yinsa babu kakkautawa, bayan hannunta dafe da bakinta yayin da ta sunkuyar da kai.
Hadi dake zaune a tsallaken teburin yayi saurin miko mata robar ruwan dake ajiye bayan ya bude murfin robar.
"Sannu.... Sannu, karbi ruwan ki sha."
Bata karba ba, don ta san matsalarta ba ta ruwan bace, wani abu kawai ta tattaro a bakinta tayi kokarin tura shi ya hadiye tarin gabadaya sannan tayi ajiyar zuciya mai nauyi, kuma da ta dago idanunta ta kalle shi, ta san sun kaÉ—a daga tasirin kalamansa da suka haddasa mata tarin. Mamaki fal zane a fuskarta tace.
"Wai auren kisan wuta kake nufi nayi Hadi?"
A lokaci guda ya girgiza kansa.
" Ko kadan. Ta yaya zaki kira wannan abin da auren kisan wuta Fanne? Na gaya miki mutumin nan fa manufarsa ta aurenki daban ce, kuma ma fa biyanki zaiyi, biyanki zaiyi makudan kudaden da ba'a koina zaki same su cikin kankanin lokaci haka ba."
Wani abu ya turnike wuyanta ba shiri, taji kamar ta mika hannu ta riko wuyan rigarsa kafin tace.
"Kaima ka san kudi ba matsalata bace Hadi,ka san da kudi nake bi a rayuwar nan ko sanina ba zaka taba yi ba balle har aure ya hada mu."
Idan ma yaji zafin naganganunta to bai nuna ba, daga hannayensa yayi duka biyu a iska alamun sallamawa sannan yace.
"Naji, naji, kar mu ja da maganar nan dan Allah... So nake kawai ki fahimce ni,ki fahimci babu ta yadda za'ayi mu sake kasancewa tare a duniyar nan dole sai ance kin sake auren wani, ni kaina ba son hakan nake yi ba wallahi, na fi ki tsanar wannan hanyar amma babu yadda zamu yi mu kauce mata. Don haka dan Allah ki fahimce ni Fanne kamar yadda kika yi min alkawari zaki bani hadin kai.
Fanne ta girgiza kanta, ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kasa, ta sake girgiza kan nata sannan wannan karon muryar tata ta fito.
"Hadi wai ka manta karatu ne ko bama ka sani bane gabadaya? Idan har naje nayi aure da niyyar sake dawowa gare ka fa, to da auren dama dawowar da zanyi wajenka duka haramun ne balle har wani ya halatta wani."
Sai ya cije lebbensa, kamar yana kokarin hana fushin dake nunawa a fuskarsa tasowa, sannan ya gyada kansa.
"Ni kike cewa banje makaranta ba Fanne? To bari kiji kece baki san karatun dake kan auren kisan wuta ba, irin wannan auren yana zama haramun ne kawai idan har yarjejeniya tabbatar da saki ta shigo a tsakanin ni da wani namijin da nake so ya aure ki. Ace munyi yarjejeniya dashi cewar dole zai sake ki saboda na dawo na aure ki.
Amma ki kalli wannan sigar auren, ban san mutumin nan ba, shima bai sanmu bai san labarinmu ba, bai san abinda muke so ba, hasalima manufar da zai sa ya aure ki daban ce, kuma ba zai sake ki ba sai yaga dama, sai a lokacin da yake so, kawai muna fata ne da saka ran cewa zai sake kin sai mu maida auren mu..."
Yayi shiru yana cigaba da kallon fuskarta, yadda yanayin fuskar tata ke canjawa zuwa yarda da fahimtarsa a lokaci guda, sai muryarsa ta karasa fitowa cike da kwarin gwiwar cin galabar tunanin nata.
"Babu inda zaki kai wannan sigar auren a duniya ayi masa kallon auren kisan wuta Fanne."
Kuma bayan yayi shiru, sai ta dauki tsawon lokaci tana kare masa kallo yayin da tunani mai yawa ke giftawa a cikin kanta, tana debewa da tarawar duka abubuwan da zasu iya yiwuwa dama wanda baza su yiwu ba a cikin kanta. Zuwa can tayi ajiyar zuciya sannan ta girgiza kanta.
"Idan bai sake ni ba kuma ba fa? Idan bai ga damar sakin nawa ba fa?"
Ta furta hakan tana kallonsa, kuma ajiyar zuciyar da yayi, ta tabbata ta godiyar fahimtarsa da tayi ne, ya kai hannu ya shafo kansa har baya kafin yace.
"Zai sake ki Fanne, dole zai rabu dake don babu wani dalili da zai sa ya cigaba da zama dake bayan ya sami abinda yake so."
Tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta koma da baya a cikin kujerarta kawai ta dago da hannayenta duka biyu ta rufe fuskarta dasu, kamar a cikin duhun da ta yiwa fuskar tata ne zata samo tabbacin amincewa wannan hargitsatsen labarin mai kama da fim na Hadi.
Hadi ya kalli dogwayen yatsunta da ta rufe fuskar dasu, kunshin jan lallen da ya tabbata na bikin da suka yi ne yana zane dal akan farar fatarta, hannun yayi masa kyau tare da kunshin yayin da a lokaci guda ya tuna da lokutan da idan tayi kunshin, zata dinga binsa dasu tana gaya masa tayi lalle don idan ba fadar tayi ba, ko ya gani baya nuna alamar cewa ya gani din, kuma zaice mata yayi kyau ne kawai idan yayi mutunci shine zai dan rike hannun ya kalla.
Amma a yanzu ji yayi kamar ya kamo duka hannayen nata gabadaya ya hade su a cikin nasa sannan ya dinga murza su a hankali daya bayan daya, Me yasa ne mutum ba ya sanin wata ni'imar da yake da ita sai a lokacin da ya rasa ta?
A daidai lokacin mai kawo abincin Restaurant din da suke zaune ta katse tunaninsa, ta karaso É—auke da abincin da yayi musu oda, don haka ya katse tunanin nasa lokaci da ta shiga sauke kwanukan abincin akan teburin yayin da Fannen ma ta bude fuskarta tana gyara zamanta.
Lokacin daya mika hannu don kokarin taya budurwar sauke kwanukan, sai akayi rashin sa'a lokacin da hannunsa ya kai kan wani karamin kwano itama ta kai nata hannun.
"Sorry..!" Ya fada da sauri yana janye hannunsa.
Idan ma matashiyar taji shi to bata kula ba ta karasa sauke kayan ta juya ta basu waje... Kuma a lokacin da ya juyo da idanunsa kan Fanne da niyyar yin magana sai ya tarar da nata idanun a tsaitsaye tana kallonsa.
"Me yasa baza ka bari tayi aikinta ba sai ka taya ta?"
Ta furta tana kallonsa, ba shiri yaji dariya ta subuce masa kafin ya hade duka tafukan hannayensa biyu.
"Allah ya huci zuciyarki ... Kina so na kina kaiwa kasuwa."
Bata ce komai ba kawai sai ta dauke kanta gefe tana kallon can waje ta cikin fararen gilasan da aka kawata Restaurant din dasu.
" To bismillah, mu ci abincin."
Farfesun kayan ciki ne da kuma soyayyiyar doya mai kwai, abincin da ya san tana so babu shakka, amma haka kurum taji babu cin abincin kwata-kwata a ranta, don maganganun da suka yi sun disashe duk wani dokin da ta taho dashi. Don haka ta girgiza kanta.
"Ni gida zan tafi."
Ba shiri Hadi ya saki cokalin da ya rike a hannunsa, kuma watakila bai san lokacin da yace.
"Gida? Wane irin gida kuma Fanne? Yau fa zaki hadu da mutumin. Yanzun nan Sameer zaizo zaku tafi tare wajensa, saboda lokaci yana kurewa kuma sauri suke yi."
Gabadaya sai ta juyo ta kalle shi, kuma ga mamakinsa dariya ta fara yi kafin tace.
" Yanzu? Yanzu fa kace Hadi? Yaushe ka taba ganin anyi al'amari yanzu-yanzu? Ka gama bani labarin yanzu kuma banyi shawara ba kawai sai kuma kace in tafi ince na amince? Wai me ka maida aure ne?”
Ta girgiza kanta.
"Ba inda zanje yanzu, ka bani isashshen lokaci nayi shawara tukunna."
Tana fadin haka ta damki jakarta dake ajiye a saman teburin don ta tabbatar masa da gaske take.
Kuma a cikin wannan damkar da tayi. Hadi ya hango yadda dukkan tsarinsa ke shirin murmushewa ya bi iska, don yaushe suke da isashshen lokacin da har Fanne zata gama shawara kuma damar ba zata kubuce musu ba?