Free chapter · Read without an account

BOOK ONE CHAPTER 15

by Hindatu Auwal · ƘYAURE KARIYAR GIDA

*USTAZ RAYYAN*


Zaune yake a falo yana rage wasu ayyuka kasan cewar yau weakend babu school sedai tahfiz nanda la'asar.




Aikin kawai ya keyi, wani sashi na zuciyarsa na kewar Aliya da batanan, sun tafi wurin Tom print na WAEC a babur dinsa.




Gabda azuhur sai ga sallamar Aliya. Murya acukule, fuskarta tai jaa alamar ɓacin rai. Ya kalleta zuciyar sa na mamakin ganinta a irin wannan yanayin da bai taɓa ganin taba.





A gefen sa ta zauna tana fadin"sannu da gida."


"Yawwa Aliya...."


Ya amsa yana tsiyaya mata raguwar ruwan gorar da yasha a cup yabata.



Amsa tai tana furta "Nagode" amemakon tasha sai ta kama magana"Ustaz don Allah so nikeyi kai min wani alfarma guda daya."



"Menene Liya ta."



Ya tambaya dasauri.



"Kasamu lokaci muje aimin gwajin ciki...."



Idanu ya waro zuciyar sa na bugawa ganin babu alamun wasa a fuskar ta.


Murya na rawa ya tambaye ta"meya faru"



"Screening muka je shine pha akaita ma masu aure da ciki favour wai saboda sunada mazaje agida kada su jirasu, Nima nai magana amma sai suka ƙaryatani sukace wai banada aure, wata ma tace" bansan ainihin ma'anar aureba balle asami ciki. Da harzan bata amsa sai nai shiru kada na fallasa sirrin auren mu, amma nai alƙawarin sai na nuna musu Ni matar aurece nan da exam yazo, zasu ganni da cikina Ni ma."




Unexpected yaji dariya ya ƙwace masa, dariyarda ta fito tun daga ƙasan zuciyar sa ba yaƙe ba, dariyar da yamanta rabon da yai kalansa.





Aliya dake zaune a ƙule sai hawaye suka gangaro mata. "Yanzu Ustaz dariya kake min?...bayan kasan dagaske inada kai matsayin mijina, kuma na baka kaina, ayanzu ma babu laifi idan aka ganni da ciki."




Acikin ƙwayannin idanuwan ta yaga yadda take magana da iya gaskiyar ta. Sai ya daurema dariyarsa ya kalleta.




"Gayamin ta yaya kika bani kanki."




"Ta hanyar yarje maka ka kai hannunka jikina, yadda nake keɓewa da kai and aima kasani tunda kai ka gaya mana a islamiyya bai halasta ba balagagggiya ta bari wani da ba muharramin taba ya rinƙa kai hannu jikinta.!!!!


Taja numfashin kukan da take yi taci gaba"a ranar da nafara period Ummi ta gaya min indai namiji yakai hannunsa jikina to zan sami ciki. Kaga yanzu ƙila na sami ciki sanine ba muyi ba."



Kai yajin jina. Ya fahimci komai yanzu. Sedai shi bai ga abin kuka a maganar nan ba. Bayan yasan tanada hakuri da kawaici, bai kamata wannan ƙaramin abin ya hassalata tai ta wannan kukan tana cin magani ba.




Wani abune ya haska acikin kanshi. Ya kalli fuskar ta, taƙara kyau sosai, pieces-pieces ɗin moment din da Aliya take cikin irin wannan yanayin yake haɗawa tun kafin ya aureta. Sign din period din Aliya shine koke-koke akan abinda bai kai yakawo ba.




Ya sauke numfashi. Ya shiga rarrashin ta ahankali har tai shiru. "Kinga Liya ta kishiru abinki. Banaso kici gaba da kuka kanki yai ciwo, yaje cikin da ƙila ba musan da shiba yasamu matsala. Kafin dai ku soma exam zan san abinyi okay."



Kai ta gyada mai. Ya jawo ta jikinshi. Ya cire mata hijjabin ya kwantar da ita akan cinyarsa yakama shafa kanta.



Dayike agajiye take. Ga kuka. Ga sign na zuwan baƙonta sai kawai tai luph ta kwanta bacci mai dadi ya ɗauke ta.



Kiraye kirayen sallahn azuhur yasan yashi kwantar da kanta ajikin pillow din kujera yamike yaje yadauro alwallah yatafi masallaci.


      ___*___

Da la'asar hadari ya haɗu. Jikinta har tsuma yake yi ruwa ya sauko. Ta miƙe taje ta ɗauko bucket ɗin robanta zata fita.



"Ke! Ina zuwa?"



"Ruwa zan taro mana."



"Ki barshi karki zazzaɓi."



"No zan taro"


Kafin ya buɗe baki ya sake magana har ta fice. Ya kurama ƙofa ido don ganin Aliya ya shigo amma shiru ka keji. Sauƙin tama ruwan babu hayaniya. Babu tsawa. Yamike ya leƙa ya gani ko lafiya sai ya hangeta tsaye a tsakiyar wurin tana rawa.





"Aliya...."



Ya kirata da ƙarfi. Manyan idanunsa na harar ta.


Dariya tai mai tsari daya ƙara mata kyau. Ya zaro mata idanu. Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya.



Bayida zaɓin da yafi yasanya ƙafarsa acikin ruwan da yakeda tabbacin tunda ya dakesa to sai yai zazzaɓi amma gwara shi ya kwanta da Aliya ta kwanta ciwo.




Sedai me yana zuwa idanunsa suka sauka akan Aliya sai yai tsaye gabda Aliya. Kusa sosai...Amma ba kusa da jiki kawai ba—kamar dai akwai wani abu da ya fi ƙarfin space din da ke tsakaninsu.

Aliya ta ɗago idanunta a hankali. Idanunsu suka haɗu. Sai komai ya yi shiru.

Ƙaran ruwan saman dake shiga kunnuwanta ya dakata. Hatta sanyin ruwan da yake ratsawa cikin jikinta sai ya ɗauke.


Abin da kawai take gani shi ne idanun Rayyan.

Idanuwan da suka dade suna ɓoye abin da zuciyarsa ta kasa ɓoyewa.

Rayyan ma bai motsa ba. Ya kalli fuskarta, sai zuciyarsa ta buga da wani irin ƙarfi.

Kamar zuciyarsa tana son tserewa daga ƙirjinsa ta faɗi a gabanta.

Aliya ta sauke idanunta na ƴan daƙiƙu, amma ta sake ɗagowa.

A wannan karon, babu tsoro. Babu tambaya.
Kawai akwai wani irin fahimta da ta wuce magana.

Ta haɗiye yawu. Muryanta can ƙasan throat ta kira sunan sa.

"Ustaz..."

Ta kira sunansa da murya mai rauni. Amma bai amsa ba.

Sai dai ya ci gaba da kallonta. Kamar yana son haddace wannan fuskar a zuciyarsa.

Kamar yana tsoron wata rana rayuwa ta raba su, ya rasa damar sake kallon idanun nan.

Aliya ta ji wani ɗumi a tsakiyar ƙirjinta duk da sanyin ruwan saman.

Ta yi murmushi a hankali tace"Me yasa kake kallana haka?"

Rayyan ya ɗan sunkuyar da kansa. Ya furta "Nothing."

Ta ɗan ɗaga gira.

"Nothing?"

Ya kalle ta kai tsaye.

"Sometimes... words are not enough."

Zuciyar Aliya ta buga da ƙarfi. Ta kasa cewa komai.


Rayyan ya ɗan matsa kusa da ita. Ba tare da ya taɓa ta ba.

Kawai kasancewarsa kusa da ita ya isa ya sa Aliya ta ji wani irin aminci da ba za ta iya bayyana shi ba.

Wani irin tsawa akayi da ya sanya Aliya firgita. Ta faɗa ƙirjin Ustaz tana ƙanƙameshi har yana jin yanda jikinta ke rawa yana tsuma.




Zuciyar sa ta doka da wani irin sabon abu dako jinsa baya sonyi balle imagine dinsa atareda Aliya.



Jikinshi na tsuma ya sa hannu ya ɗauketa kamar Baby ya shige da ita daki.

*

A tsakiyar falo yai tsaye da ita a hannunsa yana kallon cikin ƙwayannin idanuwan ta, yalwataccen gashin kanta da ya jiƙe na yararin ruwa, abinda keta kaiwa da komowa a ƙirjinsa yake ƙoƙarin haɗiye wa, yawu ce ta makogwaronsa daya bushe ƙamas kamar wanda annoban gobara yakama.



He doesn't know... feelings dinsa sukafi ƙarfinsa. Ya ran ƙwafo kansa gareta, idanunshi maƙale da nata yai shooting bakinsu wuri ɗaya. Za buran da Aliya tayi ya hade ƙirjinshi da nata har yana jin tudun laushin nata ƙirjin anasa.



Hot kiss yake mata a hankali, idanuwansa a bude yana kallon cikin idanunta.



Dagashi har ita jikinsu tsuma yake, ƙafafuwan shi dake tsaye suka gaza, sai ya dan ganata da doguwar kujeran dake gaban su yana binta ye mata rumfa da sauya salon abinda yake mata.


Wasu hawaye ne suka shiga saukowa daga idanuwan Aliya. Tsoro, firgici da sabon al'amarin da bata taɓa riska ba ya sanya zuciyar ta bugawa, ƙirjinta na kaiwa da komowa sai ya zamana kamar tana bashi support ne na enjoying abinda yake yi.




Jin hannun shi tayi yana yawo ata bayanta da wani salo daya sanya ta zabura tana sakin kuka ahankali.



Ustaz yatsaya cak!yana kallon cikin ƙwayannin idanunta dake fitar da ruwan hawaye.



Numfashi mai nauyi yaja. Ya miƙe, kansa a dafe da hannunsa. Ya soma tafiya yana haɗa hanya yashige ɗakin sa.



Aliya ta runtse idanunta. Jikinta ko ina rawa yake yi.

"wai dama haka Ustaz yake ji aduk sanda nai mai kiss ko na rungume shi?"

Tambayar ta fito daga wani wuri acikin zuciyar ta.


Amemakon ta amsa ma kanta tambayar sai ta mike, ta shige bedroom ɗinta, a bathroom ta ja burki ta cire kayan jikinta ta zubesu a roba. 



Jikinta ɗaure da towel ta fito bayan ta ɗauro alwallah saboda kiran sallahn magrib da taji.



As usual ta sanya kayan baccin ta. Ta sanya hijjab ta tada sallah. Bayan ta idar tai zaune tana karanta alqur'ani har aka kira sallahn ishai tayi.



Rashin jin motsin Ustaz tun ɗazu yasan yata miƙewa, ga kunya da nauyin abinda ya faru ɗazu a tsakanin su, duk ta danne tai knocking ɗakin sa.



Shiru ba'a amsaba. A karo na biyu tai sallama shima shiru ba'a amsa ba sedai kunnuwanta na mata gizo da jin sautin muryansa yana kiran sunanta a hankali.



Imma dagaske ne ko bada gaske bane sai ta murɗa handle ɗin ƙofan ta shiga da sallaman ta. 



Hangosa da tayi lulluɓe cikin blanket yana rawan sanyi yasan yata ƙarisawa inda yake dasauri ta haye gadon tana kai hannunta saman goshin sa daye zafi raw na zazzaɓi.



Bai bude idanunshi dake lumshe ba duk da yayi feeling ɗumin hannunta da yajishi har cikin kasusuwan jikin shi.


Arude ta ɗaga blanket din don ganin halinda yake ciki. Shi kam yai amfani da wannan daman ya fizgota ta kwanto jikinshi sosai. Ya ɗora kansa agefen wuyanta yana harɗe dogayen ƙafafuwansa da suke naked dana Aliya.



Hannunsa ya kai kan hijjab ɗinta yana ƙoƙarin cirewa ta damƙe tana girgiza kai da raguwan ƙarfin halin daye mata saura bai gushe ba.



"Please leave me Noor ba abinda zan miki. Temperature din jikinki kawai na keso mui musaye."



Yafaɗi daƙyar yana sauke mata iskan bakinshi dake fitowa zafin gaske.



Ance robot ba tada feelings, yau dai ko itace Ustaz ya ritsa akan gadon nan sai taji abinda Aliya keji.



Batada ƙarfin hanasa dan tayi losing effort dinta akansa tun sanda ya bude bakinsa.



Tana jinsa ya cire hijab din. Ya rungumota jikinsa da kyau yana kai hannunsa cikin riganta ta baya yana murzawa yayinda yake goga sajensa a gefen wuyanta, ƙirjinshi dake hade da nata na gamewa sosai.



Aliya tai laƙwass wani abu data kasa bashi suna acikin kanta na taso mata.



Lokaci ya cigaba da tafiya ba tareda sanin yanda akayi bacci ya ɗauke taba.


Ustaz yagyara mata kwanciya sosai ajikinsa yana feeling moment din.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol